Showing 48001 words to 51000 words out of 145230 words

Chapter 17 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

254

your Ife...please just listen to me" bude ido tayi tana kallon shi, shima kura mata ido yayi,

"It's me" tana kuka tace

"How comes?" Ta tambayeshi, har lokacin yana rike da fuskanta itakuma rike da hannunshi dake kan fuskanta, kallon juna suke kaman basu taba ganin junaba, kaman mai rada yace

"Please at least eat and pray..then zan gaya maki komai" girgiza kanta takara yi

"I can only pray"

"Muje in rakaki bathroom" dan dauke hannunshi tayi daga gefen fuskanta,

"Please show me the bathroom" mikewa yayi itakuma tabi bayan shi, suna tafiya tana kallon dakin

"Kaman baa mutuba?" Ta fada cikin ranta, wani kofa ya bude tabi shi, wani makeken bedroom apartment ne mai dauke da silk bedsheets, kallon girman wurin kawai take, don yayi takwas din ciki da falonsu, kofan bathroom yabude mata,

"Ki shiga" ya fada sannan ya koma yaje ya zauna bakin gado yana jiranta, shiga tayi tana tunanin

"Allah yasa mafarki nake" jitayi Salem nacewa

"Please habibty take a shower" kallon swimming pool dake gabanta tayi, bata taba swimming ba Amman tason tashiga, wani bathroom tub tagani, komawa tayi ta kulle kofan, sannan ta cire kayanta tayi wanka da wani sabulu mai shegen kamshi. Allah ya taimaketa ta iya kunna kan shower

Salem najin shower yayi murmushi sannan ya mike ya dauko Arabian gown din da majed yasayo ya ajiye mata kan gado tare da yimata fixing din praying mat sannan ya fita ya koma falo yana cewa

"Am going to try and be a perfect gentleman".

Tana gamawa tayi alwallah Sannan ta goge jikin ta ta maida kayanta ta fito, ko kallon gown din batayiba ta yafa gyalenta tafara rama sallolin da ake binta.

Bayan 30 minutes ta kammala Amman ta kasa mikewa , tunanin iri2 ne cikin ranta, Salem gani yayi har nine bata fitoba, mikewa yayi ya Dan bude dakin, hangota yayi zaune ta hada kai da kwaiwa. Takawa yayi Ahankali yazauna kusa daita, har lokacin batasan yana wajen na, tabata yayi ta dago kanta da sauri fuskanta sharkaf da hawaye

" haba habibty.. Meye haka.. Please change and come and eat..remember kina bani abinci inaci..why not bazaki ci na gidana ba?" Yayi magana kaman mai whispering, Dan goge hawayenta tayi

"Please tell me who you are.. Am scared" tafada cikin kuka, dawowa yayi gabanta ya zauna tare da yin gammo da kafanshi, hannu yasa ya dago habarta, sannan yafara cewa

"Sunana Salem Yusuf sulaiman..." Da sauri tawa ta daga kai ta kalleshi tana Dan maimaita

"Salem Yusuf sulaiman.." Kaman tanason tuna inda taji sunan, Salem yacigaba dacewa

"I am the son of former Nigeria President Yusuf sulaiman..." Da sauri tawa ta matsa baya tana kara fashewa da kuka at the same time tana dukan kanta tana cewa

"Please wake from this dream" da sauri Salem ya rike mata hannu

"Stop.. You are not dreaming.. Its real" kara matsawa kusa daita yayi ya rike two hands dinta cikin nashi sannan yafara bata labarin duk abinda ya faru har zuwa yanzu, Amman bai kara dana abinci da kuma kudin Mtn ba, tawa Dan goge hawaye fuskanta tayi, sannan ta daga idanuwanta da suka koma kaman garwashi tace

"So kai nake yiwa abinci" ahankali ya daga mata kai, tacigaba dacewa

"kuma Kaine sanadin kudin Mtn" kara daga mata kai yayi, sabon kuka tafara tana cewa

"How can I be so fooled?..."

"Am sorry... Am just searching for true love" da sauri ta zare hannunta daga nashi sannan tayi cupping fuskanshi a hannunta

"Sir look at me and look at your self... What makes you think it will work?..." Da sauri shima Salem yayi cupping fuskanta, yana girgiza kanshi yana cewa

"No..you are the person I love.. And I am 100% sure you love me too..."

"Please sir stop talking about love...you are powerful am not... You are somebody am nobody... You are educated am not... You are the richest man in Africa I am a poor helpless girl..." Girgiza mata kai kawai yake

"All those things basu da maana awurina...I love you and that's the most important thing.. This is meant to be..don't think about it..." Girgiza mashi kai kawai take still hannunta kan fuskanshi

"Baka ganeba...mutane kaman mu don't last in such stories.. We are insulted... Maltreated... Humiliated..."

"Please habibty stop it..your words are hurting me" kuka tafarayi sosai, baisan sanda yajata ya rungume ta ba, tacigaba dacewa

"I shouldn't have love you sir..." Rungume ta yayi gam yana cewa

"You are mine..nothing... Nobody is stopping it...I love you.. You deserve more..you are kind...you are special.. You are beautiful..." Tawa ma rungume shi tayi tana kuka mai ratsa zuciyan mai saurare, Salem jiyake kaman ya tayata kuka Amman shi ba mutum bane mai saurin kuka, shafa bayan ta yake

"Enough.. Ki bar kuka haka nan" tawa girgiza kanta ta dinga yi

"Barni inyi kuka...naso abinda yafi karfina..before ina tunanin zan lallashi mami ta amince in aure ka.. Amman yanzu...I don't want to die.."

"Please stop saying those horrible words.. Bantaba son abu ban samubae..kuma you won't be an exception.." Dan zame jikin ta tayi daga nashi , shikuma yasa hannu ya goge mata hawayenta

"Please nasan Kana Iya sawa amaidani Kano..please ask somebody to take me back to mami...banason kudin..please" ahankali yace

"zan maidaki da kaina..but please wait until tomorrow" girgiza mashi kai tayi

"I want to be with mami now" mikewa yayi ya dagata,

"Muje kici abinci"

"No..I want to go home.."

"Please.. Follow me..ko kuma in daukeki...kinsan we're alone..in this big house.. Anything can happen" daga kai tayi ta kalleshi ya kashe mata ido daya, kuka ta shigaba dayi,

"Ashe daman you are a cry baby.. Then tsaya in daukeki" dukawa yayi zai dauketa ta koma baya, kaman an chunkuleta tace

"Oh my Allah.. You are married"

โค๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’œโค

ยฎzuwairat(ummu maryam)

3โƒฃ4โƒฃ

"Me kikace?" Ya tambayeta pretending, dan goge hawaye tayi

"Kana da aure mana...last week was your wedding... Am together with another woman's husband..."

"Habibty stop it...ni bani da aure..am single for you alone..."

"Nasani...shiyasa ka bar Kano ranar Friday..."

"In nayi aure last week me zanyi a nan?...please enough.. Muje kici abinci" komawa tayi ta durkusa kasa

"Nidai ka maidani Kano...bansan kwana gidan nan..." Daria yayi

"Nan ne fa gidanki nan gaba..taso kici abinci" da sauri ta girgiza kanta tana kuka

"Please take me to mami..." Bai kara cewa Komaiba ya nufeta, daukan ta yayi, kara fashewa tayi da kuka,

"Please drop me..its not proper" banza yayi daita har saida suka isa dinning table sannan ya ajiye ta,

"Sit" girgiza mashi kai tayi

"Na koshi.."

"Ashe kina da kafiya ban saniba?..haba habibty... Just relax..everything will be alright..." Cikin kuka ta fara cewa

"You are not getting me...wannan soyayya ba me yuwa bane...nasan kana da aure...sannan nasan iyayenka won't like me...we are two different people" matsawa yayi kusa da ita sosai tare da rike shoulder dinta

"Look at me.." Ya umarce ta, ahankali ta daga kai ta kalleshi

"Believe me..bani da aure"

"Then waye dan tsohon shugaban kasa da yayi aure last week?"

"Da akwai yayan tsohon shugaban kasa dayawa...and about my parent..nayi masu magana kuma sun amince...." Da sauri ta girgiza mashi

"No ban yarda ba..I remember ranar Friday you were sad when I called you..ashw abinda ya sa ranka ya baci ne...."

"Oh tawa..stop it...I am the man..in da akwai matsala I should be the one to say..." Ya fada cikin fada

"No!" Itama ta fada a tsawace, tureshi tayi, ta je kan kujeran da bag dinta ke kai ta dauka sannan tayi hanyan fita, Salem tsaya kallon ikon Allah yayi, gani yayi da gaske take, da gudu ya bi bayan ta,

"Where are you going?"

"Home" ta amsa mashi a takaice, da sauri ya rike ta, kwace kanta tafara kokarin yi Amman a banza, amshe jakkan yayi ya yarda ya rungume ta, wani sabon kuka ta farayi , cikin kuka ta dinga cewa

"Please let me go...we can be together... People will laugh if they see us together..." Daga fuskanta yayi

"Nobody will laugh at us...you don't know how special you are... Please I love you.. If you love me too then forget about every body..." Tawa kura mashi ido tayi tana tunanin abubuwa kala2, goshinshi ya kai kan nata yana kallon long eye lashes dinta, cikin whisper yace

"If you don't want us to start our honeymoon early kije kici abinci" yafada yana lumshe idanuwa, itama cikin shessheka tace

"Na koshi..."

"Please" yafada kaman mai jin bacci,

"Na koshi...gida zani..."

Cikin rada yace

"I have learnt that you are stubborn... Since you are not eating...muje kibani virginity dinki..kinga that will make you bond to me..." Sabon kuka ta farayi, hancinshi ya fara gogawa kan hancinta,

"Please ka bari...." Idanuwanshi rufe sai ya maidata ya rungume, yana yi kaman masu rawa, kadan2 yake dan juyata kaman yana lulu baby, tawa sai ajiyan zuciya take, don tasan bazata karason wani danamiji kaman yanda ta so Salem Amman kuma tasan tarayyansu bamai dorewa bane.

Tasha kallon film din da mai kudi zaiso talaka Amman daga karshe talakan ke wahala, at times har kashe talakan ake, she loves him,but she don't want to be a victim.

Shima Salem tunani yake, yasan in har bai samu tawaba rayuwanshi na iya zuwa karshe, ya iyawa kanshi alkawarin samunta at all means....hannu yasa yana shafa bayan wuyanta zuwa bayanta, cikin rawan murya tace

"Sir please stop..." Shima cikin whisper yace

"Please don't stop me..." Kuka tafara yi tana cewa

"You promise mami you will take care of me"

"Kin ki in kula dake...abincin gidana kinci kikayi" yafada yana hada bakin su waje daya, passionate kiss yafara yi mata, tawa babu bakin kuka sai hawaye, hannunshi yasa kasan riganta yana shafa bear warm, and tender skin dinta, da sauri tawa ta zare bakinta tana cewa

"Zanci abinci.." Yanda tayi maganan yasa Salem yin daria,

"To muje kici" ba musu tayi saurin komawa kan dinning shima Salem da sauri ya zauna kan kujera yana daga gaban jallabiyanshi don kada taga joystick dinshi dake tsaye

๐Ÿ’›๐Ÿ’šโค๐Ÿ’œ๐Ÿ’™

Bayan hinde ta gama ta dawo, lokacin ameera ta gama cin abinci ta koma ta kwanta, sallama tayi daga ciki ameera ta amsa mata

"Badai kin kara kwantawa ba" hinde ta cemata

"Eh..har kin dawo?" Ameera ta tambayeta tana mikewa zaune

"In shigo?" Ameera dan hararan kofan tayi sannan taja karamin tsaki

"Ki shigo mana" tafada tana kara kwantawa kan katifan data maido falo, hinde shigowa tayi ta zauna tana cewa

"Wannan kwanciyan da kike yawan yi..ko dai kina da juna biyu?" Tsaki ta kara ja

"Kin taba ganin mara miji da ciki?"

"Nasani ko Wanda kuka yi baya ya zama ciki?" Hararanta tayi tana tunanin

"Wannan banza Matan ma ta iya iskanci...look at dirty foot" tafada cikin ranta, sannan tace

"Inzo kiji kwakwaf..ban taba kwanciya da namijiba" kallon mamaki hinde tayi mata tare da gyara zamanta

"Amman mijinki sakarene...ga ki kaman madubi?... Ko mace na ganin kyanki balle namiji" tabe baki ameera tayi

"Bayasona.. Ya aureni ne saboda ya dauki fansa"

"Fansa kuma?.. Koma wane irin fansa ne bai cika na mijiba...ko ma meye kyau yayi hakuri ya mori wannan jikin" ameera saita tsinci kanta tana daria

"Ke dai kice kinason gulma kuma bazan fada maki ba"

"Nayi shuru...Amman in kinason Akira maki shi ina iya fadawa babana..." Da sauri ta mike zaune

"Ban gane ba"

"Babana malamine..yana iya kira maki mijinki.."

"Kina nufin akirawoshi ya dawo nan gurina?..ko kuma ya daukeni daga nan gidan?"

"Sosai kam" dirty look ameera ta watsa mata

"Kuma cikin wannan dajin Amman baku bar mugun abuba...wai in tambayeki mana" hinde da aka gwalace tace

"Inajinki"

"Da akwai inda ake saida zinari nan wurin..ko kuma ince inda ake sayan zanari"

"Gaskiya ba nan kusa ba..sai cikin gari"

"To in na baki awarwaro na daya zaki Iya saidamin ki sayo min waya da layi?"

"Sosai kam.."

"Gobe zan baki ki saidomin sai ki sayo min waya da kayan shayi"

"Allah ya kaimu" ameera komawa tayi ta kwanta, Sai bayan magrub hinde ta tashi tafiya, ameera kaman zatayi kuka tace

"Dan Allah.. Ki turomin wata yarki ta tayani kwana..tsoro nakeji"

"Zan turo maki wata yara da auren ta ya mutu ta tayaki kwana" dadi ameera taji Amman Mara kunya cewa tayi

"Dan Allah in sabulun dazu da sauran ki bata ta wanke kanta da jikin ta kafin tazo"

๐Ÿ’›๐Ÿ’šโค๐Ÿ’œ๐Ÿ’š

Tawa tana cin abinci tana hawaye, Salem kam sai kallon ta yake with adorations.. Imagining yake kawai insuyi aure, irin rayuwa dazasuyi, ko quarter pepper chicken bata cinyeba tace

"Na koshi" tafada tana goge hawaye, Dan murmushi yayi sannan ya mike ya bude sabon wine ya zuba mata cikin cup, shima zubawa kanshi yayi

"Drink my choice" Dan hararanshi tayi

"Bana shan alcohol.." Daria yayi

"Nima ban taba shaba..its an non alcoholic wine" yafada yana kama hannunta, amsa tayi ta kai bakinta, shima Dan sha yayi sannan ya kalleta yaga ta bata fuska alaman bata jin dadinshi, cikin zolaya yace

"Nima haka naji lokacin da kika bani wannan drink mai suna maltina" tawa bata San lokacin da daria ya kufce mataba, Salem dadi yaji, sai kuma ta fashe da kuka, dan ajiye tumbler dinshi yayi ya amshi nata ya ajiye, sannan ya juya kujeranshi yana kallon ta

"Habibty gayamin Wanda zan yiwa magana yaje wurin mami.." Tawa shuru tayi bata ce komaiba

"Please habibty tell me.. I know they is someone mami respect.. Someone she doesn't turn down..we should get married soon..." Yafada cikin whisper, still bata bashi amsa ba

"Then meye sunan grandpa dinki..." Bata bashi amsa ba, ahankali tace

"Sir if you can take me home.. Zan kwanta" hannuwanta biyu ya rike yana massaging dinsu ahankali

"Kullum muna waya da dare, yau tunda muna tare muyi hira mana..."

"I want to sleep"

Mikar da ita yayi, ya zagaye hannunshi kan waist dinta, ahankali tace

"Amman ka saba da taba mata..." Daria ya karayi, bai amsa ba ya duka ya dauketa in a bridal style

"Please drop me..."

"Haba love...bari in rage maki hanya..inason in nuna maki I will be a romantic hubby" yafada yana kaita bedroom, kwantar daita yayi ya kwanta gefen ta, da sauri ta mike

"What are you doing?" Tafada arazane, dan rufe feet dinshi yayi da blanket

"Let's sleep.. I promise I will be a gentleman"

"No..." Tafada tana mikewa, riketa yayi tare da jawota jikinshi, ahankali yace

"Habibty sleep... Nasan bazaki iya kwana ke kadaiba" da sauri tace

"Wallahi ina iyawa" mikewa yayi zaune tare da kwantar daita sannan tashi daga kan gadon, blanket ya rufa mata

"In kashe maki wutan?" Banza tayi dashi, tsayawa yayi yan kallon yanda hips dinta yakara fitowa sosai data kwanta,

"Habibty ko inzo inyi maki irin tausan da mami take yi maki?" Batace komaiba ta rufe dukan jikin ta da blanket, daria yayi sannan ya rage mata hasken dakin yafita yana cewa

"Dream of me love".

Side dinshi ya koma ya chanza kayan zuwa na bacci sannan ya kwanta tare dayin rub daciki.

Tawa na gani ya fita tayi saurin mikewa ta koma falo ta dauki wayanta, gani tayi mami ta bata 3 missed call, da sauri ta kirata tana kuka, nan fa ta fadawa mami duk abinda ke faruwa, ta kara dacewa.

"mami am scared...I don't want his parent...ex girl friends su kashe mu..."

"Listen..Ife..first thing In the morning.. Ki tafi Ilorin gidan anti sikirat...zan kirata..ta jiraki a park...zan biyo ki" Cikin kuka tace

"Mami Salem fa...me zance mashi?" Afusace mami tace

"Don't ask me silly questions.. Kiyi abinda na fada maki... Kuma don't let him know you are going.. Ke kadai gareni..banason abinda zai tabaki.." Kuka ta shigaba dayi

"Wai wannan kukan da kike hala wani abu yayi maki?"

"No mami"

"Ki kwanta yanzu don ki tashi kafin gari ya waye"

"Yes mami"

๐Ÿ’™๐Ÿ’›โค๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

ZAKISAN KONI WAYE

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

ยฎzuwairat(ummu maryam)

3โƒฃ5โƒฃ

Tawa zama tayi tana kuka, duk idanuwanta sun kumbura, mikewa tayi tsaye tana kallon falon tsoro na ratsata, ko a film bata taba ganin falon mai girma da kyau irin wannan ba, tunda take bata taba kwana ba kusa da maminta ba, tasan ko kwana goma zatayi cikin gidan nan bazata taba iya bacci ba, Ahankali tafara yawo cikin falon, tashiga nan ta fita chan

"Wane irin kudi ne wannan?". Ta tambayi kanta lokacin data shiga kitchen, wasu irin kitchen wares tagani Wanda koda zaa kasheta bazata iya amfani dasuba, jitayi kanta nayi mata mugun ciwo.

Salem kam yana kwance sai juye2 kawai yake, wani irin azaban ciwon ciki yake, gani yake wannan yafi sauran azaba, sau biyu yana shan magani amma to no avail. Yasan in har ya kai wata daya baiyi aureba yana iya mutuwa ko kuma ya shiga wani halin, ahankali nace

" my oga at the top..kaje wajen ameera mana.." Juyowa yayi ya watsa min dirty look sannan yaja tsoki sannan yakoma yacigaba da juye2 wayanshi ya jawo yayi dailing number tawa,

Itama tawa saida ta tsorata da karan China phone dinta, da sauri tayi picking, ciki whisper tare da nishi kasa2 yace

"Habibty.. bakiyi bacci ba?" Itama cikin whisper tace

"Eh" rasa abincewa yayi for a moment, sai nishi yake ahankali tace

"Ifemi.. What is the problem?" Bai amsa ba ya shigaba da nishi..

"Cikina.." Ya fada kaman an fixgi maganan daga bakin shi, cikin magana Mara fita tace

"Sorry..sleep" yana nishi yace

"I can't..." Shuru su biyu sukayi for almost a 30 seconds sannan tace

"Daman haka yake yi maka ciwo kullum?" Kasa amsawa yayi don ko kadan bashi da bakin magana,

"Wayyo cikina!" Yafada da karfi

"Sorry Ife..sorry... Please do something to help your self..." Shuru yayi baice komaiba, nishi yake sosai

"Ife..kana ina?... Please kazo..." Ahankali yace

"I can't... Wayyo zan mutu" tawa kuka tafarayi sosai

"Sorry... Please call help..." Still juye2 yake, nishi yake amma kukan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login