Showing 54001 words to 57000 words out of 122108 words

Chapter 19 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

419

? Da sauri ta girgiza kanta tamkar zarara ta furta a fili wanda bata yi tunanin ya fito ba cewar" aa, bama zai taba yiwuwa ba, sam hakan ba mai yiwuwa bane, ,ba zan taba rayuwar aure da mutumin da auntyna ke so, na tabata ma ba shi bane ba zai taba zama shi ba

Sudais ji yayi sam bai ji dadin maganarta ba, daman ya ji tsoron kar a je ta yi masa irin haka, wato yarinta na damunta ai sai ya ganni

Kina nufin ke, kece dad ya auro min? Ya Allah why m?

Kasa ta yi saman gwuiwoyinta, gaba daya ta yi sanyi sai dumbin tashin hankalin da take ji, kafafuwanda dake cikin takalmi sau ciki ta tsurawa ido, ta tuno fitinar Aisha, ta hango gidan su da kalar matarsa, karyar da kai ta yi ta ce" ka yi min rai ka sawake min aurenka a kaina, ba zan iya rayuwar aure da kai ba, soyaya ba zata taba shiga tsakaninmu ba, ba farin ciki a tarayar mu, kA yi min rai ka sawake min kar rigimar da ta tunkaro ni ta shafe babina

Kowace kalmar dake fitowa daga bakin lalla tana shiga kunen sudais ne da kibiya mai mugun tsini tana kaiwa zuciyarsa farmaki,

Idannuwansa ya rintse jin yanda zuciyarsa ke hawaye mai zafi,

Da sauri ya juya ya fice ba tare da ya tankata ba

Har ya kama kofar ya juyo da mugun sauri ya karaso inda take,
Hannunsa na dama ya saka ya damki damtsanta na hagu ya duka yanda take iya jiyo numfashin sa da hucin da yake fitarwa, idannuwansa ya saka cikin nata ya ce"
*ke, ban aure ki ba dan soyaya! Na je sallah na ji tausayin tsoho mai daraja! Ki sani da na san ke ce da ba zan taba aurenki ba domin bana ra.ayin mata masu furtawa namiji kalmar so tun kafin ya taya, abinda yayarki ta aikata zaki aikata ne domin uwar rainon daya ce! Na fada uwar rainon daya ce! Ki kiyayi furtan munanan kalamai domin ba zaki ga da kyai ba! Ki shirya karbar hukuncin marin da kika buda kazaman hannayen ki kika yi min! Dole ma na rike ki na wani lokaci ko dan na koya maki hankali!*

Yana gama fada ya cika mata hannun da ta ji ya sangaye ya juya ya fice tamkar zai tashi sama

Da kallo ta bi shi ta sume a zaune, mugun tsoro ya hannata kukanma , haka ta zauna ta tsurawa kofar ido

Shi da zai nufi ma.aikata direct gidansu ya nufa
Ta babar kofa ya shigo ya tsayar da motar a wajen da ba na parking ba ya shige direct bangaren hajia kaka domin ya san suna can warhaka

Tunda ya shigo da salamar da iya shi ya san ya yi a lebensa suka tsura masa ido suka tsayar da hirar fa suke

Hafsat!
Ya fada da kakausar muryar sa

Da sauri ta kallo wajensa ta mike tana amsawa cike da nutauwa domin baya kiran sunnanta gatsau haka sai da dalili

Bai baiwa kowa fuskar musu ko wani tambaye tambaye ba ya ce" ki mike ki dauki kayanki, ke da Humaira direba ya kai ku sabon gida

Yana gama fadar haka ya juya tamkar zai tashi ya fice ya yi bangaren su inda suka raka shi da kallo

Hajia kaka ce ta ce" lahaula wala kuwata yau na zo zamani da uwa ke tsoron danta

A tare suka juyo da Momy, Hafsat da Humaira wa.inda suka mike cikin gagawa dan bin umarninsa

Momy ta ce" hajia wani irin tsoro kuma?

Hajia kaka ta karkace baki ta ce" eh man, tsoron Sudais kike, yaushe zai shigo mana zikau ba salama ba gaisuwa ba ya kuke ya bamu umarni kuma a mike ana zanzana a je a aikata

Hafsat ta saki yar dariya tana kallon hajia kaka ta ce" to ke mai ya hana ki yi masa tsawa kakus?

Hajia kaka ta ce" ni ba tsarar yaro bace, ni na haifi ubansa kinga kuwa nai masa rata, bana son ina yawon yi masa magana dan kar ya raina ni, ke kuwa dan ubanki kika kuma ce min kakus muhammadu ne zai yi mana shara.a

Momy ta girgiza kai ta yi gaba

Yau kam samir har cikin banban falon Sudais yana bin Sudais da kallon mamakin irin masifar da yake zazagawa tamkar ya ari baki ya kasa zama waje daya sai kai kawo yake

Ci gaba ya yi da fadin" ita ta isa? Wacece ita? Mai take takama da shi? Ya tsayin tsaurin idonta ya kai? Ni da na yi yawon duniya ai ba gwada min kyau zatai ba domin ba irin wada na gani! Ni har zata buda baki ta furtan bata so na? Nine ma bata so? Ni? To sai me? Mutuwa zan yi ne? Nima bana sonta na daina son ta kuma dole sai ta zauna da ni, sannan walahi sai na kara wani auren ta zauna ta ga yanda mata suke rawar kafa a kaina!

Samir ya dago ya kalle shi, bai iya cewa komai ba sai shiru da yayi aman a kasan zuciyarsa fadi yake akoy aiki aure kuma?

Sudais ya katse shi da fadin" ka je da kanka ka dauketa ka kaita vila gra, kafin ka karasa ka tabatar an kara gyara mata wajenta, a zuba dukan abinda zai sakata nishadi,

Da mamaki ya kuma kallon sudais, aa shi kam baya gane inda yake nufa a duniya, yanzu ya gama hargowar ya tsaneta kuma yana fadin a kara kawata mata wajen da ko yar president zata ji ya yi mata 100/100, gannin fuskarsa a hade ya sa ya mike daidai su Humaira sun shigo dan ta dauki hijabinta, ita kam murnar kauran nan take domin kuwa gidan nan a ce gidan mijinta ne ta faso fa, ta mugun faso sannan daman ya shaida mata ba abinda zata kai idan an tashi kaura ya zuba komai tun daga kan kayan daki kicin da sababin suturu

Da murnarta ta dauko hijabinta ta fito direba ya dauke su sai Gra


Da salama ya shigo gidan yana kwalawa, da kyar ta iya mikewa ta fito sai gannin Samir ta yi

Da dukawa ta yi tana gaisar da shi ya amsa yana fadin ta mike ta mike

Cike da girmamawa ya sanar mata umarnin ogansa kan ta fito a kaita gidansa

Da tsoro ta amsa ta juya dan kwaso kayanta

Dakatar da ita Samir ya yi ya ce" Hajia ya ce ki bar komai a nan

Murya a raunane ta ce" aman bawan Allah gadona da kujeruna da labulayena fa?

Samir ya yi murmushi ya ce " za.a kawo maki hajia yanzun dai mu tafi

Dakin ta kala da kyau, da wayarta a ciki wace da zata taho ta baiwa aisha numberta duda basu nemeta ba aman tana son rikewa ko zasu neme ta? Sannan ina za.a kaita ne haka? Ko har zai fara gabatar mata da niyar tasa na kuntata mata?

Idannuwanta ta lumshe bayan sun dauki hanya sabon hawaye ya tsiraro mata daga kurmin idonta a ranta ta furta " ALLAH KA CECE NI YA JIKAINA YA ALLAH



*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




31


*aa fa reader, comment dinku baya gamsar da ni, ba yawa a gaskiya na raina🤦‍♀, idan bai karbu bane nvl din nan sai na dakatar nima na yi uzuririkana😌, raina baya son rashin kula😁 so plz comment woh? Albishirin ku kawai yawan comment dinku tabatuwar typing wato nxt page in sha Allah😍😍😍😍*





Tafe suke ta jinginar da kanta jikin madubin motar, abinka da rana fu irin sanyin motar sai da take jin dan zafin ranar a gefen fuskarta da ta kara jikin madubin

A haka ta lumshe idannuwanta ta tafi duniyar runani wanda motar ke sheka gudu aman ita bata ganewa

Lumlumlum ta ji ba ranar, sai kuma ta ji wata iska mai sanyi tana dan buso mata da kanshin shukoki

A hankali ta bude idannuwanta a dan lumshe ai bata san lokacin da ta ware su dar ta bi wajen da suka shigo da kallo

A tsorace ta waiga baya sai ganni ta yi sun shige wani irin get a cikin wani waje ne suke

A matukar tsorace ta ja da baya ta kali gefen da Samir ke zaune daga gaba, tsoro ne ya kara kamata murya na rawa ta ce" Mmalan nan kuwa ina ne? Ina ne nan?

Samir da ya lura da yannayin firgicin da ta shiga ya ce" sorry hajia, ai nan ne gidan

Ido ta zaro ta ce" gidan wa??

Samir ya dan rage gudun ya dan juyo gannin sai juye juye take ya ce" nan ne *GIDAN KI* wato *GIDAN MIJINKI ELHAJ SUDAIS UBAN MASU GIDA*

Wani yawu ne ta ji makwad ya fice mata ta makogwaro ba tare da ta shirya ba, har yanzu bata samu nutsuwa ba, what? Gidannan? Gidan da zata zauna na dan lokaci? Wannan gidan dama akou shi a kasar nan? Aman ya haka shiru sai jibga jiban dawissu da ake kiwo suna ta baza fifike sun fi karfin irgenta masha Allah, sai aku kuturu da ta hango can wani gefe suma masu dan yawa,

Motar ta ji ya taka hakan ya sa ta bado hankalinta wajen sa

Fitowa ya yi ya bude gefenta ya ce" bismillah

Ta jima tana adu.a kafin ta yi tawakli da Allah ta fito jikinta a matukar mace sai kara kallon gidan take tamkar sabon shigowa birni

Aman ya aka yi na ga abubuwan kiwo? Bana gannin mutane? Ina mai gadi?

Samir da ya kunnawa Sudais komai tun zuwa daukota yana sauraron su ta karamar wayarsa ya ce" ba mai gadi, get din na anfani ne da command,
Akoy ma.aikata sosai suna can bangaren su na maza daban na mata daban, sun bi umarnin oga ne na baya so suna yawace yawace har sai ya zauna, sannan wannan tsuntsayen ba su kadai ne yake kiwo ba, akoy kayan kiwo sosai a gidan an jejefa su ne bisa tsarin oga

Shiru ta yi tana biyar bayansa har ya zo daidai wata kofar gilas wace ba.a gannin na ciki sai dai na ciki yana gannin na waje sosai, irin gilas din nan ne da bulet baya ratsa shi sannan duka baya yi masa sai wani ikon Allahn ke kashe shi

Jikin mabudin Oga ya fada masa wajen da zai danna ya budu dan haka ya danna ya bude ya tura da dab karfinsa domin nauyin tsiya ne da shi

Ita kam ta yi shiru biye kawai take da shi a baya

Suna shiga ya yi salama

Su Hafsat dake zaune suka amsa shi suna kallon wajen su

Kanta a kasa hakan ya sa Hafsat bata gane ko wacece ba

Humaira kuwa cike da gadara ta ce" wannan fa? Mai aiki ce ko me?

Samir ya yi dan murmushi a kasan zuciyarsa yana ayana zaki fada ne wannan ta fi karfin ikon nan naki da kike yi mana dan kina matar mai gida tamkar kece mai kudin kina yi mana abubuwa tamkar wasu karnukan ki!

Samir ya ce" aa, ba mai aiki bace,
Daga haka bai kara ba gudun kar oga ya tsawatar masa domin ko daya baya bari a raina masa iyali ita kanta tana wulakanta su ne bayan idannuwansa domin itama bai bata damar ta wulakanta su ba, su kuwa sunai mata biyaya ne domin maganarta ta fi tasu tasiri a wajensa duba da darajar da Allah ya yi mata na zama matarsa abinda ya fi kisanci da shi a gidan duniya wato matarka ko mijinki

Yatsina fuska Humaira ta yi, ita fa har ta gama cinyewa sai cin magani take tana kakauda kai ita ga matar Elhaj ta sha wani uban lesh baki ya kara fitar da hasken fatarta wly har kashe ido yake ta yi bau da ita aman kana yin kusa da ita karni zai kore ka ta ce" malan idan ba mai aiki bace ai sai ka jata ka koma da ita dan baya nan bare ka kwaso wata mai datin budurwarka ka kawowa mutane!
Ta karashe ta a dan daga muryarta

Jin abinda ta ce gaban Rauda ya kara faduwa da dan tsoronta ta dago dan gannin matar tasa ce? Ko matansa domin murya bibiyu take ji ta mata


Hafsat ce ta dan kwalalo ido gannin Rauda, da murnarta ta mike ta nufo wajen Raudar ta ce" Lah, lale da yar uwata, auntyna

Rauda ta sauke ajiyar zuciya domin har ga Allah irin yanda Hafsat ta taso har ta fara kokarin buya a bayan Samir dan ta yi tunanin ko dukanta zata yi? Rauda ba dai tsoro ba

Dan murmushin da bai kai zuci ba ta yi tana dari dari ta dan rike hannun Hafar kamar yanda itama ta rike ta tanai mata murmushi


Auta wacece ne? Ban ganeta ba
Humaira ta fada itama ta mike tana karasowa tana bada hankalinta wajen su tare da fatan ba wata ta jiki bace sosai kar ta je ta fada bata yi masu tarban kirki ba


Aunty, Aunty amarya ce fa, Hafsat ta bata amsa fara.a konce a kan fuskarta tana jan hannun Rauda dan ta karasata wajen makamakan kujerun falon wa.inda kala har hudu ne maka maka saiti hudu an mugun tsara su kalar tsanwa mai duhu da fari haka labulayen ma sun yi kala daya da kujerun sai wasu tafka tafkan tableau kwaya shida an jejefa su da wani tafkeken zanen zaki da akai a jikin bangon wanda sai ka rantse mai rai ne domin an yi shi ne da komai irin na ainahin zakin na gaske sai wata tv wace da ba dan tana haska hoton namomin dajin da suke kallo ba da sai ka rantse ba zai yiwu a yi tv mai girma irin nata ba tamkar a cinema ta cike bangon gaba daya sai wasu tafka tafkan Peau de fleur kwaya biyu farare kar sai dan kyalin tsanwan da suke an ajiye su gefe da gefen tvn wace du tsayinta sun kai daidai tsayinta ( uhum wasu kayan sai amale ) sai abin turaran wuta mai kalar dawisu an baza fikafikensa wanda ta nan hayakin turaran ke busowa a hankali an saka su har kwaya hudu a kowace kusurwa ta dakin
Sai capet mai kamar shukar ciyayi an tsara shi tamkar zanen mutun an zagaye shi da fari farin ciyayi a tsakiyar kujerun nan bai cika tsakiyar ba sai ya kara haska tiles din falon fari kar mai dan Garza garza, sanyin ac din palon ne ya saka ta dan kara kankame hijabin dake jikinta sai wani sanyin kamshin da ma.aikata ke kula du mintuna sai sun dawo sun jona sun saka turaran wuta sun fesa na ruwa mai sanyin kanshi


Humaira ta ce" eyah, ai ban ganeta ba Auta, wace auntu amarya? Ko na ce ta ina?

Hafsat ta ce" kai Aunty, ta gidannan mana matar yaya

Jin maganar Hafsat ta yi tamkar saukar aradu a tsakiyar kanta, kuturun uba, matar wa? Ba yace sai an yi adu.ar matarsa zata tare ba? Wai ma ina wa.inda suka rakota? Sannan wannan yar kauyen ce ya aura? Me ke damunsa?

Bata ankara ba sai gani ta yi Hafsat na kokarin zaunar da Rauda saman kujerar falon

Da mugun tarashi ta furta" ke hafsat kar ku karasa kar ku saki ku karasa

A tare suka ja suka tsaya da dan alamun tsoro a tatare da su don kuwa ita kanta hafsat ta yi tunanin ko wani abin ne ta gani

Da sauri ta daga kafarta ta karasa wajen su, hannunta ta kala da mugun kyankyami ta kama gefen hijabin Rauda ta jawota kiiiiiii har daidai kusa da Samir wanda yake tsaye da mamaki yana kallon lale Humaira ta samu fada a wajen oga aman bata san darajar Mata ba

Cika ta ta yi wanda har Rauda ke dan haki na mugun saurin da ta yi ta biyo bayan Humaira da kuma bugawar da zuciyarta ta yi na tsoron me haka kuma?

Humaira ta cika hijabin tana nuna kyankyamin hannunta ,
Taku daya biyu uku ta yi ta dan zagaya Rauda tana dan tafa hannayenta,
Wata dariyar tabara ta saki irin na an goge din nan ta ce" ke? Ke ce kishiyata? Lale na yarda kadara da rubutun tun ran gini tun ran zane! Bakar kadara ta kawo ki auren mijina? Sannan abin mamakin kin tare ke kadai ba dangi hakan na nuna min an gama sannin juna tun a kofa?

Da sauri Sudais ya rintse idannuwansa domin du abinda ke faruwa a kunnansa, mamaki, da al.ajabin dan adam ne ya kama shi , shi? Shi ne Humaira ke jifa da kalaman nan da zargi? Sun gama sannin junna? A tunaninsa irin yanda ta san ko shi waye ciki da bai ba zata iya yarda ta furta wannan kalmar kansa ba, murmushin takaici ya saki yana ayanawa ransa ya sani ba zai yi shaidar Mata ba, aman zai iya shaidar kansa, um ita Humaira ta sani ne da ace mata nake bi da bata layin macen da zata wanken takalmina bare har ta san sirinA nonsense kawai

Katse masa tunaninsa ta yi inda take fadin" ki sani, ni Humaira sai na zame maki jaraba masifa balakin da zai saka ki hadiyi zuciya ki mutu a tarar da gawarki! Mijina nawa ne ni kadai , ke koda zan raba shi da wata sai yar masu fada a ji ba wai ke ba yar talakawa! Dan haka hanyar da ta kawo ki ta maida ke inda kika fi wayo

Haba Aunty, menene haka kike yi wai? Tamkar marar ilimi?
Hafsat ta furta domin Rauda ta bata tausayi irin yanda take hawaye kanta a kasa tamkar ta yiwa sarki karya ita kuwa Humaira sai kara hargowa take tamkar tanaiwa yarta fada
Sam abinda ta yi bai baiwa hafsat mamaki ba domin ta santa da rashin kamun kai zata iya yin fiye da haka

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login