Showing 111001 words to 114000 words out of 122108 words
Chapter 38 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
tsayan nan ta kasa cirawa ya rike hannunta na dama
Abinka da muryar sudais bata da sirri sai dai kawai idan yayi magana a wajen da ba za.a ji ba....ya ce" da zafi har yanzu ko?
Rauda ta yi luuu da idonta da take ji yanai mata nauyi dan tsabar haushinsa take ji, aa ba zafi da yake ba mutun bace ni
Ta fada a ranta aman a fili fuskarta ya nuna da cikin ranta a bace yake sosai
A hankali take kokarin kwace hannunta daga cikin nasa shi kuwa yana kara rikewa so yake ya taimaka mata ya kaita dakin aman ina ran Rauda ya gama baci bata san lokacin da ta ce" ka cikani
Malan ka cika ni! Ka cika ni nace, ka kama hannun matar so ba ni ba, ni ba zan iya zama a wajen da ba.a sona ba! Wly ba za.a kasheni da yarintata ba na zauna ana yi min gori kulun kwannan duniya gidanmu zan je
Ke ki je din! Sudais ya fada cikin karaji da daga murya wanda ya saka gaba dayansu sukai shiru suna kallonsa
Cika hannunta ya yi ya nunota da yatsa ya ce" idan kin bar ni sai me? Idan kin yi nisa da ni sai me? Hakuri zan yi, na iya rayuwa ba ke Rauda,
Har sau nawa zan nuna maki irin tarin son da nake maki ya fi karfin na kamanta shi da yayatu na baki sai dai na aikata shi ki karance shi a aikina zuwa gareki?
A tare suke kallonsa, Rauda na yi masa kallo mai cike da soyaya, Hafsat na yi masa kallon shikennan yau ya fada hankali zai konta tana mai matsanancin jin dadi, Humaira na yi masa kallon tsoro, tsoro ya dirar mata, yana sonta? Har yake iya fada a bainar nasi du irin girman kansa da nauyin bakinsa?
Sudais ya ci gaba da magana jiki a mace ya ce" ki daina anfani da damar da Allah ya baki kina rikita min lisafi MATA, ki daina abu irin na kananuwan yara mana........
Mata na fada *ina son ki , ina son ki, ina son ki* shikenan na fada kuma za.ina fada maki kulun kin ji? Sai ki yi kokari ki damki damar nan ki bani wahala
Yana gama fada ya juya bai bi ta kan kowace ba ya fice ya nufi gidansu wajen momy
Humaira dake tsaye ta bi bayansa da kallo kirjinta na mugun doka mata
Faduwar gaban nan da ba.a so ne ta sameta ta cira da niyar shako wuyan Rauda ta kasheta ta huta sai dai ji kake dim ta kai kasa sumamiya
Da Rauda da Hafsat a tare suka kalli junna kafin cikin tashin hankali suke nufarta
Rauda ce ta fara juyota ta ga filat ta tafi , hannu ta dora saman kanta tana kallon Hafsat ta ce" na shiga ukuna Hafsat ta mutu fa
Hafsat ta zaro ido ta nufi wajen waya da gudu dan kira....
Tana samun yayanta cikin tashin hankali shima ya bada umarnin kar su tabata gayannan
Kaiwa kaiwa suka yi shi da docter Amina wada tana zuwa ta nufi Humaira ta shiga gannin ta aunata
Dago fa kanta ta yi ta ce" bata mutu ba, ku kama min ita
Sudais kadai ya cicibeta ya sakata a mota aman su Rauda suna ji suna ganni yace su zauna ba zasu je ba
Haka suka kai Humaira asibiti wace kuma wani tashin hankalin jini take zubarwa ta kasanta
Ana zuwa aka shige da ita bayan docter amina ta bada tabacin faduwa kawai ta yi aka shiga baiwa Humaita taimakon gagawa
Sun jima cikin dakin kafin suke fitowa
Docter Amina ce ta kirayi Sudais office dinta
Suna shiga ya zauna hankalinsa du a tashe ya dafe goshinsa yana kallon docter Amina
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" elhaj, jininta ya hau sosai, sannan sanadiyar faduwar da ta yi kan cikinta dan karamin cikin dake jikinta na sati hudu ya zube domin mun yi iya yin mu aman bamu samu mun tsayar da shi ba
Da tashin hankali Sudais ke kallonta, ciki? Ya furta yana kallonta
Docter Amina ta ce" eh haka ciki, ka yi hakuri Allah ya bata lafiya ya maye gurbi da mai zama
Bai iya bata amsa ba sai mikewa ya yi ya nufi dakin da Humaira ke konce
Yana shiga ya tarar barci take, a hankali ya zauna ya tsura mata ido,
Me yayi zafi haka Humaira? Gashi Allah ya bani abinda nake neman ido rufe aman ya tafi?
Ido ya lumshe ya furta astagfrullah, yayi imanin wannan cikin koda ba.a yi haka ba ba mai zama bane zai yi tafiyarsa ne aman sosai ya ji abin a ransa
Farkawa Humaira ta yi da kuka, ta kai dubanta wajen sudais tanai masa kallon tsana
A fili ta furta" ni kake cewa wata kana so a gabana Sudais?
Saidais ya mike ya karasa wajenta da sauri ya dafa hannunta ya ce" ki yi hakuri humaira kar ki kuma dagawa kanki hankali kin ji? Kin ga sanadiyar wannan tashin hankalin har mun yi asarar babynmu ki nutsu kin ji?
Humaira ta yatsina fuska, dan ta kara masa haushi ta kasa dane abinda ke ranta ta ce" ai ji daman ba haihuwar nake so ba a hakama kana wulakanta ni ina da na haihu ja tsufa?
Da wani irin mamaki yake dubanta, kafin ya ji du wani tausayinta da yake ji ya fice masa a rai
Mikewa ya yi ya fice a dakin ya je ya bayar da carte dinsa aka yi regler komai na harkar rashin lafiyar ya shiga motarsa ya tayar ya koma gidansa
Yana zuwa dakinsa ya shiga
Ya jima yana nazari tabas hakan shine ta dace da shi dan haka ya mike ya shirya cikin shigar kamala ya fice a gidan ba tare da ya nemi kowace a cikinsu ba
Bai zame ko.ina ba sai wajen alwalin Humaira.......
😌
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
6⃣1⃣
*tsaraba*
Ki samu gyadar miyarki kwaya goma idan yin farko.ne, ki dake su lufluf ki dafa kwai kwaya biyu ki yanyanka a ciki ki samu lafiyayiyar zumuwarki ki hada ki cakule yayi tamkar kwado ki cinye ki side kwannonki idan lokaci yayi ki je turaka kawai! 😉🙃😇 sai kice Allah ya sakawa ummu lalla da alkhairi🙈
Tunda ya fara magana cikin nutsuwa da zaro kalamai malan Ahmadu ke girgiza kai yana tir yana mamaki yana tunanin du yanda ake ciki iyayenta basu san da haka ba,
Kunyar Elhaj Sudais ce ya ji ta rufe shi, ya rasa ta ina zai fara har gashi mai aukuwa ta auku wato ya yanke hukuncin da dole a dube shi tunda sai da yayi dogon nazari
Cike da kunya Malan ahmadu ya ce " ka yi mutunci, ka yi kawaici, ka yi hakuri, ka nuna fushi aman da alama yarinya hata san inda aka nufa ba, na yi mamaki, na ji kunya da jin wannan lamari da wai AISHA HUMAIRA ke aikatawa a gidan miji,
Shin iyayenta basa nusar da ita ne ko kunnen kashi ne da ita?
Ban san ta ina zan faro baka hakuri ba Elhaj sai dai nace ka san yayan yanzu ka haife su ne baka haifi halinsu ba
Ka yi hakuri kuma za.a yi yanda kace din in sha Allah
Shima yana matukar jin kunyar datijon domin ya san mutunci , bai so ba kwatakwata bai so ba ta kai su ga haka da ita aman sai da ta kai shi bango, mijinta ai ba tsaranta bane....ko a shekarar haihuwa ya tabata ya bata mai yawa aman sai tana yin tafiyar rayuwarsu tamkar bata cikin musulmai ma bale a yi maganar musulma?
Bai iya kara komai daga haka ba ya mike ya yiwa malan Ahmadu alkhairi na mamaki kafin yake juyawa gwuiwa sace ya bar gidan ya kama hanyar ma.aikatarsa .........
Yana son zuwa ya daidaita wasu lamuran ne
Tunda ya je yake aiki, bai samu ya tsaya ba sai da ya tabatar ya daidaita komai yanda yake so ya kwashi wasu takardu ya rufe office din ya fito ya shiga mota suka yi da samir su hadu gida
Bai zame ko.ina ba sai aeroport ya je yayi abinda ya yi ya karasa gida
Yana zuwa bai neme su ba ya tsaya da samir suka gama tataunawa kafin yake tafiya shima ya shige gida
Dakinsa ya je ya konta ya rufe ya kashe komai yayi tsai da ransa
Wayoyinsa ke kuka tunda ya fice ya kai dubansa gannin momy ce kira ba adadi da maman humaira wanda yayi imanin humairan ne ke kiransa da wayarta ,
Kiran na momy ya daga ya yi salama
Momy ta amsa cike da datako ta ce " uban masu gida haka aka yi kuma?
Sudais ya yi tsam kafin yake cewa" hakan shine daidai Momyna
Momy ta gyada kai, zata yi masa magana aman sai ya sauko domin bai iya fushi ba bata so ta tirsasa shi a yi abinda bai dace ba,
Nan yayi mata doguwar salamar da ta sha mamaki ta yarda lale fa ya dauki abin da zafi da yawa
Karfe takwas na dare suna zaune a falon Rauda suna cin crepe haka da chocolate ya shigo dakin
Kokarin mikewa Hafsat ke yi ya ce" ki tsaya dauko mata abinda zata bukata na hanya kawai sai ki je Samir ya kai ki gida
Da mamaki Hafsat ta amsa da toh aman bata tsaya wani tambaye tambaye ba domin fuskarsa bata bata damar hakan ba
Rauda kuwa tsai ta yi tana mai kallonsa, so take su hada ido aman bai yarda ba, ransa a bace sai ta ji wani irin sanyi sanyi na ratsata tamkar bata da lafiya
A hankali ta mike da nufin nufarsa aman sai ya shigeta ya barta nan tsaye ya yi wajen kayanta
Dogon wando ne da 4iga a jikinta dan haka sai ya dauko mata wani hijab zurkubebe mai nauyin gaske mai ruwan blue ya zo daidai inda take tsaye ya saka mata ya kama hannunta inda Hafsat ta bi bayansu da yar jakar hannu
Wata motar ce baka suka shige baya su Hafsat shi kuwa ya bude gidan gaba ya shiga
Rauda gumm kake ji ta afka tunani, tsoro take ina zasu? Karde a je yayi fushi zai mayar da ita gida ne?🤦♀
Basu zame ko.ina ba sai aeroport yana yi yana duba lokaci sauran yan mintuna jirginsu ya tashi
Bai wani yi doguwan ban kwana da Samir ba suka fice yana rike da hannun Rauda wace ke raraba ido tana kallon cikin aeroport din tamkar an sakota sabuwar duniya
Haka suka je aka shigar da yar jakar hannunta da wayoyinsa kafin yake shiga ya je da passport dinsa amininsa ya jashi su je sukai shige da fice aka samawa Rauda tiketin tafiya domin abin na manya ne suka fito ya tarar da uta nan inda ake jiran jirgin
Zama ya yi ya tsura mata ido, ya tabata tanada tambayoyi sai dai baya so, baya jin zai iya amsata a wannan lokacin, bukatarsa ya samu kulawa kawai
Basu kara minti ashirin a zaunen nan ba dad ya zo suka kebe da Sudais suna zantawa wanda Rauda hangensu kawai take Dady sai dan magana yake yana dan girgiza hannun Sudais kafin suke yin salama ya juya
Nan aka shiga haramar tafiya inda suka je wajen da za.a tafi da su............
Tafiyar awa shida ne suka yi, suka sauka a kasar
Suna fitowa Rauda ta shiga raraba idannu daman bata gama rabuwa da firgitar wai ita ta shiga jirgi ba sai gata an diro da ita a wata kasa ta daban
Hannunta ta saka ta damko na Sudais da yake tafiyarsa tamkar kasarsa yana abubuwansa da kuzari
A hankali ya kallota ya ga du a firgice take, tausayinta ya ji ya darsun masa inda ya jawota da kyau jikinsa ya nuna mata wani tafkeken abu dake walwali an rubuta *DUBAI* a hankali take ajiyar zuciya ta samu ta dora kanta saman kirjinsa a haka har ya fice ya je wajen reception ya bayar da takardarsa aka yi enregistrer aka bashi kys din motarsa da ya bari a nan
Ya fito ya baiwa daya daga cikin yaran dake fitar da motocin ya je ya fitar masa da ita fes da ita domin kulawa ake basu sosai da sosai
Sai da ya zagaya ya bude ya saka Rauda gidan gaba kafin yake zagayowa ya shige shima ya tayar da bisimillah ya dauki hanyar mai cike da tsaro ya nufi gidansa dake garin
Rauda kam bata samu bakin magana ba sai da ta ganta a wani tafkeken daki, wanda suna shiga Sudais ya cikata ya zarce wajen bed din ya yi bismillah ya fada a reran tamkar yaro yana mai kai hannayensa ya yaye hiramin dake kansa yana cusa yatsusansa cikin yalwatacen gashin kansa yana lumshe ido alamar ya gaji , kuma yana tare da damuwa
Baki Rauda ta shagwabe tana kallonsa, ita gaba daya tsoron garia take, ita tsoron komai take .......mama take so, wly aba take so
Cike da sangarta ta karasa ta zauna bakin bed din tana dan jan yatsuntsansa ta cuno baki tana ta yi batai magana ba
Sudais da ya samu ya dan kallota ya girgiza kai, a ransa ya kara ayannawa yaro ,
A fili murya can kasa ya ce" kulawa ake da yannayin miji ....koda kana da uzurinka sai ka ajiye daga baya ka bayanna Mata........
Kai ni dai zuciyata a gaskiya a gaskiya batai min adalci ba ehe, bata gannin du abubuwan dake gabanna? Ta tashi ta wani fada kan yar yarinya zaman aurenma sai na koya mata da alama
Rauda ta zaro ido ta mike tana kama kugunta ta ce" me me me? Ni ce yarinyar,,,?????
Sudais dake kallonta ta kasan ido a ransa ya ayanna ta wani fannin ba, aman a fili ya ce" eh sosai yarinya karama ki wani zo ki dameni da tabetaben kafa yanzu kuma idan nace zan tabaki nima ki bare min baki kina janyo min hadisai wai na sowa dan uwanna abinfa nake sowa kaina kinai min wa.azi na ji tausayinki , to ki kuma tabani ki ga yanda zan sakaki ihu a garinnan
Da wani irin kunya Rauda ta juya sumiii sumiii domin yana maimaita abubuwan da ta fada ne a jiya daidai tana c8kin azabar nan
Wajen da take tunanin bayi ne ta fada tana mai jin gajiya tana murmushi kasa kasa kafin a fili ta furta "ina son ka sosai SIRE😉
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
6⃣2⃣
Tana fitowa daga wanka cikin sanda ta zo kusan wata farar riga shar shar da ita wace ta san ita ya ajiyema sannan baya dakin
Dauka ta yi ta saka cikin gagawa kafin take hayewa saman bed din ba tare da ta shafa komai ba domin bata gani ba
Can cikin bacinta take jin yamyamyam jikinta na yi ,
A hankali ta saka hannunta dan kwabe abinda ke bin fatarta domin a baci take jin lalausan abu na bin jikinta
Jin hannunta ta yi ya lume cikin gashi, da sauri ta bude idonta kirjinta na dokawa
A hankali ta furta" wayo Allahna, da zafi kar ka yi min plz sire
Sudais dake ta fama ya samu ya dan dago, a hankali ya karaso ya rungumeta tsam a jikinsa,
Muryarsa har ta canza kala domin daman a kame yake ya ce" ki yarje min MATA
Rauda ta dan girgiza kai ta ce" da zafi *mijina*....... tana fadi ne tana cusa fuskarta a kirjinsa
Wani irin yar ya ji da wani abu marar musaltuwa, a hankali yake kokarin dago fuskarta har ya samu ya dago ya kafeta da kallo, can ya ce " sai na ji kamar kin kirani da mijinki....kenan kin yarda da hakan?
Rauda ta sakar masa murmushi kafin take tataro du wani karfinta ta ce" *mijina*, sannan kuma..
Ta dan yi shiru kafin take saka idannuwanta cikin nasa dar dan ya yarda da abinda,take fada ta ce" *rayuwana, haskena, ruhina ......SOYAYATA*
Yanda magangannunta ke fita dala dala haka su ke sukansa daya bayan dayan tun daga zuciyarsa har zuwa gangar jikinsa, gaba daya jikinsa ya mutu...jin kansa yake a wata duniya, wani farin ciki marar misaltuwa yake ji,
*Kina so na?*
Ya tsinci bakinsa na fadi tamkar sangartacen yaro still idannuwansa na sarke da junna
A hankali Rauda ta ce" *INA SON KA*
Wani wawan riko ya kara yi mata, muryarsa a rikice ya ce" *MAIMAITA , KI MAIMAITA MIN KHALB, KI YI TA FADA MIN NA ROKE KI*
rauda da hawayen farin cikin irin lokacin nan da ta tsinci kanta a ciki ya wanke mata fuska da tsantsar kaunar mijinta da tausayinsa ya sa ta kurumce, ta manta halin da ta shiga a jiya.......ita mai tirr da mata kan wannan lamari sai gata ta yi kundunbala ta kaiwa leben sire sauka da nata, bata tsaya nan ba ta shiga aika masa da sakwonnin da bata san malamin da ya zaunar da ita ya karantar da ita ba sai ganinta ta yi tsundum a harkar tana bada hima
To ya maje zuwa biki bale sarki yayi gaya? SIRE ya tsinci kansa a halin zuru.....ya kasance yayi zuru, ya zama marar wayo sai a jikin yar karamar yarinyar matarsa....Raudansa ta diro masa a lokacin da ya cire tsanmanin da lamarin mata, ta