Showing 51001 words to 54000 words out of 122108 words
Chapter 18 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
jigum jigum suna jiran dawowarsa daga masalaci domin ya fada cewar da ya dawo za.a tafi
Daidai wannan lokacin baraka makociyar su ta kawo turaran wuta da humarar da mama ta bada dubu guda da dari uku aka kawowa Rauda,
Mama ta karba ta saka a jakar Rauda tana yiwa Baraka godiya wace ta bisu da kallo tsegumi cike da cikinta wai an yiwa Rauda Aure, wa ya aureta? A ina aka daura auren? Ya aka yi basu yi taron tarewarta ba ? Duda akoy halin babu a tare da su aman babun bata kai nan ba gaskiya haka dai ta juya ta tafi ba dan ta so ba sai dan bata samu fuskar tambaya ba
Malan ya shigo, sabuwar doguwar fara jalabiya ce a jikinsa, ya kafa hularsa harda turare ya fesa masha Allah malan ya fito das da shi
Da kallo ya bi su inda ya tsayar da kallon sa kan Rauda,
Bakin dogon hijabi ne ta dora kan riga da zaninta na atampa, ba walwala ko daya a tare da ita sai ma lagadab da ta yi
Dan girgiza kansa ya yi ya dauki babar jakarta ya fita ya dawo ya dauki kondon kayan sabulunta da kayan kwaliyar da ya dan tsintsinto mata ya kai ya dawo
Shi kam bai san mai zai fada masu ba, ya yi mata nasiha a jiya har shiga baci yanai mata nasiha dan haka ya umarceta da ta mike su tafi
Gabanta ne ya fadi, zuciyarta ta karye, ta mike a hankali ta dan fara takawa
Mariama dake tsaye ta rungume hannunta na dama saman kirjinta, ta bi yarta da kallo,
Ji ta yi wanni irin kuka ya zo mata wanda ta kasa rike shi
Tun karfinta ta sake shi ta furta sunnan RAUDA da dan karfin da ya sa Rauda ta tsaya cak daidai kofa kusan Abanta
Da sauri mariama ta karasa ta rungume Rauda a jikinta wace itama ta saki kukan zuciyarta na tsale tana jin kamar ta shige cikin mamanta ta huta da wannan tashin hankalin
Murya a raunane Mariama ke san bubuga bayan Rauda ta ce" its ohk Lallana, kin san me na tabata ba zaki sha wahalar rayuwa ba domin kin kasance mai biyaya
Kina iya kokarinki dan gannin kin fita hakina ni magaifiyar ki, kin fita hakin mahaifin ki, sai na yar uwarki,
Rauda ina sane da dukan abinda ke faruwa, ina sane da dumbin hakurin da kikai ,
Wannan aure da yardar Allah sai ya zame maki alkhairi, ki yi hakuri da jarabawar rayuwa kowa da irin tasa, kuma indai bawa ya cika mai imani sai Allah ya jarabce shi
Ajiyar zuciya Malan ya sauke yana kallon Mariama, ya ji dadin kalamanta wa Rauda, a kasan zuciyarsa ya furta" Mariamana kennan mai hali kala daban daban , wataran ta yi halaya mai kyau da nagarta wataran kuwa ta tsula tsiya😁
Haka ta rako Rauda har bakin mota,
Mota ce baka yar madaidaiciya da direba kurma a ciki
Haka suka shiga suka dauki hanya wanda suna tafe Aba na kara yi mata nasiha kasa kasa
Suna karasowa kofar gidan Aba ya ce" yaro makulin gidan a wajenka ne?
Kurman direba ya dan juyo saitin Aba ya ce" Aa Aba ai an zo an bude gidan an kuna inji
Da mugun mamaki take kallon sa harda sakin baki ta ce" kai Aba daman wannan yana magana?
Aba ya amsata da Eh man Rauda
Da mamaki ta fito hannunta cikin na abanta tana kara kallon direban da ya sada kansa kasa yana jin faduwar gaba da dana sannin amsa aba da ya yi a kusa da Hajia
Har ciki Aba ya kai Rauda bayan ya kawo mata kayanta ya saka ta yi adu.o.i shima ya yi mata ya mike da niyar tafiya
Da kyar ya samu ya rabu da ita, ita tana kuka shima yana share hawaye ya tafi ya barta a falonta dan madaidaici an kuna inji fitilu a kune na daki daya da na bayi da na falo da tsakar gida
Ta jima zaune tana kuka, a hankali ta mike ta nufi dakin mai fitila a kune ta yi adu.a ta shiga, nan ta ga kayanta gadonta da sauransu sannan harda bayi
Bata iya komai ba sai dakin da ta janyo ta rufe ta yi konciyarta a nan saman dan bed dinta ta rufe ido sai tunani
Kamshi yake bazawa, hannunsa rike da leda mai tambarin gidan suya, a yau da yake cikin farin farin ciki na karin kusantuwar marar tarbiyar matarsa sannan abin son zuciyarsa dole ya ci kazar kampanin suya
Saman doguwar kujera ya tarar da ita, ta cakare ta saka suturar siri a jikinta
Man bleating din yayi mata yawa ya sa har ana gannin jijiyoyi tsanwaye a jikinta ,
Ajiyar zuciya ya sauke ya nufi dakinsa
Da sauri ta ajiye whatsup din ta bi bayansa ta tarar ya zauna ya bude ledar da ya shigo da ita ya ciro takardu ya bude ya maida hankali ya fizga ya kai bakinsa
Da fara.a ta matso jikinsa ta dora kanta saman kafadarsa, murya kasa kasa ta ce" Uban masu gida, na daina shafa man fa
Murya ciki ciki ya amsata da " kin taimaki kanki
Lumshe idannuwanta ta yi, a hankali ta saka hannunta cikin sumar kansa ta shiga dan shafawa tana yi masa tafiyar tsutsa
Da gaya gaya ta ringa tsokalo shi, tana kokarin sai ta kai shi bango
A hankali ya fara hawa caji, sai dai yana lumshe idannuwansa hoton marin Rauda ya shigo idannuwansa wanda ya ji tassss din har kwakwaluwarsa
Da sauri ya bude idannuwansa da mugun firgita sannan ya rike hannun Humaira gam wanda har ya saka ta saki dan kara
Saurin cika mata hannun ya yi yana mikar da ita, fuskarta ya kafe da ido a zuciyarsa yake fadin" so nake na muzanta mata, na wulakantata, na yi mata abinda gabannan ba namiji ba ko mace yar uwarta zata ji tsoron kai hannunta yatsar kafarsa bama fuskarsa ba, Heartbeat koda kece lumfashina sai na koya maki hankali, sannan idan halaya mamanki kikai na son abin duniya da wulakanta mutane sai na cire maki su, sai kin zama yanda nake so kafin na nuna maki how na mace a kanki, karya kike Heartbeat soyayar ki bata isa ta saka na zama banza namiji ba, wly sai na koya maki hankali .........😟😟😟😟
A wannan ranar Humaira ta ji jiki ba na wasa ba, domin kwanakin da ya diba sai da ya sauke mata a kanta waima dan sama sama yake mu.amula da ita sanadiyar warin da take fitarwa na man bleating da ya cinye mata fata
Da safe du irin wahaluwar wannan da ta yi ki ta yi ta shiga ruwan zafi dan gudun kar fatar ta ta jimu warkewar ya zama aiki, haka ya barta ya shirya ya dauki ky din kotarsa ya yi fitar sirri da safiyar nan ( 🤔, ko baka daina dan Allah ba ai sai ka daina dan lafiyar jikinka 🤣)
Rauda haka ta kwana ido bude domin rabin kwanan ta yi tana tunani daga baya ta waye kan darduma tana ta kaiwa Allah kukanta,
Tsoro, mamaki, fargaba, tashin hankali sun yi mata yawa, kanta ba zai dauka ba, ita dai kan jiya zuwa yau bata ji motsi ba sannan bata ga shigowar mutun ba, mai hakan ke nufi?
Yar karamar wayarta ta duba ta ga karfe bakwai ta dan gita,
Tunda ya shigo anguwar ya shiga da ya sannin sakawa a kawota anguwar nan da farar safiya aman du an cika anguwar ana ta kakayatu, rabonsa da irin wannan rayuwar tun zaman tasha na dan watani lokacin yana harkar waya
Kofar gidan ya parka , ya kurawa kofar ido
Kansa ya dafe ya dauki wayarsa ya danawa samir kira
Samir dake barcin safe monday ya ji wayarsa na shaida masa kira na shigowa na ogansa
Ai wata irin tima ya yi ya dauki wayar yana amsawa
Run kafin ya kai gaisuwarsa Sudais ya ce" SAMIR aman ka gama raina min wayo, dan nacee ka samo karamin gida ne zaka saka min *MATA* a wannan gidan? Me ta yi maka da zafi haka? Ni *MATA* ta shiga nan ina raye? Samir kamar yanda tarihinta ya bambanta a rayuwana, ta zama ta farko da ta kafa baban tarihi a rayuwana haka dole komanta ya zama daban, tabas ina so na ganta a gidan da bai kai wanda na tanadar mata idan na huce ba aman kuma ba irin wannan gidan ba SAMIR!
Baki na rawa Samir ya ce" am, am, oga ka yi hakuri...abanta kuwa baka ga yanda ya yi murna ba sannan ya ce zai zuba mata abubuwan da ya yi mata kar mu saka komai
Sudais ya ja tsaki ya kashe kiran ya fita a motar ya nufi gidan
Du takunsa daya sai gabansa ya yanke ya fadi, har ya shigo falon
Idannuwansa ya kwalalo gannin irin shirin fallon, murmushi ya saki a ransa ya furta" daman akoy mutanen da kwadayi bai yi masu kanta ba du irin kangin da suke ciki irin Aba har yanzu???
Juyawa ya yi wajen tableau dake kafe mai sunnan Allahu hakan ya sa ya baiwa kofarta baya
Tunda ta ji alamar motsi ta mike ta fito a hankali dan gannin ko waye????
Tana fitowa ta hangi bayan mutun, a tsaye zambal da shi, sannan da gashin kansa luwaiwai sai sheki yake, bayan kwabrin hannayensa dake waje fari tastas ga cika da jijiyoyin wajen sun tsatsaya kyam,
Kafarsa cikin bakin takalmi sau ciki take, fallon gaba daya ya cika da kamshi
Wannan kamshin ta san shi, wannan kamshin hancinta ya saba shakar sa, aman a ina? A ina ta san kamshin nan?
Gabanta ne ya mugun faduwa wanda har sai da ta ji zata zube dan razanar da ta yi
Murya na rawa ta ce" mamamalan wanene???
Shima sai da ya ji gaban nasa ya fadi, girar sama da ta kasa ya hade, a hankali ya shiga juyowa wanda hakan ya bata damar gannin...........
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
3⃣0⃣
*CIGIYA, INA CIGIYAR NOVEL DINA BANI DA ZABI DAGA 1 HAR 42 PLEASE, NA SO TSAYAR DA SHI AMAN SISINA TA RIKICE.MIN DA RIGIMAR SAI NA KARA MATA WATO SAI NA SHIGA SOSAI, DAN ALLAH DU WACE TAKE DA TA TURON TA WANNAN NUMBER 91466605 NA GODE SAJIDA CE*
Hakan ya bata damar gannin fuskar mutumin da ya shigo mata gida da sasafe wanda idan an barta zata iya cewa mijinta ne ko wani makusancinsa
Tashin hankali wanda ba.a saka masa rana, idannuwanta gaba daya ta kwalalo waje, carbin dake hannunta fari dan karami ta saki bayan cikin lazumi take
A lokaci daya jikinta ya dauki rawa, rawa na tashin hankali, kafafuwanta suke neman zubar da ita kasa ,
Dan yatsanta na dama take kokarin tsayarwa a daidai inda yake aman sai rawa yake ya kasa tsayawa
Sudais dake tsaye sai ka rantse bai san ba wani abu wai shi sakin fuska ko fara.a a rayuwa, tsaye yake tamkar gunki tamkar zai yi arangama da mai bashi sakon mutuwarsa aman a kasan zuciyarsa fada yake da zuciyarsa wanda har zufa ta dan karyo masa ta wahala, kokowa take, luguden daka take tana hantsila tana kukan sai ya barta ta kawo ga abincinta, mai saka ta dokawa tun ranar da ta aminta da ita, so take ya je da gudu ya rungume yarinyar dake tsaye a gabansa ya rukunkumeta ya kankangeta ya dabaibayeta ya lasance koda lumfashi zata shaka sai ya biyo ta bakinsa ya shiga huhunsa ya janyo da hancinsa ya mika mata, kallon fuskarta yake ta yi fayau da ita, gurbin idannuwanta sun yi jajir tamkar wace take cikin jinya, lebenta kalar ash color sai rawa yake na sama da na kasa da abin dan yawu da ya jike shi sharkaf ya saka yake kyali tamkar ya cafke shi ya tsotse shi har sai ya cinye shi a bakinsa
Aman wani gefe na zuciyarsa ke yiwa sauran fada cewa" ita ce fa, ita ce ta daga hannunta na dama ta wanka maka mari a gefen fuskarka na hagu mai cike da yalwatacen saje da dumi na fata da cika ido dan kawai ka yi magana kan gaskiyarka, ita ce fa bayan ta wanka maka mari a bainar jama.a ta biyo la da nuna yatsa wanda a yanzu ma take nuna maka dan yatsanta karami mai dogon farce fari mai kyali, ita ce ta kafa tarihi a rayuwarka, abinda ba.a tabai maka ba ta kwana lafiya.....tabas kana sonta sudais, sai dai hakan ba zai saka ka nuna mata tun yanzu ba
Shima idannuwansa ya zaro, irin abu ya dake shin nan ya nuno ta da yatsarsa ya ce" you? Me kike a nan?
Kara zaro idannuwanta ta yi gabanta na ci gaba da dukan tara tara, muryarta na rawa ta ce" aaaaa, ai nan nan gidannn,,.....gidan wanda ke aurena ne
Bai bari ta kai aya ba ya ce" what?, ke? Kina nufin ke? No ba xai yiwu ba, ba zai taba yiwuwa ba, ke ki fitar min da matar gidan tun kafin laifukanki su fi karfin girman kanki
Da sauri ta kankame hannayenta biyu a kirjinta, ta dan dago da fuskarta ta kallo fuskarsa wace ta saka a take ta ji kamar ta fara zubar da jinin haila ( fargaba idan ta yi yawa tana takalo jinnin haila 😁🤦♀ )
Fuskarsa ta mugu mugun tsoratar da ita, sai a yau ma ta shiga tunanin abinda ta aikata, yanzu wannan fuskar ta mara da hannunta? Ita Rauda? Innalilahi wa.ina ilaihi raj.une kawai take ambata a cikin zuciyarta sannan a hankali ta sulale kasa still hannayenta a samankirjinta tana ta rawar jikin da tamkar an jona mata wayar wuta
Cikin dan daga murya da muryar nan tasa mai abin tsoro ya ce" wai ba ke nake jira ki hiwa matar gidan magana ba? Ke ko danginta ce ke sai na yi mata abinda bata taba tunani ba sanadiyar ki , sannan ki daina tsare ni da idannuwan nan naki suna saka na ji tamkar na shake ki na huta!
Karin firgici da tsoro ne ya saka Rauda dora hannunta a saman kanta, kuka ne ya kubce mata mai karfi tana girgiza kanta irin tana cewa aan nan,
Zuciyarsa ya kai nesa domin wani irin tsale ta yi masa na ya je ya lalashi abincinta, kokari ya yi ya karasa sosai kusa da ita wanda gannin ya karaso ya saka ta mike da sauri ta juya da niyar fadawa dakinta ta rufe sai dai ta makaro domin rikon barawo a hannun yan sanda ya yi mata ya juyota da karfin tsiya wanda ya saka ta daki bangon dakin ta yi tagataga da kyar ta samu ta rike kanta ta ja ta tsaya jikinta na rawa hawayenta na tsannanta gudu ,
Murya a dake SUDAIS ya ce" i said ina *MATAR SADAKA* ne?
Jin kalamansa take tamkar saukar aradu, a fili wannan karin ta furta tun karfinta" innalilahi wa.ina ilaihi raj.une, ya Allah ka farkar da ni a mafarkin nan, ka tashe a mafarkin nan,
Da sauri ta kalo wajensa bata damu da yanda kafarta ta farai mata zogi ba ta ce" kana nufin kai ne? Kai ne?
Tsareta ya yi da mayatatun idannuwansa ya ce" ni ne wa?
Murya na rawa ta ce" nonononono ba haka bane, ni na san ba haka bane, domin abin bai hadu ba ko daya, ka nemo inda nake ne ka biyo ni dan ka rama abinda na yi maka? Ka ga ka fita a gidan nan tun kafin ka jaza min fitina, na yi maka abin nan ne ranar dan ka daina wulakanta matar da ta mace a kaunarka, dan ka daina zagin mahaifan mu , idan kuwa baka yafe min ba ga fuskana ka rama dan Allah
Gefen fuskar nata yake kallo da mugun bege wanda a fuskarsa kuwa ya nuna tsantsar kyama, zuciyarsa ke fadin" ka dan shafa fuskar mana ,? Wata kuwa fadi take kai ka nuna mata kai namiji ne ka wanka mata marin da sai ta suma dan azabar zafi
Har ya daga hannunsa da tarin mugunta sai zuciyar soyayar Rauda ta rinjayi mai kin ta, da sauri ya sauke hannun nasa ya zubawa girar idannuwanta ido wada ta rufe idon ruf, du hawaye ya jiketa ta dan harhade da junnanta aman a tsaye kyam, hijabinta baki ne dai a jikinta tamkar mai takaba
Murya a dake ya ce" ke wai zaki bani amsa ne ko sai na hasala?
Rauda ta ce" na tambaye ka sire, na kasa gane inda ka nufa
Kai tsaye ya amsata da " ina nufin matar da aka bani a masalaci
Maganarsa ta yi daidai da tsinkewar tunaninta, dago da idannuwanta ta yi ta sauke su a cikin nasa kyam wanda bata ma san ta yi ba, me yake nufi? Yana nufin ita Rauda ita ce aba ya bashi a matsayin mata ba Aisha ba? Ta ya haka ta faru? Aman daman mai aure aure ne ko me? Ya aka yi sallah ta kama shi a masalacin anguwarmu a wannan ranar? Ai kafin wannan abin ya shiga tsakaninmu ne, wannan wata irin kadara ce? Wannan wani irin tashin hankali ne ke tunkaro rayuwarta da gidan su? Su kennan Haka za suna rayuwa jarabawa Kala daban daban? Ya salam ya zata yi me zata yi? Indai wannan bawan Allahn dake gabanta a tsaye wanda ta daga hannunta ta sharara masa mari, wanda yayarta ke haukar so har take ikirarin du wace ta gita ta gabansa sai ta halakata, bama wannan ba, wannan mutumen mai shegen kyau cika arziki mulki ai ya fi karfin tunaninta, aman kai da ayar tambaya a lamarin nan, wannan fa shine ake kira da *UBAN MASU GIDA* me gidan nan ke nufi? Aa ya shiga rudu ne, tabas a cikin rudu yake, in kuwa ba haka ba ne fa? In fa shi ne aka aura mata