Showing 99001 words to 102000 words out of 122108 words
Chapter 34 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
ya ayanna what? Ita da zata fita me ya hadata da turare?
Tsare fuskarta ya yi da kallo, batai kwaliya ko kadan ba, kwalinma tun na asuba ne da ta saka (wannan na daya daga cikin hudubar ma.aiki ga yarsa mafi soyuwa a gare shi wato nana Fadima cewa" du abinda kike kar ki bari mijinki ya ga idonki ba kwali😌 ( gyara ba laifi) )
A kasan zuciyarsa ya ayanna" MATA kina da tsararen kyau wanda idan kowa a duniya ke ganinsa zan ji haushi, bana son ki gane halin da nake ciki mata,
A hankali ya dan dukar da kansa ya canza harshe wanda sun iso aman basa jin me yake fadawa Samir domin basu iya yaren ba kamar ruwa ruwa wato larabci, ya ce" Samir, zaka kai su saloon
Samir ya dago yana kallon sa, ya ce" aman oga kafa yiwa mutumin nan alkawarin zamu je
Sudais ya ce" eh zamu je mana aman sai an kai su na ga dawowar su kafin mu je
Samir ya ce" idan aka daura auren fa
Sudais ya hade rai ya ce" kai malan, idan na je nine alwalinsa ne? Ka ga ka yi min abinda zan samu nutsuwa, ba zan lamunci Hafsat ta tukasu haka sake ba kuma ba zan yarda wani garjejen direba ya ja min mata ba, dan haka kumu je tare mu kaisu
Samir kam abin ya girmami tunaninsa dan haka sai ya amsa da kai kawai ya mike yana satar kallon Hafsat a ransa ya ayanna" ita harda su jan baki, idan na yi magana tace ai ita a kasuwa take, na saya na saya aman ta ki, kai gwara ma mu kaisun hankalina zai fi konciya ni din ma
Hakan kuwa aka yi, Hafsat ce ta nuna saloon din da zasu je, suna zuwa Sudais cikin hade fuska ya ce" zamu je anguwa da mun dawo zamu biyo mu tafi gida
Da toh suka amsa bayan sun yi godiya suka fice suka shiga saloon din
Katon litafi mai dauke da kalolin gyaran gashi tun daga coiffure da kitso kala daban daban aka miko masu ,
Nan mai saloon din ta fada masu cewa ana gyaran jiki ana wankin kafa ana dilka da kurkum ana gashi idan suna so
Kallon juna suka yi kafin Rauda ta dan saki murmushi ta ce" sis, ina gannin ko zaki je ki sayo mana sauran kayayakin nan ne ? Kin ga idan na je kar ya zama damuwa
Hafsat ta karba tana karantawa, ta kali hajia mai saloon ta mika mata ta ce" hajia wannan kuwa a ina zamu samu?
Hajiar na amsa tana karantawa ta ce" ai ina da su, sai dai nawa na kirki ne akoy tsada
Hafsat ta yi murmushi tana zama ta ce" wannan ba damuwa bane, yanzu abinda muke so muna son dilka da kurkum, muna so a gyara mana kanmu, a yi mata turare harda wankin kafa
Hajia tana murmushi ta ce" kawai ki ce a yi mata gyaran amarya
Hafsat ta ce" yawa Hajia , sosai fa , ki baje komai kawai ki yi mana bilan
Hajia ta kirayi biyu daga cikin yaranta suma matan ne masu kyau da su ta fada masu aikin da zasu kama mata
Hajia datijuwa ce mai gyaran amare da saloon , ta kware a aikinta bata da dar ko wa zai zo ta san yanda zata tarbe shi ya koma da jin dadi samun abinda ya zo nema
Na takaice Rauda ta samu gyara harda na mamaki, ba inda baya santsi a jikinta , hajia ta sameta ta kara bude mata idannu ta kara wayar mata da kai a wannan fannin duda bata san halin da take ciki ba, aman ta ganar da ira aure yakin mata ne kuma ta kara nusar da ita ko qa kake aure komai kyanka isarka kudinka mulkinka ke mace kece a kasa sai kin yi biyaya kuma kin yi hakurin zama da miji
Sosai Rauda ta ji dadin wannan gyara, jinta take sakayau kafarta kuwa har wani zafi zafi take tsabar ta sha wanki akaifunta haka suke daukan ido tastastas
Abu daya take maimaitawa wanda bayan hajia ta yi mata wankin kwakwaluwa ta cazata da kyau ta ce" sai fa kin cire kunya, ki tarairayi mijin Rauda sannan idan zama ya zauna ki sani kar ki zama irin matan nan wai su idan namiji bai neme su ba su sun dare wai a ja aji... wani ajin gare ki wanda ya fi ki kara kanainaye zuciyarsa yardarsa taki ce? Ke idan kika nunawa namiji kina ra.ayinsa zai ji shi tamkar wani sarki zai cewa kansa kai ashe nima namiji ne? Aman sai kin yi kokari kin cire kunya zaman aure kunya na wajensa
Murmushi ta saki tana kallon hannayenta, ta kallo Hafsat ta ce" kai sun iya gyara, duba ki ga yanda fatana yake sheki
Hafsat ta ce" ni kaina sun birge ni, kinga komai a waye sun iya aikin su
Suna tsaka da labarinsu Wayar Hafsat ta yi ringing
Tana dagawa Sudais ya ce :" ku fito
Hafsat ce ta je ta biya suka dauki ledojin abubuwan da suka saya suka yi waje....
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
5⃣4⃣
Crêpe recette = *FULAWA, KWAI, , SIGA KADAN, GISHIRI KADAN, MAI, MADARA, BEUR*
ki samu kamar kilo guda na fulawa ki saka masa kwai biyar🤗, ki saka dan siga da gishiri ba masu yawa ba ki daidaita daidai dandanon ki idan da chocolate zaki ci siga ya dan fi yawa idan kuwa da miya zaki ci gishiri ya dan fi sigan yawa, ki kada madara rabin kofi ki zuba, ki zuba mai ludayi guda ki kwaba fulawarki ki zuba ruwa ta murzu da kyau tamkar zaki yi kulin waina, shikenan sai kina toya abinki da beur zata baki crêpe kina linkewa 😋 sai ki yi mata yar dagargarar miyarta na yasa ko nikenken nama ko ki ci da chocolate
Tunda suka kamo hanya Samir ya yi gum da bakinsa gannin ogansa ya daina jin yarensa,
Ta madubin motar ya tsura mata ido, kanshin nan da suke bazawa fa?
Sun yi nisa a tafiyar ya kali Samir ya ce" tsaya
Samir ya kallo wajensa, ya ga yana nufin ya tsayar da motar ne
Tsayar da motar ya yi
Sudais ya fita ya zaga ta dayan bangaren....
Bude wajen direban ya yi fuska ba alamar walwala ya ce" ka je kawai zan karasa mu
Wannan karin baki Samir ya saki, suma suka bi su da kallo domin muryar Sudais ko ya yi niyar yin magana a hankali girman muryar ke tona masa asiri sai an ji shi
Samir kasa hakura ya yi ya ce" aman oga, me yasa toh?
Sudais ya kallo shi da wani kallo mai kama da idan baka fita ba komai na iya faruwa
Ceinture ya konce ya fita yana gyara rigarsa abin zaman mota yana kallon Sudais ,
da mamakinsa kiwa Sudais ya shige ya ja motar ya barshi nan baki da hanci a bude
Hon din mai mashin ya zaburar da shi bai san lokacin da ya furta" kan uba🤔, toh oga na zuba hauka a gaban yarinyar nan yana ikirarin sai ma furta masa kalmar so zai nuna mata soyaya bayan du wani motsinta sai ya bayanar da kansa a fili, na tabata kishi ne ya konmace ya zama direbanta da mu shaki iska daya
Yarinya Allah ya baki a gashe sai ki yi kokarin iya ci 🤣
Haka Samir ya dan taka kafin yake tsayar da mai mashin ya darw ya yi masa kwatancen gidansa, yana tafe yana mitar ai shima an dizga shi a gaban budurwarsa
Yana tsayar da motar suka fita tare suna hirarsu da ledojin a hanayen su
Hira ce suke kasakasa suna yar dariya,
Da gangan Rauda ta ki tsayawa ta yi cikin gida abinta domin sai wani shan iska yake yana kakawar da kai karma su samu damar yi masa tambayar me ya sa ya tuko su ya tsayar da Samir ko kuwa su gano wani abin a tatare da shi, shi ya sa ya hade fuska tamkar an mare shi (🤣)
Haushi ne ya mugun kama shi gannin yanda Rauda ta nuna halin ko.in kula, ita yar godiyar ma batai masa ba kamar yanda Hafsat ta yi masa
Da mugun jin haushi ya kashe motar ya fito yana kokarin shiga wayarsa ta kwashi ringin ya dan tsaya ya duba mai kiransa managen kampaninsa ne dake Saudiya daya daga ciki ya sha kai ya leko ya jima rabonsa da su aman ya kasa matsawa har sai ya saka rana sai ya cewa kansa *ITA FA?*
Yana gamawa ya shiga fallon , nan ya tarar da Hafsat na amsa waya ita faya dan haka ya kara hade fuska ya nufi dakin Raudar dan kuwa idan har ya kyaleta a irin wannan rainin na shiga wataran bama zata kula shi ba
Da karfi ya tura dakin nata dan ta san ba da wasa ya zo ba
Tsaye take ta cire doguwar abayar, ya rage mata daga ita sai dogon wando slim baki mai lafewa a jiki da breziya tana faman cireta ne itama dan ta je ta yi wanka ta yo alwallah sai jin bude dakin nata ta yi da karfi , ita gabanta har ya fadi ta yi tunanin ko Humaira ce ta shigo mata har daki yau kuma
Daga shi har ita sai da gabansu ya fadi,
Wata irin kunya ta ji ta lulubeta na gannin da yayi mata daga ita sai bra..........
Shi kuwa daskarewa ya yi a tsaye, shi bai karasa ya aiwatar da abinda ya zo yi ba, shi bai juya ba, kai kwata kwata ma bai yi magana ba
Da sauri ta rarumi abin rufa ta yane jikinta tana jin yanda jikinta ke rawa ta tsuguna jikin bed hankalinta a tashe
Da ido ya bita, har reaction dinta gaba daya yana kallonta,
Jikinsa yake ji na rawarawa zufa na dan tsatsafo masa
A haka ya yi kokari ya cira ya karasa kusa da ita,
Damatsunan hannayenta ya kamo ya dago da ita ya matse mata waje har suna jin hucin juna
*wai me kike boyewa?, an gaya maki ina ra.ayin hakan ne? Ki daina wani gudu dan kin gan ni koda ba komai a jikinki MATA, hakan na batamin rai bayan na fada maki dimniya sai ta nuna nake shanta*!
Cikata ya yi ya fice a dakin da sauri ya nufi kofa da kys din ya bar gidan gaba daya
Rauda a nan ta zube, jikinta na mata rawa, anya kuwa zata iya tarbansa gwa da gwa ? (Ai daman du budurwa kamila sai ta dage kafin ta iya hakan),
Hannayenta ta cusa cikin gashin kanta dake fotar da fitinanen kanshi, ta kuma furta" na shiga uku ni Lalla, me ke damuna haka? Aman haka kawai zangar sai na tsaya masa a gabansa haka? Haka hajia ke nufi? Bata san cewa ban san komai na? Ya salam nima kar dai na yarda cewar yar shilar ce
Ido ta lumshe kafin take yaye rufar ta je gaban madubi ta tsaya,
A hankali ta share hawayen da ya zubo mata ta ce" ba shilanci bane kunya ce, wace an nanata min sai na yi da gaske da kuma tsoronsa, ga rashin sabo........... , kana nufin ko bani da komai ban isheka kallo ba?
Kai sire zan gani
Tsakanin wannan abin da ya faru an yi kwana biyu wani abin kirki bai shiga tsakaninsu ba, shi yana nuna fushi yake ne wanda ta lura yana da saurin hawa da kuma saurin sauka , ita kuwa ta bashi dama ne dan tana neman hanyar da zata kama shi a hannunta
A haka har ranakun Humaira suka zo suka shige, suka kima zuwa suka shige Rauda batai gigin cusa kanta ba sai dan kawancen da suke na freind freind shima idan waje ya matse masu
Bata wani adon jan hankalinsa dan ta lura yana cikin abinda yake sakawa da ya budi baki yake ce mata yarinya sqi dai abubuwanta da ta siyo ta hada tana dirkan abinta , ita dadinsu take ji sosai domin kuwa daga wanda da madarar peak sai wanda da zumuwa daya nema marar dadi wanda ake hadinsa da Madara peak da kabewa
Sai sirika wa.inda take rubuta abinta da kanta ta hada da su kankana da sauran su, kaza kuwa dahuwa uku ta yi na kaza da ridi da nonon rakumi da suratul yusufa...............(SIRI NE)
A yau ya kama ranar aikinta ne, ta tashi ta yi sallah ta koma bayi
Wanka ta sallah na mamaki, tana fitowa ta saka iya pant ta dauki turare mai sanyin kanshi na humura ta samu ta shafa a jikinta cikin nutsuwa
Tana gamawa ta konta saman bed dinta ta jawo sabon bargonta ta shige ciki ta yi lamo tana ayanna abubuwa a ranta
Sai wajen karfe goma sha daya Hafsat ta shigo dakinta dan jin shiru yau bata fito ba
Tana zuwa ta tarar da ita cikin bargo ta lulube ruf ko kanta ba.a gani ,.....ita ta samu bacinta ma
Da sauri Hafsat ta hau gadon tana kiran sunnanta tana fadin lafiya?
Rauda na jinta ta farka ta rike dan karta yaye bargon ta dan fitar da fuskarta tana kallonta , ta ja hanci kafin take yin atishawa , ta rarauta muryarta ta ce" mura ne da kasala ke damuna (😂 ciwon wata yarinya yar rainin wayo🤦♀)
Da sauri Hafsat ta shiga jera mata sannu , ta fita dan nemo mata magani
Sudais yana wajen aiki tun karfe 8 na safe shi da gidan sai da yama idan ya dawo da wuri karfe 6 dan haka Hafsat ta samo mata magani panadol ta hado mata shayi ta kai mata
Da gangan Rauda ta ki sha ta langwabe jefi jefi takan dan satan kallon Hafsat du ta damu har ta ji ba dadi a ranta sai dai kuma ta ki mokewa ta ayanna idan har na ci ai zan daina kama da marar lafiya
Wasa wasa har karfe hudu na yama Hafsat na fama da Rauda kan ko ruwan shayi ne ta sha , fir ta kiya tana langwabe hijabinta a gefenta sallah kawai ke tashinta tana gamawa take komawa ta lafe kan bed
Hafsat ta dauki wayarta ta kuma kiran yayanta domin daman ta yi kiransa bai daga ba
Can ya daga ,
Hafsat ta gaishe shi bayan salama , cikin nutsuwa ta ce" ya, aunty ce take mura ka biyo mata da magani
Gaban sudais ne ya fadi, aunty? Wata auntyn ce ba lafiya? Bai iya tambayarta ba domin bai san irin tambayar da zai yi mata ba dan haka kawai ya kashe ya karasa office dinsa ya saita du abinda zai saita ya fito suka dauki hanya shi da samir
Suna karasowa ya fita, wayarsa ma a nan ya bari domin jikinsa du ya yi sanyi, bai san waye ba lafiya ba
Yana shiga ya tarar Fallon ba kowa,
A hankali ya nufi dakin Humaira
Ya tarar bata nan,
Kansa kawai ya girgiza ya juya ya shiga na Rauda
Tunda ya shigo da salama ta yi lakwas gabanta ya shiga dukan casa.in casa.in
Karasawa ya yi har yana harde kafa ya ce" aa, ciwon ya yi zafi har haka ne? Tun yaushe
Hafsat tana bashi amsa ya karasa bakin bed din,
Hafsat na gannin hakan ta juya ta fita a dakin
Sudais na karasowa hannunsa ya sa ya yaye bargon domin ta sake shi ya yaye shi gaba dayansa
Saki ya yi yayi baya tagatagal tana kokarin rike wani abin,
Bai san lokacin da ya furta " ya Salam, yana kokarin rufe idannuwansa sai dai ina sun tashi yau suma zanga zanga ba za.a hana su gannin abinda ke gabansu ba
Rauda dake kokarin hana zuciyarta balowa ta fito ta samu a hankali tana kokarin tashi tsaye, ta mike ta sauke kafarta daya tana kare kirjinta da hannunta ta mike tsaye da nufin zata dauko wani abu ta rufe jikinta
dan tafia ta yi luuuu dan haka ta saki hannayen nata dan tare kanta kar ta jibgu a kas a ranta kuwa tana ayanna kar a je daga wasa ciwo ya zamo min gaske (haba Rauda a wuni ba.a ci ba ai an dan ji jiki ba azumi ba ba komai ba )
Sudais ya daga kafarsa taku daya ya yi ya rikota karta fadi, maimakun ya kaita saman bed dinta sai ya jawota jikinsa ya
...........
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
5⃣5⃣
Wani irin riko ya yi mata ya hadeta da kirjinsa ya saka hannayensa biyu ya riketa ya lumshe idannuwansa ya kasa aiwatar da komai sai kara rukunkumeta yake yana shinshinar fitinanen kanshin da take fitarwa mai neman zautar da shi
A hankali yake kara riketa wanda ita kuwa ta rikice sanadiyar sajensa dake shafar wuyanta (🙈 saje🥺) ga uwa uba pant din nan na jikinta shi ne ba komai sai shi
Murya na rawa ta ce" wai wai meye haka sire?
Ni ba sire din ki bane
Ya fada muryarsa a cunkushe
Gaba daya karfinta ta saka dan banbare shi a jikinta sai dai ga mamakinta ko motsi bai yi ba gashi jikinsa sai kara daukan bari yake hakan ya sa har itama jijiga take sosai
Gannin tashin hankali na neman samunta, daga neman gira zata rasa ido , daga wasa yana