Showing 45001 words to 48000 words out of 122108 words

Chapter 16 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

398

wannan salaryn ya ishe ni kafin na malaki wurin...

Rauda ta yi gagawar bada zancen ta ce" Allah mai kyauta da kari, yau yau akoy murna shikennan na makaranta ya samu

Aisha ta yatsina fuska tana tatAra kudaden ta ce", makaranta? Ke da akai maki aure ki tanaji kayan daki da kicin mana daidai karfin ki.....ni kin ga tafiyata

Ta juya ta fice ta bar Basma da sakin baki
Juyowa ta yi ta ce" wai da gaske take an yi maki aure?

Jikinta ne ya yi sanyi gannin yanda hawaye ya zirarowa Rauda, da sauri ta share ta kakaro murmushi

Basma ta sako wani zancen dan gudun shiga iri yanmayi

Ya shiga rudannin kalmomin Rauda, ba wata doguwar magana kawai ta rubuta masa *YAR SADAKA CE* me take nufi?

Ya Allah ka bani ikon dawo da jarumtata a kan yarinyar nan

Mikewa ya yi ya fito sai cin karo suka yi da Aisha,

Cike da murmushi ta tunkare shi wanda hakan ya saka shi faduwar gaba ya ja ya tsaya shi ba ya juya ba shi ba ya tafi ba

Ina kwana yaya!
Aisha ta fada tana kara kunace masa waje

Hade fuskarsa ya yi tamkar bakin hadari, daidai nan su Rauda suka fito ita da Basma
Gannin Aisha na kokarin taka dokar da aka yi mata kyakaywan kashedi da kuma kuma horon canza mata wurin aiki aman har ta manta ta rike dubu dari da hamsin dinta a jaka tamkar ta kwaso kudaden banki gaba daya

Da sauri ta matso ta kama hannun Aisha ta ce" i bg u mu tafi Aunty

Aisha ta janye hannunta da karfi ta ce" a yau sai dai idan korar tawa zai yi ya yi,
Tana gama fada ta juyo wajen Sudais da ya juya da sauri dan komawa office dinsa yana adu.ar neman tsari wa fitinar nan sai dai me hannunsa Aisha ta damko da karfinta ta yi gagawar matsawa sosai kusa da shi

A mugun harzuke ya juyo ya sauke mata idannuwansa da sukai jajajir lokaci daya

Aisha ta fashe da kuka ta ce" har yaushe zaka daina yin tamkar bana raye? Har yaushe zaka mayar da ni mutun irin na kowa? Har yaushe zaka lura da ni ka gane halin da nake ciki?

Saurin rintse idannuwansa ya yi, murya a kausashe ya ce" ki fita a wajen nan Mahaukaciya tun kafin na koya maki hankali na baki tarbiyar da kika rasa!

Da sauri Rauda ta rintse idannuwanta jin tun ba.a je ko.ina ba Aisha ta jaya iyayen su zagi, domin dai tarbiya ai iyaye ke bayarwa ko? Idan ya ce haka kennan iyayenta basu bata tarbiya ba? Ranta ne ta ji yana tafarfasa
Aisha ta share hawayenta ta ce" koma mai zaka ce ni ina Son k......mmm

Kafin ta karasa fitar da garafin karshe wato Ka..... ta ji gaba daya jinta da ganninta sun dauke na wucin gadi
Luuu ta yi zata kai kasa aman kafin ta fadin ta ji karan saukar wani lafiyayan marin da ya saka ta sakin dan fitsarin da take rikewa,
Mari ne, mari ne, wa yayi marin? Rauda ce ta sakar masa mari a gefen dama, rauda ce ta takarkare ta sakar masa marin da ya saka Basma , Aisha, Da Samir daura hannayen su bibiyu a saman kansu, tsoro, firgici , da mamakin abinda ta aikata ya saka Samir furta tun karfinsa" *NA MUTU*

Idannuwanta cike da kwala ta watsa albashin da aka bata na tsawon aikin wata guda da ta yi , daidai hawayenta sun sami damar fitowa a kwarmin idannuwanta ta nuno wajen da yake da dan yatsarta ta ce"


Wayo 😳😳😳 , Mari, wai wama ta mara tukunnan? Ya kuke gannin za.a karke? Cmment😟😟😟




Readers, me nufin Rauda ne da kalmar " *YAR SADAKA CE?* shin ta raina kokarin mijinta ne ko ta riki maganar a ranta? Ya kuke daukar novel din nan? A fa yi hakuri da mu yan koyo ne🥰🥰🥰
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




2⃣7⃣


Ta ce" dan yaya sun aikata laifi sai a zagi iyayen su? Kai ka san su waye iyayen namu ko ka taba haduwa da su da har tunaninka ya baka darajar su ko girman su daidai yake da naka kana iya takawa?

Jajayan idannuwansa ya dago ya sauke a kan fuskarta, mari? Marinsa ta yi? Mari? Mace ce ta mare shi, abinda ba.a taba yi masa ba tun daga farin wayon sa har zuwa yau, ko kwalar rigarsa ba.a taba shaka ba, aman a yau mace, karamar yarinya , wace take matarsa ce ta daga hannu ta mare shi!
Kansa ya ji ya wani irin sara masa, nan da nan jijiyoyin kansa wuyansa da hannayensa suka firfito sukai rado rado ana kalon su a fili,
Wayar dake hannunsa ce ya rike irin rikon da koda kashin mutun ne zai karye ne, wannan babar wayar iphone din sai ji kake bak bak tana fashewa sannan maduban na shiga lalausan tafin hannunsa sai jinni ya fara dan tsagowa yana daso a wajen

Samir da jikinsa ke kyarma ya kwaso da gudu ya bude office din Sudais ya shiga kokarin tura shi aman ko gezau baya yi

Da mugun sauri Basma ta janyo hannayen Rauda, wace ta yi mutuwar tsaye kuma wani mugun tsoro ya darsun mata,

Janta take tamkar ana jan rago da igiya, suna fitowa Rauda ta kali gabas da yama , kudu da arewa, hanayenta ta dora saman kanta ta fasa kuka, a fili take fadin" na shiga ukuna ni Rauda zuciya ta debe ni na janyowa kaf zuri.ata barin nigeriar kanta bama garinnan ba, wayo Allahna wayo ni raina mai ya kaini aikata hakan? Basma ki taimaki rayuwana ki mayar da ni ya kashe ni idan dai zai bar hukuncin iya ni, wayo ni kaina da aurena na taba fuskar wani katon dan fushin zuciya, ashe bani da nutsuwa har haka? Ya zamu kare da auntyna a yau ni Rauda?

Kasakai Basma ta yi tana kallon ta, da harshen turanci ta ce" Rauda, dama cikin hankalin ki kika kai hannayenki kan fuskar Elhaj SUDAIS mai daraja? Ke kuwa kin san ko shi waye a fadin duniya ? Najimi ko yaro ne zaka ji tsoron aikata irin haka a gare shi Rauda

Rauda ta kara tsorata da abinda Basma ta fada, da saurinta ta juya ta fito bata ma san abinda take yi ba ta tsayar da mai mashin ta hau cewa kawai take mu tafi, mu je

Da kyar Samir ya samu ya tura Sudais aman bakinsa kan kofar ya ja ya tsaya

Samir ya rasa ya zai yi, mai zai ce? Tsayawa ya yi jikinsa na dan bari muryarsa na rawa rawa ya ce" ooooga ka ka zauna dan Allah

Idannuwansa ya dago ya sauke kan fuskar Samir, ya yi masa kallon da ya kai na minti biyar domin Samir har ya fara fida rai da zai amsa masa , can cikin murya mai amon zaki ya ce" ka bita, ka tabatar ta an kaita gida

Samir kwalalo ido ya yi, na bita? Yake tambayar kansa, ikon Allah na bita fa ya ce? Yanzu du irin marin da ta daga hannunta ta sharara masa shine zai budi baki ya ce na bita? Ko a tarihin yarintarsa ana danganta shi ne da dutse wato dunkum da shi sai ta baci zai kai naushi, ikon Allah mace ce, ta mare shi kuma yake ambaton a tabatar masa da ta tafi gida

Samir ba fita Sudais ya karasa jikin madubin office dinsa ya tsurawa wajen ido, a hankali ya sa hannunsa na dama ya shafa gefen fuskarsa, ya kuma shafawa, ya bi jijiyoyin jikinsa da kallo, ya dago dara daran idannuwansa ya sauke a kan fuskarsa kadai,

A fili ya furta" *Marina*

Juyawa ya yi ya dauki ky din mota da yar karamar waya still hannunsa da abin jini jini ya fice a office din

Direct wajen zaman mahaifinsa ya nufa, yana zuwa ya ja gaba da su kadan ya tsaya

Da kallo suka bi motar suna jira ya fito, domin ya saba idan ya zo gaishe da mahaifinsa yakan fitowa ne ya haisar da kowa cikin raha su dan zazanta harkokin yau da kulun kafin ya koma aman yau yana neman kwasan dogon kiwo

Malan Shehu mahaifin marigayiya ne ya ce" aa, kamar Elhaj? Kuma bai fito ba ko dai lafiya? Ko waya yake?

Dady da ya tsurawa motar ido, gaba daya jikinsa ya bashi ba lafiya dan haka ya mike bai ce komai ba ya karasa ya bude gaban motar ya shiga yana kallon wajen sa

Gabansa ne ya fadi gannin yanda kwatakwata ba alamar nutsuwa a tatare da SUDAIS, sai kuma abin jini jinin da ya ji ciwo da yar sauran kwalbar da ta shishige masa hannu.....
Da sauri ya kima kallon fuskarsa ya ce" hadari ka yi?

Sudais na kallon sa bai iya cewa komai ba,

Dady ya ce" ba zaka amsani ba? Mai ke damun ka haka?

Sudais ya kifta idannuwansa, yama rasa mai zai cewa mahaifinsa, ahi dai abu biyu ya sani idan ya zo wajen mahaifin sa ba zai bar shi aikata mugun abu ba, sannan ya tabata da zai sama masa nutsuwa

Ajiyar zuciya Dady ya sauke, shi kam Allah ya bashi bahagumen yaro ace abun damuwa na damunsa aman ba zai budi bakinsa ya fadi damuwarsa ba sai dai ya tsare mutun da ido koda kuwa wuni zaku yi da shi a haka? Shi kam yana gannin ikon Allah sai adu.a
Hannunda ya mika wajen kuna wakokin motar sai dai sabuwa ce baya gane systeme dinta

Fita ya yi ya dauko wayarsa ya dawo ya shiga motar ya zauna ya kunna karatu

Shima jingina yayi da kujerar motar kamar yanda Sudais ya yi ..

A kadan sun kwashi minti arba.in a haka kafin ya dago ya kalo Wajen Sudais sai ya ganni yayi baci yana sauke ajiyar zuciya

Da dabara ya samu ya matsar da shi kujerar kusa da mai tuki ya gyara masa konciyarsa bayan ya kontar da kujerar

Wajen direba ya shiga ya zauna yana adu.ar Allah ya sa motar auto ce, aman da kamar wuya wannan galeliyar motar ace auto ce

Ai kuwa yana gyara zamansa ya kunna ya ga Auto ce, dan murmushi ya yi ya tayar da motar ya nufi gidan Sudais Wanda yake cikin gra gidan da bai jima da gama gina shi ba

Wohoho zo ku ga gini har gini, gida har gida, ginnin gidan nan baki ba zai fadi tsaruwarsa ba, ya tsaru , ya ginu, an kashe kudi tamkar ba zai zama kasa ba, tamkar ba za.a mutu ba domin irin ginnin nan mai karamin imani baya zama cikinsa🤦‍♀

Hanyar kasa ce da ta sama , pave ne shinfide a ko.ina,
Bayan shigarsa sai da yayi tafiya mai nisa kafin ya samu ya tsayar da motar daidai kofar da zata haudasu bangaren Uban Masu gida

Da kyar ya samu ya dan farka daga bacin da ya tafi, ya talabo shi suka fito suka nufi accensaire din
Dady ya mugun gaji kafin yake samu ya shigar da shi ya shinfide shi saman lalausan kafet din wajen

A hankali ya zauna kusa da shi ya riko hannunsa na dama yana tofa masa adu.a har shima ya fara gyadigyadi san haka shima ya konta sai baci

Dan motsin kamar cokali ya farkar da shi a bacin da ya afka

Yana farkawa ya ga Sudais ne zaune yana motsa kofi a cikin cop

Hamdallah ya yi a cikin ransa, ya mike ya tafi cikin daki guda dan shiga bayi

Ya jima kafin yake fitowa ya tada sallah dan kuwa har karfe hudu ya yi,
Yana gamawa Sudais ya sauko kasa har yanzu muryarsa bata dawo daidai ba ya ce " ina yini Dady

Dady bai amsa sa ba ya tsare shi da ido

Sudais ya kuma sada kansa ya ce" ka yi hakuri dady, na tuba

Dady ya girgiza kai ya ce" bana so irin haka na faruwa da kai dan bana so cutar hawan jini ta kama ka,

Sudais ya sauke ajiyar zuciya, ya tabata da yana da hawan jini abinnan ya faru da shi haka a yau da ya mutu

Sauke ajiyar zuciya ya yi ya ce" dady, ina so ka yi hakuri yarinyar nan ta tare a cikin satin nan, bana so su yi wani biki wata sabga bana so su yi komai, kawai ta tare

Da mamaki dady ke kallon sa, ya ce" aman ai ba haka muka yi da kai ba ko? Da mahaifin yarinyar mun tsayar sai an yi adu.ar arba.in din Marigayiya zata tare, kuma dan me zaka ce kar su yi biki?

Cikin kauda kansa ya ce" Dadyna, wannan damar duka a hannunmu take, ni bana so su yi mata komai, indan da hali dady idan har da hali ta tare hakannan.

Dady ya dan yi jim, tunani ne ya yi na dan lokaci, tabas ya san mai daki shi ya san inda yake masa yoyo,
Sudais ya cika zurfin ciki wai a nan yana fadawa dadynsa wasu sirrikansa ne ma, sannan a duk lokacin da ransa ya baci ya kasance mai yin shiru, baya magana a lokacin, ba yana nufin ya yafe ba, idan yana nigeria damuwarsa ya yi yawa yakan je wajen mahaifinsa domin shi baya takura shi da tambaya a lokacin da ransa ke bace, koda ya huce baya takura shi sai dai ya yi masa nasiha shi ya sa a yau bai tsaya wani abin ba ya nufo wajen mahaifinsa aman har yanzu ya kasa yafe mata wannan abin mai girma wato ta daga hannu ta wanka masa mari a kan gaskiyarsa mari,
tambayar kansa yake a kasan zuciyarsa wai ma ya aka yi bai ga zuwanta ba? Aa ya ga zuwanta bari ya yi har ta cin masa, shi yayi wasa har ta kai zuciyarsa mizanin da dan abin haushi ta daga hannunta ta wanka masa mari aman ya kasa daukan mataki mumuna a kanta, aman shi, shi ya san matakin da zai dauka a kanta
(😳😳😳😳)


Marfin tukunyar ta kumA wurga mata ya sameta a hannunta na hagu ta dafe tana kara sakin yar kara
Da gudu mama ta shiga tsakanin su ta ce" Ke Aisha, ya isa haka sai kin kasheta ne a kan da namiji? Yar uwarki ce fa? Ki zo mu je mu nemi malan a san yanda za.a je a bashi hakuri tun kafin wani mumunan hukuncin ya tabata a gare mu,

Aisha cikin muryar kuka ta ce" mama, walahi ba yar uwata bace Rauda, kawai ba yar uwata bace, me ruwanta dan ya zage ni? Ai ni ya aibata da rashin tarbiya ba ita ba ko? Mama ki barni da ita a gidannan yau na lalasata, mama ki barni na koya mata hankali domin na lura rashin hankali da kaurin talauci bai ishi kanta ba , banza marar tunani

Ni dai ya isa haka dukan, ya isa , ki duba ki ga ko daga saman mashin baki barta ta sauka ba kika wartota kike dukanta, ya isa haka ba zaki hada min zafi uku ba, da me zan ji?
Ta juya wajen basma da du jikinta ke ciwo sakamakon dukan da Aisha ta yi mata, dan kuwa ta daketa kamar da wasa ta ce " a kulun fada maki nake ba kowa ya san darajar na gaba da shi ba, ba lale ne ki ce ke dole sai an mutunta maki iyayenki, ke ba karfin da zaki tari abin ne da ke ba, dole a wannan zamanin ka yi hakuri da rayuwa a yanda ta zo maka, haba Rauda haba Raudana

Tausayinta ne ya ji ya mugun kama shi, harma ya ji kamar ya juya ya shaidawa Elhaj wannan bukata da wuya ta yiyu , bai taba ganninta cikin rashin tudun dafawa irin na yau ba,
Daman zata yi sanyi haka?
Cijewa ya yi ya shigo gidan nasa da salama, wanda jin muryarsa ya sa Aisha ta yarda icen dake hannunta ta yi gagawar nutsuwa domin tunda abinnan ya faru wato auren da ya daurawa Rauda take shayinsa, ......

Malan AHMAD KENNAN
..



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




2⃣8⃣

*WANNAN PAGE NAKI NE NA SIS LADEEFA ALKHAIRIN ALLAH YA TABATA A GARE KI*

kuna da yawa fa, walahi sosai kuna da yawa, na gode da kulawarku jiki yayi sauki alhamdulilah💓💓💓💓💓💓💓





Salamar malan ta saka Mariama juyowa da dan saurinta, ganninsa ya sa ta saki ajiyar zuciya domin ta san dai ko menene malan zai tare mata

Kallon su ya yi gaba dayan su , bai ce komai ba ya juya ya shige dakin su

Murna fal zuciyar Mariama domin rabonsa da ya shiga dakin su tun ranar da abin ya faru,

Hannun Rauda ta kamo ta tsayar da ita kofar dakin ta shiga ciki dan gudun kar Aisha ta kuma dukanta

Malan Ina yini

Kalonta ya dan yi ya amsa ciki ciki wanda hakan ya sa gwuiwarta ta dan sace

Neman guri ya yi ya zauna, ya ce" na dawo kan maganar auren yata , wace na isa da ita

Da sauri Nana Mariama ta sada kanta , bata ce komai ba,har ta tuna masa zamanin amarcin su

Ya ci gaba da fadin" na yi mata aure sannan mijinta ya shirya tarewarta domin ya ce yana so ta tare karshen satin nan

Da sauri ta kalo wajen sa, murya na dan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login