Showing 27001 words to 30000 words out of 122108 words

Chapter 10 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

405

ba ne, wajen ki zuba basirarki ne ki yi aiki tukuru, takardun nan ki koma ki karance su , ma.anar ki fara karantawa dan koda da wani abinda bai dace ya karaso wajena ba ki cire idan kuwa baki fito da niyar aiki ba sai ki kara gaba

Sauraron tsagwaron rashin mutuncin wannan bawan Allah take, mamaki fal zuciyarta to aman meye laifi dan bata iya aiki an koya mata ba?

Cikin sauri ta shiga tatarewa hannunta na rawa ta juya da sauri ta koma office dinta, wato dai lokacin da ya dace ta je ta ci abinci sai ya kasance ta kare shi a aiki


A wannan ranar bata gama aiki ba sai da ta yi yama sosai ta fito a office din inda ta ga sai yan tsiraku

Neman Aisha ta yi bata ganta ba ta juya ta kama hanya ita kadai

Tana shigowa gida magariba na kawo kai, ta shigo da muguwar gajiya har juwa take gani sai dai kafin ta rufe bakinta da salamar da ta yi sai ji ta yi an dauketa da mari

Da sauri ta kallo mai marin, Mamaki shinfide a fuskarta, Muryar mahaifinsu ce ta katse mata mamakinta yana cewa" Aisha, Aisha ina yi maki hani da saurin hannu, tabas kece yayar Rauda aman ki kiyaye saurin bugu sannan yanzu na gama fadar ki yi hakuri ta zo na ji ko?

Murya a raunane Rauda ta ce" Aba me na yi?

Mahaifinsu ya ce" Rauda, ya aka yi kika amince da wajen da yar uwarki take so bayan kina da zabin kin karbar aikin?

Cike da mamaki take kallon Aisha, dama saboda wannan aikin ta zabga mata mari haka?
Bata gama tunaninta ba Aisha ta ce" ta fada min daman tana daya daga cikin masu bakin cikin wannan waje nawa ko me? Daman idan na hau abu na sauka zaki hau shi Rauda? Mai na yi maki da zaki yarda ki yi aiki a kusa da shi, a tunanina koda korarki za.a yi ba sai dai a kore ki ba? Shi ne aka kai ki wajen da nake aka kawo ni wajen da kika bari cikin matan da suke tunanin kanmu daya da su? Du sai na sa ya kore su daya bayan daya, sai na zame masu barazana a aikin su, domin ni na fi karfin su !

Tana gama fadar haka ta juya ta shige ranta a bace, mahaifiyarsu kuwa ko kanzil bata ce ba alamu dai itama tana goyon bayan abin

Murmushi mai ciwo Rauda ta saki, ta kali mahaifinta ta ce" ka yi hakuri Aba , insha Allahu gobe zan je na ajiye aikin dan samun farin cikin kowa a gidan nan


To readers shin ta ajiye aikin ne???





*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




1⃣5⃣



Cike da tausayi ya bi ta da kallo, shi kam bai san yaya zai yi da wannan lamari ba kuma du bai gane inda magangannun Aisha suka nufa ba, aman ba komai ya tabata Allah na tare da mai gaskiya

Sukuku ta yi komai, ko abinci kasa ci ta yi ranta a bace ta yi mamaki da Aisha ta biyo ta wannan hanyar ta fadawa iyayensu, to aman ita bata da tunani ne? Ta ya ma.aikatar da ba ko sisin dalarta za.ace wai tana da damar ta ce a canza mata? Idan har hakan ne ai da itama sai a ce tana da damar cewa nan take so ba zata bar wajen ba ko?
Baci dai sai barawo ya sace ta, tana tunanin idan kudin da za.a bata basu kai na biyan makarantar nan ba fa yaya zata yi kennan?
Gannin ba barcin zata samu ba, sai kawai ta dauro alwallah ta yi nafilolinta ta zauna ta yi ta adu.a kan Allah yayi mata zabin abinda yafi zama alkhairi a rayuwarta

Da safe ma da wuri Aisha ta yi tafiyarta du irin saurin da ta yi dan su tafi tare bata tsaya ta ba

Tana fitowa ta gaisar da mahaifiyar su

A dakile ta amsata dan tun jiya take jin haushin wai ita da take kanwar Aisha maimakun ta taya ta yakin soyayar wannan mutumi ko sa warke da wannan bakin talauci aman aa ita ce ma ta amince da hanyar da zata kusanta yar uwarta da warakar su

Jiki a sanyaye ta ce" umma zan tafi

Amsata ta yi da A sauka lafiya

Fuskarta ta kure da kallo, can ta juya ta fita

Kwata kwata kudin hannunta naira dari da hamsin ce, itama tsohuwar ajiya ce da ta yi dan irin wannan rana domin idan ran su ya bace bata ba ta kudin mota

Bos ta shiga , ita ta kai ta ma.aikatar wace a yau bata zo da niyar yin aiki ba ta zo ne da niyar tambayar salama

Tunda ta zo take zaune ta gama duba takardu ta je office din sa ya fi a kirga sai dai baya nan abin ya daure mata kai kuma ita bata ji an ce baya nan ba

Tana zaune har lokacin tashi ya yi ta fito ranta a jagule tana cike da zulumin abinda zata je ta tarar a gidan ta kama tafiya cikin sauri dan kudin su isa kaita bakin titi

Humaira ce take mikowa Sudais cofee sai turiri yake

Fatiha ya shafa na wuridin da ya zauna ya yi, ya mike bai karbi cofee din ba ya juya ya koma saman table ya dan tatare rigarsa ya zauna ya daura kafa daya kan daya

Da ido Humaira ta bi shi, a ranta kulun mamakin irin yangar Sudais take sai kace wata mace ko a me ya dauke ta tana tsaye har ya gama gyara zamansa sannan ta juya ta tarar da shi wajen table din ta dan risina dan ta san dalilin haka ya sa yayi kamar bai gan ta ba

Karba ya yi ya ajiye saman table din kasa kasa ya ce " thanx (dabi.unsa kennan yakan godewa abin alkhairi yakan yaba kwaliyar matansa da sauransu....)

Kujerar dake gefensa ta ja ta zauna, ta bude kulolin abinci ta zuba a plat daya , ta saka cokali biyu ( shima na cikin dabi.unsa, isan girkin mace ne zata tardo shi ne bangarensa ta gyara ta yi komai ta saka turaran huta dan kuwa du kudinsa bai amince yan aiki su yi aikin bangaransa ba , su dai matansa anai masu komai aman shi sai dai su yi, hakan na saka masu matsala da Humaira domin a kulun sai yayi fadan bayinsa bata wanke ba, zanin gadon da ya tashi a shi bata canza ba turare bata saka ba, wani lokacin sharar kanta bata samuwa sai daga baya ya gane kazanta ce kawai da ita sai ya yi hakuri ya shareta)

Tana zubawa ta tura tsakan table din a hankali ta furta bismillah

Ba tare da ta tsaya ya fara ba, ba wani dan rarashi, ba irin dan ta matsa kusa da shi kawai abincinta ta fara ci
Tana gamawa ta zuba jus na kwali wanda su kadai suke shan abinsu, Sudais yana da son irin jus din natural aman baya samun hakan sai dai ya sha ruwansa kawai wani lokacin ne ma Khairat ke yin na kwakwa

Tana gama sha ta mike ta fice ta yi bedroom dinsa dan canza zanin gadon (🤦‍♀)


Ajiyar zuciya ya sauke bayan shigewarta, ya bi yannayin tsaruwar falonsa da kallo, a ransa yake fadin " to ko dai da ake cewa haisawa basu iya tatalar miji hakan ne? Dukiya ta gidan duniya Allah ya malala masa, sai dai kash ya kasa samun yanda yake so 100/100

Mikewa ya yi yana duban agogon dakin, karfe goma na dare ya nufi dakin Khairat dan gannin jikinta domin a yau rashin lafiyarta ya hana shi tafiya kampani, athmarta ne ya tashi da kyar aka samu ta konta

A hankali ya tura dakinta ya shiga da salama

Tana konce da doguwar bakar abaya, idannuwanta lumshe tana sauke ajiyar zuciya, sosai wannan rashin lafiya ke wahalar da Khairath, bata isa ta kwana biyu lafiya ba sai ta tashi hakan ya sa baya so yana nesa da ita dan Khairath akoy son ta kyautatawa wanda take tare da shi bale shi da ya zama mijinta, dan ma yannayin jikinta na hana ya wani abin aman ta san da bata da girman jiki da ya samu exactly irin kulawar da yake so

A hankali ya duka kusa da gadon nata, ya tsurawa fuskarta ido,
Fuskarsa ya matso daidai da nata, ya dan goga mata sajensa daidai lebenta dan ya lura bata ma san ya shigo ba

A hankali ta bude idannuwanta, sai ya gan su sun yi fari kal kal harda wasu ruwa ruwa a cikinsu sannan sun dan fada

A hankali ya shafi gefen fuskarta da hannunsa na dama murya kasa kasa ya ce" *YA KE MAR.ATUN SALIHA, JIKIN NE BAI DAINA CIWO BA?*

Murmushi ta yi da jin sunnan da ya fada mata, ta dago hannunta da take ji ya yi mata wani mugun nauyi marar misaltuwa ta dora a kan nasa na dama ta ce" yayana, mijina, abokin rayuwa na

Shi ma murmushin ya yi mata ya lumshe idannuwansa
Bai zata ba ya ji ta ce" ba ka taba furtan kalmar so ba *SUDAIS*, ko zaka furta min na kwana da farin ciki a yau?

Idannuwansa ya tsura mata ya kai minti hudu, suna yiwa juna kallon ido cikin ido, kokowa yake da zuciyarsa, fada yake yi mata kan ta daina irin haka har matarsa ta san bai taba furta mata kalmar so ba? Khairath ta cancanci soyayarka koda yar kadan ce dan haka ya sakar mata murmushi ya dafe hannayenta sosai ya ce" *KHAIRATH* sanninki alkhairi ne khairana, *ina son ki*

Wani irin murmushi ta saki har da ajiyar zuciya,

Kansa ya dan girgiza ya lakaci hancinta ya kai mata kis a goshinta ya ce" na yafe maki laifin yau da kulun da wanda na sani da wanda ban sani ba,

Itama murmushi ta yi, wannan dabi.a da ta koya masa tanai mata dadi fiye da tunanin mai karatu, itama a hankali ta ce" na yafe maka laifin da ka yi min na yau wanda na sani da wanda ban sani ba, na yafe maka na kulun kukulun *mijina* kuma ina son ka sosai fa

Shima murmushin ya kuma yi ya yi musabaha da ita ya ce" ki huta lafiya uwar Yayana, Allah ya tashe mu cikin hankalin mu

Da amen ta amsa shi , ya juya ya tafi
Sai bayan ya tafi ta share hawayen idannuwanta ta koma hannunta na dama ta yi adu.a ta shafa ta rufe idannuwanta da fatan Allah ya sa tana cikin masu rai

A kadan ya dau minti talatin a dakin Khairath, yana shigowa wanka ya fada , yana gamawa ya saka kayan bacinsa ya yi bisimillah ya hau bed din sa

Adu.a ya zauna yana yi sosai, bayan ya gama ya shafe ilahirin jikinsa yana kokarin kontawa Humaira ta shigo,

Ta sha shirinta na barci wanda da mai gida ya gani zai rude ne,

Bed din ta hau itama ta yi adu.a ta shafa ta konta ta dora kanta saman kirjinsa

A hankali yake dan shafa gashin kanta, ya jima yana haka kafin yake kokarin fara isar da sakon sa wa ita

Tsai ya tsaya, ya janye hancinsa a hankali ya dan shafa kanta da sigar da zata fahimta ya ce" Humaira

Dan dago da kanta ta yi tana kalon sa dan ta san maganar mai mahinmanci ce,

Idannuwansa ya lumshe tamkar ya rufe su, shi kuwa kure ta ne ya yi da kalo, ya ce" abin nan ya yi yawa Humaira, yana damuna da yawa, bana samun sakewa da ke domin ya kai ya kusan cinye kwayoyin dake baiwa fatarki kariya wanda idan ya gama cinye su baki kuma da inda zaki dafa ki dawo yanda kike,
Farin nan ya isa haka, da ni kika bi da baki yi abinnan ba, dan kuwa bakin ki mai kyau ne

Tunda ya faro maganar bleating din da take ta dan hade rai , ya fito ya gaya mata kawai wari take menene za yana kwana kwana da ita?, shi dai ya fiya takura ita kuwa a gaskiya bata ga abinda zai gaya mata ko yi mata ya hana ta shafa mn bleating ba!

Bata iya ce masa komai ba dan ya hana ta daga muryarta sama da tasa, ita kuwa ta tabata a haka idan ta buda bakinta ba zata fadi alkhairi ba, sauke kan ta ta yi daga kirjin nasa ta yi konciyarta dan nesa da shi

Shima gyara konciyarsa yayi, dan kuwa ba zai bata hakuri ba dan ya fada mata gaskiya tana nufin ba.a isa da ita ba kennan!

Kamar yanda ya saba tashin wuri haka ya farka, ya dauro alwallah ya shiga nafifilunsa

Sai wajen karfe biyar ya mike ya tAsar da Humaira ya fice yana mamakin ya aka yi Khairat bata fito ba

Dakinta ya tura, ya yi niyar shigewa sai ya hango ta inda ya bar ta, saman doguwar gukerarta, sannan abin mamaki konciyar nan dai ne da ya barta ko har ta juya ta kuma juyowa?

Matsowa ya yi a hankali ya mika hannunsa ya dan bubuga gefen da take konce

Bata da alamun motsawa, ya shiga dan bubuga jikinta shiru dai

Gabansa ne ya ji ya yi mugun faduwa dan haka da sauri ya juyota ......


........
..........



.......


*❣IDAN KA RAINA IN DA KA KE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




1⃣6⃣




Faduwar gaban da rabonsa da ya ji irinta har ya manta, saurin taba wuyanta ya yi aman ina sanyi karai jikinta tamkar an saka ta a frij ne, idannuwanta da suke dara dara a dan bude aman ba.a hango bakin nan dake tsakiyar idannuwan,
Hannayensa biyu ya dora a kansa, a fili ya furta" INNALILAHI WA INA ILAIHI RAJ.UNE, INNALILAHI WA.INA ILAIHI RAJ.UNE

gannin kamar tana kalonsa ya saka shi yin karfin halin matsawa sosai kusa da ita ya yi adu.a da dan ruwa a gefe ya shafe mata ido hakan ya sa idannuwan suka rufe
Kirayen kirayen sallah ne ya saka shi mikewa, ya dauko dardumarta ya shinfida ya kabarta sallah dan kuwa ya san ba zai iya fita haka ba

Yana kai kansa sujada na karshe ya ji zuciyar sa ta karye, domin jinsa yayi tamkar jariri, ya ji wani irin kuka ya zo masa, ya ga idan bai fadawa Allah ba wa zai fadawa? Ya ji shi a gaban shugaban shuwagabanni, wanda shi ya ba shi Khairath a matsayin mata kuma a yanzu da ya karba sai ya ji yana bukatar kai kukansa ko zai ji sanyi,
Sosai yake hawaye yana yiwa Allah godiya da irin wannan jarabawa ta yau, ya roki Allah ya ba shi ikon cinye jarabawar, ya karbi bakuncin matarsa ya sa Aljanna ta zamto makomarta, a cikin sujadarsa yake fadin" ya Allah, Khairath matata na yafe mata dukan kuraran da ta yi min da wanda na sani da wanda ban sani ba,
Ya jima yana adu.a kafin yake dagowa ya yo tahiya ya salamce,
Adu.a ya tsaya ya yi sosai kafin yake mikewa

Table din dakinta dogo baki ya sauke shinfidar saman ya dauko shi ya ajiye ya koma ya ciko ruwa a bokici mai girma ya dauko moda ya saka, ya dauko turaren miski dake gaban madubinta mai yawan gaske, ya dauko auduga ya dauko tawul biyu sababi masu girma, jikinsa a matukar mace ya bude akwatinta dake ajiye ya ciro *SUTURAR KARSHE* a wajen da ta nuna masa a dinkin karshen da ta yi domin takan dinka wata ne idan ta kara kiba ko ta zube ya fito yana kara share hawaye

Hannun rigarsa ya dan gyara ya samu da kyar ya dora ta saman table din domin nauyinta ya karu sosai abinka da gawa

Niya ya dauka a cikin zuciyarsa kafin ya maida hankali cikin nutsuwa yana binta a hankali ya cire mata tufafinta ya rufe mata sirinta da tawul din nan wato *TUN DAGA SAMAN MAMANTA HAR ZUWA DAIDAI GWUIWARTA, IDAN KUWA NAMIJI NE DAGA SAMAN CIBIYAR SA SUWA DAIDAI GWUIWAR SA* , cikin nutsuwa ya saka hannunsa na hagu ya dago ta kadan ya san jingine ta da jikin sa ya dan dadana cikinta dan ya baiwa damar datin dake cikin ta fitowa,
Bayan ya gama ya mayar da ita ya kontar kafin ya saka safar hannu a hankali ya wanke mata sirinta ya wanke du wani dati kana ya fara yi mata wankan sabulu,
A hankali ya bi ta da sabulu ya wanke ta tas da ruwa yana yi yana karanta mata suratul yasine a cikin zuciyarsa
Bayan ya gama yi mata wankan sabulu ya dawo ya bi ta ya yi mata alwallah (cikin alwallar ba.a zuba ruwa a baki sannan ba.a shaka ruwa a hanci sai dai a dan shafa) sannan bai wanke kafafuwan ba ya koma ya kuma yi mata wanka da ruwan zamzam ya fara wanke kan ta, ya wanke gefenta na dama har kafafuwanta ya dawo na hagu ma ya yi hakan sannan ya dora kafarta na hagu kan na damarta, ya yi dabara da kyar ya samu ya wanke mata bayanta sau uku, haka ya yi da dayan gefen ma
Yana gamAwa ya dauko dayan tawul sin ya bi ta a hankali

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login