Showing 42001 words to 45000 words out of 122108 words

Chapter 15 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

422

fada tana kallon direban da fuskar sa ke kallon wajenta aman idannuwansa a sade

Kansa kawai ya iya daga mata alamar eh sannan ya yi mata nuni da hannun sa
Da mamaki take kallon sa, a ranta ta ayanna" wayo bawan Allah ashe kurma ne, aman yana ji, to aman ya aka yi ya hada ni da direba kurma? Wani irin tuki zai yi?
Kafadunta ta daga ta dan yi murmushi ta ce" aa ke kuwa Rauda ai yana ji yana kuma gani maidawa ne baya yi dan haka zai ji hon din wani sannan zai gani, komai dai sai Allah ya yarda dan haka Allah kare mu

Shiga motar ta yi ya ja bakinsa gum bai furta ko a ba

Suna zuwa ga mamakinta zarcewa ya yi, masu tsaro basu wani tare shi ba, aka wangame masu get motar ta shiga da su, sai da ya kaita har bangaren da zata hau ta nufi office din su ya sauke ta,
Ta sauka tana al.ajabin wannan mutumin da aka aura mata ko waye ya yi mata farin sani, dan ba zai ce mahaifinta ne ya fada masa wajen aikinta harma da kofar kofar aikin nata domin shi kansa bai sani ba

Shi kuwa direban yana ajiye ta ya juya wajen samir dake tsaye kusa da motarsa yana kara jadadawa cewa idan ta zo kar wanda ya hana ta shiga da irin shigar nan tata umarnin oga! Domin a ma.aikatar ba.a shiga da irin wannan kukuf din ko da nikaf dan gudun mugaye

Yawa Adahir fatan ka kula da dokokin oga

Wanda aka kira da adahir, wato direban Rauda ya yi murmushi da mamakina ya ce" haba Elhaj, ai koda cewa aka yi na yi tuki a konce zan yi balatana wannan ai a kurma ma ta dauke ni kuma insha Allah ba zan taba yi mata magana ba kamar yanda oga ya hana ( to ka ji)


Malan Ahmad ne zaune kasan shukar maina , faskarensa gefe ajiye, sai bakar ledar da ya anso shinkafa da wake lwajen laure mai tuwo ya tisa ledar ya kasa ci" a fili ya furta ko mai zasu ci yau?

Ajiyar zuciya ya sauke ya dago hannun nasa na dama dan cin abincin sai dai ya tsaya tamkar an tsayar da shi ya tsurawa hannun nasa ido, a fili ya furta" da wannan hannun ne na mare ta! Da wannan hannun na mare ki Mariamna, kin ga kin ja na kaucewa wa.azi cewa idan matarka ta bata maka rai har ka yi niyar dukanta ka dake ta a bayanta (duwawunta) dA karan tsintsiya aman ke kin saka na gabza maki hannun gardi ko? Na biyu kin ja na taba lafiyar jikin ki wanda har wajen adu.ata nake rokon Allah ya bani ikon gama rayuwana ba tare da na taba lafiyarki ba ko? Mariamna kin ja na hukunta baiwar Allah, har na shiga zulunmin wani hali zata shiga? Shin mutumin nan mai kudi ba zai wulakanta min Raudana ba? Mariamna ya fuskar ki? Fatan bata haye ba? Kin ga kin saka na zama abinda ba haka nake ba, aman dole na hukunta ku, dole na nuna maku ni na san darajar kaina!

Can kuma ya js numfashi ya ce" Raudana, Allah ya baki farin ciki mai dorewa, ya sa halayen ki na kwarai su zamto silar shigar ki farin ciki, ya sa kar ki canza hali har zuwa kushewar ki..........


Tana shigowa mai goge goge wato Rabilu ya gaishe ta aman kansa a kasa
Da fararan idannuwanta take kalon sa ta amsa shi muryarta a shake , ta juya da niyar hawa matatakalar da zai sada ta da office dinta sai dai da mamakinta sai ya nuna mata accensaire🤨 din Elhaj Sudais ya ce" *HAJIA* an bar salahun idan kin zo ki daina bi ta nan ki bi ta cikin nan ya hauda ke, sabon tsarin da aka fido ne

Mamakinta ne ya ragu, duda ta san ba mai shiga sai shi kadai, shi dinma idan baya zagaye, aman jin sabon tsarin gidan ne sai ta juya ta dana ya bude ta shiga bayan ya shaida mata numbe 9 ne daidai office din su a ranta take ayanna " *oh na aunty AISHA sarkin iya yi, ya dai saka muma har mun ji dadi mu tsufa da kafafuwa

Kokowa yake da zuciyarsa tunda ya ga fitowarta ta nufo office dinta, tsale zuciyar sa ke yi tana murnar ta ga abincinta , ingiza shi take da ya fito da gudu ya yi mata oyoyo ya tarbe ta ya rungume ta a kirjinsa ya fada mata *how yake son ta*
Mikewa ya yi da saurinsa da karfinsa ya tunkari kofar office din sa ya kama kamar zai bude , ya koma....
Ya kuma tasowa ya koma ya zauna ya hade bayansa da jikin kujerar ya dafe daidai zuciyarsa dake yi masa kida tammar zata bala kirjinsa ta fito
Tamkar zarare a fili ya ce" haba SUDAIS, kar ka manta da irin yanda ka yi niyar zuwar mata, kar ka manta sai ka san wacece ita kafin ka yi mata tayin so, dan haka ka daina irin wannan bayar da kan naka har ta fahimci abinda kake ciki

Lumshe idannuwansa ya yi, ya yatsina fuska tamkar wani ne ya yi masa maganar sai ya baiwa kansa amsa ya ce" ka gane abin ne zai yi matukar wahala gani ga *MATA* a matsayin matata aman bani da damar nuna mata ? Akoy damuwa domin ina sonta da yawa....
Ya shagwabe bakinsa ya kontar da kansa domin wata muguwar kasala ce ta shiga jikinsa lokaci guda,
Wayarsa ce ta dauki kara dan haka ya bude idannuwansa dake lumshe ya mika hannunsa ya janyo wayar ya daga ya kara a kunnen sa bai yi magana ba

Samir da ya tabata yana jin sa ya ce" oga, Direban ya bi dukan dokokin da ka dora Alhamdulilah ya kawo ta lafiya

Samir ya yi shiru ko zai bashi amsa aman shiru har kusan minti biyu kuma ba.a kashe wayar ba,
Dan haka ya ce" oga ko baci kake?

Sudais murya a can ciki ya ce" samir, ba zan iya wannan tsarin ba, *INA SON ABINA* kuma zan tafi na fada mata yanzu
...

Wata irin zabura samir ya yi cikin gagawar murya ya ce" aa, aa, aa Ka saurare ni kar ka aikata haka , ka tuna dalilin da ya sa ka ce zaka yi mata haka, kar ka manta kana son sai ka ware zare da abawa.....

Samir na cikin magana karaurawar office dinsa ta dan yi kara irin na neman izinin shigowa

Firgigit ya kali saman computersa dan gannin ko waye domin ya shagala bai ga zuwan kowa ba
Mikewa ya yi tsaye hannayen sa suka kwashi bari, muryarsa kanta rawarawa take ya ce" Samir...... ita ce....

Bai tsaya ya ji amsar samir din ba ya.....



*ā£IDAN KA RAINA INDA KAKEā£*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERSāœšŸ¼ ASSOCIATION*šŸ¤šŸ»
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




2⃣6⃣

*MOM KHALEED GODIYA MAI TARIN YAWA ZUWA GARE KI, NA BAKI PAGE DIN NAN KYAUTA KI YI YANDA KIKE SO DA ITA, COMMENT DIN KI NA SAKA NI NISHADI*




Bai tsaya ya ji amsar Samir din ba ya datse kiran, ya zabura ya shiga gyara doguwar jalabiyar dake jikinsa mai ruwan ash kala, ya gyara hiraminsa ya dauki papier ya goge agogon hannunsa mai ruwan ash color mai haske, ya dauki turaran sa dake ajiye saman table dinsa ya kara yiwa jikinsa wanka da shi ya koma kan kujerar ya hakimce ya hade fuska ya dana bouton din dake bude kofar

Sanyayan kamshi hade da mugun sanyin ac ya watso mata wanda duda uwar shigar nan ta jikinta sai da ta ji sanyin nan, ita kam tana mamakin wannan mutumin ko dan yana zaman saudiya ne? Sanyi baya ce masa komai
Muryarta a shake ta ce" morning sire

Bai iya dagowa ya kale ta ba ya daga mata hannu cike da basarwa , aman kasan zuciyarsa yana tambayar sa mura take? Mai ke damunta? Mura? Muryarta a shake ko dai kuka ta yi?
Gabansa ya bada ris, kuka? Kukan me ta yi? Na bata son aurensa ko me?

Takardun hannunta ta ajiye saman table, ta dan gyara muryarta ta ce" sire ga takardun nan

Dago da fuskarsa ya yi cikin wani irin yannayi da rashin nutsuwar jin kalar muryarta ya zuba mata idannuwansa su ba jajaye ba su ba farare ba an yi daidai itama ta kalo wajen sa, wani irin abu take ganni a idannuwansa tamkar mai galla mata harare hakan ya sa ta yi gagawar sada kanta jikinta na kyarma ta fara kokarin kunce nikaf dinta domin ita a tunaninta ko dan nikaf din ne yake harararta

Kasa kifta idannuwansa ya yi daga kanta, har ta cire nikaf sin ta cukuikuye shi a hannunta sannan ta shiga cire safar wanda hakan ya baiwa fararan hannayenta damar bayana
Kanta kasa murya na rawa rawa ta ce" ka yi hakuri, nnnnna , an hana ni yawo ba su ne ka yi hakuri Sire ....tana maganar ne tana cike da tsoron sa, tsoron kar a je ya dauki mataki a kanta sanadiyar saka nikaf a ma.aikatarsa harda safa, hijabin kansa yayi girma da yawa kan ka.idar kampanin

Ajiyar zuciya ya shiga saki, muryarsa ciki ciki ya ce" ki mayar da abinki

Da sauri ta dago ta dan kale shi, ta kawar da idannuwanta tana mai godiya da Allah da ya fahimci manufarta ya taya ta yiwa mijin da bata sani ba biyaya

Takardun ya shiga dubawa yana saka hannu, kasa kasa kuma yana satar kalonta , ta hadu da jikin garun office din kanta a kasa sai murza hannayenta biyu take
A kasan zuciyarsa ya ambata " bata cikin farin ciki
Aman menene dalilin shigarta damuwa?
Karar kofar ya dawo da shi ya kali wajen ya ga Samir ne,
Kallonta ya yi da kyau ya ga ta mayar da komai dan haka ya danna samir ya shigo ya gaishe shi ya ja ya tsaya masa

Kansa ya girgiza dan ya san manufar samir, ya bata izinin tafiya

Da dan sauri ta fice ta shige office dinta, tana shiga ta zauna tana sauke ajiyar zuciya, a fili ta furta" ashe yana da dan fahimta ? Allah na gode maka da hakan bai jaza min damuwa ba dan idan ya nace sai dai na bar aikin bana son abinda zai batawa mahaifina rai

Tana fita ya maido kalon sa wajen Samir, da girarsa ya yi masa tambayar lafiya?

Samir ya sauke ajiyar zuciya ya ce" oga ka ce idan na ga zaka fada mata sirrin dake ranka na yi gagawar tunasar da kai dalilin da ya sa zaka fito mata a ba kai ba dan kar a je ka fada kuma bata zama yanda kake so ba

Sudais ya yi murmushi ya ce" ta saka kayan Samir, ta yi yanda na fada mata

Samir ma ya yi murmushi ya ce" Allah ya sa ta mutunci ce mau halub mutunci

Bayan salar isha.i

Fitowa ya yi ya zauna saman table dinsa, yana amsa waya da chairman suna maganar sabin kayan da zasu shigo a satin nan,

Kwaliya ta sha , iya kwaliya ta fito tana yauki ta nufo inda yake zaune ta zauna ta bubude abinci ta dibar masa nasa ta zuba masa miya , ta suba masa salak gefe ta gyara masa komai abinda bata taba yi masa ba

Wayarsa ya gama ya mika hannunsa ya dauko salak din ya gyara shi ya yi bisimillah ya dan fara ci

Yana gamawa ya sha jus din na kwali wanda shan sa ya zame masa dole

Bai tashi ba kuma bai yi magana ba har ya ga ta gama cin abincinta ta sha ruwa ta yi gyatsa

Murya a kausashe ya ce" jiya kika ce na sake ki?

Da sauri ta dago da kanta gabanta ya mugun fadi, ita ta san daman ba mantawa yayi ba, kamar yanda ya saba ne idan sun bata masa rai baya magana a lokacin sai ya kwana , wani lokacin har sai ya yi tamkar ya manta sannan yake taso maganar dan kuwa gaskiya ya fiya bin dindigin abu
, ta tuno yanda suka yi da mamanta a jiya inda take yi mata fada ta ce ai sai ki balo auren ki dawo mu jera, kina gani tunda kika yi aurennan ba ni ba mahaifinki kansa ya daina bautawa gwamnati muna morewar mu mu wanke goma mu tsoma biyar, ai sai na fadawa Elhaj zaki balo auren dan haka maza ya fara neman aiki dan kin san sai an ci abinci za.a rayu banza marar tunani, ke bai sake ki har ke zaki nemi saki? Kar ki manta daga gidan kara muka koma na bulo, wuta ruwa yan aiki salary na du karahen wata sai managensa ya kawo mana , ki ce na fasa kuna ac dan na kusa daina sha na dawo zaman rana banza ,

Firgigit ta yi ta kalo shi, ita kanta a yanzu ba zata iya zama wajen da ba ac ba dan ya saba mata rayuwar luxe

Murya na rawa ta ce" ka ka yi hakuri dan Allah

Tsareta ya yi da ido, can ya yi kwafa ya mike,
Har ya fara tafiya ya dawo ya ce" momy da dady ne kadai suke da wannan pride din ba ke ba, u'r my wife ba mom dina ba so be careful!

Yana gama fada ya juya abinsa ya tafi ya barta da ciza yatsa

Malan na bata ambelope fara da sako wanda ya shaida mata inji mijinta, ya juya da niyar barin gidan

Da mugun sauri ta biyo bayansa har tana tuntube ta ce" malan, malan , malan.... dan girman Allah ka saurareni

Cak ya tsaya ya juyo yana kallonta,
Ji yake tamkar ya shekara bai ji muryarta ba, Allah yana gani tun baya sonta har ya dawo ya fita sonta aman halayenta suna neman mayar da shi wani kala

Malan ya haka? Jiya baka kwana gidannan ba, yauma kana faman ficewa, da alama fushin nan naka na neman sakaka ka sabawa Allah , kar ka manta hakokinmu dake kanka

Murmushin takaici ya sakar mata, wai shi zata fadawa haka, shi da ya san wannan shirmen zata fada masa ai da bai tsaya ba, hannayensa ya watsa ya ce" kinga kuwa bai shafe ni ba, hakinki bani da shi, kin ga ni talaka ne bani da abin baki, dan haka ki je wajen yar uwarki ta ciyar da ke

Yana gama fada ya fice yana nema mata shiriya a cikin ransa (mata , wani lokacin mu ne masu jazawa kanmu damuwa, mu ke koyawa mazajen mu muguyen halaya, idan sunai mana kokari bama gani har su dawo su daina! Uhum Allah ka sa mu dace)


Wajen Raudat ta koma, wace ta yi wanka aman jikinta har yanzu dumin suturar da ta wuni da ita bai bar jikinta ba, ita har ji take gumin na fita da wani laushin fatarta ( sirrin lulube jiki, bayan bin umarnin Allah da mazon sa, kare mutunci a cikin al.uma, samun daraja, harda gyaran jiki domin fatar ki ba zata bushe maki ba!)

Mama ce ta shigo ta ce" wai ni Rauda menene Malan ke shigo maki da shi?

Ta dan kawar da fuskarta ta ce" sako ne wai daga wajen mutumin da ya aura min

Aisha ta ce" hum mama wai kin ga magangannu na rashin mutunci? Ko waye wannan mutumin bashi damutunci magangannu haka gatsaigatsai

Rauda ta kallota da mamaki, ta ce" Aunty, ke kuwa a ina kika ga haka?

Aisha ta ja tsaki ta ce" daukowa na yi a cikin kano ta yi zahin ki, na karanta dan na ga harda su letter may be wani baban ne sai dai na ga lettern da hausa na ga javaliyan magangannunsa na yaga ta

Rauda ta girgiza kanta ta mike da ambulope din ta daina budewa danma kar ta kuma saka mata ido, ta lura sai fa ta jajirce zata samu damar yiwa mahaifinta biyaya dan kuwa idan dai zata ci gaba da sauraron su Aisha ne ba zata ga da kyau ba

Da asuba ta buda ambelope din ta duba, sai da gabanta ya fadi domin sababin yan dubudubu ne har ashirin,

Da sauri ta mayar ta rufe jikinta na kyarma ta dauko takarda da alkalami ta zauna ta yi rubutu kamar haka


" *YAR SADAKA CE*
Sannan ta saka a leda ta zauna har gari ya waye ta baiwa abanta ya ba mutumin nan, tap ita ina zata shiga da kudi har haka? Ya Allah ka sa ba wani mugu bane wannan bawan Allahn

Yauma kamar jiya shigowa ya yi ya leka su, da Sauri Rauda ta duka ta baiwa mahaifinta ledar kanta a kasa bata iya cewa komai ba dan nauyin ta cewa babanta ya kaiwa mutumin nan sako take ji

Murmushi ya yi ya juya da ledar ya fita, Samir dake zaune yana jiran fitowarsa ko da sako ne ya karbi ledar yana godiya ya juya

A layi suke suna shiga office din da ake biya masu dauka a nan , wasu kuwa an zuba masu a account din su har sun sami alert,
Tana faman ta yi ta gama ta fito Basma ta shigo tana ta murmushi ta zauna tana ambata Wash na gaji da yawa

Rauda ta kaleta da murmushi a fuskarta ta ce" ai shi yasa nake so idan an dan rarage sai na je na karbo nawa,

Basma ta yi murmushi ta ce" ai ga naki, an karbo maki

Rauda ta kaleta , tana shirin tambayarta wa ya karbo mata sai ga Aisha ta shigo da murnarta

Zama ta yi gaban Rauda ta nade kafafuwanta ta zazago kudin daga jakarta fara

Ido Rauda ta zaro bakinta har bari yake ta ce" sisister wannan uban kudin fa?

Aisha ta mike ta shiga kwaso shoki tana juyawa ta ce" dubu na gugar dubu sai da aka bani dubu dari da hamsin, tawa , ta kaina🤣, ni kam na daina.karatun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login