Showing 90001 words to 93000 words out of 122108 words

Chapter 31 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

428

jikinta du ya yi la.asar bai san dalili ba..............









Sajidar mama😍


*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




4⃣9⃣





Kyauta gare ki kausar tun daga saudiya,



A haka ya karaso anguwarsu , nan ta dago ta shiga bin layinsu da kallo, yana nan yanda yake ..., canjin da aka samu sai karin kwatoci da kananun yara suna yawo ko.ina datin jikinsu ma ya ishe su,
Sai gugun gugun samari ana zaune ana tadi sai dan tsirarkun yan mata wasu daga makarantar islamiya , wasu an aike su, wasun kuwa kawai yawon anguwa ne basa nan basa can

Daidai kofar gidansu ya ja ya tsaya
Sai a wannan lokacin gabanta ya fadi, tuno auntynta da ta yi ya boye mamakin ya aka yi ya san gidabsu kwata kwata

Ko mu juya?
Ta ji muryarsa mai tsada ya aiko mata da tambayar
Cikin nutsuwa ta girgiza masa kai
Ta ce" mu mu tafi tare?
Domin a yau ji take tamkar bakuwa a gidan su, sannan bata san me zata tarar ba... auntynta na nan? Me ta fadawa mamansu kan mijin da ke aurenta? Shin ya mama ta dauki lamarin?

Bata ma san ya fita a motar ba sai da ya bude gefen da take ya mika mata hannunsa na dama bai iya ce mata komai ba

A hankali ta saka nata hannun ta fito cikin nutsuwa aman kafafuwanta suna mata rawa

Gannin mutane ta shiga kiciniyar karbe hannunta aman yaki saki
Kasa kasa ya ce" *MATA* ki bani nutsuwa mana kar ki fadi

Ajiyar zuciya ta saki kafin take jin dan karfi karfi ta kama kanta du da haka ta dan labe a bayansa tana bin yan anguwa da aka fara taruwa ana " lah Rauda ce, wly Rauda ce

Shiga ya fara yi da salama, domin shakuwa ta shiga sosai tsakaninsa da su aba har an janye masa iyaka da gidan

Mama ce ta dago tana faman hasa wuta a bakin murhu dan dora koko ta damawa Aba ya sha kafin ya fita domin yau shi kawai aka samu

Amsawa ta yi tana murmushi ta mike tana kara gyara hijabinta baki har kasa sai dai me Raudanta ta hango a bayansa
Du kawaicin mama sai da ta ce" Rauda? Da mamakin anya kuwan Raudan ne?

Ai Rauda tamkar jira take da gudu ta je ta fada jikin mama ta saki wani irin kuka
Mama kanta idannuwanta ta lumshe ta hana hawayenta zubowa, a hankali ta shiga dan bubuga bayan Rauda kafin ta dake ta cireta a jikinta ta ce" ke bana son sakarci kukan fa? Ke har yanzu ba zaki girma ba?

Rauda ta tsaya tana kikifta ido tana faman komawa jikin Maman

Muryar Abanta ta ji ya ce" Raudana ne?

Ai da qani irin ribos ta juyo ta gansa ya fito daga daki da rigarsa doguwa jalabiya da hula , ta tabata da kayan aiki a kasan wa.innan
Da sauri ta karasa wajensa ta kamo hannunsa ta dora kanta shima ta fashe masa da kuka

Aba ya ce" kai kai kai, autan Abanta kuka kuma? Kar ki ce min na murna ne domin na fi so a dara min idan har farin cikin ganina ake

Ai sai ta dago kai tana kallon sa ta shiga dariya hadi da kuka tana shesheka

Shima ya yi dariya yana goge mata ido daidai nan ya ja hannunta wajen tabarmar da mama ta shinfida har Sudais ya yiwa kansa masauki yana kallon yanda Rauda ke zuba shagwaba

Amsa gaisuwar sudais ya yi a mutunce kafin yake cewa" ka yi hakuri fa yau mutuniyar yan rigimar a kai suke an shigo da kuka

Bakinta ta turo ta kara lafewa a jikin Aba tana mamakin kennan sun san wa suka aura mata ko me?

Nan ma ya dan jima kafin yake tashi ya ce zai je wajen aiki idan ya taso zai dawo ya dauke ta,
Da ido yake kallonta ko zata taso ta yi masa rakiya ya hana ta kukan nan aman ina sai ma ta sauka ta zauna sosai jikin mama tamkar ta koma cikinta ta ki gane yaren sa
Haka ya fita yana tunanin bata ci komai ba ya fito da ita da kuma koke koken nan shi fa tana faman caza masa kwakwaluwa da tunani

A hankali ta dago daga jikin mama, ta shiga waiwaigawa bata ga aunty ba, ko ta je makaranta?

A hankali ta kallo mama da itama ita kawai take kallo tana jin farin cikin Raudanta ta samu konciyar hankali,
Murya a shake Rauda ta ce" Mama, wai dama kun san wa kuka aura min?

Mama ta ce" da farko ban sani ba, sai daga baya
Rauda ta gyada kanta, ta ce" mama, ban sani ba mama, ban taba sannin shi bane sai da na gansa, na yi kuka na yi kuka har na gode Allah mama, ba zan taba amincewa da haka ba da da sani na

Mama ta hada rai ta ce" me kike nufi da hakan?

Rauda ta shagwabe fuska ta ce" mama baki gane shi ba ne? Shi ne fa na wajen Aunty? Mama auntyna tana fushi da ni na tabata

Mama ta ce" ehe sai aka yi yaya?

Rauda ta shige share hawayen idannuwanta ta ce" ba sai ya sawake min ba ya aureta?

Mama ta zaro ido ta buge leben Rauda ta ce" kul, Rauda baki da hankali? Aure ya kusan kwana arba.in ki zo min da maganar mijinki ya sake ki ya auri yayar ki? Wani zama ne kike a gidanki da mijin ki? Ke ina islamiyar da kika kwashe rayuwarki kina zuwa? Me ake koya maku ne a can? Ya Rab Rauda bayan shirmen harda rashin hankali ke damun ki?
Sosai mama ke fada kafin ta sasauta muryarta cikin nutsuwa ta ce" Rauda, auren shi ake kira da ba wanda ya isa ya hana shi, tabas da zai zo da wani ja.in jar mu da kafin a daura shi Allah zai sanar mana, ke yanzu kike gannin a wannan lamari kina da ja ne? Ni auren nan bani da abin fadi sai adu.a Allah ya sanya alkhairi Rauda, auren nan ina ji a jikina du wanda ya ce zai ja da shi yana cikin rigimar rayuwa,
Rauda ki kontar da hankalin ki, wannan mutumin Allah ne ya hada auren nan naki da shi, ki bi shi ki yi masa biyaya a matsayinsa na mijin ki, ki faranta masa ki nemi lahirar ki, ba wanda ya isa ya ja da abinda Allah ya tsara Rauda, ki kadara in dai har auren nan naku ya rabu da wannan bawan Allah to fa Allah ne ya yi zaman ku ba mai dorewa bane, kar ki yarda ki furta masa kalmar ya sake ki koda kin furta ki nemi gafararsa, ba inai maki wannan nasiha dan yana wani a nigeria ba, inai maki ita ne dan ina son ki shiga inuwar aure ki samu albarkarsa gobe kiyama ki samu rabauta

Rauda kam du ta yi sanyi, bata taba kawowa mama zata yi mata nasiha kan auren nan ba, kanta a kasa tana jin du abinda mama ke fada har ta tsaya tana sauke ajiyar zuciya domin har zuwa lokacin a hasale take da irin furucin Rauda wai ya sake ta, tana jin kunyar kanta domin tabas wannan na cikin dabi.arta , ba komai ban3 a wajenta ta yi tsaye daga wani abin ya hado su da malan ta ce masa ya sake ta a gaban yayanta ko shi ya sa du irin ilimin da ta baiwa yayanta na islamiya da boko hakan bai yiwa Rauda nauyi a bakinta ba ta fade shi gatsal haka?

Hawaye ta ji sun tarun mata a idannuwanta kafin ta goge har sun samu damar zubowa

Hankalin Rauda ne ya tashi ta riko hannun mama ta ce" mama kuka? Mamana kuka kike? Ki yi hakuri mama ba zan kara ba, ba zan kuma ce masa ya sake ni ba koda yankan naman jikina yake, bana son bacin ranki mama

Mama ta janyota sosai kusa da ita ta ce" wai ke din mai dama daman kennan ina ga yar uwarki? Na cuci kaina na zuba rayuwa tamkar ta dabobi ina baranci a gaban yayana gashi yanzu ina gannin abubuwan da sukan iya tsayar da bugun zuciyata ,

Ina aikin me na ringa ginawa kaina ramin mugunta ina muzantawa mijina a gaban yayana a tunanina isa ce dan na isa da shi ni yar wane ni yar gata ni meron miji ina tuka sitiyarin ragamar rayuwarsa ina iza shi du a tunanina isa ce ashe ni na gama ginawa kaina ramin da in ba Allah ya tsaya min ba idan na afka na kade ?

Mama ki daina irin magangannun nan , ba zan kara ba na yi maki alkawari ... Rauda ta kuma fada tana kara rike mamanta

Mama ta ce" ba zaki fahimta ba Rauda,
Aman yanzu ki misalta min irin yanda hankalinki yake tashi idan ina hawaye?

Rauda ta shiga kikifta ido itama tana hawayen a hankali ta ce" ya fi karfin kwatance hawayen mahaifiyata

Mama ta lumshe ido ta ce" ki taya ni kara rokon gafarar abanku, ya yafe min aman ya kara yafe min ya saka min albarka, Rauda du irin girman darajar miji da Allah ya ce *Da zai umarci mutun ya yiwa mutun sujada da ya umarci mace ta yiwa mijinta sujada* , aman na take, na halbe, na dane, na yi ta wasa da shi tamkar birin wasa na,

Sai dai na godewa Allah da ya nusar da ni kafin na koma gare shi a irin wannan rayuwa

Tashin hankalina a yanzu shi ne ku yayana ... bare ke da Allah ya nuna min kin yi auren
Rauda shin a ya kike daukan girman darajar wannan sunna wato *MIJI?*
kina da niyar aiki ko nace kamanta yanda ma.aiki ya koyar da mu dan gannin kin kare hakokin *MIJIN KI?*

Mama ki dakata mama, dan Allah mama ki daina tsoratar da ni! Rauda ta fada tana mai rusa kuka

Mama ta ce" kina tsorata a yau a gabana dan na titsiye ki, ni mahaifiyar ki ina da ranar gobe kiyama idan Allah ya tsayar da ke da litafin rayuwarki ya hasko ki gaban bainar nasi ya kirayi sunan ki ya bayanar da fila fila a aikace aikin da kika aikata a gidan duniya tunva na mijin ki ba ( la haula wala kuwata illa bilah,,,, 😭,,,, ya Allah ka bamu ikon kamantawa, ka bamu ikon yina mazajen mu biyaya mudin ran mu )

Da sauri Rauda ta fada jikib mama ta rungumeta, tana hawaye a hankali har ta samu ta dan tsagaita jin mama ta yi shiru tana taping bayanta dan ta yi shirun itama

Murya a raunane ta ce" mama, tabas dan adam butulu ne, yakan mance duban alkhairin da Allah ya babaye shi da shi rudin duniya ya rude shi,
Wani lokacin tsoro da fargaba da nagatan da basu tsoron Allah kan kai bawa ga aikata laifi mafi muni ga wanda ya yi duniyar da abubuwan cikinta baki daya..... mama ina zamu je? Ya zamu yi? Me muka tanada? Me zamu ce masa?

A hankali mama ta ce" *mu gyara, sai mu samu rabauta domin shi din gafurun rahim ne Raudana*

Mama ta ci gaba" du wace ta ce maki kalau ne, ita mijinta bai taba yin fushi da ita ba, ko bai taba daga mata murya ba, ko ya kasance yan rigingimu na yau da gobe tace ita bata sani ba karya take, ta fada maki haka ne dan gadara da karya sai dai kuwa idan ba a hayacinsa yake ba wato asiri wanda na rantse idan har kika yarda kika yi shi ko a kiyama kar allah ya hada ni da ke Rauda, biyayar nan dai, hakurin nan shi na toke ki da ki yi kar ki yi anfani da abinda na aikata a baya ki yi kokarin gyara naki kema rayuwar idan ransa ya bace ki yi shiru, idan naki ya baci ki tausashi zuciyar ki kar ranki ya bace ki ringa sakin magangannun da ba da.a a ciki

Kanta kawai take gyadawa bata kuma cewa komai ba

Aba ya saki murmushi, ya juya a hankali ya koma dan samo masu koda kosai ne su ci domin kuwa coco sai dai na gobe in da rai,
Yana alfahari da Mariamarsa, yana jin wani irin kuzari har daga kai yake shima ya fito magidanci, matarsa na shayin bata mata domin *Indalahi*


Sai wajen karfe biyar na yama Sudais ya yi salama,

Rauda dake tuka tuwo ta mike tana amsawa kafin ta rage idacen murhun dan kar ya kone ta tako a hankali jikinta du a mace haka ta wuni domin mama batai kasa da gwuiwa ba wuni ta yi tana kara kusantata da ni.imar aure harda yan dabaru da karin jadadawar hakuri shi zai sa ta ci riba

Kallonsa take tamkar ta ga sabuwar halita, a hankali tamkar gidansu ya karasa ya dauko hijabinta ya saka mata, cikin nutsuwa ya kamo hannunta ya ce" *Mata* shiga daga ciki ina zuwa

Juyawa ta yi ta shige ciki bisa umarninsa , shi kuwa ya yiwa samir bip suka shiga shigowa da abinda ya zo da shi dan cin yau kawai






More cmment more pgπŸ˜‰

*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🀝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




5⃣0⃣



Page din ki ne *MADAME DAKKWARO* πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“πŸ’“


( *Walahi na tsani sticker, idan kina da damar yi min comment ki yi min plz idan kuwa ba dama ba laifi aman kar ki yi yunkurin sakoni a gaba da na yi typingπŸ˜‰* )


Kallon kayan kawai mama take, kayan abinci ne na cikin carton carton, ga su jus da chocolate
Ita kanta Rauda zuciyarta ta cika da murnar hakan duda ta san hakan ba komai bane a wajensa aman kam tana tare da farin cikin yau mama da aba zasu more da kayan marmari

Haba haba kai kuwa, kayan nan mu je ina da su? Gashi irin na sakawa a frij ne idan ba.a saka ba suna iya lalacewa? Aa ko malan ya dawo ya tarar da abin nan kuma na karba zai saba min ne aa ya dawo su kwashe ka yi hakuri
Mama ta fada tana ta mamakin wannan abin

Sudais ya ji wani abu ya darsun masa a zuciyarsa na kaunar datijuwar wato mahaifiyar abin kaunar sa, aa wai ita ce ko me ya sameta?

Lumshe idannuwansa ya yi bayan lura da ya yi Raufa sai sakin murmushi take , ya ce" mama daman d'a na yiwa iyayensa alkhairi su maido? Ko dai ni din ne ba.a haihuwar da ni? Ya karashe yana shagwabe fuskarsa sosai irin na yara kannanuwan nan

Kunya ce ta kama mama, Rauda kuwa ta zaro ido tana kallon sa ta ce" lah Sire menene haka wai kamar wani baby?

Mama ta zaro ido ta kallota ta ce" ke? Ya ishe ki haka bar shi ya yi bacinsa ai mamansa ya yiwa,

Murmushi ya saki kafin yake yo mata gwalo ita kuwa ta yi gagawar rufe idannuwanta da hannunta tana murmushi wai ta ji kunya

Maama ta yi murmushi kawai ta kawar da kanta, ita soma take ta gudu domin ta lura mijin Rauda ba ya jin kunyar yin wani abin

Suna haka Aba ya dawo kafin suke mikewa dan tafiya
Aba kansa fadan yawan kayan ya yi ya ce sam baya son irin haka ya je ya rike masa yarsa da kirki kadai ya isa ya saka shi farin ciki har karshen rayuwarsa , sannan ya shiga yi masu nasiha kan zaman tare da hakuri ya dora da cewa" idan rai ya baci hankali ke nemo shi, sannan ya zama wajibi ku sani zaman tare na dorewa ne idan ana tataunawa , koda wani abin ya faru tsakanin ku ku yi kokarin gannin kun tatauna a tsakanin ku da yardar Allah zaku samu hanyar samun lumana a tsakannin ku

Sosai Sudais ya ringa jin wata nutsuwa tare da sirikan nansa harma ya dora ayar tambaya a irin kallon da ya yiwa mama da farko (shiryuwa ta yi Sudais)


Shagwagwabe fuska Rauda ta yi kafin take fashewa da kuka tana kallon iyayen nata, tafiya zata kuma yi ta bar su? Kai ina iyaye dadi ne da su komai dadin da kake ciki nesa da su ragage ne (annata😟😟😟😟😭)

Sai da Aba ya yi rarashi kafin take yin shiru mama kuwa hararta kawai take kafin ta girgiza kai, kai Rauda ba wayo

Har sun kama hanya ta dawo murya a raunane gannin har dare ya yi ta ce" mama, Aba wai ina aunty ne? Na yi tunanin ko tana makaranta gashi kuma har yama na yi bata shigo ba? Ko har dare suke kaiwa?

Mama ta kalli Aba , Aba ya kale ta , ta kikifta ido ta ce" ke, ki je mana yana jiran ki zaki dauko wani zance kuma?


Rauda ta yi tsaye tana kallon su, du sun dan daburce ba kamar mama da ta shiga sosa hannunta na hagu tana dan zaro ido , takan yi haka idan ta daburcewa wani abin

Matso su Rauda ta yi da kyau ta ce" me ke faruwa?

Mama ta ce" ba nace ki tafi ba?

Malan ya mika hannunsa ya kamo na Rauda ya ja ta wajen kofa, daidai soro suka tsaya ya kaleta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login