Showing 114001 words to 117000 words out of 122108 words

Chapter 39 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

425

shayar da shi mamaki, ta saka shi farin ciki a lokacin da ya nema ya nema ya nema ya rasa, kai Allah amin Allah ya dawamar da shi da Raudansa , Rauda Kamshi santsi, Rauda dandano🙈 haka santin Sire ya kasance inda Rauda ta kuma jin jiki domin wannan karonma komai da zafi zafi yake zuwa, 😟




Dan karamin Hauka ne take zuba masu a asibiti tunda ta buda idannuwanta ta ga mahaifiyarta mahaifinta a zazaune sun yi zugum
Tambayar da ta fara jefo masu itace" ina Elhaj kuwa

Wani sakaran kallo uwar ta watsa mata kafin ta ce" yana inda kika aike shi AISHA Humaira! Yau dai kin samu abinda kike neme, yau dai kin yi kokari wasan naki yayi armashi.....kin kai shi bango Humaira sai ki warke a salame mu mu fice gida mu je ki rungumi ubanda zaki runguma

Da kallon Rashin fahimta take bin mamanta da shi,
Kafin ta juya wajen mahaifinta,
Kai ya kawar shima haushinta yake ji aunun, ya kali matarsa ya ce" ki bari mana har mu je gida

Ra kallo shi ta ce" ka bar ni na haifar da bakin ciki Elhaj, ita a nan har ji take ta shanye shi sai yanda ta yi da shi ko me? Yarinyar nan kwakwaluwar kifi ne da ita, banza ce wawuya ce bata san ruwan dake wankarta ba

Mama, pls ki tsaya, me kike nufi da magangannunki ne? Ni na kasa fahimta
Humaira ta fada tana kokarin tashi daga koncen tana faman janye abin karin ruwan da aka saka mata

Mama ta ce kai tsaye" ina nufin hankalinki ya konta, ya koroki gida sakamakon rashin hankalin da kike toya masa, ya gaji domin ba tare aka halice ku ba, ya gaji da tabara da hauka dan kuwa ba haihuwarsa kikai ba, yace ki je gidanku

Wani ihu humaira ta saka ta cire karin ruwan ta dora hannayenta saman kanta, a fili ta furta" na shiga ukuna na lalace, kaji sharin kishiya...du zaman nan da mukai da Elhaj bai fadi haka ba sai yanzu da ya yi aure? Ni Elhaj ya kora? Yana nufin ya sakeni ko me? Walahi bai isa ba walahi sai ya mayar da ni dakina

Abanta ne ya matsa ya daga hannu ya bige bakinta ya ce" kul ki yi min shiru sakarya, ke yanzu har kina da kunya da bakin magana? To tashi tunda na ga halama lafitarki kalau sangarta ce ta masu kudi, fice mu je gidan banza ki ci kaniyarki......mu je ki tarar da dakin da babu ac ba luntsumemiyar shinfida
Ba cima irin na kasar waje, ba motoci... rayuwa zaki irin ta kowa ba wai ta matar Elhaj Sudais ba, Humaira dole ki yi aikin gida kuma ki ajiye shafe shafe koda zaki yi hauka ne

Kamar sakara baki bude take kallon yanda abanta ke hankadata, ta bani kennan dai Sudais ya fadi komai? Ya salam

Du laifinsa da bai yi mata dukan mutuwa har ta sare da duniya ba Elhaj, na sha fada mata ba ita ba mu kanmu da Allah muka dogara ya bamu bango Mijinta, aman maimakum ko dan alkhairin da yake yi mana a rayuwa idan bata dauki darajar kalmar miji ba ai ta sasauta wani haukan, ke bakya jin kunyar mahaifiyarsa? Kina dai gani tun mutuncin anguwa daya da muke kawance da ita, Allah ya daukaka yaronta ta jajirce sai da ya aure ki, ke kanki Humaira kin san ba kalarsa bace, kunya da biyaya ya yiwa iyayensa aman ke gaki katuwar banza kin kasa yi mana biyaya, ba komai na ga halamar *Raina inda kike ki kai,* sai mu je gidan ki ci abinda muke ci, kuma indai ni na haife ki ni Baraka daga yau na raba ki da du wata kawa, idan kika yarda kika kuma biyewa wata kaya gaki ga duniyar nan

Da sauri ta kali mamanta, aa , wai ba wanda zai saurareta ne? Sai gasata suke ba wanda zai rabeta ta ji sanyi ne? Mijinta, abin alfaharinta, abin takamarta, tinkahonta karyarta du shi ne, gashi du uban dukiyar sa yake bata kawaye na zugata tana siyarwa a ci banza a ci wofi a sayi man shafe shafe masu tsadar balaki a saka atach na karshen kudi a yi mak up na hauka a baza turare du dan a nunawa kawa an fita, yau bata da komai idan Sudais ya saketa ya zatai?
Kuka ta fashe da shi lokacin da suka shiga yar karamar motar Aba ya tayar ya halba bakin titi
Tana kuka ta ce" haba abanna , ku tausaya min mana, kun ga fa bari na yi

Aba bai san lokacin da ya ce" aa ubanki ki kai Humaira, mutuniyar banza ai ke kin yi sa.a da bai fito da hanjin cikin gaba daya kowa ya huta ba, sai me dan kin yi bari? Shima dan Allah ne ya rufa masa asiri bai taka kasa a matsayin danki kina aikata haka ba, ke bara ki ji Allah ya kaimu gidan nan lafiya zan ga ni da ke wa ya fi iya tsageranci idan baki tuba kin natsu dan Allah ba zaki tuba dan ubanki ne!

Gumm ta yi tana kifkifta ido, ita bata da waya a hannunta da ta kiraye shi ko.ina yake ta je ta bashi hakuri, yanzu haka zata shiga gidansu ma.aikata da take yiwa dagin kai ita matar elhaj su ganta a haka? Ina ba zai yiwu ba ko ka sake ni sai ka yi hakuri mun yi zaman mu


Wanki take tana ta zufa, kayan abansu ne mama ta fitar irin dangin jalabiyoyi , kaya ne masu shegen kyau domin Aba kam an shiga layin Elhazawa Elhaj Sudais ya tatakura ya wanke sirikan nasa Aba ya sha jalabiyoyi na manyan mutane ya nada hirami mama kuwa ta daura atampa ta gani ta fada ta matan manyan da dinkunnan manyan daraja, ta danyace abinta sai shagali take mata a gidan malan Ahmad🤣

Mama na hira Aisha ne da iya karfinta, da ma.aikata da komai aman sai su sha zamansu abinsu ko su je su yo wani aikin du yan aikace aikace Aisha ne ke yi har malan kan tausaya mata wani lokacin sai mama ta murje idannuwanta ta ce" lokacin da Raudana na yi ita kadai ai itama mutun ce, ni ban ga anfanninta ba idan ba zata aikatu ba haka kawai katuwar budurwa sai dai mu ciyar da ita? Ita ba mijin ta fitar ba ita ba karatun ba ta tsayar da komai? Ai gwara aikatau din
Sai malan yayi murmushi kawai ya fice abinsa domin ya tabata Mariama na haka ne dan ta ladaftar da yar tata

Aisha na tsaka da shanya aka yi salama

Dago kanta ta yi ta sauke kan wata mata da yaro a hannunta da kuma goyo

Matar ta duka har kasa ta ce" baiwar Allah aikatau muke nema da yan yaranna mun nema mun nema mun rasa dalilin datin dake jikin mu, ku taimaka ku bamu konce ko ku dauke mu aiki komai kankantar biyan Allah ya saka masa albarka

Aisha ta ji wani hawaye ya zubo mata tana kallon matar, ita daya ce dai a tsakar gidan dan haka ta matsa kusa da matar ta ce" baiwar ke kuwa ina gidanki? Ina mahaifin yayanki?

Matar ta ki yarda ta dago da kanta, ta ce" mahaifinsu yana kauye abinsa, ni kuwa na ga ba zan iya ba kulun cin tuwon bakar dawa da tsanwar miya shine na dauko kananiwan yayana muka shigo birni dan samun aikatau muma mu murje ba zan iya zaman talauci mai muni irin haka ba

Aisha ta sauke ajiyar zuciya tana kallonta, can ta nisa ta ce" ba zan ga laifinki ba, domin ban san wace irin rayuwa kike yi a gidanki ba, rokona da ke shine idan har kin ga da hali ki waiwayi gidanki yar uwata domin duniyar nan girma ne da ita abubuwan cikinta nauyi ne da su, wani idan ka kalla wanin ya fi karfin kallon ka, ki yi kokari ki yi tunani domin zama lafiya ya fi zama dan sarki,

Bara na je wajen maman mu idan da hali ta taimaka maki kin ji?

Aisha ta fada tana juyawa da niyar shigewa baban falon sai ta dan waigo

Idannuwanta ne suka sauka a fuskar matar, gabanta ya yanke ya fadi, ba zata manta fuskarta ba ita ce
Wani murmushi matar ta sakarwa Aisha kafin take juyawa ta fice fitt da wani irin sauri

Hannaye biyu Aisha ta dora a ka nan ta silale sumamiya.....m





💓



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




6⃣3⃣





Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une
Shine abinda suke ta maimaitawa bayan malamin da yayi ta yiwa Aisha Rukiya kwana da kwanaki kafin ake samu ta yi magana, da sai dai zuru sai kuma ta yi ta ihu tana nuna waje tana gatannan ta dawo itace itace

Mama ta yi saurin matsawa kusan malan, murya kasa kasa ta ce" walahi ina tune da ranar, ta shigo tare da yayanta kwaya biyu ta nemi da mu taimaka mata aman sai Aisha ta wulakantata ta kore ta, bayan ta fita ne Rauda ta kwashi wasu suturunta ta bi matar ni dai ban san ya sukai da ita ba da ta dawo ta jima kagin take cewa mama abin mamaki matar nan sunana ta kira , ni kuwa nace da ita to ai ba mamaki domin tana fita a waje ma sai ta ji sunanki da haka muka ci gaba da shagulgulan gabanmu

Da kyar aka samu ta barta bayan ta maimaita ba wani nisa zatai ba domin irin masu halayan Aisha take nema dan ita jininsu ne abincinta

Daga wannan ranar Aisha ta kuma dawowa wata shiru shiru da ita sosai, bata yawan magana, sannan abu kadan sai ka ga tana hawaye ko ta tsorata,
Hakan ya kara tayarwa da mama hankali ta shiga adu.a tana nemawa Aisha sauki wajen Allah

Tsohon Saurayin Aisha dai Fahad ne ya dawo yake nacin zuwa wajenta, wani lokacin mama ta fatataketa ta fita wani lokacin ta fashewa mama da kuka wai ita walahi tsoro take ji yana da mata fa, sam ba dan rainin abin hannunsa ba sai dan tsoron matarsa
Mama takan ji tausayinta a ranta aman a fili ta nuna ai mai matan shine daidai ita me take tunani? Tana jiran saurayi santali ya fito mata ne? Ai wannan ma Allah ne ya ji kanta ya turo mata da shi dan haka ta karba kawai ta yi hamdallah......


Rayuwar Sudais da Rauda a kasar saudiya

Rayuwa ne mai cike da tsari, dumbin kulawa, Rauda na samu wajen mijinta haka shima yana samun tarin soyaya, kulawa, uwa uba nutsuwa a tare da yarinyar da ta yiwa zuciyarsa dirar mikiya sannan ta shayar da shi mamakin yar shila ma mace ce😂

Zaune take ta tsurawa windows ido, filfilfil iskarnan mai dadi mai saka nutsuwa na hurawa, dadin garin manzo ni.ima daga nan ta fito,
Hadarin da bai yi shawara ba cida ba komai ne ya fara sakin ruwa, sai garin fiyayaen halita garin gagara gasa garin masoyina 😌,

A hankali ta mike ta je ta rufe windows din ta dawo ta zauna zuru da ita

Ya jima yana kallonta kafin wayarsa ta dauki ruri ya nufeta

Mom shine abinda ya gani dan haka ya daga da salama

Bayan sun gaisa Mom ta ce" watanku nawa son ? Ba zaka zo na ganka ba ko?

Sudais ya yi murmushi, Mom kennan, wai ya zo ta ganshi, so dai take ya zo ta kara kakaba masa yarinyar nan ya dawo yana ta fama tamakar wani yaro karami kulun bakinsa yana haiga idan ya tarota ta nan sai ta bule ta can

Sai da suka gama wayar ya ajiye ya dauki uar karamar ta ma.aikata ya yi kiran wani balarashe imran sukai magana suka gama kafin yake karasowa a hankali wajen Rauda da wata wayar a hannunsa

Yana zuwa ya zauna inda ske facing din juna,
Yar doguwar riga baka ce a jikinta, gashin kanta ya yi mata luwaiwai sai hannunta na hagu da wani dan abin hannu siriri ta daura shi shikenan sai kanshin da take bazawa
Rauda ta zama wata fresh da ita, fatar jikinta ta zama wata mai sulbin gaske sannan ta kara haske, hutu ya bayana ta ko.ina a jikinta koda yaushe cikin gyaran kanta take bata yarda dan sun yi wata biyu da kwana goma sha hudu da shi ba tace wai sun saba, a kulun takan tashi da niyar wannan bakona ne, wanda nake son na birge, na ja ra.ayinsa, na yarda da kalmar tsoka daya ne a miya kowa wawa yake kai masa, dan haka nima ba kowa bace dan ya nuna yana sona ba hakan zai bani damar na zubar da makaman yakin yakar zuciyarsa ba, domin kuwa zama wahe daya ya kori komai,
Hakan da ta sakawa ranta ya saka take binsa da dukan matsayinsa na miji a wajenta, tanai masa biyaya ne mudin ranta, sannan tana kokarin bashi hakinsa a duk lokacin da ya nema kai harma kokari take ita kanta ta nema dan ya jita a ransa
Tako taka rawa ya yaba harba yayi kari, domin salolinta sun zo masa a yanda yake so,
A ranar da cikin baci ya jita tana kai masa hari.....wato tana nuna bukatarta a gare shi , ya ji shi tamkar wani sarki....cike da nustsuwa ya amsa gayatarta harda yayi dare a wajen, tun daga lokacin ya kara sarawa ya sake komai kawai Yar shila ta gama da shi (🤣)

Habarta ya saka hannunsa na dama ya dago, kafin yake kashe mata ido daya ya ce" ni wai shashare nin na menene?

Bakinta ta turo ta juya masa baya tana dan alamun kuka zatai

Juyo da ita yayi, ya shagwabe fuska kamar yanda ta yi ya ce" a sasautawa Sudais yana neman kansa

Rauda ta yi walwal da idannuwanta kafin ta ce" sire, a gaskiya ina kishin mijina.....ta ya za.a ce wai ministan wannan gingirmemen garin yana nemawa yarsa aiki a ma.aikatarka sannan a matsayin secretariarka? Aa, ni fa ba yarinya karama bace na san magana idan aka yi, mu koma gida ni gida nake so

Ta karashe tana fashewa da kuka bilhaki

Ajiyar zuciya ya sauke yana taping din bayanta, har wata zufa ya ji tana karyo masa ta tashin hankali

Murya a rine ya ce" ki yi hakuri Mata, yanzu ya kike so a yi?

Sasauta rigimar ta yi tana kallonsa ta ce" idan har dole sai ka dauki mace a matsayin secretaria ka dauki matanka aunty da ni mu kasance a kusa da kai

Dariya ya fashe mata da shi har yana dan rike ciki kafin yake tsagaitawa ya dan nunota da yatsarsa karama ya ce" ko ku kori du macen da ta zo siyaya wajen mijinku ba, bayan sana.ar dan almajin du yawanci harkar kayan matan ne....shikenan sai mu yi tsawa mu dawo gida abinmu

Raudama ta yi murmushi ta fada kirjinsa murya kasa kasa ta ce" koda mijina ya shekara goma a gabannnan a zaune bana tunanin wani zai gane cewar baya aiki domin Allah ya rufa masa asiri fiye da tunaninsa,
Farin cikina ina kishin mijina domin ina sonsa


Ajiyar zuciya ya sauke ya bata wata runguma mai zafi,
A kunnanta itama ya kawo lebensa, a hankali ya ciro harshensa ya lashi gefen kunnen nata, ya kai bakinsa sosai ya ce" kin san meye an fasa daukan nata, sai dai zuciyata ba zata iya harbawa ba in dai tana tunanin kina can waje wajen da wani gardi na iya ganinki, Rauda zan haukace idan na ji labarin kin taba son wani a duniya, zan shiga mugun hali idan na ga wani na kallon min mata........yanzu kuwa duniya ta ki gaskiya, mutane sun lalace......rudin duniya na halakar da bayi, mazonmu ba zai ji dadin wannan lamari ba duda ya san da zuwan zamanin, al.umarsa tana ta manta dumbin alkhairinsa a gareta tana tafka tsiya a doron kasa bayan ta manta wanda ya yita ya fita gannin kanta......ba zan iya barinki ki fita aiki ba, ki yi hakuri Mata

Kankame shi ta yi ta shiga kai masa farmaki, yana zuwa da zafi zafinta wanda basu iya tashi sun karasa bed ba sai nan kan lalausan kafet din falon suka baje koli.......🤦‍♀



Haba dady, dan Allah ka yi hakuri ban gansu bane da na hada har su

Dady ya watsa mata harara ya juya ya fice abinsa
Mahaifiyarta dake zaune tana danna waya ta ce" ke idan kin gama wankin na babanki ki maida hankali ki dora girki mana

Mikewa Humaira ta yi tana sharar kwallah ta nufi kayan ta kwashe ta je wajen yin wankin inda mahaifiyarta ta bita da kallo,
Gaba daya jikinta ya yi wani tabo tabo
Wani wajen tamkar an kona,
Fuskarta kuwa ta yi wani mahaukacin baki ta yi mata tsaba tsaba tambar jikin tsaka
Humaira dai ta dawo sai kace zarara ita kadai ma magana take idan tana zaune, somin har mafarkin khairath take tsabar ta sakata a ranta fadi take alhakin Khairath da Sudais ne ke binta , khairath bata duniya bale ta yafe mata sudais yana duniyarma aman ta tabata ko tsafi take ba zata iya kai kanta inda yake ba
Kuka ne aikinta ba dare ba rana, sai tana susar fatarta tamkar ta yageta ta huta, ta dawo wata kala da ita, abin sai adu.a, takan saka abinci gaba sai ta fashe da kuka, tun bata iya girkawa ba har ta iya wasu abubuwan , aman sam ita bata jin dandannon su a bakinta
Sama ta kalla bayan ta gama wankin ta ce" khairath, ina kike? Ke mutuwa kikai........ki godewa allah idan har Allah ya cida ke kin huta, mijinki ne ya wanke ki yana hawaye, cikin nutsuwa ya suturtata ki sannan shi ya raka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login