Showing 39001 words to 42000 words out of 122108 words
Chapter 14 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
irin taka? Dan aunty ta yi maganar nan ne zaka wani biye mata? A yanzu da muke murnar Allah ya bilo mana hanyar da zamu ci mai dadi ne ka yi min wannan danyen aikin?
Dago da kansa ya yi ya ce" ki sasauta muryarki Mariama ki daina yi min ihu a kaina
Aisha ta yi saurin zubewa a kasa ta ce" aba, aman ai banda ni ka daurawa airen ko aba?
Da kallon tausayin halayenta ya bi ta, ya so ace a jiya ta samu wanda ya taya ta koda mai hucewa ne da ya daura mata shi , itama cikin kakausar murya ya ce da ita" *Baki samu mai so ba, aman da zarar na samu kema zan aura maki!*
Malan walahi baka isa ba, haka kake so yayan nawa suma ka kaisu gidan da har sai fatar su ta dawo kalar tawa dan wahala? Mai na kashe maka da har ya jaza min wannan wulalancin malan? Me na yo maka a duniya da zafi haka? Wly sai ya saketa ko dan gidan uban wanene!
Su duka basu ga lokacin da ya mike ba, har ya kawo wajen Mariama da take tijara tamkar zata daku da shi ya aikata mata abinda bai taba yi mata ba, abinda bata taba kawowa ranta ba zai iya aikata mata! Abinda ya girgiza yayan su su kansu sukai mutuwar tsaye domin Rauda kanta sai da ta mike tsaye jin saukar marin da Malan Ya shararawa Mariama
Yatsarsa manuniya ya nuno mata , ya kada kai ya fice bayan ya dungurawa Rauda akwati a kusanta ya fice kwata kwata a gidan
A hankali Mariama ta sulale hannunta dafe da kuncinta ta hade bayanta da garu wanda a daidai lokacin da gudu suka rukunkumeta kowace ta saki kuka, Aisha na borin fadin kar ta bari itama ya aura mata Wani bayan ga wanda take so kamar ta mutu
Rauda kuwa kukan abinda ya salamo rayuwarta da irin yanda fitintinu ke bilowa tsakannin iyayenta da tausayin mamanta dan ta san auren su da abanta ba na duka bane auren soyaya ne aure ne na hakuri aman tunda yau har ya yi duka tabas ya daki gawa ne dan mai rai ya ji tsoro, tsoronsa da tsoron hukuncinsa suka cika mata zuciya da tambayar shin wanene mahaifinta ya aura mata?
Mariama kuwa ta kasa lalashin yayanta, tashin hankalin da take ciki ya girmami tunaninta harma ta nemi hawayenta ta ji su a kafe, zuciyarta ce ke mugun buga mata tana yi mata sama da kasa lumfashinta yana fita da gagawa, muryarta na rawa ta ce" *innalilahi wa ina ilaihi raj.une! Na kai malan wajen da ya taba lafiyar jikina, saurin dago yayan nata ta yi daga jikinta murya a matukar raunane ta ce" AISHA RAUDA MALAN DUKANA NE YA YI?*
..........................
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
2⃣4⃣
Aisha ce ta yi karfin halin cewa" mama, walahi Aba ya canza, abanmu mai hakuri yau harda duka? Mama ni dai kar ya yayi min aure da kowa kar nima wannan yar uwar taki ta jaya min mama ni *ELHAJ SUDAIS* nake so kuma da shi zan rayu
Sai a wannan lokacin kuka ya zowa Mariama, ta dago hannunta na hagu wanda ta dafe kuncin nata da shi ta ce" a nan ya dake ni, a nan ya mare ni, bai taba yi min haka ba, ya kasance mai hakuri da dukan shirme na, ba zan iya tunkararsa da wannan magangannun ba, ni kaina a yanzu walahil azim tsoronsa nake
Cike da mamaki suke binta da kallo, daman mamansu na tsoron abansu haka aman take shagalinta? Ko dai tana anfani da irin yanda baya iya yi mata komai ne take taka rawarta ba kida?
Hannayen su ta gamo ta fi bada hankalinta ga Rauda ta ce" yau zan baku tarihin rayuwar mu,
Da farko Ahmad baya so na ko kadan, ni ni na yi ta naci har ya saurare ni! Na taso a gidan mu mu biyu mata ni da aunty sai namiji guda musbahu . Mun kasance............................ta kwashe labarin rayuwar su da yanda ta fara son Malan Ahmad da irin wahalar da suka sha, da irin gatan da malan ya yi masu, bayan rasuwarsa irin neman da malan ya ringa yi dan kar na shiga wahala kar na sha wuya, a haka har na haife ku daga baya ya dawo faskare
Malan bai taba ko da wasa shakunata da fuskar fada ba, ya kasance mai hakuri da ni!
Raudat, na ji haushin hukumcin da malan ya dauka a kanki, aman a yanzu ni da kaina neman kaina nake! Ki yi hakuri idan ya sauko daga fushin nan da ya tafi sai mu tatauna na tabata zai warware maki auren nan
Mama ni fa? Muryar Aisha ta katse mahaifiyarsu wace jikinta har ya dauki zafi, ta kasa yarda da hannun Malan ne ya kawo jikinta da niyar fada
Ta ce" sai mu yi fatan Allah ya sanyaya masa zuciyarsa kar ya yi maki ke ma
RAUDA kam a daskare take ta fada cikin tunani, labarin iyayenta ya birge ta sannan sun bata tausayi, daman iyayen mamanta da ran su? Sannan masu kudi ne sukai watsi da ita dan kawai ta auri talaka.? Oh duniya ina zaki damu, a yanzu kawai idan baka da shi ba lale ne a ganka da daraja ba
Ta kali mahaifiyar su dake rarashin Aisha a kasan zuciyarta take aiyana to ko dan mama ta fito daga tsatson masu kudi ne ya sa ta daina gannin kokarin Aba a kan su? Ko shi ya sa ya kasance *TA RAINA INDA TAKE?* to aman ai *IDAN KA RAINA INDA KAKE INDA ZAKA YA RAINA KA* wannan gidan kadai rufin asiri ne domin mutane da yawa suna mararin gannin su a irin wannan gida, zaka ga mai arzikin yana bin gidajen haya
Rauda kar ki saka abinnan a ranki kin ji? Kar ya dawo ya hadasa maki cuta daman ba gama warkewa kika yi ba, insha Allahu malan zai saurare ni..... (KO?)
mai kake so duniya ta dauke ka? Ya kake so a dauki lamarin? Haba SUDAIS bayan ka san irin yanda sunnanka ya yi fice a nigeria ? A gidan nan waye bai tako ya zo dan yi maka ta.aziyar rashin matarka ba? Aman a ce ko adu.ar 40 ba.a yi ba ka shigo min da maganar ka yi aure?
Mahaidiyar sudais ce ke fada tun karfinta bayan Humaira ta suma sun yayafa mata ruwa ta farfado tana rusa kuka, gefe guda kuwa Auta ce ta yi tsutsuru sai Hajiya kaka da Mahaifin Sudais
Aman kai yaron nan mai ya kaika aikata irin haka a kasar mu ta hausa? Bayan ka san duniya da kin gaskiya baka gudun a yi maka wata fasarar daban? Hajia kaka ta furta haka tana talabo habarta
Humaira ta ce" mai na yi maka Elhaj? Mai na tsare maka? Yanzu du kukan da ka sha da rashin baci da sauke gadon dakinka dan matarka ta rasu aman ka je ka kara aure da wurin nan haka? Ta juya wajen Momy ta ce" momy mutuwa zan yi nima, walahi momy ina jin zafi a zuciyata, mai na yi masa da zafi haka? Wa na kashe masa? Ni dai ba zan iya zama da shi ba ba zan iya zama da kishiya ba sai dai ya sake ni !
Momy ta kamo Humaira ta shiga rarashinta ta ce" kar ki furta haka, karki fadi haka Humaira, ba dai ke ba zai saka sai dai ya saki ita yarinyar da ya auran! Wannan wani irin tashin hankali ne kuma kai da kanka Dady ka yi ja gaban daurin auren? Ba zai yiwu ba ya jaza min zagi a cikin gari
*TO KIN ZABI FUSHIN ALLAH KENNAN A KAN ZAGIN CIKIN GARI?* DADY ya furta da kakausar murya
Ke yanzu daman fadan naki dan kar a zage ki a duniya? Du iliminki? Ku dai mata idan abu ya shafi kishiya ne ba zaku yi masa kyakyawan zato ba? Shi dai aure rai ne da shi kuma lokaci ne !
Hajiya ai kin ganni, shi yake daure masa yana rashin mutuncinsa, ki duba fa ki ganni Hajia "Momy ta karashe tana kara zabgawa Sudais harara
Hajia ta tsuke dan bakinta ta rafka tagumi hannu bibiyu, ita kam bata san mai zata ce ba ko yanda zata kashe wutar nan ba, tabas ba wanda ya isa ya hana abinda Allah ya halasta, duniya kiwa ba.a iya iya mata du irin kokarinka na ka iya mata zaka gaza ne
Auta ta dago kanta ta shagwabe fuska ta ce" momy please ki yi hakuri a bar maganar haka
Momy ta hayayago mata ta ce" auta kaniyar ki! Na ce kaniyar ki , ke tashi ki ba mutane waje an ki a yi hakurin!
Sudais dake zaune saman kafet, ya kurawa waje daya ido du wannan hayagagar da ake bai furta ufan ba ya yi gum tamkar ma ba dashi ake ba
Ta kuma juyowa wajen sa ta ce" kai ba zakai min magana ba ka bar ni na yi ta yawan magana kennan?
Sudais ya dago idannuwansa ya sauke kan mahaifiyarsa murya a cunkushe ya ce" ki yi hakuri momy, ki yi hakuri
Daga shi bai kuma furta komai ba, ita kanta sai ta rage fadan aman Hulaira sai rusasa kuka take tamkar ranta zai fita tana rantse rantse
Hajia kaka ce ta matso kusa da shi ta kamo hannun sa ta ce" tashi mu tafi, mu je ka konta ka huta
Mikewa ya yi da hanzarinsa ya shige gaba daman abinda yake jira kennan wanda zai fitar da shi daga gaban mahaifiyarsa a wannan lokacin
Suna fitowa ya daga kafa ya shiga sauri dan barin wajen
Hajia kaka ta ce" kai ya haka? Ka tsayani mana, ka tsaya ka san fa tsoron hanyar nan nake ga nisan tsiya ga shiru tamkar kushewa, me ke damunka haka ne?
Dan dakatawa ya yi ya juyo, wannan tsohuwar na son ta hadasa masa ciwon kai, a dan kufule ya ce" dababayi na yi maki ne? Ki daga kafarki ko na yi tafiyata abinda zai kama ki ya kama ki a hanyar
Hajia kaka ta ja ta tsaya ta rike habarta ta ce" iye, ka ji dan nema, ai ni ba makauniya bace, Allah na tuba ni muna yan mata kawance fa na yi da Ina kika fito fada ina zaki fada mai kike fada, ni har ka gwada min karfi? Kai din karfin ne da kai dan kana ganninka jibgaga sai shegen tsayi da jiki a tunaninka zaka iya tsare min wani abin ne?? Solopiyo kawai
Sudais ya girgiza kai ya yi kwafa ya yi gaba abinsa ya barta a nan,
Shiru ta yi ta jima tana waige waige can ta juya tana tafe tana fada tamkar ta ari baki ta koma bangaren Su momy wanda tana shiga Humaira na fitowa ta yi tamkar ta bangajeta ta fice
Yana zuwa rigarsa kawai ya iya cirewa ya konta rigingine ya zubawa siling ido
Humaira ce ta shigo ba ko salama ta ja ta tsaya tana cika tana batsewa ta kasa ci gaba da zuba rashin mutuncinta kamar yanda ta fara a wajen su momy
Baya ya juya mata ya ja bargo ya rufe jikinsa ya shiga tunanin abinda yake ciki, shi sai ma yake jin baya zumudin auren nan a yanzu ko dan ya ji halayan mahaifiyarta ne?
Oh duniya yana mamakin irin yanda mutane son kudi ya rufe masu ido
Asuba ta gari angon RAUDA🥰
yanda ta ga rana haka ta ga dare, Malan Ahmad bai kwana cikin gida ba, sam bai ko leko su ba har garin Allah ya waye
Motsin yayanta suna shiga wanka ya saka ta mike dan dora masu zazafe
Tana faman hasa wutar ya shigo da salama ciki ciki,
Da sauri ta mike ta amsa ta shiga gaishe shi aman ya yi tamkar bai ganta ba ya ja ya tsaya kofar dakin su Rauda ya kirayi sunnanta
Da sauri ta amsa ta zumbula hijabinta ta fito ta duka tana gaishe shi
Yannayinta yake karantawa, kamin ya sauke ajiyar zuciya, a sake ya amsa mata tamkar ba abinda ya faru ya ce" akwati da na baki jiya su ne suturun da mijin ki ya umarta da ki dawo sakawa, sannan ya ce akoy takarda a ciki , sai maganar zuwa aiki ya ce akoy waya a cikin akwatin idan kin dauka zaki ga sunna daya a ciki sai ki kirayi number ya kaiki wajen aiki ya dawo da ke
Kanta a kasa take dan dagawa mahaifinta har ya gama ya ce" Allah ya yi maki albarka , ya juya ya barta nan tsugune ya fice a gidan ya bar Mariama baki bude, ta shiga tambayar kanta " kai malan fushin nasa har ya kai haka?
Raudat kuwa ta shiga wani hali, a kasan zuciyarta take tambayar kanta " wannan shi kuwa wanene? Yaya sunnan sa ? A ina yake? Anya kuwa zai yi adalci a rayuwa? Ya ba zai zo ya isar mata da sako ba sai dai ya aiko mata da mahaifinta?
Komawa ta yi dakin ta zauna ta jawo akwatin ta bude
Dadagawa ta shiga yi cike da al.ajabin wannan lamari,
Dogayen hijabai ne da dogayen riguna bakake kirin ba komai a jikin su sga sheken kauri sai gam irin ta hannu da safa da kuma likaf!
Cike da mamaki ta mayar da kayan gefe ta dauko wayar yar karamar nokia ce tsohuwa harda wani dan zare an daure ta, da mamaki ta juya ta dadaga kayan, sababi ne, sannan da gannin yadidikan zasu yi tsada, kuma basa warin gonjo, aman wayar ko a dari biyar da wuya a saye ta, mamaki ne ya kashe ta ta mika hannunta ta dauko takarda fara kar da ita an yi rubutu kamar haka..............
.........
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
2⃣5⃣
Lettern ya kunshi magangannu kamar haka: A yau na zo masalaci dan gabatar da sallar da ta kama ni a hanya na tarar da datijo ya zo da maganar zai aurar da yayansa *sadaka*, ina zaune ina kallo har kowa ya watse ba wanda ya taya, na jinjina abinnan harma na yiwa kaina tambayar *WHO ARE YOU* haka da har *bakin jini* ya yi maku mugun shiga? Ko kuwa *Munin ku ne ya yi yawa?* ko kuwa kun *tsofe* masa ne a gida ba mashinshini? ko dai *HALAYAN* ne sai a hankali? *I don.t know🤷♂* gannin du an watse an bar shi *Tausayin* datijon nan ya saka na kasa tashi sai da na karbi *tayin sa* aka daura min aure da karamar mai sunna *RAUDA*
*ASALAMOU ALAIKI RAUDA* ni musulmi ne, wanda ya san darajar aure, koda kuwa ban sanki ba dole ne na fada maki cewa ina kishin du abinda yake nawa! *RAUDA YOU ARE MINE!* an aura min ke ina so ki kare min mutuncina kafin na bada lokacin da zaki zo gidana da matana domin ba ke daya bace,
Mahaifinki ya shaidan kina aiki dan samun kudin makaranta, bani da damuwa da *NEMAN NA KANKI* da kike a yanzu aman ban yi maki alkawarin zai dore ba, ga tufafi ki yi anfani da su,su ne zabina indai zaki tsalake soron gidan ku, idan da magana sai ki rubuta ki baiwa Malan zai bani! Kar ki manta *AUREN HADI* aka yi, *BIYAYA* wa umarnina ya zama dole.
Ta maimaita karatun wasikar nan ya fi a kirga har Aisha ta yi tafiyarta tana mitar bata gama ba
Firgigit ta yi kamar wace aka zubawa ruwa a jikinta ta jujuya takardar tana tunani, ita fa daga jiya zuwa yau ta kasa gane a raye take ko a mace? Takardar ta kuma budawa dan sake karantawa sai ji ta yi wasu zazafan hawaye sun wanke mata fuska,
Kanta ta kifar a jikin bed dinta ta saki wani dan marayan kuka wanda yake fitowa da kyar domin muryar ta a shake take sosai
A fili ta furta" *WHO ARE YOU 2?* ya aka yi ka iya zarowa mutun dan adam zafafan kalamai haka dan Allah ya hada ka da shi? Ka yi hakuri, kar ka koya min baudadan halaya domin nakan koyi yanda mutun ke son zama da ni ne, ka yafe min *ka sake ni* domin ni ma bani da sanayar za.a hada ni aure da kai da na kiyewa wannan kudiri!
Ta dan jima kamin ta mike ta goge idannuwanta ta saka doguwar rigar ta zumbula hijabin sannan ta saka safar hannun da na kafar gaba daya bakake ta dauko nikaf din ta dauki yar wayar ta latsa kira aman har ta mutu ba.a daga ba
Gannin ta kusa minti ashirin tana jira kawai ta dauko pos dinta ta fito ta yiwa mahaifiyarta salama jiki a sanyaye ta fita inda mariama ta bita da kallo
Tana fitowa abin mamaki ta ga wata mota kofar gidan baka da bakaken madubai sannan kamar ta mugun jin jiki kamar an yi accident da ita dai,
Hon aka yi mata sannan flashing ya shigo wayar dan haka ta nufi motar gannin an bude kofar bayan dukan alamu suka nuna ita ake yiwa magana
Asalamu alaika malan ko kai ne aka turo ka kai ni wajen aiki?
Rauda ta