Showing 75001 words to 78000 words out of 122108 words
Chapter 26 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
yi Aisha ta tsareta da kallo ne na tausayi, a gaskiya tana tausayawa kanwarta kennan har yanzu basu shirya da mijin nata ba? Shi yasa da ta ganta ta rikice, gaskiya aba ya iya hukunci, han ai Allah ya taimake shi ba ita yayiwa haka ba da ya sha kunya
Aisha ta taba kafadar Rauda ta ce" haba lallana, menene? Har yanzu baki shirya da mijin naki ba?
Rauda gannin Aisha bata fahimci inda ta nufa ba ya sa ta shiga gurgiza kai tamkar ta yi laifi mamanta ta tsareta da bulala, murya a sanyaye ta ce" shi ne fa aunty?
Aisha ta ce" mene? Wai meye ne?
Gannin Rauda ta kasa amsata ta juya wajen sarah dake kallon Rauda da yannayin tambaya, irin shigar jikin Rauda da yannayin fatarta bata nuna a cikin wahala take ba duda ta dan fada aman ba wani can ba, aman wa take aure haka? Ki waye shima ba laifi somin gaskiya sam Rauda bata yi kalar wace ke cikin wahala ba
Kafin Aisha ta yi magana Sarah ta matso tana mai cire gilas din idonta ta ce" kinga Aisha mu yi mu je mu gama abinda ya kawo mu tun kafin yama yayi, domin na ga kanwar nan taki banda jaje ba abinda ta iya
Aisha ta sauke ajiyar zuciya ta kuma kallon Rauda ta ga du a rikice take tamkar ta yi karya, sai zufa ke tsatsafowa daga goshinta, hankalinta ta bata da kyau domin ta sani haka kawai Rauda bata irin haka sai da kwakwaran dalili, muryarta ta kausasa ta ce" menene? Kukan me kike?
Rauda ta kara riko hannun Aisha sa kyau ta ce" ni kaina sai da ya zo na ganshi!!!! Ta karashe tana mai fashewa da kuka
Aisha cikin kufula ta ce" wai wa?
Rauda ta dago da sauri muryarta na rawa ta ce" shishishii......elhajin, Elhaj Sudais din ,..........shi Uban masu gidan
Gaban Aisha ne ke faduwa haka kawai tun kafin ta idasa fahimtar inda ta nufa, ta ce" Elhaj Sudais, wani abin yayi maku ne? Mijinki aiki yake yi masa ko? Wulakantaku yake ko me?
Rauda ta jimke hannun Aisha , cike da sakin baki ta ce" shine Aba ya aura min, Aunty shine mijina! Aman aunty mu dukanmu a rashin sani aka yi, baya sona nima bana sonsa, aunty daman cewa na yi daga an yi adu.ar arba.in din matarsa zan nemi sakina na nemi alfarmar ya aureki, Aunty ni kaina ban san haka zata faru ba sai da na ganshi
Sudais dake tsaye shi da Samir mutuwar tsaye yayi, ba abinda ke dukan kunnensa sai bana sonsa baya so na, soma nake ya sakeni!
Karar mari ne ya saka shi kallo wajen da sauri
Aisha da ta yi mutuwar tsaye ce ta daga hannunta ta wankawa rauda wani kafirin mari mai kausashen kara da zazafen zafi, kafin ta sauke hannunta na dama ta kuma wanka mata da na hagu a dayan gefen, ta cakumi wuyan rigarta wanda har rigar ta dage, sosai ta yi mata shaka wanda Rauda taki kokarin kwatar kanta ta tsaya tamkar wata sauna Aisha na jijigata
Da gudu Hafsat ta zo ta shiga kiciniyar kwatar Rauda , Wanda Aisha ta yi kukan kura ta hankadasu gaba dayansu
Rauda da kwatakwata ba laka a jikinta ta je zube nan Hafsat kuwa ta yi tagataga zata zube da kyar ta rike kanta
Zaman yan bori Aisha ta yi tana kallon Rauda, ta jima kafin take kwala wani uban ihu ta ce" mijinki? Mijinki ko mijina? Mijina ne dan ubanki! Nace mijina ne Rauda Ahmad! Ni da ke wa ya fara ganninsa? Ni da ke wa ya ce yana sonsa? Na gina mafarkin rayuwana ne da shi, ko bashi da komai na tsara rayuwana ne da shi, me ya kaiki gangancin nan? Kece shaidar irin azabar da na tabatarwa du macen da ta yi gigin rabarsa! Aman shine ke kika aure shi?
Tana gama fadar hakanan ta mike ta nuno Rauda da yatsarta da irin kallon nan mai shige da kashedi ta yi kak da bakinta ta juya ta bar Sarah nan tsaye tamkar gunki, Sarah abin tsoroma ya bata, wai daman Rauda ce Elhaj Sudais Uban masu gida ya aura? To ta yaya aka yi haka? Daman aban ya san ko waye? Ina ba zai yiwu ba dole sai ko ya kara da ni ko ya saketa kowa yayi biyu babu dan ba zai yiwu yar gidan Ahmad mai faskare ta auri wannan mutumin ba, ya fi karfinta
Itama da sauri ta juya ta bi bayan Aisha wace ta nema ta rasa
Idan ka ga Aisha na sheka gudu zaka rantse da mahaukaciya ce, fuskarta shabe shabe da hawaye, idannuwanta jajir, majina wata kan wata
Gudu kawai take ita kanta bata san iya gudun da ta yi da kafarta ba, iya adadin lokacin da ta dauka tana yi ba, sannan kltn da ta ci ba, ita dai ta ganta a anguwarsu harma mutane na binta da kallo wasu su mike suna masu tambayarta lafiya? Wasu su shiga hangen bayanta ko biyota aka yi? Wasu kuwa su zundo bakinsu a fili su furta" kontan gidan Malan Ahmad ce, tana yawon nan ita batai auren ba ita bata zauna a gidansu waje daya ba, mai yiwuwa ta jajibowa kanta hauka ( wa iyazubillah )
A dubu ta afka gidansu,
Tana shiga ta nufi malan dake kokarin ajiye faskarensa ta tsaya tana kallonsa tana muguwar shashekar kuka,
Hannayenta ta cusa cikin kanta ta yamutsa, murya a shake dan irin kukan da ta ci ta ce" na kasa yarda da abinda ya faru Aba,
Aba wa yake auren Rauda ne?
Mama da ta fito da ruwa a buta ta saki butar ta fadi kasa, tsoro ya hanata karasowa dan a yanda ta ga Aisha bata so kalma daya ta fito a bakinta kan Rauda dan tana tsoron ta furta Rauda ta mutu
Malan Ahmad kansa gabansa sai da ya fadi, me ya sami Raudarsa? Rabonsa da ita tunda ya kaita bai kuma bi ta kanta ba, meke faruwa ne?
Aba ya ce" Aisha Lafiya?
Aisha ta daki garun dakinta da hannunta na hagu cikin karaji ta ce" Aba wa yake auren Rauda nake son ji!
Malan Ahmad ya matso da sauri kusa da ita ya ce" wani abin ya faru da raudar? Shi nake son ji Aisha ki daina fadar min da gaba dan Allah
Aisha ta juyo wajen Mama, da sauri ta karasa wajenta ta riko hannunta suka matso kusa da Malan ta ce" kin san wa Rauda ke aure? Kin kuwa san wa take aure? Rauda na auren burin raina! ABA, wanda kika ce shine mahaifina , ya yi zabunta ya aurawa Rauda mutumen da nake son aire, Mama Rauda na Auren Elhaj Sudais mama
Da sauri Mama ta dafe kirjinta, nan take ta shiga maimaita innalilahi wa inna ilaihi raj.une,
Kallonta ta maida wajen malan tana jiran jin karin bayani
Malan yayi sokoko shi kansa yana jin wani aabon magana kuma, shi dai yakan tsinci magana Aisha na yawaita fadin Elhajinta, Elhaj sudais dinta, aman daman Elhaj Sudais din da Ya aurawa Rauda? Tabas shi ne ( Aba ya san wanda ya aurawa Rauda, domin mahaifin elhaj sudais ya fada masa komai a tsanake bayan daurin auren sannan ya fada masa suna son a kaita wannan gidan, bai fada masa dalili ba shi kuwa bai yi tambaye tambaye ba, shi dai ya san Elhaj sudais ya fi karfin ya saka matarsa a muhalin nan, sai kawai ya taya shi yin abinda yake muradi ya ringa baiwa Rauda sakon Sudais idan direba ya kawo ko Samir, kuma ya karbi na wajen Rauda ya basu ) har ga Allah, Har cikin zuciyarsa ya ji wani iri, sannan ya ji tausayin Aisha, koda soyayar Da take yiwa Sudais ba wai ta ko yana halin rashi zata iya zama da shi ba domin idan bashi da shi ya tabata Aisha ba zata iya zama da shi ba, aman duda haka ya sani so ciwo ne
Dan sanyaya muryarsa yayi ya ce" Aisha, ki yi hakuri, Du abinda kika ga Allah ya dorawa bawansa dan ya jaraba imaninsa ne, idan kin yi hakuri na tabata zaki girbi alkhairin hakurin,
Aisha da muryarta ya gama shakewa cikin yannayin taratsi ta ce" bana so, bana so, ka yi shiru, a yau ina da kokonta idan har kai ka haifeni
Mama da sauri ta ce" Aisha!
Aisha ta juyo wajen mama ta ce" mama ina kokonton hakan, mama na fada ! Na fada!
Mama ta daga hannu ta wanka mata mari abinda bata taba yi mata ba, sannan murya na rawa ta nunata da yatsa ta ce" mace bata taba yin shege ba, ko cikin dubu ta san waye uban yayanta! Ban taba kauce hanya ba, ina adu.ar da na kauce gwara Allah ya karbi raina, ki tauna harshenki kafin ki jefemu da magangannu mararsa fa.ida
Aisha dafe da kuncinta ta tsare su da kallo, magaifinta jikinsa a mace yana ta kukan zucin yarsa bata da tarbiya , sai mama dake kuka tana tsaye itama tana kallon Aishar
Juyawa ta yi ta harhada kayanta cikin yar jakarta gari yayi zahi ta fito da hijabinta buguzun buguzun zata fita
Ido mama ta zaro ta nufota ta kamata ta ce" Aisha ina zaki je? Menene haka wai? Me yasa kika fiye daukan duniya da zafi?
Aisha ta ce" tafiya zan yi inda na fi wayo mama, na bar maki gidan!
Kokarin rikera mama take tana daukaka kukanta Aisha ta fizge ta fice
Da sauri ta juyo ta zo wajen malan tana nuna masa da ya hana Aisha fita,
Hannayensa ya saka ya jawota jikinsa ya rungumeta da kyau yana dan bubuga bayanta (😳), murya irin ta manya ya ce" zata dawo, in sha Allah kuma zata dawo yanda ta fita domin sai ta fita zata daina *RAINA INDA TA KE* mu sakata a adu.a kar duniya ta yi mata mugun horo
Jikinsa a mace ya karaso inda take yashe,
A dan tsorace take kokarin tashi ya mika hannu ya tayar da ita tsaye
Kunace mata waje yayi, murya can ciki ya ce" *YA AKA YI KIKE MIN IRIN WANNAN KIYAYAR HAKA?*
Fuskarta da take kawarwa tana ta sheshekar kuka, abin yayi mata yawa, ya rike da kyau ya saka idonsa cikin nata ya ce" *sai dai ki sasauta kiyayarki domin rayuwa da kiyaya ba kyau fa, kuma kinga aurena ba saki*
Yana gama fada ya saketa cike da jin ciwon magangannunta wai bata sonsa ! Shi a ina ya taba ce mata baya sonta? A gaban Hafsat, da Samir, harda bakin fuska ta furta kalaman nan
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
4⃣1⃣
Yana komawa ya zauna cikin mutane yayi jigum da shi, su Abansa ne da jama.arsa datijai da samari, *Bana son sa* ya daki zuciyarsa wanda ya ji tamkar ta watsa masa mari, bana son sa, ya sakeni,
Kawar da kansa yayi ya ce" *MATA, NI INA SONKI*
Wayarsa ya lalubo ya sami number Hafsat,
Tana dagawa bai tsaya dogon turanci ba ya ce" ku fito direba ya kaiku gida,
Hafsat na kokarin yin magana ya katse kiran
Dubanta ta mayar wajen Rauda dake zaune tana jan carbi hannunta na dama na hagun kuwa ta talabe fuskarta
Momy ce ta shigo da salamarta ba mai kara ba, tana zuwa Rauda ta gyara zamanta irin dai zaman gaban sirikai ga mai kunya 🤣
Wajen madubin dakin Hafsat Momy ta zarce ta jawo ta bude ta ciro wata leda da ta yi ajiya ta taso da niyar tafiya Hafsat ta ce" mom yaya ya ce mu juya gidansa yanzu
Jim ta yi ta juyo, ta kali Hafsar kafin take maida dubanta wajen Rauda da take ji tamkar tace ba zata je ba, sai ji ta yi momy na cewa" ALLAH YA TSARE
Haka suka fito wanda bayan sun fito suka ga fitar motar Humaira, da alama dai ba su kadai aka kora gida ba
Direba na kaisu gida Hafsat ta fice ta shige, da gangan take yiwa Rauda fuska, taki ta kulata ko yayama
A hankali jiki a mace Rauda ta fice ta bi bayanta sai dai wani tashin hankalin Su Humaira ne da kawayenta biyu gogagun yan bariki an baje koli ana rangada buda ana ta dariya irin dariyarnan mai kara tamkar an yi masu albishir din ba zasu mutu ba aljannah kawai za.a saka su!
Cikin sanda da takun da bata so a lura da ita take kokarin shigewa bata san ta makaro ba domin kawar Humaira wace ta zo karbar gold dinta ta kai ta anso kudin ta ganta
Iye? Haka ake maki bariki a cikin gida kawas? Wannan kugu haka? Kike yarda ana saka abaya kawai a cikin falo?????
Humaita ta juyo, gannin Rauda ta buga wani uban tsaki, ta ce" daga baya ba, mijina ya fi karfin yan yawo a titi suna neman cin yau da muhalin kontar da kai kafin gari ya waye a fantsama, ke uwarsu fa har gobe yawon maula take!
Kuma du isar yarinya da wani fi.ilinta a banza domin mijina bai damu da shinfidarta ba
Wani irin birki Rauda ta ja ta tsaya, juyowa ta yi ta sauke kwayar idannuwanta da sukai mata jajajir sakamakon kukan da ta sha, a kasan zuciyarta take ayanna wai wannan matar me take nufi da ni? Sanyin halina? Ba yana nufin ina daukan iskanci kan iyayena ba? Su kuwa meye laifin su? miji? Gaba daya kanka ne nake gannin wannan abubuwan? ELHAJ SUDAIS kai ka yi min, matarka ta yi min, duniya ta yi min, gidanmu a yi min? Kanka kai daya kwalin kwal? Na sani kai din nama ne daya cikin miya, ka zamto lu.u lu.un al.umah ! Ido Aunty ta rufe ta wanka min mari sanadiyarka! Ta yi ikirarin ni da ita mun shiga takun saka....... ga matarka na zagar min iyaye
Ke ubanta fa almajiri ne, kuma faskare yake na itace kofa kofa kafin ya samu naira dari sai ya wuni yana bin rana
Hafsat ce ta fito da sauri ta nufo wajensu domin magangannun da suke tun karfi suke yi dan su hasalata, har hafsat dake danne zuciyarta ta kasa ta fito ta ce masu su daina ba kyau, da sauri ta karaso wajensuta ce" haba Aunty, haba aunty, menene wannan din dan Allah?
*HAFSATTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTTT* .....da mugun karfi ta ji sunnanta kamar daga sama
Waigawa suka yi a tare wajen da amon muryar ya fito sai ganninta sukai ta tunkaro wajensu a mugun harzuke
Tana zuwa ba tare da wata wata ba Rauda ta daga hannunta ta tsinke Humaira da wani gigitacen marin da ya saka Humaira gannin walkiya ,
Kan uba , kawayen Humaira suka furta tamkar an hada bakinsu sannan suka dora hannu a saman kai,
Abinka da mai bltng tuni fuskar Humaira ta haye san hannun tas ya fito saman fuskarta, kawayenta tsofafin guzumaye suka zazaro ido, mai suna Laure ta.ce" kutumar ubancen, ke Humaira lale wannan karon an dauko maki ruwa dafa kanki, wannan mari haka ? Aman gaskiya idan har kika kyaleta ta gama shawo da ke
Humaira abin ya zo mata a ba zata, me? Mari? Ita anya ko tana yarinya an taba marinta kuwa? Kuma mijinta ba mai duka bane, shi ya san wajen dukanta, aman yau gashi yarinya karama ta daga hannunta ta sharara mata mari, rasa mai zata ce ta yi sai ta ce" ni kika mara?
Rauda dake tsaye kuda da Hafsat , Hafsat sai zaro idon mamaki take tana kara kallon Rauda, daman ta iya fada? RAUDA ta ce cikin dakakiyar murya" an mare kin, ko kin fi haka tsufa kika zagar min iyaye sai na nuna maki na san darajarsu, kuma a kan menene kike wannan abin? Kan Miji? *MIJIN MU?* bani da niyar zama da shi a da, aman walahi zaki gane ba a hayagaga take ba, zaki banbance aya da tsakuwa! Du wace bata bi ni a laluma ba , zamu kure iskanci ni da ita daga ke har du wata mai jin tashen iskanci dan na Auri ELHAJ SUDAIS! *yanzu na dauri damarar zama da shi shege ka fasa*
Humaira wani irin duhu duhu take ganni, kukan kura ta yi ta shigi Rauda da dukan karfinta da duka inda kawayenta ke turata
Da dukan karfinta take tarewa inda Hafsat ta samu ta banbareta daga jikin Humaira ta jata kiiiiiiiiii da gudu sukai dakin Hafsat din domin shine a kusa da wajen
Sai bayan sun shiga Rauda ta ga gashi a hannunta da sauri ta yar , Hafsat ta bi abin da kallo karin gashin ne Rauda ta tsigo daga kan Humaira ita kuwa ta cira mata mabalan riga sannan ta yage mata wuya da hanu
Hafsat ido kawai take zarowa tana kallon Rauda, daman ta iya fada haka? Daman ta iya maida martani haka? Kennan kamar da ake cewa mutun na mayar da kansa wawa dan a zauna lafiya hakane? Bata taba tunanin akoy abinda zai sa Rauda ta daga muryarta , ta rama kai har ta kai da jikinta ya tabu ba, ya ilahi Raudar ce kuwa? Kai yau ta birgeta karshe, lalai in dai haka ne hankalinta ya konta ta yarda Rauda ta san me take yi, ta tabata irin wulakancin da yayarta ta yi mata ya sa zuciyarta ta fara kekashewa, idan kuwa hakane ai abin yayi dadi ta kaita bango ya kasance ita dinma ta daina raga mata domin na ga yayar nan tata sam ba tausayi da tunanin abinda ya dace a lamuranta ( to fa😌, an kai Rauda bango ta fara duka🙆🏽)
Aisha bata zame ko.ina ba sai gidan su Sarah,
Tana zuwa da kuka ta zube jikin aunty ta kwashe komai tana hawaye ta fada mata
Da kallo aunty take binta, ta karewa jakarta kallo, dankari yau ake balaki, tana nufin a nan zata zauna? To