Showing 3001 words to 6000 words out of 122108 words

Chapter 2 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

411

din da ta yi saura yana ayanawa a ransa cewar gobe idan zasu tafi makaranta naira dari bibiyu zai basu ya tabata Aisha zata yi murna da hakan (😭)

Da salama sannan da karfinsa ya shigo gidansa , inda ya tarar da iyalinsa kyawawa zaune saman tabarmar ledar dakin matarsa suna hira sannan ga abinci suna ci cikin annashuwa

Ba yabo ba falasa mai dakinsa ta amsa gaisuwarsa inda Raudat t mike d sauri ta karbi ledar hannunsa da gatarinsa tana ta jera masa sannu da zuwa ta kai gatarin ma.adaninsa sannan ta nufi dakinsu da ledar

Cikin fara.a ya ce" Raudana aa wannan naku ne mikawa mamanku

Cike da murna ta mikawa mahaifiyar su ledar wace ta dago a yatsine ta karba tun kafin ta bude ta ce" ba girin girin ba dai ta yi mai

Fitar da takalman take a yatsine sanna ta dago tana dubansa wanda yayi kasakai yana jiran gannin fara.a a fuskarta sai dai kashhhhhhh abinda fuskarta ya bayanar masa sai yayi dan daman ma bai shigo gidan a wannan lokaci ba

Ba tare da ra bayana farin cikinta ba ta mike ta zubar da su a nan ta kare yi masa kalo ta shige dakinta

A hankali aisha ma ta mike ta yi kamar bata ga abinda ake yi ba ta kwashe kwanon namanta ta shige dakinsu

A tare suka raka su da ido,

Raudat ra yi gagawar mikewa ta kwashe takalman, tamkar wata yarinya karama ta shiga murna harda dan tsalanta ta matsa wajen mahaifinta ta kamo hannunsa ta ce" Abanmu, kamar ka sani kuwa takalmanmu sun tsufa, kai Abanmu Allah ya kara budi ya saka maka fa gidan Aljannah ya kara maka wadatar zuciya da arziki mai anfani

Bai amsata ba, sai wani ciwo da yake ji yana kara yin sama a zuciyarsa
A hankali ya mika hannunsa wajen fuskarta da ta jajir ga sawun yatsutsai wanda du idan an taba lafiyar jikinta baya buya yakan shaida kansa ne koda kuwa an kwana

Dan shafawa yayi ya dago jajayen idannuwansa ya zuba su a kan fuskar yarsa, wace shi yayai imanin da bata tare da shi da tuni zuciyarsa ta buga a irin halayar matarsa da yarsa ta fari, cikin yannayin damuwa ya ce" RAUDANA kin tsokani magana bayan bana nan ko???????


Rauda ta ce.....

.......

......



.......






Tafiya sannu kwana nesa❣





*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*



3⃣



Na: *Sajida*




Raudat cikin mutuwar jiki da abubuwan dake faruwa a gidansu da mugun tausayin mahaifinsu ta sada kanta ta ce" babanmu ba komai

Dan murmushi ya kakaro ya dauko canjin aljihun nasa ya rage naira dari kawai ya mika mata ya ce" Raudana yau alhamdulilah an yi samu sosai, kin ga canjin na rago maku ki baiwa yar uwarki

Tamkar ya malaka mata duniya haka ta yi ta godiya tana kwararowa mahaifinta adu.a wace tanai masa a fili shi kuwa yanai mata a zuciyarsa a haka ya juya ya fice dan gabatar da sallah a masalaci


Washe gari ya kama ranar laraba, tun da safe yar karamar wayarsu wace Aisha ta zamneta take ringin , kira na uku ne Amina ke kiran wayar aman Aisha taki dagawa dan cike take da ita

Ran Rauda fari kal tana adu.ar Allah ya sa tarayar tasu ta kawo karshe domin sam ba alkhairi a wannan taraya tasu

A hankali ta warware rigar wajen mahaifiyar tasu domin yayarta ta dage sai sun saka su yau ta dora saman kananun kayan da ta saka wankaku tas

Jiyowa ta yi ta saki baki cike da mamakin yayar tata, somin ta daga wayar ta bude kararta tana yatsina tana ci gaba da fente fuskarta ta amsa da ina jinki

Daga dayan bangaren Amina ta ce" sowi kawata , na san jiya ban kyauta ba aman ki gane motarta ta samu matsala shi yasa kuma kinga su basu saba shiga motar haya ba shi yasa nace bara kawai na kai su aman yanzu ki yi ki fito zan zo na dauke ki kin san fa yau bamu da lecture da yawa

Aisha ta yi gagawar katseta da fadin sai kin zo, dan kar ta idasa maganarta

Rauda ta kifta idanuwanta cike da mamakin yayar tata, aman kuwa lale wani rashin zuciyar ma mai ake da shi

Yaya dai??? Aisha ta jefowa Rauda tambayar tana mai bin yanda rigar rauda ta mugun yi mata kyau harma ta fara kokonta a kan zabanta da ta yi na rigunan

Rauda ta kawar da kanta tana kokarin warware gugar hijabinta da ta yi fari kal mai hannu sannan ga tsayi har kasa ta ce" gani na yi jiya jiyan nan kika gama rantsuwar kin daina shiga motarta aman yanzu ta yi kiranki bama dan ta baki hakuri ba sai kara caba maki magana da ta yi aman du da haka kika amsata da sai ta zo?

Rauda kina da motar da zaki kaimu ne? Ba gaskiya ta fada ba cewar nice na saba da yawo a bos aman su mai suke da bos motar talakawa? Shin idan na yi fushi ta ina zan samu hanyar zama watar? To kinga ki saurara min binta zan, sannan idan kina zuwa gaskiya ba zamu daukeki da wannan hijabin haka sai kace wace zaki tafi masalaci mtsssssss " Aisha ta karasa maganarta da jan wani uban tsaki

Rauda ta sauke ajiyar zuciya sannan ta bi hijabin jikinta da kalo, ta kuma dagowa ta kali yayar tata sai kawai ta zura hijabinta ta lakaci mansu mai maski ta dan gogawa lebenta ta juya ta shiga harhada takardunta

Tana kalo yayarta ta yaye kanta da dan kwalin rigar wanda hakan ya baiwa dogon gashin kanta damar fitowa a bayanta sosai sannan daga gaba ma yayi konce gaban goshinta ana ganinsa sosai
Takalminta plat ta dauko ta saka sannan ta dan goga turarensu da ya dauko hanyar karewa ta fice ba tare da ta kuma fustawa Rauda kalma daya ba

Itama cikin nutsuwa ta gama ta fito ta nufi wajen mamansu ta ce " umma zan tafi

Dago kanta ta yi ra zuba mata ido, kamar mai nazarin wani abin sai can ta ce" oh to ni dai Rauda ko dai wani kasurgumin ustaz zaki aura? Na cire kudina na sayo maku rigunan aman dan wulakanci shine zaki hadata da wannan uban hijabin da ubanku ya saya maku? Shiyasa ashe Aisha tayi tafiyarta ta barki kina fama da hijab

Ita dai kanta a kasa bata furta komai ba har mahaifiyarta ta gama fadanta ta ce" na tafi umma

Ajiyar zuciya Nana Mariama ra sauke ta ce" a dawo lafiya Allah ya bada sa.ar tafiya

Ta yi murmushi ta juya da kudaden da mahaifinsu ya basu, bata tsaya nemansa ba dan ta san idan ransa a bace sabkon fita yake

Tafe take tana sauri dan isa bakin titi wani mai adaidaita ya zo ficewa ta tsayar da shi dan ta yi lati sosai , sai dai mai adaidaitan ya ki ya dauketa koda a naira dari da hansin ne , haka tana kalonsa ya tayar yayi gaba abinsa

Tana isowa bakin titi ta tsayar da bos yafi a kirga sai dai du a cike basa tsayawa da kyar ta samu guda wace ita dinma ta kudan cika domin an tsatsaga mutanen sosai sannan harda maza a ciki

Yaron motar ne ya fito ta kare mar kalo, garjejen kato ne sai wari dati yake , a hankali ta ce" dan Allah malan ku dan matsa na shige ciki

Kowa yana muzurai suka dan ja kafafuwansu ta samu ta shige can ciki jikin window ta makale tana neman sheda

Haka suka ja motar nan suna tafe suna tsayana suna sauke wasu suna daukan wasu

Daidai danja motar ta tsaya suna jira a sake su
Kan Rauda a kasa tana dan jan nunfashi tana share gumi da dan kyanlenta mai tsafta tana dan hura hijabin nata

Kamar ance ta dago da kanta sai idannuwanta suka sarke da wani mutun a zaune a bayan wata wuleliyar mita baka sai dai gilashin motar ana gannin na ciki kamar yanda yake gannin na waje,
Abinda ya bata mamaki sai ta ga tamkar gala mata harara yake, kwarjininsa ya saka mata faduwar gaba hakan ya sa ta sada kanta aman mai sai zuciyarta ta dameta da son sannin shin hararan nata ne yake da gaske ko kuwa?

Kuma dago da kanta ta yi ta dan sato kalonsa aman mai tabas harara ne yake gala mata irin mai cike da haushin nan

Cike da mamaki ta bi motar da yake ciki da kalo daidai lokacin da danja ta saki motocin suka fice shat shat tamkar iska ke tafe da su

Bata san tana sauke ajiyar zuciya ba har sai da na kusa da ita ya ce " malama sannu kin matse ko??

Kawar da kanta ta yi domin wani irin warin baki ne ya daki hancinta daidai motar ta tsaya wajen jami.a

Da sauri ta sauka ta biya kudin ta yi gagawar sayan piyawata ta cira ta kwararawa fuskarta ta shiga sauke ajiyar zuciya tamkar ta yi tsere


..........

A wannan rana sai ta rantse bata ga anfanin zuwanta makaranta ba domin da ta shiga aji bata samu gabagaba ba sai can baya dan an jima da fara lecture, inda ta samu kuwa daman wajen zaman yan bata aji ne banda labarai ba abinda suke

Suna fitowa ta zauna tana duba litafenta

Wata sansayar murya ce ta yi mata salama cewar"asalamu alaiki ya ke ma.abociyar kyau

Bata dago da kanta ba aman bata ci gaba fa karanta takardar ba ta yi tsam ta shiga tunani,
Wannan mutun wanene? Du inda na yi yana biye da ni, shi ba wani mai shekaru ba ko daga kalon fuskarsa aman du inda ya ganni ya kama kure min kalo sannan kokarinsa mu kasance iya mu ya samu damar yi min magana
Du wannan magangannun cikin zuciyarta take yi jin shiru ya saka ta dan dago da kanta tamkar mai tsoron ya kamata

Murmushi ya sakar mata yana mai yi mata irin kallon kurullahn nan

Hade fuskarta ta yi, ta sada kanta kasa

Gannin haka ya ga a yau fa wannan itace damarsa wace idan yayi wasa da ita may be ba wata

Muryarsa ya kara sasautawa tamkar munafuki ya ce" na tabata zaki cewa zuciyarki wannan mai nacin haka fa? Ki yi hakuri ko na hakura zuciyara sai ta shiga fada tana tsale tana fadin dan me ai itama mai inci ce dan haka ke ta zaba

Wani irin gingirigin take jin zancensa, ba wai dan bata saba ji ba aa sai dan wannan da salon yan gayu a ciki

Dago da kanta ta yi a karo na biyu, yana da kalar nutsuwa, yana da matsakaicin tsayi sannan kakaura ne bashi da rama ko kadan, irin mazan nan ne masu kiba harda dan tumbinsa na fura(😂)


Katse mata tunani yayi da fadin" sunana Abdurahaman, ni ba kowa bane sai mai nema tun karfinsa, ina da shago a rijiyar lemu ina siyar da kayan yan mata da na mak up, daifai gworgwado ina da rufin asiri sannan ina karatu a wannan jami.a inda nake karantar kasuwanci domin wannan rayuwa komai sai da ilimi, na taba aure matata ta rasu tun kafin ta tare, hajia Rauda na jima ina bibiyarki a gaskiya nutsuwarki ta fi kwadaita min son kula alaka ta alkhairi da ke, na sani ke din kalar manya ce aman na zo da kokon barata zan hau takara idan rabona ce kinga ai sai hamdallah , ya karashe yana mai sakin dan murmushi

Tausayin kanta ne ya dirar mata lokacin da ya kawo aya ta tuna maganar mahaifinta inda yake cewa *Raudana kinga rayuwa ki yi fatan samun miji na gari, kar ki yarda rayuwar wani ta rude ki ko ki sakawa kanki dogon mafarki wanda ba zai fishe ki ba, ita duniya komai Allah ne mai yi, kina iya nacewa mai kudi ki zo ki aureshi ya talauce, dan haka ki barwa Allah zabi du wanda ya fito maki idan mai mutunci ne ki amince a yi maki auren ki domin ni dai a yanzu banban burina shine na aurar da ku kafin kasa ta rufe idannuwana....* , babar damuwarta mahaifiyarta domin ita fa a wai take ji wai zata so da namiji, wani irin so kuma? Kawai sai ta kali garjejen kato ta ce masa tana sonsa? Ita wani abu ne zai kaita ga aikata haka? Bata tunanin kyau isa ko arziki zasu yi tasirin karkata mata tunani haka aman ance idan aka zauna da mutun anfi shakuwa da shi, ta sani bata taba kawo koda mai keke ne gidansu ba hakan ya saka mamansu ke koran dukan manema aurenta tun tasowarta shekara goma sha biyu har zuwa yanzu da take cikin ta ashirin da daya , wannan bawan Allah harda mashin dinsa wanda take ganinsa yawancin lokuta a sama, tabas zata saurareshi koda kuwa a kansa ma bata ji soyayar ba idan Allah ya sa shine mijinta shikenan ta yi aurenta Abanta ya samu konciyar hankali

A hankali ta ce" ka yi hakuri, ka bani lokaci zan je na yi shawara

Murmushi ya saki, ya ce " ki taimaka wajen shawarar nan ki yita da mai kaunana

Dan murmushi ta saki domin ya bata dariya wai da mai kaunarsa, ta sada kanta kasa ta mike ta tatara kayanta inda ya bita yana magiyar ta zo ya kaita gida aman fir ta kiya karshe ma sai ta tari adaidaita ta mika masa duka canjinta ya dauke ta suka dauki hanyar gida




Mita na tsayawa ya bude ya sauko ya shiga taku cikin hanzari ya shige part dinsa ba tare da ya waiwayi kowa ba

Yana shiga ya rufe dakinsa ya dauko remote ya danna ac ya kara masa gudu dakin ya garwaye da kanshi da kuma sanyi

Botiran maroon din jalabiyarsa ya bale daga gaba, ya konce dan nadin da yayiwa kansa tamkar balarabe ya fada gadonsa da baya yana fadin" bismillahi rahamanin rahim


Daga bakin kofa ake buga masa kofarsa ya bata rai ya dago hannunsa na hagu yana dubawa ya ga karfe 12 ne yayi

A hankali ya furta" ai ba zuwa kasar ba , auta ta dami mutun, yama aka yi ta sauko da wuri haka????? = domin kaf gidan nan ba wanda ya isa ya ratso kofofin nan ya zo har bangarensa sai ita ! Dan kuwa baka ga fuska bama bale har ka rabe shi, wai danma ya zurfafa a adinni domin har sunna sukai masa da ustaz....

Mikewa yayi ya mayar da botiransa ya bude kofar sannan ya saka hannunsa ya kare danma karta shige masa daki dan kuwa ransa a bace yake

Fuskarsa ta karewa kallo, gannin ransa a bace ya saka ta daina fada masa abinda tayi niya, ta ce" big broth what happen????

Idannuwansa da suka canza kala ya lumshe a hankali ya ce" ina son komawa saudiya

Ido ta zaro, a ranta ta furta komawa fa tap, ai ka zo kennan dan kuwa naji Aba na fadin saudiyar nan ta isa haka kuma ka zauna a kasarka

Murmushi ta yi ta ce" haba yayan *Hafsa* , mai yayi zafi harda zai kone? Mu muna son ka zauna da mu plz yayana,

Ajiyar zuciya ya sauke ya rufe dakin ba tare da ya bata gamsashiyar amsa ba

Cike da sanyin jiki ta koma, ita fa abinda ta yi niya sai ta yi domin so take ta yi masa birthday na surprise ta gayato kawayenta harda kawarta *AMINA* dake mugun son koda magana ne yayanta yayi mata


Yana rufe dakin ya ja wani uban tsaki, a fili ya furta" ba zan iya zaman garin nan ba, kana tafe ne ranka na baci , a cikin tafiyar hanya ma zai ka danne zuciyarka karta buga da abin haushi ina da ka zauna zaman dindindin, yanzu in ba rainin hankali ba macece fa ta shige can ciki maza sun saka ta a tsakiya haka tana shakar shedar su suna shakar nata koda maharamanta ne shi sam bai ga dacewar hakan ba ( wayo Rauda a bos🤣 )


Haka yayi ta fada shi kadai har lokacin sallah yayi ya mike ya shige bayin dakin nasa ..........
(Wannan kennan )





*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*



4⃣




Na: *SAJIDA*



Bayan kwana biyu

Zuru Aisha ke zaune a tsakar gidansu tana kallon waje guda , yannayinta ya nuna tana cikin tsantsar damuwa

Mamanta ne ke zaune a bakin murhu tana faman kada miyarta ta kuka da ta sha kayan hadi ba laifi

Dayan gefen kuwa Rauda ce zaune ta dukar da kanta kan litafin adinni tana ta tilawa

Mama,..... " Cewar Aisha cikin sanyin murya

Dago da kanta ta yi ta amsa tana kalon yar tata

Aisha ta sauke ajiyar zuciya ta ce" Mama, kawar Amina ce ta gayaci amina gidansu, ita kuwa ta gayace ni ana wani sabga a gidan, mama kayan da kika kawo mana gaba daya na saka du sun ganni da su, sannan gidan gida ne na manya baki ga yanda Amina ke rawar kai tana murnar zata je gidan ba, shine abin ke damuna kuma abin nan ya kama gobe ne da safe .... ban san ya zan ba

Shiru Nana Mariama ta yi ta afka tunanin ya zata yi ta taimaki yarta?

Ba tare da ta tambayi wace irin sagba bace, sannan ba ruwanta da sannin ina ne, abinda yarta ta fada cewar suturar da ta kawo masu du ta saka tana jin kunyar a kuma ganninta da ita bai dameta ba a matsayinta na mai neman cin yau .... sai ta fahimci hakan a matsayin kankarowa kai girma, sannan abu guda ta san idan dai ta yiwa Aisha sai ta yiwa Rauda domin du inda zata je dole sai rauda ta raka ta wannan kam ta kasa hana wannan dokar ta malan du nacinta

Cikin nutsuwa ta ce" karki damu

Shine kawai abinda Nana mariama ta fadawa Aisha wanda ya saka ta washe ta mike ta shiga shiryawa wannan tafiya ta gobe ta hanyar kyalkyale kyalkyalen kafafuwanta da shafa masu man bulanga dan su kara taushi su dauki kalar wankA(😂)

Can cikin bacin su take jin dan muryar mahaifiyarsu kadan kadan tana fadin" to me na na yi maka yanzu kuma?

A hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login