Showing 1 words to 3000 words out of 145230 words

Chapter 1 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

269

๏ปฟ๏ปฟ๏ปฟ๏ปฟ๐ŸŒท Muhammad ๐ŸŒนKabeer๐ŸŒท

Documentation work shop

08160112181

๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’›โค

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’›โค๐Ÿ’™

ยฎzuwairat(ummu maryam)

1โƒฃ



Ahamdulillah. Ya rabbi ya amshi ibadunmu. Happy sallah to all muslims.

Ban yarda wata ko wani ya maida wannan novel din document ba saida izinina.

Wata babe ce zaune cikin wani katafare falo wanda girmanta zai yi 100by100, fadin tsarin falon is a waste of time amman kuyi imagining kyawun falon masu hannu da shuni, budurwan sai kada kafa take da alaman ba gidan ta bane, kaman mai gidan take jira. Wasu hadaddun designer english wears ne jikinta, sai kamshi take, da ganin ta kaga wayayyun babe masu aji.

Bayan kaman minti talatin aka bude kofa, wata kyakyawa babe ta shigo, aikam afusace wacce ke zaune afalon tamike fuskanta daure, ta nuna wacce ta shigo da dan yatsa sannan tace

"wato mimi baki ji ko.." bata karasa ba wacce aka kira da mimi ta tuntsure da dariya sanna tace

"ke uban wacece da zaki nuna ni da dan yatsa...ko kin manta ni fina na fiki tunda ubana ba hannun efcc yakeba..banza karuwa.." bata karasaba taji saukan mari

"dan uwarki ni mate dinkice dazaki gayamin magana?...sau nawa nake gaya maki ki rabu da slim...

." itama bata karasaba aka dauke ta da mari

"ke har kin isa ki rabani da slim..uban wa ke baisan ke kike binshiba?..kuma kowa yasan duk big boys din abujan nan ke kadai ke binsu ...kariya" haba nan suka shake junasu.

Sunfi minti biyar suna dukan junansu at the same time suna gayawa junansu bakaken magagganu. Ni kam mamaki nake wanene wannan guy din da kyawawa yanmata ke dukan junansu sabodashi. Fina rike gashin mimi tayi da niyyan janta waje amman weavon din dake kanta ya cire, afusace mimi ta juyo tare da cire designer shoe din dake kafanta ta wullawa fina, da sauri ta kauce ya sami wani katon canema dake jikin bango nan take ta tsage. Itama fina cire nata takamin tayi ta wullawa mimi itama ta kauce ya sami wasu glass decor dake kan dinning nan take suma sauka tarwase, dukkansu babu wacce ta kalli barnan datayi suka cigaba da fadansu fina na cewa

"wallahi bari slim ya dawo....yau sai ya zaba tsakanina dake.." mimi da kanta babu wani gashin kirki kuma fina ta cire karin datayi ta rike a hannunta gam, mimi sai kokarin amsan brazilian hair dinta take tana cewa

"dalla bani weavon dina, don kudinta ya fi karfinki...."

"bazan badaba..ki tsaya ahaka har slim ya dawo ya ga kwalkwalin kanki". Itama mimi kaman kan fina tayi ta fixge nata karin gashin. Nan take itama kanta ya bayyana. Dukkansu biyu babu mai gashin kirkin amman kansu kyare suke . Da weavon mai suna brazilian hair wanda kudinta yakai 600k suke amfani. Kowannesu klokarin amsan karin gashinta take.

Afarfajiyan gidan wani katafaren gate ya bude, wasu manyan motoci kiran bentley guda uku suka shigo gidan, wurin parking suka nufa, suna gama parking da sauri wasu guys guda uku suka fito daga cikin motan gaban at the same time guys biyu suka fito daga cikin motan baya suka nufi motan tsikiya, ahankali daya daga cikin guys din ya bude murfin motan tsakiya. Wani hadadden kafa nagani sannan mai kafan ya fito, wooooow, kawai nace don fina da mimi basuyi laifiba da suke cin abun junansu sabodashi, don guy din tamkar shi ya hallici kanshi, wani suitmai tsada ne kwance jikinshi , ahankali ya mika hannu ya amshi briefcase din dake hannun daya daga cikin guards dinshi sannan ya sakar masu murmushiai bayyana hakora, wow nasake cewa don wasu fararen hakora nagani tare da wushirya tsakiyansu. Nikam ban taba ganin mutum mai kyau har cikin hakoraba don komai nashi wonderful

"alhajis na gode" naji yace, nikam wooow na kara cewa don muryanshi so cool and gentle. Suma guys din murmushi suka sakar mashi, juyawa yayi yafara tafiya, yana daga kai yaga wani range rover sport tare da hummer tsaye, nan take ya hada giran kasa dana sama, don yasan masu motocin. Girman gidan yayi hecter daya, da akwai manyan flat a farfajiyan gidan, amman wanda yafisu girma ya nufa, su kuma guys din sukayi wani bangare daban.

Yana zuwa bakin kofan falonshi ya taddata bude, afusace ya shiga falon, adaidai lokacin da su mimi da fina sukayi wa karin gashinsu kacakaca a falon, suna ganin shi kowa yasha jinin jikinshi

"kam babban burouban nan!!!!! " saurayin ya fada a fusace, wanda yasani rasana don yanda yayi magana sai ya firgita duk wanda ke saurarenshi, yacigaba dacewa

"who the fuck gave you bitchies permission to enter my house? " dukansu shuru sukayi, ahankali mimi tace

"slim ni kake kira bitch? " ta fada tana nuna kanta, a fusace yace

"aa sugar badake nakeba da uwarki nake... I said uban waye ya bude maku falona? " fina na gani ya watsawa mimi bakar magana ta saki murmushi tare da nufoshi tana cewa

" habibi welcome " harara ya watsa mata tare dacewa

"gidan ubanki nazo?

Banza yayan barayi" itama fina cewa tayi

"are referring to me" dan girgiza kanshi yayi sannan yace "da lankwaceccen ubanki nake... Bazaku gayamin ubanda ya baku izinin shigowa gidanaba kafin insa guys dina suci uban da ya haifeku? " fina tace

"ni na bude"

"who gave you my password? " ya kara daka mata tsawa

"last weekend da mukazo b day dinka na rike passwords din... Kasan am smart "

"kika rike passwords dina don in bana nan kizo kiyimin sata ko" ido mimi ta bude

"sata kuma slim... Ni kake cima mutunci haka? "

"eh mana... Ba sata ubanki yayi efcc suka kamashiba? Nasan ko kin gada?" fina bata kara cewa komaiba ta koma baya, takalminta ta dauka da niyyan sakawa, itama mimi designer hand bag dinta ta dauka, ajiye briefcase dinshi yayi gefen inda yake tsaye tare da harde hannuwanshi kan kirjinshi yan kallon yanda fina ta duka ta saka takalminta, mimi zuwa tayi zata wuceshi, ya fixgeta tare da wullata cikin falon

"where did you think you are going?... Ubanwa kuka barwa gashin doki chan" ya nuna weavon din dake sakar falon sannan ya kara cewa

"in kun bar gidan nan sai kun gama gyaramun falona... Banzaye second hand bitchies" irin fixgan da yayiwa mimi yasa batayi gardamaba ta koma tafara kwace karin gashinta tare da maida tro pillows din da suka wullawa junansu. Magananshi kara batawa fina rai yayi, bata kalleshiba tazo zata wuce inda yake, wani irin damka yayi mata tare da turata baya

"safina kina son nuna min taurin kai ko?... To wallahi in baki gyaramin falonaba dukan tsiya zansa ayi miki kuma kisan nothing will happen " murtuke fuska tayi kafin tace

" gaskiya ko agidanmu ban aiki so yanzu ma bazanyiba" wani irin dariyan rainin hankali yayi wanda ya kara bayyana kyauwunshi

"ai yarinya kwanda ki fara koya don satan da ubanki minister yayi aka kamashi...bailing shi zai maidaku matsiyata..." bai karasaba ta yaji tace

"dadin abun ba ubanmu kowai ke barawon government ba.... " dauketa yayi da mari.

" kio ubanki baya magana in inayi balleke...." bai karasaba ya daga kai yaga cinema dinshi fashe, wani ashar ya kara saki sannan yace

" wacece ta fasamin plasma! " ya fada afusace, fuskan fina murtuke tace

" nice ko abiyakane....tunda kasan ba matsiyaciya bace"

"abinda ya zama dolema..ai comfirm sai kin sa an kawo zaki bar gidan nan" batace kara cewa komaiba ta kira bodyguard dinta dake waje ta sanar dashi yayi amfani da ATM dake hannunshi ya sayo mata the largest plasma.

Fina kallon mimi dake tsaye tayi sannan tace

"malama kema ki kisa akawo mashi glass decor dinshi" sai lokacin slim. Ya kalli wurin dinning dinshi yaga barna da sukayi mashi, still cewa yayi sai mimi ta biyashi, itama bodyguard dinta takira yazo. Ciki ta bashi ATM dinta tare da nuna mashi abinda zai sayo.

Har lokacin salem bai bar inda yake tsayeba, mimi da fina zuwa sukayi zasu wuce ta inda yake, rike masu hannu yayi tare da kallon fuskan ko waccensu sannan yace

"meyasa kuke fada sabodani? " dukkansu babu wacce tace komaiba, yacigaba dacewa

" ko dan kudi da neman connection?" ahankali mimi tace

" haba slim why are you saying this.. Kasan ni badan wani abu naka nakesonka... " itama fina cewa tayi

"kaima kasan i love you" dan tabe baki yayi don yasan karya suke

" naji...amman kuna iya fada saboda security ko wani mara hali? " dukansu shuru sukayi sannan yakara cewa

".kuna iya bin mai gadin gidanku gidanshi?..." kaman hadin baki sukace

" i love you!! " suka juya tare dawullawa junasu harara, shi abinma dariya ya bashi

" naji...muje bedroom dina in nuna maku wani abu" su biyu kallionshi sukayi alaman yana son kwanciya dasu lokaci. Babu kunya fina tace

"gaskiya slim i can't share you with her" ta fada tana nuna mimi, shidai baice komai ba yacigaba da tafiya dasu har bakin wani katon kofa, daidai wani scanner dake jikin bango ya tsaya tare da dukawa, abun yayi scanning idonshi, nan take kofan yayi sliding gafe daya sanna ya shiga rike da hannun ko waccensu.

๐Ÿ’œ๐Ÿ’šโ™ฅโค๐Ÿ’™

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’š๐Ÿ’™โคโ™ฅ๐Ÿ’›

ยฎzuwaira(ummu maryam)

2โƒฃ

Suna shiga dukansu suka bude baki don tunda suke basu tabha ganin bedroom mai girma da kyau irin nashibha don ana iya gina katon three bedroom flat da filin bedroom dinshi. Sakin hannunsu yayi ya shiga bathroom dinshi ya daure alwallah ya fice daga dakin ba tare daya kallesuba

Bayan sun dawo daga daga masjid direct inda cook ya shirya masu dinner kan carpet suka wuce. Suna cin abinci suna hira, inkazo wurin baka gane waye oga don sai dariya suke.

Around 8pm suka gama dinner still masjid suka koma don sallan ishai. Shidai salem kullum bashi da aduan da yawuce Allah ya bashi mata tagari.

Suna dawowa suka zauna tsakar gidan wanda ke da haske tamkar rana. Su shida ne tare da salem su bakwai. Hira suke suna daria, bayan kaman minti 30 daya daga cikin guard dinshi mai suna Jibril yace

"sir in babu abinda zanyi maka ni zan tafi wurin madam,," dukkansu daria sukayi

"kaji masu iyali" inji daya daga cikinsu mai suna abdul.

"ai sunji dadinsu...inama ni" inji Salem, dukkamsu kallonshi sukayi sanna Jibril yace

"sir ai kai ke bakason auren..don don nasan ko mata hudu kakeso kana iya aurensu rana daya...tunda ga naira ga kudi" dan tabe baki Salem yayi sannan yace

" ai abinda bana so kenan...so nake in aure macen da zata soni don allah ba don connection ko kudinaba" dan daria sukayi sannan daya daga cikinsu mai suna majid yace

"ai sir da wahala ka gane macen dake sonka don Allah yanzu tunda ko wacce mace pretending zatayi tana sonka don abin hannunka"

"kaji problem din" ya fada sannan ya kalli Jibril

" alh Jibril yaushe ka auri matanka" yace mashi don haka yake kiransu ALH kasancewan dukkansu sunje hajj a sanadiyanshi. Ahankali Jibril yace

"Yanzu shekaranmu biyar da aure...dukda dai nasan mata kudi sukeso gaskiya sir banda matata... Don sanda mukayi aure teaching nake a private school kuma albashina 15k.. " bai gamaba Salem ya kwalo ido waje tare dacewa

"alh Jibril 15k fa kace?:" ya fada with disbelieving voice " daga mashi kai Jibril yayi tare dacewa

"yes sir.. " da sauri salem ya sake cewa

"ya mutum zai yi surviving da 15k balle har da mata? " dan murmushi Jibril yayi sannan yace

"sir shi yasa nace matata is different don a wannan lokacin ita ke karfafa mani gwaiwa...wallahi sir da akwai lokacin da zamu kwana babu abincin kirki...amman she stands beside me with love" duk jikin Salem da sauran guys din yayi sanyi, ahankali Salem yace

"inama ni.. " da sauri Jibril ya katseshi dacewa

"sir kar kayi fatan shan wahalan da ni da matata muka sha" ahankali Salem yace

"but you have true love..and it's among what matters most in life...i wish ina iya samu macen da zata soni.. I can do anything for true love..don gaskiya ban iya aure sai na sami true love " dukkan guys din shuru sukayi suna tunanin maganan ogansu.

Few seconds later abdul yace

"sir kaman yanda majid yace da kyar ka gane mai sonka, don ina tabbatar maka babu macen dazata ki ka" yadan tsaya sannan yacigaba dacewa

"sir tunda kana neman true love... Ina da shawara... " dukkansu harda Salem suka maida hankalinsu kan abdul

"am all ears" Salem ya fada mashi. Abdul shiru yayi ya kasa magana, don yasan Salem baya daukan rubbish,

"kaifa nake jira... " Salem ya sake cewa. Shuru Abdul yayi for a while sannan yace

"sir abar maganan kawai" don yana tsoron abinda zai faru in har ya fadi abinda yayi niyya

"ai baka isaba... Am listening " Salem ya ce mashi.

Sadakarwa Abdul yayi yafara cewa

"sir.. Da cewa nayi why not ka dan maida kanka talaka for a while.... " darian guys din ya hanashi karasa abinda zaice, shi kam salem kallon Abdul yake ba kiftawa, daga kai yayi ya kalli guys din, nan take sukayi shuru sannnan ya kara maida kanshi wurin ABDUL din da yayi tsuru2 sannan yace

"alh Abdul taya zan maida kaina talaka bayan ni ba talakan bane... Please explain your self " ahankali Abdul ya ce

"sir..ina nufin kayi disguising kanka... I mean kana iya maida kanka taxi driver...." wani irin dariya dukkansu suka sakeyi, banda Salem daya hada giran sama dana kasa, a hankali ya mike ya taka zuwa gaban Abdul sannan ya dafa gaban goshinshi don tabbatar ba zazzabi yakeba. Jiya yayi temperature dinshi normal, shi kam Abdul gabanshi sai disco yake.

Salem bai ce komaiba ya wuce side dinshi. Dukkan guys din kallon Abdul sukayi suna cewa

"you fucked up... Yanzu kasa ran sir ya baci..."

Salem kam tunani yake ya sakar wa bodyguard dinshi jiki da yawa tunda abun ya fara kawo raini tsakaninsu...

"wai ni taxi driver...hmmm i will treat your fuckup" ya fada yana bude kofan falonshi, yana shiga agogon hannjunshi ya fara ringing cos waya ce, dan murmushi yayi kasancewan yasan mai kiran don wakan sweet mother ne kawai ke tashi daga agogon hannunshi, ahankali ya yi picking tare dacewa

"good evening first love... " bai karasaba naji wata irin sweet mature female voice tana cewa

"son ka rainani ko?.. " da sauri yace

"first love kiyi hakuri..." matan ta katseshi da cewa

"keep quiet silly child...kullum am sorry.. Yanzu where are you?" Salem kan kujera ya zauna yana shafa kanshi irin na mara gaskiya sannan yace

"first love ina ABUJA.. "

" me ka gayamin da safe? "" matan ta tambayeshi, ahankali yace

" umma cewa nayi zanzo yola yau... "

"to yanzu a yola kake? " matan ta sake tambayanshi, dan girgisza kanshi yayi sannan yace

"no... Umma sai karfe eight na tashi daga off... "

"yimin shuru makaryaci... Nasanj dalilin dayasa bakason zuwa...don't worry zansa abbanka ya zaba maka mata cikin family ko cikin yayan friends dinshi.... " sanin halin ummanshi yasa shi saurin cewa

"wayyo Allah first love kiyi hakuri na kusa kawo mata...please don't talk to abbah.. " ahankali matan tafara cewa

"love why are you treating me like this?... Ko don ka san you are my only son?...sisters dinka suna chan gidan mazajensu kai kuma bazaka kawo min yarinyaba?... "

"first love give me a little more time... Inshort ki bani maximum of five months... In ban kawo mataba ki auramin kuturuwa..." darian ummanshi ya katseshi , shima murmushi yayi

"habibi ka maidani kakanka ko.."

"no first love am serious.. Kibani wata biyar kawai...kinji please "

"naji..amman let your five months be five months.." da sauri yace

"yes umma" dan hira sukayi for about 20 minutes sannan sukayi sallama. Dan ajiyan zuciya ya saki sannan yace

"atleast zan dan huta da fadan mom na wata biyar... " relaxing yayi yana lumshe ido ahankali yana tunanin ya Allah kabani mata and she will be the luckiest girl.

๐Ÿ’›๐Ÿ’™โ™ฅ๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’›โ™ฅ๐Ÿ’™

ยฎzuwairat(ummu maryam)

3โƒฃ

Su mimi suna ganin ya fita suka kalli junansu sannan suka fara kallon dakin, komai na dakin golden color ne, wani irin makeken gado ne a tsakiyan dakin wanda ke kamada baa kwanvciya samanshi don komai very neat, mimi dan matsawa tayi kusa da dressing mirror taga kayan shafa kaman da mace don ko a mata sai masu hali zasu iya siyan irin kayan shafanshi cos ko su da suke yayan minister basu da yawan kayan shafanshi, perfume kam tamkar nan ake saidasu, itakam fina wani kiofa da aka rubuta my wardrobe ta bude sai taga dakine amman abin mamaki duk girman wurin suturanshi ne shake da wurin, suit sunfi kala dari da hamsin kuma dukkansu designer ne like wise takalma ma basu irguwa suma yawancinsu daga companin prada ne, juyawa tayi ta kalli inda yake ajiye agogo da glass suma sunfi kala 40 suma designer, itama mimi dakin tabi fina, itama tana shiga ta bude baki

" the guy is beyond our expectations.." fina juyawa tayi ta kalli mimi tare dacewa

"ni tunda nake zuwa shopping abroad ban taba ganin boutique dake dauke da yawan designer clothes waje daya kaman na slim ba... Kalli vallantino pijamas.. Babe mu ajiye fadamu waje daya mu dangwali arziki..wallahi this guy is loaded " murmushi mimi tayi tana tunanin ai ko a ta hudu tana iyan ajiye pride dinta ta aureshi, itama fina tunanin da take kenan don salem ya fi duk yanda take tunani, wata

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login