Showing 33001 words to 36000 words out of 122108 words
Chapter 12 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel
ta yi, ta dora hannunta a saman wuyanta, da sauri ta janye hannun tana fadin ta faru ta kare domin kuwa jikin Rauda har wani huci yake saki kuma da alama bama ta gane wanda ke kanta ta fara yin nisa
Jiki a sanyaye ta konce harshen zaninta, daman da dari uku ta tashi, mahaifin su Rauda ya kara mata dari hudu kafin ya fita, Aisha ta karbi dari hudun ta bara mata ukun wanda ta yi niyar ta baiwa Rauda dari biyu ita kuwa ta sha garin kwaki da rana
Ajiyar zuciya ta saki domin kiwa dari ukun nan ko kudin mota ba zai ishe su zuwa asibitin gwanati ba bale a yi maganar siyan magungunna dan kuwa koda an duba ka kyauta kai zaka sayi maganinka
Mayar da dubanta ta yi wajen Rauda, dan haka ta mike da gagawa ta janyo hijabinta ta kara dakin na rauda ta fita da mugun sauri ta tari mai napep ta dawo ta talaba da kyar ta saka mata hijab ta fito da ita ta rufe gidan suka shiga adidaitan ta yi masa kwatancen gidan yar uwarta ko Allah zai sa ta bata wani abin ta kai Rauda asibiti
Suna zuwa ta fito da rauda ta bashi dari biyu da hamsin yayi mata sauran naira hamsin ta talaba Rauda ta shiga gidan bayan ta gaisar da mai gadi ta gaisar da kishiyar yayar tata wace ta amsata a yatsine tana nuna kyankyaminta a fili
Tana shiga baban falon Yayar tata ta samu ta shinfidar da Rauda saman doguwar kujera saman wani dan kwali ne ko hula ita kam bata tsaya lura ba
Mai aikin Aunty salma ce ta shiga dan sanar da ita zuwan kanwarta NANA MARIAMA
AUNTY salmar ce ta fara fitowa da fara.a a fuskarta ta zauna suna gaisawa nan ta lura da Rauda ta ce" kai wannan kamar mai kin gidanna ( haka take kiran Rauda, domin sam Rauda bata son zuwa gidanta dan yarinyarta Sarah dake da wani irin hali irin na mahaifinta wulakanta talaka koda kuwa dan uwanta ne)
Murmushi Mama ta yi ta ce" eh ita ce, zazabin nan nata ne ya zubo mata, mu kuwa mun tashi garin a cure
Auntu salma ta fahimci inda zancen Mama ya nufa, ta sauke ajiyar zuciya ta dafe kanta, murya a bace ta ce" kinga irinta ko Mariam, kin ga abinda nake fada maki ko? Ki duba ki ga irin rayuwar da kika zabarwa kanki , ke soyaya ko? Ki duba ki ga da kyanki, da dirinki kika kare a talaka wanda shi kansa bai samu cin yau bare na gobe ba harda su haihuwa da shi dan kasada, ke yanzu da ban sa an tsayar da haihuwar nan taki ba fa da kin ci gaba da zubo masa yaya yana takama ya ajiye zudediyar mata a gida bayan ya kasa magance maki matsalolin ki bare na yayanki, yanzu wannan abin kunyar har ina? Yarinya karama da ke aman du wahala ta saka kin yamutse tamkar kece babar ni kuwa kanwarki,?
Rauda ce ta fara sakin dan nishi a hankali ta shiga dan mimikewa tana juya kanta a hankali wanda ke nuni da tana jin jiki sosai
Ido ta dan zaro ta ce" wai kwannan duniya dama haka zazabi ke wahalar da ita? Kuma kin tabata ba wani ciwon ke dawainiya da ita ba?
Mama ta sauke ajiyar zuciya bayan ta bi Rauda da kallo, ita tama kasa magana sai gyadawa yayarta kai kawai da ta yi
Sunnan Sarah ta kwala da kira wace ta fito da waya tana ta zuba sangarta tamkar yarinyar goye ta mikawa mamanta waya tana fadin" Mom kin ga grandma ko? Wai dole sai na je birthday din limo ni dai aa ba zan tafi ba
Ido Mariama ta zubawa Auntynta wace ta karbi wayar mahaifiyarsu tana dariya tana amsa kiran , ji take tamkar ta karbi wayar ta zube a kasa ta bata hakuri, ta fada mata ta yi nadamar bijire masu da ta yi , ta fada masu su yafe mata su karbeta da yayanta
Tana ji tana ganni har ta gama wayar ta kashe sannan ta yiwa Sarah umarnin ta dauko mata dubu goma a cikin jakarta
Sarah ta yatsina fuska, ta bi kanwar mamarta da kallo mai shigen harara bata iya ta gaisar da ita ba ta juya a kasan zuciyarta tana furta sai na fadawa grandma ko matar nan mai nacin tsiya zata bar mu mu sarara a cikin gidan ubana!
Tana fitowa ta mikawa mamanta kudin ita kuwa ta baiwa Mariama ta mike tana godiya ranta a mugun jagule ta cicibi Rauda ta talafota ita kadai suna kallonta har ta fice a fallon
Da kyar ta samu mai napep ta tsayar ya dauko su ya kai su asibitin gwamnati
Yelemin kuwa suna zuwa aka basu gado aka rubuta magungunna ta tafi nema wanda tashin farko sai da ta kashe dubu biyu ta dawo ta mikawa likitocin nan aka yi mata allura aka saka mata karin ruwa
Yau kwannan Rauda biyu a rike a asibiti, sai dai sam bata dayo yanda ake so ba
A yau ne Sudais ya diro kampani dan gyara takardun biyan ma.aikatansa
Tunda ya zo yake zuba ido dan gannin ta inda zata fito, aman shiru ba ita ba alamarta har lokacin cin abinci ya yi Salif ya kawo masa nasa ya juya aman ya kasa koda kallon abincin ne bare ya sa ran zai iya ci, a hankali ya dana wayarsa ya shiga laluben lambar SAMIR
Salif na fitowa ya dubi kofar Rauda, shi kam ya rasa ya zai yi da tunaninta, ta zo ta tsaye masa a zuciya ta hana shi sukuni aman yau zai bi yayarta ko zata fada masa inda take ( kai ko😳)
Tunda ta fito yake dan binta da motarsa 4×4 aman ta ki tsayawa
Gannin ba zata tsaya ba ya saka shi fitowa da sauri ya sha gabanta ya hade hannayensa biyu ya ce" Auntynmu dan Allah ki saurare ni, ki yi hakuri aunynmu na kasa jurewa ne kwana biyu bata zo aiki ba, ina cike da zulunmin ko ta fasa aikin a nan ne, Aunty ina Rauda ta shiga kwana biyu?
Ja ta yi ta tsaya, cikin yan sakwani ta karanci Salif, ba laifi gy din ya hadu sannan da yan canjinsa ta yi murmushi a ranta take ayanna wace rana Rauda ta yi abin kanta, dan kuwa Salif bashi da laifi
Dan yatsina fuska ta yi ta ce" menene tsakaninka da kanwata?
Salif ya dan sosa keyarsa ya kallo Aisha ya ce" auntynmu ina fatan dai ba.ai mata miji ba?
Aisha ta dan saki murmushi ta girgiza kanta ta ce" eyah, LALLANA bata da lafiya ne tana asibiti ma an kama ta
Ido ya zaro harda dora hannun a kansa ya shagwabe fuska ya ce" eyah, rashin lafiya bai yi min adalci ba, aman aunty ya za.a yi na ganta ne?
Aisha ta kara waigawa ta kali motar, kalar ruwan baki ce, a ranta ta ayanna ba laifi zan dan kankaro mutunci , ta ce" ai yanzu ma can na nufa idan kuwa zaka je mu tafi
Samir dake nesa da su bai san mai suke tataunawa ba, shi dai yana biye da ita ne bisa umarnin ogansa dan sannin inda Rauda ta shige kwana biyu wanda da kyar ya kwaci kansa bisa uzuri da ya nema ogansa ya yi masa
Gani ya yi Aisha ta shige motar Salif, ya girgiza kansa a fili ya furta ke kam sai kace taxi? Kowa ma so kike!
Biye yake da su har suka karaso wajen asibiti inda Salif ya tsaya wajen masu abarba da lemo da sauransu ya sayi kaya guda ya biya suka shiga
A hankali Samir ya tsayar da motarsa ya fito ya bi bayansu
A cikin dakin mutun biyar ne a konce, kowane da masu jinyarsa abinka da ba mutun daya ko biyu ba sai dakin ya dume yake fitar da wari wari hakan kuwa du iya kokarin mama wajen kuna turaren haki da ya cinye sai warin ya dawo
Suna shiga Aisha ta ja dankwalinta ta rufe hancinta ta nufi wajen gadon tana yiwa Salif iso
Har kasa ya duka ya gaishe da Mama mariama, shi kuwa Samir ya ja kusan wani tsoho marar lafiya da yake barci ya tsaya yana sauraron su
Aisha cike da fara.a ta ce" mama, wannan saurayin Rauda ne a wajen aikin mu yake shi ne gaba daya chef din bangaren abinci
Wata irin bugawa kirjin Samir yayi , jin abinda ake fada , Salif.... ne saurayin Raudar??????
Katse masa tunani suka yi lokacin da Salif ya dawo da docter yana fadin" docter, a taimaka a bamu patient dinmu mu koma privet hospital
Dumdumdum gaban Samir ya kuma faduwa, ya rasa hanawa zai yi, kallo zai yi har su gama? Ko ya zai yi? Shi dai abinda yake da tabacinsa shine ba Salif kadai ba shi kansa a matsala yake.......
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*
Na: *SAJIDA*
*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*
*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*
*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```
https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation
2⃣0⃣
Bai gama yanke hukuncin abinda ya dace ya yi ba ya ga nurse biyu sun tura RAUDA saman garon asibiti mai taya an shige ambulance da ita su kuwa su Salif sun shiga motar sa da Mama da Aisha
Hannayensa biyu ya dora saman kansa a fili ya furta" na shiga uku!
Daidai lokacin wayarsa ta kwashi kuka, da sauri ya daukota a aljihunsa ya duba sunnan mai kiran *OGA SUDAIS* ya gani a rubuce hakan yayi daidai da bugawar zuciyar sa
Kin dagawa ya yi ya nufi motarsa ya tada ya bi bayan su a guje wanda da kyar ya samu ya cin masu suka karasa asibitin tare
Karban su aka yi da hannu bibiyu aka basu gado , nan kwararun likitoci suka shiga aikin su kan Rauda
Jiki a sabule Samir ya juya ya nufi gida wajen Sudais......
Aba na zuwa asibitin gwanati ya ga wayam ba su Raud ba alamunsu gadon da take har an dora wani tsoho
Gabansa ne ya yanke ya fadi, shi dai da safe kafin ya tafi Nema a yanda ya barta bata ma shaida wanda ke kanta domin jikinta zafi rau ta zubo mata kuma yanzu ya dawo ya ga basa nan
Da mugun sauri ya juya ya nufi wajen likitocin, tun kafin ya karaso yake yi masu nuni yana tambayar su inna yarinyarsa?
Da yake wasu likitocin ne suka canji wa.incan sai suka tsaya sokoko dan kuwa basu san wace yarinyar tasa ba!
Abinka da halayen wasu likitocin har sun fara yi masa masifa , daya daga cikin wanxen nurse din ta fito ta gan shi nan ta fada masa ai sun canza asibiti sun koma ta kudi ta fada masa sunnan asibitin
Tsai ya yi ya dan jima kafin yake samu ya fita a asibitin
Tafe yake yana tunani a cikin zuciyarsa, tambayar kansa yake wai dama idan *baka da kudi ba.a gannin mutuncin ka? Maganarka ma zaka rasa mai saurare?* yanzu ya dace abinda Mariam ta yi masa kennan? Koda bashi da karfi, koda ba lalai ne ya bada gudunmuwarsa a haka ba koda aljihunsa ba nauyi yana da iko na matsayin da Allah ya bashi na mahaifin yaran nan, aman komai ta tashi sai ta shige gaba ta aikata abinta ba ruwanta da ya zai ji, mai zai ji, bale a kai ga abinda yake so a yi ko kar a yi wato umarninsa ko ra.ayinsa! Yakan tambayi kansa shin rabuwarsa da uwar yayansa ne ya fi masa alkhairi bayan tsayin shekarun nan ko hakuri zai yi ya ci gaba da fuskantar matsaloli irin haka kamar yanda aminina Salisu ya sha fada min Allah jikan rai cewa *Ahmad Auren yar masu kudi kai talaka gaba da baya,? Ahmad kana son ka saka kanka a tashin hankali ne ko me? Menene damuwarka da zaka kai kanka ka saka a irin wannan rayuwar a matsayinka na wanda aka ajiye ba baka ba wani ajiya ba? Dadaya ne a cikin irin yayan masu kudin nan zaka aure su ku zauna lafiya kai ko mai kudi dan uwansu sai ka zamto a sama kake kaima! Ka kara tunani kar ka dawo ka ringa dana sani daga baya*
Ajiyar zuciya ya sauke ta barkatai a fili ya furta" ba laifina bane aminina , giyar soyaya da tausayin Mariama ne suka kwashe ni idannuwana suka rufe ta yaudare ni sa kalamanta da nuna tsantsar soyayarta wa ni ta dawo yanzu take wulakanta ni,
Ya Allah ka yi min magannin wannan damuwar ya ubangiji
Glas na inox ne ya saki ya fadi kasa tartsatsa cike da tashin hankali ya juyo ya ce" bata da lafiya? Tun yaushe? Me ke damunta? Kuma a ina take? Wani likita ke kulawa da ita ne?
Samir ya ce" oga ai a asibitin gwamnati take, yanzu salif ya mayar da ita ta kudi
Tsai yayi ya dakata jin suna salif, wai salif waye kuma salif?
Tsare Samir ya yi da ido, yana jiran jin karin bayani aman shiru samir sai wani kara sada kai yake tamkar yana gaban sarki
Sudais ya ce" a tunanina bata da dan uwa muharaminta mai suna SALIF! WAYE SALIF! Ya karasa yana daga murya
Samir ya dan ja baya ya shiga koro masa dukan abinda ya faru a gaban idannuwansa
Sudais kai tsai yayi tamkar gunki yana sauraron abinda Samir yake fada, wai wani gardi, gardin ma Salif, yaron da ko gaishe shi zai yi sai ya risina yana girmama shi yana kiran shi da yayan sa, yaron da idan fito na fito ne ba zai yi gigin ya dora sahunsa a kan na Sudais ba shi ne yake son *MATA!*
juyowa ya yi ya ce" du yanda aka yi laifinta ne, laifin yarinyar nan ne, dan me ita du inda take sai ta yi kokarin tayar min da hankali ta ja min bacin rai? Wai me ke damunta ne haka? Yanzu a shiga wajen cin abincin har ta yi sabon da ta kula soyaya da wannan karamin yaron?
Ya hade hannayensa ya jimke ya ce" Ni kuwa karya suke gaba dayan su, ba zai yiwu na yi takara da wannan yaron wajen neman soyayar Mata ba! Ko ya ki ko ya so, ko mutuwa take itama sai ta barshi! Samir menene aibuna da yarinyar nan ta kasa fadawa tarkon so na kamar yanda sauran yan matan ke so na? Ko dai ita ganina take tamkar dodo?
Ya karasa yana tsare samir da ido
Samir ya sauke ajiyar zuciya, domin a yanda ya tsamaci abin ya zo masa da sauki, aman abinda yake tsoron fada a yanzu shine abinda yake son fadawa ogan nasa
Samir ya dan kara gyara zaman sa ya ce" Elhaj ni da san samu na yi da na fada maka salon yan matan zamani masu aji
Sudais ya dan dage girarsa ta dama ya kara tsare Samir da kallo
Samie ya ci gaba da magana gannin bai kyare shi ba ko ya dakatar da shi, ya ce" wato oga, yan mata fa sunna suka tara, wasu zaka ga dan tsabar zubar da aji su da kansu zasu fadawa namijin suna son sa, wasun kuwa cikin dabara zasu karlato da hankalin saurayin, wasun kuwa koda soyayar namijin nan zai kashe su ba zasu taba amincewa su sanar masa ba da jan aji da gudun kar namijin ya raina su
Sudais ya zauna da kyau kamar da gaske dauka yake ya ce" to ai ni ba zan rainata ba dan ta furtan kalmar so, ainahi ma shine abinda nake zaman jira a nigeria Samir
Samir ya yi tsam, ya kare yiwa ogan nasa kallo, a ransa yake fadin lale oga bashi da ranar barin kasar nan,
Samir ya ce" aa oga ai kai ya dace ka tunkare ta, ka nuna mata alamar soyaya, ka furta mata kalaman so hakan zai sa ta karbe ka kila wa kala
Sudais ya yi murmushin da bai kai zuci ba ya ce" ya ake yi kennan?
Samir ya dago galala yana kalon sa, wai yanzu yana nufin bai taba yin haka wa matansa ba?
Aman dan gaskatawa ya ce" ai oga yanda kake nunawa Su Gajia
Sudais ya girgiza kansa, ba zai iya furtawa Wani sirrin dake tsakaninsa da matansa ba, ba zai fadi hakan ba, dan haka ya kuma sakin murmushi ya ce" kana dai nufin na shirya, na yi wanka na je kofar gidan su na aika yaro kiranta, idan na ci sa.a ta fito sai na isar mata da sakon zuciyata cikin lalami da roko ko?
Samir ya saki murmushi ya ce" haka nake nufi oga, ka lalabata ka bita zaka ga an dace
Sudais yayi yar dariyar da rabonsa da ita har ya manta, ya tafa hannayen sa biyu ya nuno samir ya ce" SAMIR ai ban san cewa tare da dakiki nake zaune shekara da shekaru ba sai yau! Samir ka tabata karatun sa ka yi ba.a yi maka taimako irin na yayan manya ba? Ina da ja a kararun ka sannan ina da ja a hankalin ka,
Kai yanzu yarinyar mai shekara 22 a duniya ce zan je godai godai da ni na hade hannaye ina neman soyayar ta? Karya take, kaima karya kake Samir, sannan du wani banzan da zai nufeta karya yake! *RAUDA'S MINE* kuma zata nemo SUDAIS dinta da kanta!
Samir galala ya yo tamkar sakarai, wai ashe du sauraron nan nasa da oga ya yi dan ya auna girman shirmen sa ne? Ya salam!
Sudais ya kakausa muryarsa ya ce" abinda nake so da kai ka tashi ka kai ni asibitin na canza mata waje na kaita clinik!
Yana gama fada ya mike ya fice inda Samir ya biyo bayansa da sasarfa a kasan ransa yana tambayar kansa ta yaya kennan hakan zata faru???
👏🏻😊👏🏻
*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*