Showing 21001 words to 24000 words out of 122108 words
Chapter 8 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
wajen jeux de lumiere din dake hasko wajen, nan ta fahimci inda ta sanyo kafa
Tunani ta afka, ita dai a jakarta naira dari biyar ce, wace zasu cacafta kudin yau da na gobe ne kowa da nasa a jaka domin idan bus ne baki danja ake ajiye su
Dago da kanta ta yi, ta kali ruwan Awa da aka ajiye mata wanda haka ake yi idan dai ka shiga wajen nan to za.a yi maka kyautar ruwa masu sanyin ni.ima
Ajiyar zuciya ta sauke ta ce" excuse me plz
Ta fada tana mikewa dan barin wajen
Murmushi yayi, a yanda ya fahimta tana cikin matsi ne, sai yayi murmushi kawai ya bita da kallo har ta fice haka kawai ya tsinci kansa a cikin nishadi na wannan dan lokacin da ya kali wannan baiwar Allahn
Yau tafiyar kowa tasa yayi, tana zuwa gida wanka ta yi domin tana cikin fashin salah, ta zauna ta dauki litafin hausa mai suna *Neman na kaina*, tana jin dadin yanda ta cikin litafin le neman halalinta ba tare da ta kauce hanya ba
Raudar na ciki ne?
Muryar mamansu ta katse mata karatun ta amsa tana fadin" eh mama gani na zo ne?
Shigowa ta yi tana fadin" aa aa,
Zama ta yi gefen Rauda ta karbi litafin hannunta ta maida dubanta wajen Rauda wace itama ta tataro hankalinta wajen mahaifiyar nata
Nana mariama ta ce" Rauda, wai ya haka nake jin shiru haka? Ita Aisha idan na yi magana sai ta nuna ai ita ga wanda take jira ke kuwa shiru kawai ba magana
Rauda ta lumshe idannuwanta bata ce komai ba, mamanta ta ci gaba da fadin" ni na rasa mai ke damunki haka? Mai kika rasa na ya mace aman na kasa samun wanda zai fito yana son ki da aure, ko dai ke kike korar su?
Ajiyar zuciya Rauda ta sauke, a hankali ta ce" mama, aman ai ina da manema ko?
Nana Mariama ta ce" ke dan Allah kar ki kawo min wannan zancen, su waye maneman naki? Daga mai bayar da hayar kura, sai malamin primari, sai mai kanti? Ke kina tunanin zan amince da wannan shirmen ne? Ko daya wannan ba abin duba bane dan haka ki yi zuciya irin na yar uwarki ki zakulo min wani elhajin nima nan da yan kwanaki na zama uwar hajiyoyi
Rauda kasa furta wata kalmar ta yi domin abin ya girmami tunaninta, mahaifiyarta ta mike ta fita, har ta tafi ta dawo ta dage dan labulen kofar dakin nasu ta ce" sai dai kar ku manta daga ke har yayarki abinda bana gajiya da maimaita maku *duk wace ta amince da Da namiji ba da aure ba ban yafe mata ba!*
Tana gama fada ta fice
Rauda ta yi murmushi mai kuna ta gyara shinfidar katifarta ta konta ta daina karatun novel din domin ta daina jin dadinsa
.Washe gari.
A makare Rauda ta farka tana mamakin bacin da ta kwasa, tana duba agogo ta ga bakwai da minti ashirin da hudu
Cike da mamaki ta kai dubanta wajen Aisha sai dai wayam bata nan,
Sai a lokacin hancinta ya jiyo mata kanshin turarenta sannan wajen kayan kwaliyarta ta cakula su
Ajiyar zuciya ta kuma saukewa a ranta tace kennan Aunty tafiya ta yi ta bar ni
Mikewa ta yi cikin hanzari ta shiga wanka ,
Tana fitowa ta zauna ta shafa mai ta dan murza farar hoda ta shafa man lebe ta fito tana dan gagawa ta gaisar da iyayenta ta fice a lokacin har takwas sauran kadan
Tana fita ta ga Abdurrahman, cike da mamakin ganninsa take gaisar da shi, ta yi mamaki ne domin ita batai masa kwatatancen gidansu ba,
Ya sha farin yadinsa, ya kafa hula baka da takalmi baki, ba laifi ya fito domin kuwa sutura ita ce mutun
Tana gama gaishe da shi ta mike da niyar tafiya
Da sauri ya ce" aa, Rauda sauri kike haka?
Rauda ta ce" eh wly ka yi hakuri ina sauri ne na tafi dan kar latin nawa ya yi yawa
Da sauri ya hau mashin dinsa da ya sha wanki ya ce" ki yi hakuri na kai ki mana Hajiya Rauda, kin ga a hanya sai mu tatauna domin kuwa na sha wahala sosai kafin na samu na zo wajen nan dan na kai sati uku ina zuwa jami.a da kyar aminiyar Auntynmu(Aisha) ta yi min kwatancen gidan
Rauda ta ce" eyah, haka, aman ka yi hakuri Zuwa wani lokacin zamu zauna aman yanzu gagawar dai nake, kuma ka ga ba zan hau mashin dinka haka kawai ana kalona ba
Murmushi yayi yana kokarin ci gaba da zubar ta yi gaba abinta
Sauri take zubawa cikin doguwar rigarta ja, ta yane kanta da mayafin rigar baki yar pos dinta baka sai takalminta irin takalmin robar nan baki
Shar da ita domin sutura komai arharta takan yiwa jikin Rauda kyau ne domin kirarta sai dai a ce masha Allah
Mai adaidaita ta kai hudu ta tsayar kowace sai dai ace mata ai ba zasu kaita a dari biyu ba
Kara saurin tafiyar nata ta yi ta karaso wajen titi ta tari bus ta shige
Abinka da bus sai da aka dauki lokaci kafin ake ajiyeta bakin titi , Tunanin tafiyar ta yi, ta dubi kudin hannunta,
Har ta yi niyar yin tafiyarta da kafarta wani abin yace mata kin ga Rauda ki bi aikin nan naki a sanu kar ki bale shi, domin kuwa a jiya kun yi laifi kar ki kara a kan wanda yayarki ta aikata
Idannuwanta ta rufe ta tsayar da dan acaba
Naira hamsin yace zai kaita dan haka ta haye ya tayar ya kwasheta da mugun gudu
Yana zuwa bakin ma.aikatar ya ja ya tsaya
Ta je sauka kafarta ta dan gurde hakan ya sa ta yi saurin dafe kafadarsa ta hagu tana ambaton sunnan Allah,
Shima yayi tunanin faduwa zata yi dan haka ya dan tarota kadan yana fadin" sanu a hankali dai hajiya kar ki yi ki ji ciwo
Kamar daga sama idannuwansa suka sauka a wannan abin, domin tunda ta zo ya zauna gaban cctv ya tsura wa ecran ido yana mamakin yanda aka yi bai gansu ba
Yana nan ya ga shigowar daya banda daya
Hankalinsa dai bai konta ba yana tsoron kar a je itama aikin ta zo bari dan haka ya hade fuska ya ki bata damar ganninsa ko fita bai yi ba dan kar ta hadu da shi ta gabatar masa da takardar barin aiki
Yana zaune ne yana duba time yana kallon wajen zaman kowace, dayar na nan dayar bata zo ba
Kamar daga sama idannuwansa suka sauka a kan abinda ya faru
Kansa ne ya sara masa nan da nan zufa ta karyo masa mai zafin gaske
Ji yayi jikinsa ya fara bari, kwakwalwarsa tamkar ana yakuna masa ita ne
Mikewa yayi da wani irin karfi ya cire hiramin kansa yayi wurgi da shi ya fara mutsutsuka ido lumfashinsa ya fara sama yana kasa sakamakon bacin rai da sabon yannayin da yakan tsinci kansa a ciki idan ya shafeta
Samir da yayi kira tun fitowarsa ya shaida masa ne ya samu shiga bisa jagorar Aisha da ta yo masa jagora
Suna shigowa sukai tozali da Sudais a cikin wannan yannayi
A tare suka nufe shi, Samir na salati yana sanar da ubangiji , Aisha kuwa ta fashe ta kuka ta ja ta tsaya jikinta na bari na gannin halin da muradin zuciyarta ke ciki
Da kyar samir ya samu ya talafo shi , still jikinsa na barin ya kawo shi saman doguwar kujera ya kontar ya kama takalmansa sau ciki ya cire masa ya bar masa safar ya saka hannu da sauri yana lalubo waya yana kokarin kiran likita
Hannunsa na mugun bari ya dago jajayen idannuwansa ya sauke a kan Samir dake kusa da Aisha wace ke kuka bilhaki tamkar iyayenta ne suka mutu🤦♀, murwa na rarabe masa ya ce" *SSSAM...IR, SAMIR, MATA CE👉*
cike da tashin hankali Samir ya juyo wajen Aisha ya ce" ki kira min number likita plz,
Shi kuwa ya shiga yi masa fifita duda irin sanyin ac din dake office din
Tana kiran likitan ba.a dauki lokaci ba sai ga shi da wata nurse rike da akwatin kayan aikin nasa sun shigo
Suna shigowa suka bukaci su basu guri dan haka Aisha da Samir suka fito
Suna fitowa Aisha ta nufi office dinta, daidai Rauda ta biyota su shirya dan kuwa idan ta biyewa Aisha sai su yi ta fushi haka
Tana shigowa coridor dinsu ta hango Aisha na tsaye tana kuka tun karfinta
Zuciyarta ne ta buga, ta daga kafarta da sauri ta karasa wajen Aisha ta dafa kafadarta ta ce" Aunty, mai ke damunki haka? Baki da lafiya ne? Mai yake faruwa?
Aisha cike da tashin hankali ta riko hannun Rauda ta bude idannuwanta ta sauke a fuskar Rauda ta ce" mai ke damunsa ne? Mai yake hadasa masa cuta irin haka ne? Wacece ya ambata da *Mata*? , shin yana da aure ne? Idan yana da aure bai yi min adalci ba domin ni nafi kowa son sa, ni nake sonsa ba wata ba, ya dace ya kula da ni, ya gane so yana iya halaka ni Lallana
Ta karashe tare da rushewa da kuka
Samir da yake kai kawo ya ja ya tsaya cak, bai san lokacin da ya dora hannayensa biyu saman kansa ba cike da tashin hankalin da yake hangowa
Murya kasa kasa ya ce" *wata rayuwar.......*
I.m sorry nah, typing din dan lokaci ne, kuma bakwa comment balatana na ji ina ai sai na yiwa readers typing😇😇
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
1⃣2⃣
Na: *SAJIDA*
*_🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION_*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
Rauda ta hadiyi wani yawu mai zafi, ta rike hannun Aisha ta ce" ki kontar da hankalinki aunty, du abinda koncin hankali bai bada shi ba tashinsa ba zai bayar ba, Aunty plz ki nutsu mu je office din ki
Girgiza kanta Aisha take ta ce" ba zan iya tafiya ba tare da na ga halin da yake ciki ba, ki tsaya su fito mu je mu ga jikinsa
Ajiyar zuciya ta dawo saukewa domin bata ga ta inda zata bi ta kontarwa da yayarta hankali, wannan lamari sai dai du.a.i kawai
Samir da ya gama kalonsu cike da tashin hankali, domin sai yanzu ya gane inda lamarin ya dosa, a hankali yake taka kafafuwansa har ya koma office din Sudais wanda likita ya gama dubasa ya zauna yana yi masa magana kamar haka" Elhaj Sudais, ka kula da lafiyarka , ka kiyaye abubuwan da ke jefa ka a irin wannan hali domin idan ana haka za.a iya yin barna.... ita zuciya da ka ganta idan ta fara nuna irin haka abinda ya fi dacewa shi ne a kiyaye, a tatale ta, a raba ta da dukan abinda zai kasance izgili wa ita,
Kafin ya karasa magangannunsa Sudais ya dago ya sauke idannuwansa a kan Docter, bayan docter ya hango samir na tsaye shima yana sauraron abubuwan da likitan ke fadi sai gefensa na hagu nurse din ce ta mayar da kayan tana jira su fice
Murya kasa kasa ya ce" har yanzu tana can ko?
Da sauri Samir ya karaso ya dafa kusan hannunsa ya ce" aa, ta shigo daman dan acaba ne
Da yannayin bacin rai Sudais ke kallon samir a kasan zuciyarsa ya ce" Acaba? Acaba fa ka ce? Daman *MATA* na hawa acaba har ya taba jikinta? Daman tana yi min irin wannan gangancin? Shin yaushe *RAUDA!* zata fahimci abinda nake nufi da ita ta furta abinda nake jira daga gareta mu shige rayuwar da nake mafarki nake fata?
Du wannan magangannun yana yinsu ne a cikin zuciyarsa inda Samir ya ci gaba da fadin " suna kofa suna jira docter ya fito su shigo ganninka
Dagowa yayi da sauri jin knocking
Kafin yayi wani yunkurin har Samir ya bada izinin shigowa
Kansa ya mayar ya lumshe idannuwansa yana jin yanda bugun zuciyarsa ke karuwa
Aisha ce gaba Rauda na bin bayanta a tsorace domin sam bata son abinda zai kuma hada ta da wannan mutumi, ita dai bata san dalilin da ya sa take tsoronsa ko dan ya kasance mai akoy sannan mai gidansu a wajen aiki ne? Sai marin da ya yarfawa Aisha har yanzu idan ta rintse idannuwanta yakan sakata saurin budewa domin wulgawarsa kawai take gani
Tsayuwa suka yi, mirya kasa kasa Aisha ke tambayar jikinsa, inda daga inda Rauda take ta dan tsura masa ido, a ranta take fadin" lale wannan bawan Allah dole ya ringa wulakanta yan matan da suka je gare shi domin Sudais kallo daya zaki yi masa idan dai kina da cikakiyar lafiya ki yi fatan samunsa a matsayin miji
Ga kudi ga kyau dole mata su yi haukansa
Dan bakinta ta murguda a ranta ta ce" ba duka yan mata ba domin ni a nan ban ga abinda za.a tarba a zubar da mutunci ba
Samir ne ke amsawa Aisha duda du ya daburce ya rasa ta ina zai bi Rauda ta tambayi uban masu gida da jiki.ba dan kuwa du yanda aka yi hakan zai.sanyaya masa zuciya
Matsawa yayi gefe yanda zasuna ganinsa da kyau ya ce" ku karasa ku yi masa ya jiki mana?
Aisha cike da farin ciki ta ja hannun Rauda sai kusansa suka ja suka tsaya inda Aisha ta yi masa ya jiki,
Bai amsa ba, sai adu.a da yake yi kar ya mike ya tataka su a wajen nan dan kuwa kowace cikin su haushinta yake ji
Muryar Rauda ta daki dodon kunensa ta ce" sannu Allah ya baka.....
Bata kai da karasa maganarta ba ya bude idannuwansa tar a kanta, fuska a hade, ya zabga mata hararar da ta kada hanjin cikin su ya ce" get out f my office!
Da sauri Rauda ta rintse ido jin yanda maganar tasa ta karade office din da wannan muryar tasa mai kama da amon zaki,
Bata gama tantance a inda take ba muryar ta kuma razanar da ita inda ya firfito masu da idannuwansa ya kalo su gaba daya ya watsa masu kallon kyama ya ce" i said ku fice min a ofiice ko bakwa jin sautin murya ne?
Da sauri Raudat ta juya ta fice Aisha ma ta biyo bayanta
Basu zame ko.ina ba sai office din Aisha,
Rauda na shiga ta zarce ta dauko ruwan sanyi cikin frij ta bude ta sha sannan ta shiga sauke ajiyar zuciya,
Bata san lokacin da ta ce" tap, wannan mutun akoy jikeken kawai, gaskiya masu zama kusa da shi suna shan masifa duba fa ki ga yanda yake lumfashi da daydaya aman ya iya ya dakata ya masifaci mutanen da suka shiga dan yi masa sanu
Ra karashe tana dafe kai
Aisha ma murmushi ta yi ta ce" ai banbancin nasa kenan da wasu gajojin, kin san yanda yake yi mana na ban sha.awa hakan na nunin bashi da fade faden mata komai kyansu
Rauda ta tabe baki ta ce" uhum, aunty wly ni ban ga abin birgewa a wajen wannan gabjejen, kin ga idan Allah yayi aurenki da shi idan alkhairi ne, koda na ziyarce ki to fa sai baya kasa dan kuwa wannan mutumin bashi da wani fara.a
Aisha ta yi dariya domin ta lura Rauda iya gaskiyarta take fada kenan, ta mike ta nufi tatara takardunta a ranta tana fadin" an kusa, dan kuwa yauma ya kuma sauke idannuwansa a fuskata,
Ta lumshe idannuwanta ta ce" Namijin duniya kallonka mai tafe da harara.......
Allahu Allahu La ushirika bihi shai.a.... shine adu.ar da Sudais yayi ta nanatawa a wannan koncin bayan korar su Rauda da yayi,
Gefensa Samir ne zaune a kujerar nan mai juyin mutun guda, ya zubawa abincin da aka kawo wa Sudais aman ya ki ci..
Tunani ne ya sako shi gaba, ya rasa ta ina zai kamo wannan lamari, wai dama *AISHA* ke son ogansa? Shi kuwa ogansa ga dukan Alamu ba Aisha ce ke jan ragamar zuciyarsa ba
Ajiyar zuciya ya sauke ya juyo wajen Sudais ya ce" Elhaj,
Sannin ba zai amsa masa ba, ya ci gaba da maganarsa dan kuwa ya san in dai ya ji koda bai bashi amsa ba ba zai yi masa karya ba, Ogansa baya shakun magana da kowa kai tsaye ya fada masa gaskiya
Samir ya ce" oga mai zai hana ka tunkari matsalar nan da kanka ne? Ina nufin ka tunkareta ka fada mata damuwarka?
Sudais ya dan bude idannuwansa ya jima yana kallon ac din dake daidai kansa , kamar ba zai yi magana ba kuma can ya ce" mai kake nufi?
Samir ya bayar da hankalinsa sosai ya ce" ina nufin oga damuwar nan tunda har ta fara kawo ka haka mai zai hana kawai a fada mata ta amince a yi komai a gama ko hankalinka zai dawo waje guda? Idan ka yi duba da wannan rashin lafiyar da ta fado, da irin yanda harkoki suke sanya, Elhaj baka taba zuwa gari ba ka shigo kampani baka yi zagaye ba sai wannan karin, kar ma.aikata su ankara su fara kokarin kawo sanya a harkar neman nan
Dan tsagaitawa yayi da maganarsa yana adu.ar Allah ya sa bai bata masa rai ba, kai koda ya bata masa sai dai yayi hakuri domin bai ga wa zai fada masa ba, shi kam yana mamaki mutun kamar Sudais yana tsoron mace? Tsoron mace mana sai dai yana labewa a bayan kar ta raina shi da wasu kudiririkansa nasa, harma abin na kokarin jan dama dan kuwa yana hango rigima yana tsoron ka ja na ja ne za.a yi a wannan lamarin
Jin shiru ya sa Sudais ba tare da ya dago da kansa ba ya ce" ci gaba
Samir ya dan daburce, can dai ya ce" daman oga bana son abinda zai saka ka yi kasa ne, aman ka yi hakuri
Sudais ya yi dan murmushi, ya sauko kafafuwansa kan takalminsa ya tsurawa Samir ido, a ransa yake fadin" kennan har ana gannin feeling dina a kan wannan yarinyar haka? Har an gane halin da nake ciki? Ko da yake shi ai shi na saka aikin ya bibiyar min ita dole ya fahimci halin da nake ciki...., sai dai kash