Showing 66001 words to 69000 words out of 122108 words

Chapter 23 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

421

Mutumin da tunda ta ji Aisha nada hanyar da zata ganshi ta makale mata dan kawai idan ta sadata da shi ta kwace mata shi sai kawai su tarar da mumunan labari wai yayi aure? Kuma wai yar gidan sarauta!

Ta fi Aisha hawa, ta fita jin haushin wannan mumunan labarin dan haka ta juya rai bace ta shige motarta ba tare da ta tsaya ji daga Aisha ba ta nufi gidansu dan fadawa mamanta wani mugun abin murnar su ta koma ciki ko kuwa su kai maganar ga abanta shi ya bilowa lamarin ta hanyar da ya dace domin yana daukan kaya a kampanin Elhaj Sudais na shinkafar Niger

Da mamaki Aisha ta bi motar da kallo, a pos dinta naira dari ne kacal wanda ta yi imanin ba za.a kaita gida a hakan ba sai dai bus, ita kuwa ta jima rabonta da hawa bos sai adaidaita ko motar Sarah aman yau ta yi tafiyarta dan ance Sudais yayi aure, lale Sarah tana tayata kishi har haka (sorry Aisha )

Da tashin hankali ta shige gidansu kamar yanda ta saba sai dai yau da kuka wiwi tana fadawa mahaifiyarta da ta taryota cewa wai Elhaj ya yi aure

Daga bayi Aba ya fito buta a hannunsa na dama ya ja ya tsaya yana kallon Aisha, a kasan zuciyarsa yana tambayar kansa wanene wai Elhajin nan?
Ganin Aba ya sa Aisha ta saki mama ta shige daki da dan gudunta

Mama bata yi gigin bin bayanta ba domin har zuwa yanzu ba wani sake mata Malan yayi ba , yana dai kula ta yana fitar mata hakokinta dake kansa aman ba wani sake mata yake kamar da ba

Ya jima nan kafin yake samun tsaftacecen wajen da yake alwalah ya zauna sosai ya yi alwalarsa cikin nutsuwa kafin yake mikewa ya fice a gidan

Sai bayan fitarsa mama ta juya hankalinta ba a konce ba domin daman yanzu suka gama maganar ya barsu su je su ga Rauda da irin zaman da take ko ba ita mamar bama ko Aisha kadai ta je ta ganta aman ya murje idannuwansa ya saka bakin glass dan kar su ga fuska ya furta kalmar aa a barta ta kontar da hankalinta ta gina rayuwar aurenta idan ya ga da hali sai su je

Labulen dakin ta dage ta shiga ta tarar Aisha sai kai kawo take ta hada zufa tana yarfe hannunta ta babarza gashin kanta du sun bazu tamkar sabon kamu

A hankali ta samu ta kamo hannunta ta zaunar da ita bakin katifarta

Hannayenta gaba daya biyun ta rike ta ce" ki nutsu Aishana , dan Allah ki nutsu

Aisha ta dan yo tsai tana kallon mamanta, Mama ta ce" Aisha, suniyar nan na dawo daga rakiyarta tun lokacin da na ga Malan mutumin da du irin badalar da nake kirba masa sai dai ya kawar da kansa bai taba koda yi min ihu ba aman ya daga hannunsa ya sharara min mari tsoro ya kamani, tabas ko waye kai ka yi anfani da damarka, ka riki lokacin da Allah ya ara maka na zama tauraro ko wanda yake fada a ji ka aikatawa rayuwarka da kanka abin alkhairi tun kafin damar ta kubuce maka ka dawo kana bin mutane suna gudunka suna kyankyaminka

Wannan bawan Allah Aisha bai ma san da kina doron duniya ba a sanina ,

Aisha ta wurgowa mama wani kallo aman bata ce komai ba ta ci gaba da kallonta

Mama ta ce" Aisha, me zai hana ki bar maganarsa ki saurari manema auren ki , ki yi aurenki ki yi tafiyarki kema gidan mijinki ki adana kanki ki adana rayuwar ki?

Aisha ta yi wani dan iskan murmushi ta ce" mama, baki gane mai nake nufi ba kennan? Wa cikin samarin nawa kike nufi? Balarabe mai gidan mai kwaya daya tak? Shamsu mai shagon atampa kwaya daya kwalin kwal? Ishak mai siyar da kayan mak up kawai? Ko kamalu dan makaranta? A cikin wa.inda na zana maki wa kike hangen zai gina maku tankamemen gida ya siy maku motoci ku iyayena mutanen da basu wanke nasu iyayen bama suna karkashinsu har yanzu bale a hango nawa? Ni kuwa fa? Sai kawai su zo su aureni a kaini a kimshe a daki , ba wani nishadin rayuwa sai daga gida sai gida mafarkin bai zama gaskiya ba? Haka kike so na kare a yawo a motar haya kamar yanda kike fama?

Mama ta sauke ajiyar zuciya bata karaya ba ta kuma rike hannayen Aisha tana dan masagin irin ta yarda da maganarta din nan ta ce" Aisha believe me da kadan ake baba, dadaya ne zaki ga sun taso cikin kudi sun haye da kudi, da yawa kudin nan mai firgitarwa ana yin su ne daga baya
Sai fa ki ga kin auri mai mugun kudin ya dawo ya talauce, kuma ki auri talakan kun zama hamshakai abin kwatance, shi Allah ba.ai masa wayo, yana yin abinsa ne bisa tsarin yanda ya hukunta
Ki yi hakuri da Sudai....

Kafin mama ta kare maganarta Aisha ta mike da karfinta ta fizge hannunta ,
Kanta ta dafe da hannunta na dama kafin cikin daga murya tamkar tanaiwa kanwarta fada ta ce" haba mama haba mama haba mama, ina biye da ke a tunanina ke din mai sona ce ashe ba haka ba? To mama bara ki ji ni Aisha ko da ruwan balaki sai na auri Sudais domin da shi na dace da zama a gidansa na dace ba wai wasu masu kamo nan hada da nan ba!

Har ta juya zata fita ta dawo wajen mama da ta saki baki da hanci zuciyarta na wani irin dokawa ta ja tunga kusa da ita ta rage murya ta ce" mama, kwarai mai kusi yana talaucewa Aman ba Sudais Mijina ba!

Juyawa ta yi ta fice a dakin
Mama ta kai minti goma na banza tana tunani, dumi ta ji a kuncinta tana lalubawa ta ji hawaye ne, a fili ta furta" wace irin tarbiya na baki Aisha? Wani irin halaya na nuna a gaban idannuwan ki? Tun yaushe na kashe ki da nunin kudi ya fi komai mahinmanci a rayuwa, Aisha Allah fa? Ya Allah ka kiyashe yayana da nadamar rayuwa, ka shiryar min da yarana ka basu dangana ga abin duniya, ya Allah ka yafe min kurakuran da na tafka a rayuwa ka bani ikon yiwa mijina biyaya , ka sanyaya zuciyarsa ya dawo min Ahmad dina

Ta jima kafin take share hawayenta ta mike ta yaye zanin katifar Aisha ta fito ta hada a kayan wankinta

Aunty mahaifiyar Sarah yayar mama wato nana Mariama ce ke kai kawo , can ta lailayo ashar ta afka ta juyo wajen Sarah ta ce" ke dan ubanki du fitar nan da kike, na kai zuciyata nesa na barki da yarinyar nan yar matsiyaci kina yawo dan ki bigi bakinta ki damo yanda zamu samu shiga wajen mai gidan abanki domin ci gaban mu ne gaba dayanmu ke ki aure shi ki zame masa fitilar gidansa sannan uwar yayansa , daga ni har ke Elhaj (wato mahaiffinta) ya daukaka martarbar mu mu yiwa yan bakin cikin mu nisa aman dan iskanci ki shigo min kina tayar da kura ki fdan yayi aure? Na rantse maki ko da boka ko da malan ko da balaki sai ya aure ki, ke ko matansa hudu ba wai biyu kacal ba sai fa ya aureki idan kin shiga mu fitar da sauran

Sarah dake zaune hankalinta konce ta ce" mom na san sai kin kwato min wannan man din, ki gane ko ba maganar kudin ba man din yana ja, yana kawo fire.... mom idan ina shakar numfashi daya da yar yar uwarki ji nake tamkar na shaketa ta mutu, du na bata suturuna dan kar a ganmu tare kawayena su raina ni, aman a gaskiya na kagauta a yi a yo min auren nan da Elhaj baba na ware na bar banza da karnin talauci

Murmushi aunty ta yi ta guada kanta ta ce" barsu da ni suke magana, haka muka taso da banzar yarinyar nan dan tana da farfadiya kin ga yanda su momy ke sonta suna riritata, sai da na samu na cucusa masu mumunan ra.ayi a kan son kudin su sannan na hada da na malamai suka yi mata korar kare, aman yanzu haka bokana ya fadan in dai mama ta ganta ido da ido to fa soyayar da take mata zata tashi ta fi da aman idan maganarta ne aka yi mata sai ta ji ba wanda ta tsana kamarta duniya, ahi ya sa ko waya muke da momy bana bari ta ji muryarta kanta dan kuwa some somen hauka zubar da yawu

Haka ta yi ta banbaminta tana aibata Nana mariama da iyalanta sannan tana kara jadadawa Sarah haka zasu yi ta shiga jikinta har su samj biyan bukata
(To fa)


Wasa wasa sai da sudai ya yi jinyar kwana uku cir ko falonsa baya fita,
Jinya ne yake na abu biyu zuciyarsa da rashin natsuwarsa
Du Sudais ya yi laushi, burinsa ya ga koda wulginta ne aman matsalar bai saka cctv a gidansa ba bangaren da matansa suke sai a can bangarensa kawai na siri , bai saka bane dan baya son shiga rayuwar matansa, yana fadi cewar kowa nada siri a rayuwa, in dan gudun wani abin ne Allah na tsare su sannan shi kamsa Allah na tsare shi sai kuma irin matakan tsaron da ya saka na zamani harda dakin da idan aka shiga bindiga bata ratsa kofar, kai ko bom sai wace ta amsa sunanta ba karama ba da zata dan yi busssss ta dan tsoratar ,
Aman a yau sai yake jin haushin rashin sakawar da bai yi ba, harma ya dauki aniyar sai ya saka a dakunansu ko dan ya ringa gannin shigarta da fitarta

Shiryawa yake a yau cikin suit, ya saka farar rigar ya bala boturanta saman wando ash kala mai santsin gaske mai duhu ya mugun yi masa kyau
Kum dinsa ya dauka ya caje sumarsa yana ayana sai ya yi gayaran fuska domin yau kwanansa shida bai gyara fuskarsa ba ya rage gashin kansa

Rigar saman ya dauko ya rike a hannunsa bayan ya saka cravate din aman bai matseta ba ya dan sasautata sosai daidai botiran rigarsa kwaya biyu da ya bari

Agogon hannunsa ya duba karfe tara , a yau yana son zuwa aiki ya yi aiki sosai sannan yana son yin magana da Samir, aman yana gannin maganar zai fara yi da samir din

Yana gamawa ya dauko yar karamar jakar computersa kampanin hp wace a cikinta ya saka kys dinsa da waya kwaya daya yar karama subulbula mai suna samsung fara kar da ita

Gaba daya sauran wayoyinsa ya bari a nan dan baya son takura
Yana shirin fita Humaira na shigowa ta karaso ta dafa gefen wuyansa ta ce" honey har ka samu karfin zuwa aiki?

Sudais ya lumshe idannuwansa wa Humaira, a hankali ya dan janyeta a jikinsa ya kauce ya fice ya barta nan tsaye domin ko a daren jiya yana mu.amala da ita ne yana dane ciwon cikin dake murdarsa sanadiyar warin nan dake damun hancinsa wanda mamaki take bashi irin yanda ita baya damunta, da fada da komai ya samu yar nustuwa ta hanyar zubar da wahalar da ta kara dadabe masa mara

Da harara ta bi bayansa ta watsa hannayenta ta yi dakin wajen da yake ajiyar kudi ta bude ta kwaso dan tana so ta aikawa mamanta a kasan zuciyarta kuwa tana ayana zaka gama fushin ne , ni din dai ni zaka dawowa dan na san abinda ka dorawa kanka na baka hulda da macen da bata kai mizanin shekara ashirin da shida zuwa sama ba, wannan yar shilar taka sai dai ta gaji ta kama gabanta banza da ita

Sudais na fitowa Samir ya karaso da sauri ya karbi jakar hannunsa yana gaishe shi da tambayarsa saukin jiki

A takaice Sudais ya amsa shi da " Alhamdulilah

Tafe suke Sudais na zaune gefwn direba Samir kuwa na tuki shiru cikin motar sai uban sanyin ac dake tashi

Sudais murya a dake kamar yanda ya saba ya ce" ka dakata mu sha caputulo

Samir ya amsa da " an gama

Wani makeken restaurant ne na masu hannu da shuni, nan samir ya kai motar su gefwn wajen park ya tsayar da motar suka fito

Idan ka gansu sai ka yi tsamanin abokai ne domin Samir ma sabon jini ne mai san kama kansa , sosai ya iya gayu da hade fuska idan hakan ya taso

Sudais kuwa tafe yake cikin tafiyarsa ta kakarfen namiji, sai ka ce irin turawan nan masu shegen karfi domin a yau irin shigarsu yayi

Wajen kujerar ya ja zai zauna ya dan bale botun din rigar costume din tasa na tsakiya wanda daman shi kadai ne ya saka ya zauna inda Samir ya yi commander din abincin ya ja shima ya zauna

Sudais ya tsare samir da kallo tamkar juju na karewa mai laifi kallo dan ya ingiza shi ya fadi gaskiya

Wannan kallon du ya saka samir A uku, damuwa karara a fuskarsa da tsoro domin Sudais bai taba yi masa irin kallon ba, shi ya kasa samun nustuwa sai dan mutsu mutsu yake yana dan dagowa ya kali Sudais ya sada kansa kasa

*Me kace sai na yi?*
Sudais ya jefowa Samir tambaya a dake ba tare da ya bashi kofar gane me yake nufi ba

Nan da nan zufa ya fara karyowa samir, ya dan gyara rigar shadar jikinsa a ransa yana ayana ni na san ba banza ba , domin a kampani ba irin cafe din da babu aman Wai oga ya bada umarnin su tsaya a gefen titi su sha caputilo?

Muryar samir rawa ta fara, shi yana jin haushin irin yanda Sudais ke yi masa kwarjini aman yana danganta haka da irin yanda Sudais din ke da kwar jini , da kamala

Samir ya ce" oooooga ban fahimci maganar ba

Sudais ya kawar da kansa ya ce" ina so ka fada min etape par etape yanda zan bi na karkato tunaninta kaina, ta so ni,
Samir rayuwana ne ke tangalgal tamkar ruwa a kan bokici a kan yara, ban zauna na koyi karatun soyaya ba , ban san ta ina zan fara ba, ban iya bin mata ba, damuwar *RAUDA NA TAFIYA DA BUGUN NUMFASHINA, NA LURA IDAN NA YI SAKE LUMFASHINA NA IYA DAUKEWA A CIKIN YAN DAKIKUN DA BA WANDA ZAI ANKARA BALE YA KAWO MIN DAUKI, SAMIR KA SAKA NI A HANYA NA GANE MATATA*


da mamaki, da tausayi Samir ke kallon Sudais,, lale ya yarda *So mugun wasa ne*, ya yarda *So guba ne*, kuma ya yarda *So sarki ne*, a gaskiya sai da ya dago ya karewa Sudais kallo, a ransa ya ayana ELHAJ SUDAIS UBAN MASU GIDA!, ya zama bashi da karfi bale dabara a gaban yar cininiyar yarinya

Kansa ya sada, ya kuma dagowa daidai lokacin da aka kawo Caputulo 🤤 aka ajiye
Cike da ilimi Samir ya dauki papier ya yaga ya dan goge bakinsa da hannayensa biyu sannan ya yiwa Sudais nuni da hanayensa da idannuwansa kan ya dauka mana

Sudais ya hade rai ya yi masa kallon karfa ka raina ni,
Gannin haka ya samir dam ya ajiye nasa ya gyara zamansa ya ce" oga, ka yi hakuri da abinda zan fada, na farko dai dole, dole, dole sai ka ajiye abinda ke sakawa tana jin tsoronka, wanda kai ka dauke shi a matsayin ba komai ba ..... sai dai wannan shi ne damuwar

Ba tare da Sudais ya kali samir ba ya ce" me ne!?

Samir ya ce""""""""







*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




3⃣7⃣



Samir kai tsaye ya ce" tsare gida, girman kai, da wannan abin wai sai ta ce tana sonka a farko

Sudais ya zaro idannuwansa, ya cije lebensa kafin yake saki ya nuna kansa da yatsa daya ya ce" Samir, ni ne mai girman kan?

Samir ya dan dago yana kallonsa, dan daburcewa yayi ya dan ja kujerarsa nesa da sudais kadan yana dan sine kansa dan kar ya kai masa bugu

Sudais ya yi dan murmushi ya ce" karka damu , ci gaba ai ni na tambayeka

Samir ya sauke ajiyar zuciya ya ce" oga, ka gane, mata fa akoy masu aji...., akoy matan da suka san kansu, suke kare mutuncin kansu, wa.inda kudin mutun ko kyansa ba zai saka su saki layi ba , bayan wannan ga irin matsalolin dake tsakanin Hajia (wato Rauda ) da kuma kai, wa.inda ita idan baka yi da gaske ba su ne hujojinta na gudunka a rayuwa,
Sannan sai ka kai zuciyarka nesa ya kasance ka sadako ka sauke kanka ka isar mata da sakonka ta hanyoyi daban daban,

Sudais ya tsare Samir da ido, a ransa yake ayanna wato shi wannan kamar ma mai jin haushina, sai kace wanda yake jiran irin hakan ya wankeni, uhum aman ba komai na tabata shi iyakar hakan ne kuma yanda ya fadan na tabata Samir mai kareni ne a waje ba dai ya hadu da wasun masu yi min muguwar fasara ba, to aman me yake nufi? Ni na sada kaina na bi ta,
Dan murmushi yayi wanda har Ya sa Samir sauke ajiyar zuciya domin a tsorace yake da Sudais,
Sudai bai ce komai ba kuma bai sha caputulon ba ya mike ya dauki rigarsa dake rataye ya yi wajen mota

Da sauri samir ya bada carte dinsa suka saka suka cire kudin caputulon suka mika masa shima ya bi bayan Sudais ba gare da ya sha Caputulonsa ba😟

Haka suka karaso wajen aiki wanda suna shiga aka fara tarbo sudais da takardu

Murmushi yayi gannin Shuraim

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login