Showing 30001 words to 33000 words out of 122108 words
Chapter 11 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
ya goge ta sosai har table din sannan ya bude miskin nan ya dan shafa mata kafin yake dauko suturarta wace zata kasance suturarta ta karshe 😭, lokacin da ranta ya sha yi mata tambayar dan me take yawan ajiyar likafani? Sai ta yi murmushi ta ce masa tanadin likafani ne dan bata san a ina zata kasance? Tana so idan ta same ta ta samu cikaken sutura, tana fatan ya suturta, sai yayi murmushi yace mata idan fa na rigaye ki mutuwar fa? Sai ta yi saurin rufe masa baki ta ce" ban san misalin da zan yi maka ba, ni dai na sani zan yi kuka sannan zan so na shirya ka dan na yi a hankali ina yi ina karanta maka suratul yasin sannan idan an dauke ka na zauna na yi ta karanta maka kul.huwa lahu ina nema maka sa.ar shiga kabari, na yi ta yi maka adu.a, sai dai ni na san sai na rigaye ka ko dan hukar nan da ta sanyo ni a gaba
Sai ya girgiza kansa ya ce: jikinsa yayi A kulun ina fada maki cuta ba mutuwa ba ce rashin lafiyar ki ya daina tayar maki da hankali sai lokacin ki ya yi zaki mutu ,
Dan tsam ya yi yana karewa fuskarta kallo, tamkar ya kirayi sunnanta ta amsa, tamkar ya kama hannunta ta biyo shi, jikinta ya yi mugun laushi, bata da wata kazanta, yar kunfar fitan rai bata wari ba komai, Gawarta ta kasance gawa mai tsafta , Ya Allah ka sa makoncinta ya kasance haka da.iman
Audugar nan ya cira ya saka mata a kofofin hancinta da kunayenta da bakinta
Sannan ya gyara likafaninta ya suturce mata jikinta yanda ake yi
Zuciyarsa bugawa take sosai, haka jikinsa ya dauki wani irin dumi idannuwansa sun yi hulu hulu fatar jikinsa ta yi jajajir irin yana cikin tashin hankali
Turaran nan ya kara shafa mata a jikin likafanin ta ya yi tsai ya kuma tsura mata ido, a hankali ya ce" Khairath, Mar.atusaliha😭, Ni Sudais Mijin ki na yafe maki dukan kuraran da zaman tare kan haifarwa wanda na sani da wanda ban sani ba, ina rokon ki da ki yafe min nima, Khairath kin rasu ke kadai sai Allah sai mala.ikan da ya dauki aron ran da Allah ya baki
Ina rokon Allah ya sa wannan rana ta zame maki ta farin ciki, shiga kabarin ki ya kasance maki shiga hutun ki, Allah ya sa annabi ya tarbe ki Khairath
*Khairath* ki sani ni.........
Pagam Humaira ta turo kofar falon nata na biyu tana fadin" wai ya haka Sudais tun da asuba ba zaka bari ka fita a girkin nawa bama ka zo nan ka tare😒
Idannuwanta ta sauke a kan sa, sannan odannuwanta suka sauka a kan abinda ke gaban sa,
Ido ta zaro ta murza idannuwanta tabas Sudais ne tsugune gaban gawa da take ganni tamkar Khairath ya yo jina jina tamkar ya tashi a jinya jikinsa du da dan ruwa da ya jika masa suturarsa gefe guda kuma abyar da ya cirw mata ne
Ai bata san lokacin da ta dora hannayenta a saman kanta ta kurma ihun da ya sa sudais ya katse abinda ya yi niyar kara fada mata ya mike da sauri dan yin waje da Humaira kar ta daga masa hankali ta kuma bata masa lokacin nan da yake samu na karshe da matar da ta so shi domin Allah daya
Ai kuwa kamar ma mai jin tsoron ya taba ta ta juya ta arce a guje tana ihun kuka tana fadin a taimake ta ta yi gefen mahaifan sudais
Gaba dayan gidan wannan labari ya girgiza su, a tare suka dugunzuma dakin na khairath banda Humaira da ta yi dakinta tana kuka cike da tsoro ta dauki wayarta ta shiga bugawa dangin ta
Dafa kafadarsa mahaifin sa ya yi, shi kansa hawayen ne ya cika masa ido, yana tausayawa dan nasa na cikinsa da yayi muguwar jarumtar nan, ya wanke matarsa da kansa sannan ya zauna yanai mata adu.a
Murya a raunane ya ce" ka yi hakuri SUDAIS , ka yi hakuri, ka kara a kan wannan, ka kara yafe mata iyayenta suna hanya ka fito mu je ka sake wannan tufafin mu je mu yiwa matar ka rakiya, Sudais Allah ya jikanta da rahama ba.a so a cika jinkiri da gawa a shinfide
Haka ta kasance a wannan rana ta talata, Khairath aka yi mata rakiya gidanta na gaskiya *KULU NAFSIN ZA.IKATUL MAUT*
Haka suka dawo aka ci gaba da karbar gaisuwa a gidan SUDAIS UBAN MASU GIDA😟😟😟
RAUDA ce zaune ta buga uban tagumi, wannan abin ya dame ta, yau kwana takwas kennan da take fama sai yau labari ya iso masu cewa matar ogan su SUDAIS ta biyu ce ta rasu domin mataimakinsa yana wajen makokin shi ma sai da Samir ya nemi izinin a fada dan a zo a yi mata adu.a ya bayar da izini
ai kuwa nan hankali ya tashi an shirya a gobe za.a je a yi masa ta.aziya motocin ma.aikatar zasu hadu su kai su gaba dayan su an ce a zo karfe goma kowa da kowa
Labari na kaiwa Aisha cikinta yayi wani irin juyawa sai kuwa wani kugi ya sa kuuuuuuuuuu wanda ya sa Rauda ta juyo da sauri tana kallon ta,
Kafin ta samu damar yi mata tambaya har ta fice a wajen cin abincin cikin gagawa ta tari napep, itama ta biyo bayan ta dan a tunaninta ko bata da lafiya ne
Sai dai suna karasowa ta sa kuka mai zafi hannayenta a saman kanta take rusawa
Da kyar aka samu ta budi bakin ta ta ce " da matan sa har biyu? To ita wannan ta godewa allah da ta koma tun yanzu Wly ba zan iya raba shi da wata banza ba, ba zan iya ba ba zan iya ba sai na halaka........😳😳😳😳😳😳
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
1⃣8⃣
Tana neman arcewa ya damki hannunta ya ja ta kiiiiiiiiiiiiiiiiii
Bai zame ko.ina da ita ba sai bangaren sa, yana zuwa baban falon bangaren sa ya cika hannun ta
Tsai ya yi ya dafe goshin sa, zuciyar sa na yi masa duka ta hana shi sukuni sannan ya cika da mamakin kanwar sa
Tsoro ne ya kama ta, firgici da tsoron yayan nata ya bayana a tatare da ita, da sauri ta durkusa jikinta na rawa ta ce" yaya, dan Allah ka yafe min, ban shiga wayar ka dan na duba wani abu ba sai dan na tura kati kuma na kali hotunan abaya da Sarkoki, ina cikin kallon ne na ga dossier mai sunna *MATA*, ni a tunanina mata kamar mayayaki irin su abayar ne sai dai ina shiga na ga hotunan nan kamar rayuwarta ce a ciki domin du yawanci wajaje ne da ta yawaita rayuwa a ciki
Yaya ka yi hakuri, yauma da na ganta abin ne ya yi surprise dina na tuna ashe ta zo birthday din nan da na so yi maka
Dan tsagaitawa ta yi gannin ya tsura mata ido, ai kuwa tsoro ya sa ta saki kuka ta dan kankame hannayenta a jikinta tana dan girgiza kanta tana cike da tsoron sa dan ba zata taba son abinda zai sa ya kai hannunsa kanta ba xan ya taba duka a gaban idannuwanta mutumen ya suma daga marinsa da ya yi
Ajiyar zuciya ya sauke gannin Auta kanwarsa wace ya fi kauna cikin yan uwansa yana faman tsorata ta haka bayan bai taba koda shakunarta ba
Kansa ya kawar a kalonta ya ja numfashi murya a kausashe ya ce" ki tashi, ba komai zan yi maki ba
Da sauri ta mike tana dan kara gyara hijabinta ta matso shi sosai cike da sangarta irin ta autanni ta ce" yayana baka saki fuskarka ba
Ya juyar da kansa ya ce" hafsat, tafi
Ta kara shagwabe fuska zata yi maganar ya daga mata hannu ya dora dan yatsansa a kan lebensa sannan da dayan hannun ya yi mata nuni da ta tafi
Da sauri ta juya ta fice a kasan zuciyarta tana ayana lalai fa wannan lamari mai girma ne, wannan al.amari sai ta saka manya a ciki...
Bayan fitarta zama ya yi a saman babar kujerar fallon, waje guda ya tsurawa ido ya jima a hakan yana tunani..., tambayar kansa yake damuwar nan ta kai har ya fara nunawa? Ya san halin kanwarsa ta cika mayar da hankalinta kan abu da nacin abu aman bai taba tunanin zai manta abinda yake ciki ba dan kawai yarinyar nan karama tana kusa da shi! A fili ya furta" ba zaki ci galabar zautar da ni ba *MATA* !
Humaira ce ta shigo da bisimillah, gannin bai amsata ba ya sa ta cire zumbulelen hijabin da ta saka tana sauke ajiyar zuciya dan kuwa yayi mata nauyi ya saka sai gumi take hadawa
Kallonsa take a kasan zuciyarta ta shiga furta" ohohoh mutumen nan har yanzu ya kasa sakewa dan kawai wannan rusheshiyar matar tasa ta rasu, to dama mene sauran ciwo kawai ita kulun tana fama ita ba ga kura ba, ita ba turare mai karfi ba, ita ba cin tashi ba, ita ba shan kankara ba, ita ba shan ac ba abubuwa dai da yawa ita sun fi karfinta wannan ai mutuwa hutu ne gareta ma🤦♀, ta yatsina fuska ta ci gaba da zancen zucin ta tana fadin sai ka ci gaba da tunane tunanen sai na ga gaban nan wa zakana fakewa da halayensa kanai min gorin na yi koyi da shi domin kuwa Allah ya sa ni din nan dai da ka yawaita nuna bani da halaya ni ce daya kwalin kwal matar naka MU SUDAIS
nufarsa ta yi ta dan duka, wanda warin man bleating din da take kamar hauka ya bige shi ya hautsina masa yayan hanji ya saka shi zabura da dawowa a duniyar mutane sannan ya dan ja baya ya sauke mata jajayen idannuwansa a kanta
Farfar ta yi da idannuwanta ta kara matso shi sosai ta kashe muryarta ta yi kalar tausayi ta ce" ya dace mijina ya kula da lamarina, kwana takwas fa ba wasa ba
Tsai yayi da idannuwansa a kanta, ya kasance namiji mai yawan bukata, yana da yawan kaiwa iyalinsa ziyara sai dai a yanzu ya kasance cikin zulumi, yana afkawa duniyar tunani na irin warin da matar da ta kasance kwalin kwal a wajensa a wannan lokacin da take fitarwa, warin da ba haka take ba ta dai siyawa kanta dan ta birge, wanda yake hana shi nutsuwa maimakun ya samar masa, wanda ke rikita masa dukan wani abin dake tatare da farin cikinsa dan karni ne take tamkar an zuba mata jini a jikinta hakan kuwa koda ta yi wanka da turare ne
Katse masa tunaninsa ta yi lokacin da ta dora hannunta na dama saman nasa ta ce" tunanin me kake haka? Har yanzu ba zaka daina tunaninta ba? Ka yi hakuri ka bita da adu.a kar ka shiga hakina
Lumshe idannuwansa ya yi bai iya ce mata komai ba, ya mike ya shiga babale boturan rigarsa domin rabun masan nan da ta yi ji yake shi kanshi ya kwashi warin
Dakinsa ya nufa yana shiga ya tarar an mayar da katifarsa, an gyara gadonsa an canza zanin gadon da komai harda su turaren wuta
Direct bayi ya nufa dan watsa ruwa ya konta ko zai samu bacin da ya jima rabonsa da shi domin kansa har ji yake ya yi masa nauyi sosai
Zuzuta kyaunsa, zuzuta kyaun gidan su, na yan uwansa take tunda suka dawo, can ya dora kafa daya kan daya ta ce" mama kin san wani abu kuwa
Mamansu ta girgiza kai ta ce" aa sai kin fada
Aisha ta ce" matar sa, matar sa, man bleating ne take ya mugun ci mata fata ya shige ta sosai ya bata mata kafa domin kafarta ta shaida ta da hannayen ta, ta wani hakimce ita ga matar gida sai shan kanshi take tana basarwa tamkar ita ce mai kudin, uhum mama zata gane bata da wayo idan na shiga gidan oga SUDAIS, zai ajiye fari na ainahi, kyau na Allah, halita tsarara ba irin nata ba, Mama koda a cikin hijab take ina iya gane yannayin tsarin halitarta ba wata tsarara bace sam wannan ba matar gaban mota bace
Mama ta ce" aa, ya akayi du gayun sa ya tsaya a mai bleating? Duk matan nan na duniya?
Aisha ta ce" mama, ina tunanin dan na more rayuwana ne Allah ma ya sa ya auri mai bleating
Mama zata yi magana wata mata ta yi salama,
Cira cira da ita, hijab ne mai ruwan kasa a jikinta aman har ya zama baki dan dauda, ga yaronta ta matkayo shi jikinsa dati har wani shuni yake na dati
Gaba daya suka zuba mata ido, ta zube kasa ta shiga gaishe su
Mama da Rauda kawai ke amsawa inda Aisha ta yatsina fuska ta tashi ta dauke kofin su na shan ruwa ta mika daki ta dawo tana hade rai tamkar ta ga kashi
Matar nan ta ce" dan Allah hajia ki taimaka min ki ban aikin aikatau koda siyen kayan miya ne na ringa yi maki ina samun abinci koda kanzo ne ina ci ina baiwa yarona
Ta karasa maganar tana kara risinawa ko Allah zai sa a dace
Ido kawai Rauda ta zuba masu, wani tsoron Allah ya kara shigarta a ranta take furta alhamdulilah Allah mun gode maka da ni.imar da ka yi mana , Allah ka kara yi mana arziki mai anfani
Muyar mama ce ta katse ta tana kallon matar ta ce" baiwar Allah, da ake zuwa aikatau gidan masu da shi dan ka samu abubuwan anfani na alkhairi ka karu har ma ka kara wasu da shi ke kuwa mai zamu baki a nan? Mu kanmu mun samu na yau muna neman na gobe ne fa
Ta kuma sada kanta ta ce" hajia mun yi yawo ne har mun gaji kofa kofa sai dai a kore mu ko a bamu hakuri dan datin nan dake jikin mu, ku yi hakuri ku dauke ni inada kuzari ba zaku yi kuka da ni ba
Ke ke ke, malama tashi tashi tashi, mai kike nufi? Da wannan kazantar ta jikin ki da goyo zaki yi wa wa aiki? Kinga mike ki kama gaban ki mu kam ba zamu dauke ki a nan ba! Aisha ta katse ta da mugun fada ranta bace tana nuna kyankyaminta a fili
Kara risinawa matar nan ta yi , kana ganninta ka tabata ta jigata, a gajiye take sosai , wahala ta nakasata, ta share gumi ta ce" ki yi hakuri hajiya, yanda Allah ya taimake ki ki taimak........
Ke dAllah malama nace ki mike ko ana dole ne? Ki fice mana a gida tun kafin na wulakanta ki haba!
Saurin mikewa ta yi tana kara gyara yaronta da ya tsalara kuka yana kankame jikin mahaifiyarsa cike da tsoron yanda Aisha ke zazaro ido tana masifa tamkar zata doki mamansa
Mama bata iya cewa komai ba dan tana gudun furta wani abu ran aishar ya baci hakan ya sa ma ta mike ta yi daki
Da sauri Rauda ta fito da leda baka ta bi bayan matar nan da gudu ta ce" malama, malama
Dakatawa ta yi ta juyo tana kallon Rauda
Rauda ta karaso ta miko mata ledar da naira dari ta ce" ki yi hakuri ki ci gaba da neman aikin, Insha Allahu zaki dace, ga wannan tufafina ne duda sun sha ruwa ki samu ki canza naki sai wannan kadan ne ba yawa nima iya shi ne ya rage min Allah ya sa ki samu aikin
Godiya ta yi ta yiwa Rauda inda ta tsaya ta bita da kallo har ta shige gidan su
Murmushi ta saki ta bi kudin da Tufafin da kallo a fili ta furta" *alkhairin ki zai bi ki RAUDA* (😳😳😳😳😳)
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
1⃣9⃣
Matarnan na gama fadar hakan ta fice!
Rauda na komawa ta tarar aisha sai fada take tamkar ta ari baki, tana rantsuwar idan ta Auri Sudais ba zata dauki yan aiki a nigeria ba dan kuwa ba zata amince tana ji tana gani a kawo mata karnin talauci ba!
Rauda ta girgiza kai kawai ta shige bayi dan dauro alwallah
Har karfe tara na safiyar larabar nan Rauda bata fito daga dakinta ba, hakan ya sa mahaifiyarta shiga tana fadin" RAUDA, lafiyarki kuwa na ga har kin yi lati yau bayan nan da kwana hudu za.ai maku albashi kar ki yi wasa fa a taba maki albashin ki
Rauda dake konce saman katifar su tana ta bari, jikinta ya dume da mugun zafi ta kasa furtawa mamanta komai dan kuwa bata jin zata iya buda bakin nata
Da sauri Nana Mariama ta karasa tana fadin" subahannalahi, Rauda da zazabi kika tashi yau? Ya Allah ka ji kaina kar ta yi maki irin abinda take maki
Idan rauda na zazabi takan yi mata duka ne mai zafin gaske domin har combilser take tana zabura jikinta na dumewa da mugun zafi har rike su ake a asibiti , zazabi dai bayai mara da dadi
Janye rufar da ta yi da hijabi