Showing 18001 words to 21000 words out of 122108 words

Chapter 7 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

406

ma.aikatansa da du suka juyo suna kalonsa kafin suke fara miko masa gaisuwarsu daya bayan daya yana amsawa hankalinsa konce domin kuwa manyan mutane ne , manyan ma.aikata ne na kasa daban daban da na nigeria du wanda ke wajen nan gagarumin mai ilimi ne dan gayu na bugawa a jarida


Coridor din da zai sada shi da ainahin offishin nasa ya nufa wanda a cikin coridor din office din Aisha da na wani mai suna Abdul majid wanda ke kula da computer wajen

Tunda ya tunkaro wajen yake jin dariya kasa kasa wace ta saka shi daskarewa waje guda, da kyar ya ja numfashinsa ya sauke ajiyar zuciya a zuciyarsa yake fadin ke baki isa ba haba, ta ya ke macen ki ringa saka ni faduwar gaba bayan nine namijin ni ya dace na ringa saka ki jin hakan *MATA* ,

Cijewa yayi ya gyara tsayuwarsa ya doshi office dinsa kai tsaye sai dai me yana karasowa suna fitowa

Ja yayi ya tsaya ya shiga yiwa zuciyarsa fada cewa" ki nutsu ki kama kanki, kar ki manta sai mata ta fara furta maki kalmar so kafin ki karbeta, karki manta ke din ta daban ce, ke din ba zaki iya tunkarar wa.innan yan matan zamanin masu halayar rashin kamun kai ki furta masu kalmar so ba dan kwatakwata hakan bai dace da ke ba, ki nutsu fa!

Duda yanda yake gayato jarumta ji yayi yana neman gazawa, lumfashinsa na neman gagararsa
A hankali ya kai hannunsa na dama ya bale boturan da ya saka na wuyansa wanda yake ji kamar ya shake masa wuya a yanzu ya saka hannun yana dan shafa wuyan nasa

Da sauri guard din nasa ya matso cikin harshen turanci ya ce" sir lafiya? ?

Yana kokarin yin magana suka juyo wajensa a tare

Aisha cike da mamaki da farin ciki take kalonsa da wani irin yannayi mai wuyar fasara,
Alkawarin da ta yiwa kanta, abinda ta jima tana jira kennan, wannan rana ta jima tana tsara yanda take so ta zo mata sannan irin abinda zata yi a ranar

Sakin hannun Rauda ta yi wace itama ta yi mutuwar tsaye da gannin ogansu mutumin da ya haukata zuciyar yayarta tsaye a gabansu tamkar a naso shi

Aisha ta daga kafarta tana nufar Sudais, wanda hakan ya hadasa masu faduwar gaba gaba dayansu,
Shi yana mai faduwar gaban ganninsu gashi ga su a karo na uku, Aisha na faduwar gaban abinda ta yi niyar zuwa ta sanar masa wanda ke hanata baci da sukuni, Rauda na faduwar gaban abinda Aisha zata aikata dan karfin hali wa mutumin da ya fi karfinsu wanda hakan na iya sakawa ta jaza masu hasarar aikinsu (idan abin ya tsaya iya aikin ma ai da kyau)

Ja ta yi ta tsaya a gabansa, ta kafeshi da wa.innan idannuwan na mahaifiyarsu masu fizga dan tsananin tsarinsu da girmansu da kyansu, ittafa a yau a yanzu ba sai an jima ba zata amayar masa da sirin dake ranta koda kuwa zai raba gangar jikinta da numfashinta ne

Cikin siriryar muryarta ta ce" welcom *SUDAIS*!

Gabansa ne ya yanke ya fadi da gannin abinda ke shirin faruwa, bai kai karshen tunaninsa ba ta ce" Sudais, *My Sudais* sunana *AISHA AHMAD* ina tsananin farin cikin dawowarka a wannan lokacin, Sudais ba zan iya ci gaba da rike damuwana ba,
Tayi tsai tana sauke ajiyar zuciya ta ci gaba cikin sasarfa ta ce" koda gizo ne kake yi min ba kai bane zan fadawa fatalwanka, Sudais Ka tambayi Rauda, kanwana ce bana iya baci, bana cin abinci bani da sukuni SuDais
Ta kuma kiran sunansa wannan karon cikin sanyin jiki ta ce" *Sudais* wanda yayi daidai da jin bugun zuciyarsa na karuwa

Da sauri ya dago jajayen idannuwansa ya sauke su a fuskarta, ji yake tamkar ya tsayar da ita , ji yake kamar yayi da baya da baya ya koma ya kasance bai bayana a wannan waje a wannan lokaci sannan a gaban *MATA* ba

Katse masa tunaninsa ta yi, ta katse masa lumfashinsa na wucin gadi sanadiyar maganar da ta furta, cike da tabacin abinda take ambata ta ce" *SUDAIS I LOVE U SUDAIS* ka so ni koda bai kai rabin rabin son da nake maka ba, ta hade hannayenta tana kokarin ci gaba da magana
Cike da tashin hankali SuDais ya dora hannayensa biyu a kansa, ji yayi wata irin juwa na neman yarda shi,
Taga taga ya yi ya kusan zubewa da sauri guard dinsa yayi kokarin tare shi yana ambatar subahannalah sai dai Sudais ya daga masa hannu ya dafe bango da hannunsa na hagu
Ji yayi ba zai iya furtawa Aisha komai ba, a daidai wannan lokacin bukatarsa shine ya gansa a gida ya kauracewa kowa da komai ya samu yayi tunani,

Saurin juyawa yayi yana kokarin komawa hanyar da ya fito sai dai kafin ya tabuka wani abin Aisha ta rike masa gefen jalabiyarsa, muryarta na rawa ta ci gaba da magiya kan ya saurareta kar ya tafi ya barta a wannan halin da take ciki dan bata san irin abinda zao iya samunta ba😭


Cikin zafin nama ya juyo ya janye hannunsa kafin ta tantance wani abin ya dauketa da gigitacen marin da ya saka Rauda da Guard dinsa mugun zabura

Cike da tashin hankalo Rauda ta tako da gudugudu ta tare Aisha ta fado jikinta ta riketa sosai sosai ,
Da wani mugun kallon tsana ta dago ta sauke idannuwanta kan fuskarsa wanda ya kusan saka zuciyarsa bugawa dan kuwa da wannan kallon da ta yi masa sai ya gwamace dama mari ta wanka masa

Aisha ta cukuikuye hijabin Rauda ta riko hannun Rauda jikinta na mugun bari, hankalinta a tashe,

Har wata kwallah ce ta tarunma Rauda a idannuwanta, a hankali ta rikw hannun yayar tata murya kasa kasa ta ce" mai ya kai ki kallon wannan mutumin da baya gannin mutuncin wanda ya rabe shi furta masa irin wannan kalma? Aunty ki yi hakuri da wannan soyaya domin bata da anfani

Aisha ta ce" Rauda aa, Rauda ki yi shiru

Shirun kuwa ta yi ta samu da kyar ta kama Aishar suka mike ta kamo hannunta da niyar ratsa ta gefensa su yi tafiyarsu

Idannuwansa ya zaro, domin gaban goshinta gashinta ya fito sosai sanadiyar cukuikuyeta da Aisha ta yi,
A shigowarsa kuwa ya tarar da maza sosai , ba tare da wani dogon tunani ba ya yi gaba da sauri ya fice su yayi waje

Harara rauda ta raka shi da shi sannan ta tsaya tana kara baiwa yar uwarta hakuri


Suna cikin haka Basma ta shigo wajensu , sai ta nuna bata ma san abinda ya faru ba ta ja su cikin office din Aishar, nan ta jawa Rauda hijabinta ya rufe mata gaban goshinta da kyau suka zauna suna tataunawa inda wayarta ta yi ta ringin sai mikewa ta yi ta kara ba tare da ta yi magana ba

Muryarsa a dagule ya ce" bata fito gashinta a fili ba dai ko?

Basma ta amsa sa da " eh na dawo da su office gaba dayansu na rufe masu kansu

Ajiyar zuciya ya sauke ya datse kiran ya kurawa hanya ido inda direba ya sake baiwa motar wuta

A hankali ya ce" Ya Rab, ba itaba, Allahna ba itaba, *MATA* dan me kina tsaye kina kalo hakan ya faru? Mai ya sa baki hana faruwan hakan ba,

Idannuwansa yayi gagawar rufewa dan a lokacin hararar tsanar da ta jefo masa ta kuma fado masa a idannuwansa , da sauri ya dafe kansa yana ta maimaita innalilahi wa.ina ilaihi raj.une.......................



Comment ko?🤧



*ā£IDAN KA RAINA INDA KAKEā£*



1⃣0⃣



Na: *SAJIDA*


Haba sis ba zan dawo ba, ba zan dawo ba aikin nan mun bar shi daga yau ! Rauda ke fada cike da bacin rai da kunyar abinda yar uwarta ta aikata yanzun

Rauda Ta ci gaba da fadin" a matsayinki na mace aunty, mace da aka sani da kunya da jan aji, mace da aka sani da tarbiya da wayo da dabara, haka kawai ki tarbi gaban wannan garjejen katon ki furta masa kalmar so? Aunty ko mazan a yanzu sun daina irin yanda kika yi, su kan yi dabara ne su jewa mutun ta inda zasu samu gamsashiyar amsa ba wai kawai daga shigowarsa ki tare shi ki furta masa kalamai haka sannan ki yi tunanin zai saurareki, kin ga mu yi tafiyarmu sannan mu yi hakuri da aikin da karatunma gaba daya aunty dan kuwa koda bamu yi tafiyarmu ba shi zai kore mu ne!

Da mamakinta Aisha sai ta saki murmushi harda dan sautin dariyarta mai kayatarwa ta ce" lallana, menene? Wannan abin ne ya daga maki hankali kike kai kawo har kike ikirarin mu bar aiki? Idan muka bar aiki ya zamu yi da cikar burikanmu? A ina zaki samo kudin karatun da kike mafarkin yi dan ki talafawa DAD?
Ta dan tsagaita sannan ta dafe daidai zuciyarta ta ce" ni kuwa ta ina nawa mafarkin zai cika na samun muradin zuciyata? Wannan ai ba komai bane lallana, wannan abin da kika gani somin tabi ne, wannan marin da yayi min sister ai farkon sanina ne, sau nawa kika ga an yi haka an ci riba? Na tabata zai bani hakurin marin nan da yayi min

Cike da mamaki baki bude Rauda ke kallonta, can ta ce" kina nufin Aikin nan da muke kina yinsa ne dan ki sami wannan mutumin?

Aisha ta yi murmushi ta ce" burina kennan, ina da burin na sami matsayin da koda bai so ni dan kyauna ba, bai so ni dan Halayana ba, bai so ni domin Allah ba, zai so ni dan arzikin da zan yi , sai Allah ya taimakeni na zo ma.aikatarsa, Lallana duba ki gani wannan daular watarana zan zama matar mai wajen nan? ???
Ta mike tana juyi tana sakin murmushi ta ci gaba da fadin" kin ga zan sayi wuleliyar mota, za.ina daukanki da mama mu zagaya gari, zan je na yiwa su Amina, du sati biyu za.ina leka dubai, zan rushe gidan nan na murje shi , zan sayi vila na zuba talakawa ma.aikata oh sister zan yi rayuwA!

Cike da takaici Rauda ta dauki yar pos dinta ta fito bata kuma furtawa Aisha komai ba ta zo wajen kujeru na cafetaria ta zauna ta zuba tagumi ta fada kogin tunani

No no no , Ya Allah, ya Rab ka farkar da ni a wannan mafarki mai firgitarwa, Allahna ka farkar da ni a irin wannan mafarki domin sam bai dace da ya faru da ni ba

Khairat da ta shigo cike da gajiya ta yi masa salama a gefensa

Dago da kansa yayi, idannuwansa da suka kade sukai jajir ya zuba mata yana mai amsa salamarta

Karasowa ta yi kusan shi tana cewa" Husband lafiya? Me ke damunka? Ya aka yi ka dawo da wuri haka?

Kuma dago da kansa yayi da yake tsananin sara masa, bai iya ce mata komai ba sai mikewa yayi ya cire doguwar rigarsa ya rage masa daga shi sai dogon wandon dake ciki ya karasa wajen da ba moket ya konta kansa na kallon sama jikinsa ma wato konciyar rigingine, ya kai hannayensa wajen kansa ya shiga yin abdomino

A kadan ya yi ya kai sau hansin bashi da niyar dakatawa

Mikewa ta yi , abinka da mai jiki rigar du ta shige jikinta ta ja ta gyara ta nufi firij, ta dauko ruwa Awa, ta dauko kofi na kwalba ta nufo wajensa tana tunanin abinda ke damunsa? Domin hakan na daga cikin dabi.unsa idan ransa ya baci yakan zo ne yayi ta sport har sai an hana shi ko ya ji ya kasa tashi

Tana zuwa a hankali ta zauna a nan kasa, ta jakudo ta daidaici ya dago ta yi gagawar saka cinyoyinta yana dawowa sai kansa ya sauka a saman cinyarta

Kokarin kuma mikewa yayi ta yi saurin rike hannayensa, ta dora dayan hannun nata ta cire masa hiramin kansa, ta shiga shafa masa kansa da kirjinsa tana sauko da hannunta har kan fuskarsa tana shafa sajensa da yayi konce lufluf tana kara yi tamkar tana shafa mage

A hankali yake kontar da kansa har ya sakar mata nauyin kansa, idannuwansa a lumshe sanu a hankali har lumfashinsa ya fara daidaituwa har ya dan dawo normal aman tana iya hango yanda zuciyarsa ke bugawa
Sosai ta yi mamakin abinda ya saka masa damuwa haka,

A hankali ta ce" *yayanmu*

Bai amsa mata ba aman ta san yana jin ta dan haka ta ci gaba da shafa kirjinsa ta ce" me ke damunka ne *UBAN MASU GIDA?*

bai amsa ba dai , itama bata daina shafarsa ba sannan bata maimaita tambayarta ba,

A kala ya kai minti goma da ta yi masa tambayar, a hankali ya miko hannunsa na hagu ya riko hannunta na dama hakan ya bata damar bin damtsen hannun da kallo yanda jijiyoyin wajen birde birde da su, makwat ta hadiyi yawun da ya tsaye mata a makoshi tana mai kara hamdallah da Allah ya malaka mata miji irin wannan

Tunaninta ya katse daidai lokacin da ya dora hannun nata daidai saitin zuciyarsa,

Da sauri ta kai kallonta wajen, tsoro ya kamata, tsoro take kar a je ciwon zuciya ne yake? Sai dai wata zuciyar ta bata amsar da ciwon zuciya ne da ya kasa aiwatar da komai domin kuwa ciwon zuciya ai ya fi karfin tunanin mai tunani

Idannuwansa ya bude ya sauke su a fuskarta wanda ya saka gabanta ya kuma yankewa ya fadi sanadiyar jan da sukayi

Da kyar ya samu ya ciro magangannun bakinsa ya ce" *KHAIRAT, kadara ce, wace na kasa tantance fara ce ko baka, abinda na sani gwagwarmaya ne mai zafi wanda cin galaba a ciki sai an dage da adu.a da kuma hakuri, Khairat ya akayi hakan ya faru da ni? Mai ke shirin faruwa da ni? A tunanina BAN RAINA INDA NAKE BA! Domin ina baiwa gonakina shuka da wadatacen ruwa daidai gwargwado, sai gashi wata kadara wace Allah kadai ya san me zata zame min gobe tana neman dauken natsuwana, Khairat ki tayani da adu.a abinda nake ciki Allah ya bani mafita domin ni ba kowa bane, a gaban wannan kadara nakan kasance sauna sususu wawa marar tunani marar anfani, bani da zabi, nakan rasa duniya nake ko kiyama, ki tayani da adu.a na fi karfin hakan Khairat*


Magangannun mijinta sun saka ta a halin tunani, Khairath ta kasance mai sanyin hali ba kamar Humaira ba, ta kasance mai saukaka abu , hakan ya saka ta sauke ajiyar zuciya domin sai tunaninta ya bata cewar ko kan harkar kasuwancinsa ne? Ta tabata baya son ta zurfafa shi ya saka ya bata abin a dunkule ... hakan ya saka ta jimke hannunsa dake kan kirjinsa da nata hannun ta ce" *bawa baya tsalake kadararsa, du iya dubararka sai ta riskeka, kadara abu ce da Allah yake kadartowa bawansa, kowani bawa da irin jarabawar rayuwarsa, fatanmu Allah subahanahu wata.ala ya bamu ikon cinye jarabawar rayuwarmu, ya kadarta mana farar kadara UBAN MASU GIDA*


Bai kuma furta mata komai ba ya lumshe idannuwansa ya shiga adu.ar Allah ya sanyaya masa abinda ke shirin kuno masa koma ya ce ya kunno masa





*CIGIYA*

*NI SAJIDA YAR MUTAN NIGER INA BADA CIGIYAR LITATAFAINA MASU SUNA DUK KARYAR KADA, BANI DA ZABI, NEMAN NA KAINA, DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA, YAR MAHAUKACIYA.....! DOCUMENT COMPLET*

DUK WANDA Allah ya sa yana da ya taimaka ya turo min ta wannan number *92466605*




*ā£IDAN KA RAINA INDA KAKEā£*



1⃣1⃣



Na: *SAJIDA*


*Cigiya*

*NI SAJIDA YAR MUTAN NIGER INA BADA CIGIYAR LITATAFAINA KAMAR HAKA: YAR MAHAUKACIYA, DUK KARYAR KADA, NEMAN NA KAINA, BANI DA ZABI, DAGA TAFIYA DAUKAR SOJA, DOCUMENT COMPLETE DAN ALLAH WANDA ALLAH YA SA YANA DA SU YA TURO MIN TA WANNAN NUMBER 92466605 NA GODE*





Tunda ta zauna a cafetariar nan bata furta kalma daya kwakwara ba, idannuwanta na kallon waje guda tana tunani, abinda yafi tsaye mata a rai shine du wannan wahalar da suke sha daman Aisha dan kawai ta malaki wannan mutumin ne? Daman ba dan su talafawa rayuwar iyayensu bane?
To aman Aisha tana da hankali kuwa? Mai ya sa take wasu abubuwan? Yaushe Namiji koda dan gwal ne zai daga hannu ya wanka mata mari aman wai ta furta kalmar cewa wai ai ya lura da ita? Irin yanda maza dai ke bin yan mata har su amince masu da soyaya take son yi? Abin nan yana daga mata hankali, soyayar nan da Aisha ke yiwa wannan bawan Allah tana daga mata hankali domin kuwa irin wannan lamari yana iya kai ta ga halaka!

Hajia lafiya kuwa??? SALIF saurayin dake kula da harkar cafetariar wanda du wani abu sai ya biyo ta hannunsa kafin ya je wajen masu girkawa da sauransu , Salif saurayi ne mai ilimi, musulmi ne da ya karanci fanin kicin ya fito chef,
Salif yana da mutunci bashi da raina mutun, sannan akoy adini
Salif shi ke rike da gidansu, saurayi ne bai taba aure ba Allah ya taimake shi ya samu wannan aiki a wajen Uban masu gida

Firgigit ta dawo a duniyar mutane ta yi saurin dan jan kujerarta baya domin sai ta ga kamar ya dan matso kusanta sosai

Salif ya ce" sorry, ai mun tsorata ne domin na jima ina magana baki motsa ba

Raudat bata iya ce masa komai ba sai ajiyar zuciya da ta sauke ta kawar da kanta

Menu na abubuwan da suke da a wajen ya miko mata, kalolin abinci ne wanda a cikinsu lipton kawai ake yi kyauta aman dukan sauran kudade ne domin ko kapicilo sai ka biya dubu guda

Sai a wannan lokacin kanshin wajen ya fara buso mata, sai a sannan ta ji wani irin sanyi na ac na ratsa kashi da bargonta, da sauri ta daga kanta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login