Showing 87001 words to 90000 words out of 122108 words

Chapter 30 - Idan Ka Raina Inda Kake Book 1 Complete Hausa Novel

31 Oct 2025

414

sanyi ga sanyin ac
A hankali ya sako hannayensa ta cikin cikinta ya dan shiga shafawa kafin yake kai hancinwlsa wajen wuyanta ya shiga shinshina
Mamaki, da wani irin nutsuwa ya ji na sauko masa kafin a hankali yannayin jikinsa ya fara canzawa

Murya kasa kasa ya ce" na zata shi ya kawo ki? Ai ni idan an zo wajena nemansa ne kuma nakan yi iya yina dan gannin na biyawa mutun bukatarsa dan ina gudun hakin mutane

Gaba daya ji take tamkar yana bin jikinta yana saka mata wani abin da bata san da shi a duniya ba, feeling, feeling ne na tashin hankali ke sauko mata, ba dai wani abin yayi mata ba aman gaba daya ta rikice tana neman fita a hayacinta

A cikin kunnanta yayi magana wanda shi kansa ya fara hawa layi, laushin damatsunnanta da hannunta da ta kawo saman nasa da niyar bambare shi daga jikinta aman ta kasa sai ma ya kasance ta shiga shafa hannun maimakun bambarewar, sai yannayin kanshinta da shima bako ne a wajen sa, iya wuyanta da wajen kunnenta kawai ya iya sinsinowa aman ba karni, ba karni ko warin ruwa babu ko kadan baya ju a jikinta,
Ji yayi ana sara masa kansa, a hankali ya fara sasauta rikon nata jin gaba daya jikinsa ya fara mumurdewa

Ajiyar zuciya take saki a kai a kai tamkar ta yi tsere, da sauri ta shiga jan duwawunta domin ya cikata ya konta nan

Tana sauka daga kan bed din ta aniyar tserewa sai dai gaba daya tamkar an zare mata laka , bata da karfi ko kadan a jikinta ,

Baki fadi abinda ya kawo ki ba

Muryarsa a wani irin amon murya ya daki kunnanta

A hankali ta juyo ta ga sai mamatse kafafuwansa yake yaki zama

Kasa kalonsa ta yi domin sai take gannin tamkar ba shi ba,

Kanta ta sada kasa , murya na rawa ta ce" dama , dama , na zo ne na tambaya yaushe zan koma bakin aikina?

Bai san lokacin da ya bufe idannuwansa ba ya sauke mata kwayar idannuwan a kanta

Gabanta ne ya yanke ya fadi sakamakon irin yanda ta ga kwayar idonsa sun koma jajajir, da sauri ta cire nata idannuwan daga nasa ta kuma sada kanta kasa

Kallonta yake yana nazartarta, can murya kasa kasa ya ce" me yasa kike son yin aiki?

Dago da kanta ta yi da dan mamaki,, wata zuciyar tace ba abin mamaki bane may be bai san cewa a gidanku ku biyu kawai iyayenku suks haifa, mata, wa.inda da Allah da ku suka dogara , da ya san yanda mahaifinta ke nema tun karfinsa da bai yarda ko da wasa ya yi mata tambayar me zata yi da aiki?
Bata iya ce masa komai ba sai kanta da ta dan girgiza

Ajiyar zuciya ya sauke , a hankali ya ce" zan yi nazari

Juyawa Rauda ta yi ta fice tana adu.ar Allah ya cidata

Wani wankan ya sako kafin yake zuwa ya shiga shiryawa yana yi yana duba agogon dakinsa

Kansa ya dafe domin har an yi salar magarib an bar shi dan haka da hanzari ya dauki tapi ya shinfida ya shiga gabatar da Sallah cikin nutsuwa

Bayan ya gama ya jima yana adu.a kafin yake mikewa ya shirya da niyar fita ya yi sallar Isha a waje sannan ya je anguwa

Kayansa yake sakawa yana fadin" wato dai sai an daga maka hankali , aiki? Me zaki yi da aiki *MATA?*

Tare suke da Samir tunda suka fito daga masalaci wajen meeting na manyan mayan yan kasuwa masu rike da kaso 60 na nigeria fannin talafi wa Gwamnati, suna gamawa Samir ya jawo motar wanda kira.a ke tashi sannu sannu

Sudais ya ce" SAMIR, KAI NI GIDAN Su MATA

samir ya juyo ya dan kallo shi, gidansu kuma? Me zai je yi gidansu? Ko laifi ta yi masa?
Aa halayen Sudais ba irin na ya kai kara bane dan matarsa ta yi masa laifi domin ko mahaifiyarsa baya yarda ta san tsakanninsa da matansa dan yau da gobe sai Allah tana iya tsanarsu shi kuwa idan yana da bukatarsu a tare da shi a samu matsala

Samir bai zame ko.ina ba sai kofar gidan su Aba,

A daidai wannan lokacin Aba na zaune saman dan dakalin kofar gidan yana kallon gari haka dai yana dan nazarin duniya

Sudais ya jima yana kallon gidan, da bangon gidan, sannan ya maido dubansa wajen Aba wanda kallo daya ya yiwa motar da ta tsaya a dan gefensa ya kawar da kansa , SUDAIS ya sauke ajiyar zuciya ya tina rayuwarsu ta da can baya su sun ma kasance masu rufin asiri, a hankali ya furta " *ALHAMDULILAH*

Issa mai kanti ne ya zaburo ya zo kussan motar yana dan lekawa sai rawar jiki yake yana fatan Allah ya sa ta samu

Ganninsa ya sa Sudais ya dan zuge gilas din motarsa kadan dan jin lafiya?

Barka yalabai,
Issa mai kanti ya fada yana yage bakinsa hakoransa suka bayana da jan goro futu futu


Sudais ya yi murmushi, sosai rayuwarsu ta da take fado masa, suma sun zauna a irin anguwar nan, sannan sun rayu da irin mutanen nan , wani murmushin ya saki da ya tina majalisar su Abansa, yakan je ne tare da Abba dommin shi yana yaro ma akoy shakuwa tsakaninsa da Abansa sosai

Hannunsa ya fitar ya mikawa Issa sukai musabaha, kafin yake fadin" Gidan MALAN AHMAD muka zo
Domin ya san tsegumin hakan ya fitar da shi, kuma yana sane ya fada masa dan ya san zai iya buda baki ya ratafa masa magangannu yana son sannin datakun surukan nasa

Lumfashi ya sauke kafin yake cewa" ina fatan dai ba yarinyar gidan ba kake so Yalabai? Domin dai kana hangensa can? Wannan shi ne Malan Ahmad, shi kam mutumin kirki ne, talaka ne da ya iya talaucinsa sai dai yayi shirme ya kai yayansa boko, yaran mata ne suka girma har suke kokarin tsofewa a gida tun ana bibiyarsu har ya kasance an janye domin shegen idon cin naira ne da su
Ita karamar dai uban ya bayar da ita sadaka har wasu na cewa ko auren jari yayi wa yar , sai dai tunda aka yi auren yana nan yanda yake jiya i yau baya maganin naira goma sai shegen sabkon zuwa wajen Aiki Faskare

*Faskare?* Sudais ya maimaita a hankali,

Issa ya ce" Faskare ne sana.arsa, har an gajiya aman ba wata sana.ar sai shi

Kai Sudais ya girgiza ya yiwa Samir nuni da ya salami Issa domin ya fara caza masa kwakwalwa

A hankali yake takawa har kofar gidan su Rauda

Yana zuwa yayi salama wa Malan Ahmad

Aba ya juyo yana mai amsa salamarsa,
Sai dai abin mamaki kafin ya mike Sudais ya zube kasa gaba dayansa kansa a kasa ya ce" Aba barka da hutawa

Sai a sannan Malan Ahmad ya gane SUDAIS , ikon Allah daman a samari akoy sauran masu biyaya haka? Mijin Raudansa ne ,

Da sauri Aba ya amsa yana mai umartarsa da ya tashi ya tashi domin wajen ba dai dati ba , kun dai sani😌

Kin mikewa Sudais yayi sai da suka gaisa sosai da Aba kafin yake cewa" zuwa na yi daman na gaishe ku

Malan Ahmad cike da jin dadi yake amsa Sudais, harma ya ce da shi bara ya fadawa mamanta ya shiga su gaisa

Kafin Sudais yayi magana har Aba ya shige dan haka ya shiga dan shafa sajensa

Shiga suka yi a tare inda Sudais yake dan bin gidan da kallo da yannayin hasken farin wata

Tabarma mama ta shinfida kafin take takurewa can gefe ta zauna

Har kasa itama ya duka ya gaisar da ita inda ya ji muryarta irin na Rauda

Mikewa ta yi ta dauko masa ruwa a randa mai sanyin gaske ga kanshin laka ta zuba a kwanon silba na aba na shan ruwa ta kawo masa ta ajiye

A nan hasken farin watan ya bashi damar gannin fuskar mahaifiyar abin kaunarsa
Kamarsu daya shi ne abinda zuciyarsa ta ayanna masa

Mama na so ta tambayi Rauda sai dai kunya da nauyi sun hanata yin hakan har Sudais ya mike ya tafi ba tare da ya ajiye masu komai ba (notez bien bai basu komai ba)

Yana zuwa suka shige mota suka tafi da Samir yana ayanna abubuwa a kasan zuciyarsa

Konci tashi yau an yi sati uku wanda a sati ukun nan zuwan Sudais gidan Su Rauda sau biyar

Ya maida wajen wajen zuwansa ya zauna su zanta dan halin rayuwa da iyayenta harma ya ci abinda aka kawo masa ya tashi ba tare da ya basu ko naira biyar na alkhairi ba

Abinda ya fara birge shi shine bai ga canji a fuskar su koda a wajen amsa gaisuwarsa ne
(Nuna kwadayi ga abin wani, na sakawa ka zama hadamamen mai zalama)

Yana karantar rayuwar iyayen matarsa cikin nutsuwa yana fahimtar abubuwa da dama

A yau ya dawo daga gidan da ya saka ake gyarawa daya daga cikin gidajensa ya shigo a dan gajiye domin ya je ne ya ga irin tsarin kayan da aka zuba a gidan kama daga gadaje kujeru tv kayan kicin da sauransu

Yana zuwa ya tarar da su zaune a falo suna game gardama ya kaure tsakanin su

Ba zato ya zauna shima ya ce " a sake, a saka ta mutun uku

Da mamaki suke kallonsa daga Raudar har Hafsat din
Girarsa daya ya dage yana kallonta ya ce" sannan ni zan fara

Au na manta, mama ta ce a gaishe ki, da ABA

Da sauri Rauda ta dago tana kallonsa, muryarta na rawa rawa ta ce" mammmmamana? Sire Abannna????????

Tana fada ne tana matsowa kusa da shi sosai wanda ya dago idannuwansa ya sauke a kanta.......ya ce""""

*❣IDAN KA RAINA INDA KAKE❣*







Na: *SAJIDA*




*_LITATAFAN MARUBUCIYAR_*

*_Duk Karyar kada_*
*_Yar Mahaukaciya_*
*_Neman na kaina_*
*_Bani da zabi_*
*_Daga tafiya daukar soja_*
*_Idan ka raina inda make_*




*🌈KAINUWA WRITERS✍🏼 ASSOCIATION*🤝🏻
```{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}```

https://www.Facebook.com/kainuwawritersassociation




4⃣8⃣








A hankali ya lumshe idannuwansa ya shiga lailaya lebenta kafin yake isa cikin bakinta, kanshin maclean na frz ne yake shiga bakinsa, idannuwansa ya kara lumshe kafin yake cafke lebenta ...... ..
Sako yake bata iya nan, sakon da ya zo mata a rashin shiri sannan daga mutumin da take shayi........ bata taba kwatanta irin haka da kowa ba, bata taba kawo haka lamarin yake ba........jikinta ne ya dauki rawa ta damke damatsunan hannunsa ta shiga dan girgiza masa kanta dan ya tsayar da kissing dinta kar ta sume masa

Elhaj Sudais Uban masu gida yau ya zama dan gida, ya mace ne a bukatar kara gaba daga nan domin lamarinta na zuwar masa da ba zata kala kala......
Bakin Mata kanshi yake fitarwa, wari bai dake shi ba
Bakin mata laushi, haka jikinta.... gashin kanta kanshi ya salam...... ya salam.......
Cikin nutsuwa ya kame bayan keyarta ya kara kusanta jikinsa da nata still yana kissing dinta ...
Gani yayi tsayuwar bata yi masa a hankali ya cirata a jikinsa bai saki bakinta ba yayi bakin bed da ita
A hankali yake kara sarafa harshensa da nata lumfashinsa na wani irin gudu

Gannin Sire baya jin yarenta ta fashe da kuka tana kokarin cije lebensa
Tsai yayi da abinda yake yi a lokacin kuma aka buga masa wani irin abu na tunani....yarinya ce, sai ta warware, sai ta zama bunkasashiyar budurwa zata iya da kai Sudais....ka bari kar ka tsorata ta mana ka yi hakuri da bukatarka gareta har sai ta isa daukan nauyinka
Du kwakwaluwarsa ce ke yi masa fadan nan wanda a hankali ya samu ya shinfidar da ita saman bed din yana shafa gefen gashinta alamun rarashi

Ajiyar zuciya kawai take saukewa idannuwanta a rufe domin kunyarsa take ji sosai(ki shirya fa) wai dama haka yake?

A hankali ya mike ya daidaita mata gudun ac ya kuma dawowa kusa da ita ya duka sosai ya shafa gefen fuskarta murya can kasa ya ce" ki yi baci, kar ki yi tunani ki dauki rayuwa a yanda ta zo maki *MATA*

Tsikar jikinta sai da ta mimike ta bi shi da kallo har ya mike ya fita a dakin nata

Sudais na shiga dakinsa ya je ya yi wanka ya fito ya yi nafilarsa ya zauna ya yi adu.u.insa kafin yake mikewa a hankali ya hau bed
Bashi da tunani sai nata, bashi da buri sai na kasancewa da ita... yana son a haka ya shigeta ba tare da ta ankara ba, ya kasance bugun zuciyarta wanda sai ta yi nisa da shi zata gane shi ne ita ita ce shi
Yana begenta har baci ya daukesa

Da safe bayan ta gama abinda ya zame mara al.ada wato gyaran dakinta, wankin bayinta, wanke bedsheet dinta... kafin take shiga wanka
A wajen wanka a kadan Rauda na daukaninti goma sha biyar wanka kadai ba wani uzurin ta kasance mai kwalkwalce kwalkwalce, taba nan , wanke can, goge nan, takan hada ruwa har kala uku tana wankanta cikin kuzari kafi ta fito
Abin busar gashi ta dauka ta busar da gashinta cikin nutsuwa kafin take shafa masa man gashi mai sanyin kanshi ta daure shi a gadon bayanta

Yau kuma ta tashi da son saka kayan hausa dan gaka ta dauko wani lesh mai ruwan sararin samaniya (bleu ciel) da dan fari fari wajen adon....lesh din sabon fitowa ne, wato lesh din matan gwana😂, ya hadu ya hade an yi masa dinkin yan matan zamani riga wace ake ce mata makeba sai dai ba mai tsayi har kasa ba bakinta gwuiwa da zaninta da dan kwalinta
Dinkin ya dinku dogon hannu ne da shi cigarette sai wuyan kuwa bateau ne ..(c tres joli l model) cikin nutsuwa ta shafa mayukanta na humra wa.inda suma a dakin aka jera mata domin Sudais ma.abocin kanshi ne
Bayan ta shafa ta saka kananun kayanta pant nd bras kafin take daura zaninta irin daurin hausawa ya hau kugunta ya dauru da kyau ta saka rigar ta ja zip
Dan kwalin ta konce ta dauko abin daurin dan kwali baki dogo na yayi ta kontar da dan kwalin ta saka ta gyara shi da kyau kafin take zuwa gaban mirror ta daura shi ya zauna dasss ta yi daurin zahra bahari aman bayan ta yi shi yayi tamkar bindin zakara kosashe

Tana kokarin dauko sarka ya shigo dakin da salama a bakinsa

Da mamaki ta juyo domin sam bata ji karar shigowarsa ba sai kuma abin jiya ya fado mata a rai wanda ta kwana tana tunawa ta yi saurin juyawa tana dan rurufe ido

Murmushi ya yi ya shiga takawa cikin nutsuwa har ya karaso wajen sarkokin nata
Wata yar siririya fara kar mai dan bul shima farin ne aman mai haske domin ana ganin cikinsa tamkar ruwa ne a ciki sai yan kunayensa siraru suma bakin kafada domin da dan tasayinsu ya dauko ya nufota yana murmushi

Yana karasowa ya gyara sarkar ya sakota a hankali ta wuyata kafin yake balawa ya dan raba kansa da wuyanta sajensa ya shafi wuyanta ta lumshe ido
Murya can ciki ya ce" morning *MATA*

kunya ce ta sakata ta narke a kirjinsa na gaisheran da ya fara, bata iya amsawa ba sai kara lumshe ido da ta yi tana kara shigewa kirjinsa domin yanda sajensa ke hawan mata wuya sai tana jin tamkar yanai mata tafiyar tsutsa ne

Murmushi ya saki, ya ce" wani turare ne kike anfani da shi haka?

Idannuwanta dake lumshe ta dan bude ta kallo shi,
Dan yatsanta ta nuna masa wajen da turaran yake
Dubansa ya kai wajen tarin turarukan ya lumshe idannuwansa, a ransa ya ayanna lalai zai kara oder irinsu domin kanshinsu daban ne a jikin *MATA*

Haka kawai ta rasa abin ce masa sai cewa ta yi" a ina ka koyi saka sarka wa mace?

Tambayar ta bashi mamaki, wa mace? Aman sai ya kawar da hakan ya ce" ya dace mai sana.a ya iya sarafa abin sana.arsa *MATA*

Du idan ya kirata da mata takan ji sunnan wani iri, ya aka yi baya kiranta da RAUDA sai dai ya kireta da sunnan mata mata mata ta dan kebe lebenta


A hankali ya cikata ba dan ya so ba ya ce" ki shirya mu je ki ga mama da Aba

Rauda ta kwalalo ido ta matso da sauri ta riko shi ta ce" dan Allah ? Zaka kai ni na ga mamana?

Idan kika kuma cewa mamanki ke kadai za.a fasa

Da sauri Rauda ta shiga girgiza kai bata ce komai ba ta juya ta shiga neman hijab har jikinta rawa yake

Ya girgiza kai yana murmuahi ya fice

Hijab ta dauko fari kar mai hanaye ta saka ta kara turare ta dauko takalma masu dan tudu farare kar ta saka, ta shafa lips ta juya da dan sauri domin du ji take zai fasa ne

Tana fita ta ga Hafsat sai cika take an ce ba da ita za.a tafi ba
Ai rauda bata iya tsayuwa rarashinta ba dan zumudi ta bi bayansa da sauri

Tana fita ta ga galeliyar mota mai wani irin tsari tamkar kifi domin gabanta ya mike kamar gaban jirgi
A hankali ta taka ta karasa ta ga Humaira zaune a gidan gaba ta sha itama shiri aman itama hijab ne a jikinta ta zagaya a hankali ta bude bayan ta shiga ba tare da ta yiwa kowa magana ba

Cikin nutsuwa yake tuki har suka karaso gidan su Humaira
Nan ta fara fita kafin Sudais ya umarci Rauda da ta fito su shiga su gaisar da iyayen Humaira

Sai da gaban Rauda ya fadi, a ranta ta ayanna lalai dole Humaira ta ringa daga kai ashe iyayenta masu kudi ne haka, tap tama yi kokari domin da wata ce abin sai ya fi haka ( baki san garin ba )

Har kasa ta duka ta gaisar da mahaifiyar Humaira , ga mamakinta raji raji tamkar ba ita ce maman Humairar ba domin sam halaya bai zo daya ba
Harda yar nasiha ta yi mata kan su zauna lafiya Allah ya hada kawunan su
A haka sukai mata salama suka fice

Tafe yake a hankali yana tuki da kansa , yakan dan waigo ya kali Rauda da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login