Showing 105001 words to 108000 words out of 145230 words

Chapter 36 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

261

ta kawai take. Gani take Salem ya saba da using mata yana sakinsu secretly batare da sanin mutane ba.

"No wonder he's romantic and caring..he always knows the right words to say..." Tafada cikin muryan ta da bai fita sosai, bata kai minti biyar da kwanciya ba bacci ya dauketa.

Salem na sauka down stairs ya nufi dakin da take gabanshi sai faduwa take don gani yake zata kara ci mashi uwa. Ahankali ya bude ya gangeta kwance kudundune cikin gyalen dake jikin ta, tafiya yayi a ahankali ya karasa wurin ta, yaga tana bacci, gabanta ya koma cima ya kwanta nan kasa kusa daita, fuskanshi daidai nata sai shakan numfashin ta yake, kallon yanda iduwanta suka kumbura yayi, kuma dukda tana bacci bata bar shessheka ba,

"Am sorry... Please" yafada kasan makoshinshi, ahankali ta bude idanuwanta da sukayi mata nauyi tana ganin shi tayi saurin mikewa ta matsa baya, shima mikewa yayi zaune yana kallonta

"Baby am sorry...this is not us...we should be happy... Yau ya kamata..." Bai idaba ta katseshi dacewa

"Yau yakamata ka dauke pride dina don kaji dadi sakina ko?...you will not get what you wanted... " ta fada ta sake sabon kuka, kai kawai Salem ya girgiza

"I have never slept with any woman... You are the first woman that sees my nakedness.. Wallahi..." Bai idaba ta bar wurin ta bude kofa ta koma falo, gani tayi an kawata wurin dinning table ga abinci anjera Sannan ga wani candlelight a wajen looking so romantic. Zama tayi Salem ya biyota ya zauna nan kasa kusa daita, baya ta juya mashi ya kara komawa gabanta

"Baby..please let's eat..." Yafada gwanin ban tausayi, banza tayi dashi

"Please...'" Still batayi responding dinshi ba, mikewa yayi ya rike mata hannu, buge mashi hannu tayi da karfi har ya saki kara yana rike wrist dinshi data buga don ba kadan yaji zafin bugunba, dan shaking hannu yayi ya saki kara saboda azaban da hannun keyi mashi, tawa kam ko daga kai batayiba balle ta ce mashi sannu,

"Baby kin karya min hannu..." Yafada yana cizon lips dinshi saboda kafin da hannun shi keyi mashi, batace mashi uffan ba tacigaba da kukanta, kara shaking hannun yayi ya tabbatar yaji da gaske wrist dinshi zafi, kuka yafarayi kaman yaro yana cewa

"I don't deserve the punishments.. Wallahi abinda na fada maki is nothing but the truth.. Yanzu nasan ba sona kikeba..wallahi in da nasan haka kike da taurin zuciya da ban...." Sai kuma yayi shuru, itama tawa mikewa tayi

"Da baka aureni bako?... Complete it...nima danasan haka kake da ban aureka...kuma it's not late...kana Iya maidani gidanmu... I hate you with passion... I don't care if you die...ban zama da kai..." Salem shuru yayi yana kallon ta

"Anya kece Tawakaltu Dana aura?...my Tawakaltu is nice and considerate...she's understanding..." Baki ta tabe

"Makaryaci kawai..." Ta fada Sannan ta koma kasa ta zauna ta cigaba da kuka ko bata gajiya da kukane oho. Salem tsayawa yayi yana kallon ta dama haka quite people ke da masifa, hmm lallai the devil you know is far more better than the angel you don't know, tsayawa yayi zuciyanshi na up and down Kuma hannun shi sai zugi takeyi mashi. Bai Kara cewa komaiba ya koma kan wani kujera dake falon ya zauna hannun shi daya rike da wrist dinshi don ba karamin zafi yakeji ba, hannu yasa cikin aljihunshi ya fiddo wayan shi ya kira wani abokinshi.

He can't believe this is happening.

Bayan kaman hour daya akayi ringing doorbell Ahankali yaje ya bude kofa har lokacin tawa na zauna kanta cikin kwaiwanta sai ajiyan zuciya take, wani handsome looking baturene ya shigo, gaisawa sukayi Salem ya nuna mashi hannun shi, wani briefcase dayazo dashi ya bude ya dauko wani Abu yana Dan danna hannun Salem dashi ihu Salem ya saki

"I think is fractured..." Doc. Yace, Salem Dan daga kanshi yayi ya kalli tawa ko zata daga kanta sai yaga ko gizau batayi ba, daure mashi hannun doc yayi sai dan ihu Salem yake, tawa mikewa tayi ta shige bedroom abinta Salem ya bi bayanta da kallo, doc na gamawa sukayi sallama, Ahankali ya mike da abun daure karaya hannun shi, still dakin da tawa take ya shiga, ya ganta kwance kan gado, wurin ta yaje ya zauna bakin gadon, yadan matsa kusa daita

"Please ko tea ne kisha..." Ya fada mata sounding so heart broken, banza tayi dashi,

"Please.. Kawai don't take me as your husband.. Kawai take me as a friend who cares for your wellbeing... Muje kici abinci..." Bata kalleshi ba balle ta amsa mashi. Kara mikewa tayi

"Leave me alone..stop following me.." Ta fada tana kara fita daga dakin,

"Ikon Allah.." Salem yafada yana binta falo, shi kanshi yana mamakin irin son da yake yi mata, yasan nobody tries him this way.

,,ameera kam tana ganin tafiya taki ci taki cinyewa tasan ba gidan Salem zaa kaitaba, Sannan tasan ba Kano zaa kaita ba, shuru tayi tana adua cikin ranta, bacci kawai take ji ga juwa tana gani.

Har 9:45 Salem bai bar lallashin tawaba amma ko kallon inda yake batayiba balle ta tausaya mashi, duk idanunshi sun koma ciki saboda yanda fuskanshi ta fada lokaci guda, suna cikin haka jet ta sauka, da sauri Salem yaje ya buda kofa, tawa kam tana zaune kasa har lokacin tana ganin Salem ya fita ta koma bedroom ta kwanta, Salem na fita yayi daidai da da aka sauko da kofan jet, ameera ta fito tana kallon inda take gidan take kallo da Wanda ke tsaye bakin kofan hannun shi Dan bandage, Ahankali ta karasa wurin ta tabbatar da Salem ne, mugun kwarjini yayi mata, don ba karamin kyau yayi mataba, fuskan Salem kam babu walwala ko kadan, wuceta yayi yaje wurin pilot yayi mashi magana, Sannan ya dawo ya kalli ameera dake tsaye bakin kofan, kura mata ido yayi yaga ta rame fiye da sanda yaje, kayan jikin ta ya kalla, itakam ameera banda faduwa babu abinda gabanta yake, Kaman zata fada kasa cos ko kadan kafanta bai daukanta, kanta kasa

"Shegiya kaman wata mutuniyar kirki" ya fada cikin ranshi, kara kallonta yayi yaga yanda take yasan tawa zata amince da ba zaman aure yayi daita ba, zaman cin ubanta yayi

"Ke!... Meke damunki kika rame haka?.โ€ฆ ko kudin da aka kawo maki baki cin abinci dasu?..." Ya tambayeta sounding so disappointed, banza tayi dashi kanta kasa

"Ke am taking to you..." Yafada afusace

"Bani da lafiya .." Ta amsa mashi atakaice,

"Shiga ciki yayi tayi tsaye nan waje bata shigo ba, itakuma sai mamakin abinda ya sameshi take don dukda suna dare bai hanata ganin yanda idanuwanshi sukayi jaba Sannan ga hannun shi rataye da wuyanshi.

" get in..." Ya fada mata, Ahankali ta shiga ciki, wuri ya samu ya zauna yana kallon yanda ta sadda kai kasa, tafi minti biyar tsaye Sannan Salem ya mike yana Dan kuntun tsaki, bakin kofan da tawa take yaje ya bude amma ya jita kulle, komawa yayi ya zauna Sannan ya kalli ameera

"Ga abinci chan...serve your self... In kin gama Go upstairs ki kwanta...," ya fada mata yana mikewa, upstairs yayi yaje ya kwanta kan dogowar kujera cos dukkan kujerun downstairs one seat ne, yana tafiya ameera ta daga kanta ta fara kallon falon,

"Kambu..." Tafada looking so excited, kan dinning taje ta ga irin hadadden abincin mai rai da lafiya, da alaman babu Wanda ya CI, dankwalinta ta ajiye gefe ta fara serving kanta don at that moment she feels as if she's on top of the world. Duk saita nemi mentral cramp dinta ta rasa, abinci taci sosai tana aduan Allah yasa ba bayerabiya ta dafa ba cos ita kyamansu take imagining that, tasha assorted drinks Sannan ta hau sama, gani tayi Salem na kwance, da sauri ta bude kofa ta shiga cikin bedroom da aka shirya don honeymoon sai tunani take ko ina bayerabiyar matarshi take. Mikewa tayi kan gadon bacci yayi gaba daita, nace ko tana tunanin ita akayiwa wannan beautiful arrangements ne? Oho. Acikin su uku ameera ce kawai tayi bacci mai dadi daon rabon da tayi irin wannan baccin tun tana gidan su, bangaren Salem kam yanda yaga rana haka ya ga dare ga azaban ciwon hannu dana kai itama Tawakaltu batayi bacci ba don gani take kaman kanta zai tsage gidan biyu ga jikinta zafi rau.

The following day sai bayan sallah Salem ya koma bacci, itakam tawa da kyar tayi sallah cos tasan she's sick nan inda tayi sallah ta kwanta bacci mai nauyi yayi gaba daita,

Abangaren bakuwarmu kam dama ba cikin yanayin sallah take ba baccin ta tasha har wajen 10:30am Sannan ta farka, direct bathroom ta shiga tayi wankanta ta daura daya daga cikin towel din dake cikin bathroom ta fito, bakin window dake kallon falon da Salem yake taje ta yaye ta ganshi kwance har lokacin, muryan ta ta daga Sannan tace

"Good morning...." Gani tayi yayi motsi ta kara maimaitawa da karfi, bai amsa ba ya juya kwanciyan shi. Komawa tayi cikin dakin ta fara kalle2 wani kofan ta gani taje ta bude kaya ta gani birjit shiga tayi tana dubawa ko zata gan abinda zata Iya sawa, gani tayi duk English wears din are not her size, har ta hakura zata koma ta saka old wrapper dinta ta hangi brown men jallabiya kara duba shi tayi taga bashi da zurfi sosai kuma ko yayi mata tsawo ba sosai ba,daukan shi tayi ta zurmuka ta koma falo ta zauna tana tunanin inda zata samu pad.

Tawa kam sai 11 ta farka da kyar ta tashi don ba karamin ciwon kai take ba, wanka ta shiga ta fito ta maida kayan data cire ta koma ta kwanta, Salem ba tunda ameera tayi mashi magana bai koma bacci ba, kwanciyan shi kawai yayi for about 30 minutes Sannan ya mike ya shiga dakin da ameera take ko kallon gadon baiyi ba ya shaga bathroom yayi wanka ya bi ta kofan shiga closet ya shiga ya chanza kaya da kyar ya Iya saka kaya cos da hannu daya kawai yake amfani yana fitowa yayi hanyan falo kaman ance ya juya yaga ameera kwance cikin kayanshi

"Kan burouban nan!..." Ya fada yana komawa inda take, ameera rufe idanuwanta tayi kaman mai bacci, bayan ta ya tafkawa bugu

"Ubanwa yace ki sakamin kaya?.โ€ฆ" ya fada afusace, wurin da ya bugeta ta fara shafawa kaman zatayi kuka

"Before I close my eyes and open it...kije ki cire min kaya...in ba hakaba na lahira sai ya fiki jin dadi...idiot..." Yafada Sannan ya fita daga dakin.

To jamaa ga Salem ga Tawakaltu ga Aisha.. Now the fun is about to start

๐Ÿ’š๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค๐Ÿ’œ

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

ยฎzuwairat( ummu Maryam)

6โƒฃ5โƒฃ

*Habiba Habibty.. This whole page is yours Allah ya barni jone da ke, I love you wujiga wujiga* ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ *baki cikin mutanen da zasubika private su nemi friendship da kai daga baya su zageka suna tunanin bazaka saniba* *munafurci dodone kuma mai ita yakeci*

๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ _wayyo Allah naji hausa wella_

Yana fita kam ta koma tayi kwanciyan ta, cikin ranta sai tunanin dalilin dayasa Salem ya kawota nan take,

"Ko sakin zai bani?..." Ta tambayi kanta.

Salem na sauka down stairs yaga Mrs Samuel tana shirya dinning table da alaman breakfast is ready kasancewan in zata tafi da dare tana tafiya da keys don karta ta dashi daga bacci, gaisawa sukayi Sannan tace

"I was about calling you for breakfast.." Bai ce mata komai ba ya nufi kofan dakin tawa, knocking yayi yaji shuru, ya kara knocking still no response, kanshi ya dora bakin kofan ya fara cewa

"Love.. I know you can hear me...please ki bude min...I miss you..." Yafada ahankali, tawa kam tana jin shi amma bata da kuzarin bude mashi kofa, lankwace take kan praying mat har lokacin bata bar shessheka daga kukan datayiba, sai kyarma take, Salem cigaba da knocking yayi

"Please baby open.. I know you can hear me.." Ya fada Ahankali, yafi minti sha biyar yana knocking babu response, yasan rabonta da abinci tun safiyan jiya don Wanda yaci cikin jet ma bataci ba

"Just leave her alone... Stay away from her for now..." Yaji Mrs Samuel tana cewa,

"I can't...tana iya hurting kanta,..." Ya fada yana kara knocking,

"Then use spare key..." Ta kara fada mashi, sai lokacin ya tuna da yana da spare key. Upstairs ya tafi ya shiga bedroom, side locker ya bude ya dauki spare key, kallon ameera yayi

"Har yanzu baki cire min riga ba ko?...ya fada yana nunata da dan yatsa,

" bani da kayan da zan saka ta fada tana da Jan baya da alaman tana tsoro, kallon ta yayi for a moment,

"At least kina da tsoro..." Ya fada cikin ranshi, ya bar dakin.

Key yasa ya bude dakin da tawa take, ganin ta yayi kudundune, da sauri ya karasa wajenta

"Habibty.." Yafada yana dagata da hannun shi mai lafiya, gani yayi idanuwanta sunyi mugun kumburi, kuma jikinta rau kaman wuta, bakinta bushe

"Baby am sorry... Wallahi ko a lahira bazan kara boye maki komai ba... I know now that you hate lies...please let it go..." Yafada hawaye na taruwa idonshi, Mrs Samuel ya kwalawa kira bayan tazo ya fada mata ta kawo mashi cup of tea, babu wasting of time ta kawo very creamy tea,

"Please for the sake of Allah drink..." Yafada mata in a caring tune, Dan girgiza kai tayi

"I can't..." Ko kadan muryan ta bai fita, cos she can't hear her own voice, ko Salem da bai kalli bakinta ba bai sanin abinda take cewa

"You can please..." Ahankali ta mike zaune ta amshi tea din, hannun ta sai shaking yake, kadan tasha taji kaman zatayi amai ta ajiye shi, forcing dinta Salem ya karayi tasha babu laifi amma fa fuskanta Sam babu walwala. Ajiye cup din tayi ta mike tsaye ta taka ahankali kaman zata fadi ta hau gado ta kwanta, Salem binta yayi

"Please baby muje kici abinci..." Banza tayi dashi tayi kwanciyan ta,

"Baby...yarinyan tazo...please ki bari in kirata ta fada maki gaskiya..." Kai kawai ta girgiza mashi,

"No..tunda baki yarda daniba..ki bari ki saurareta..." Ya fada Sannan ya koma falo, da zuwa zaiyi ya kira ameera sai kuma ya tuna jallabiyanshi ce jikinta, Mrs Samuel ya kira ya fada mata yaje upstairs ya tambayi ameera kalan kayan da takeso, har ta fara hawa sai kuma ya kirata,

"Just buy anything formal..." Ya Bata umarni, Sannan ya dauko master card ya bata. Kan dinning yaje ya dan hada tea yasha Sannan ya koma dakin tawa, har tayi bacci kwantawa yayi gefen ta yana jiran dawowan Mrs Samuel, bayan kaman hour daya ta dawo da manyan Leda biyu, Salem ya umarceta data kaiwa ameera Sannan ta fada mata ta fito ta fito taci abinci.

Saman bene Mrs ta hau ta shiga bedroom tare dayin knocking, da sauri ameera ta mike zaune don tana tunanin Salem ne, wata baturiya ta gani ameera tace

"Tofah..." Kasan makoshinta, gaidata Mrs tayi tana mamakin irin kyawunta, nace Dan ma baki ganta tana ameerarta ba, bayan sun gaisa ta mikawa ameera ledojin ta kuma fada mata ta shirya breakfast is ready.

Tana fita ameera ta buda ledas din taga kayane masu kyau na nagarta kuma dukkan su fitted gown ne sai dai wasu zasu matseta da yawa, dakin da ta dauko kayan Salem a koma ta cire mashi keyanshi Sannan ta dauki wata purple gown ta saka ta rufe kanta da wata hula cikin kayan looking so nice ta fito ta nufi downstairs har lokacin bata bar tunanin ina matar shi take ba. Kan dinning ta zauna tayi serving kanta, tafara cin abinci.

Salem kam yana kwance gefen tawa sai kallon yanda take ajiyan zuciya yake, yana mamakin irin zuciyanta yanzu koda wasa bazai boye mata komaiba in har Allah yasa sunyi scaling through. Ameera ce ta fado mashi arai,

"Is high time we let bygone be bygone..." Ya fadawa kanshi ahankali yanda bazai tada tawa dake bacci ba. Kiss yayi mata agefen bakinta cikin bacci tadan dauke kanta Dan murmushi yayi ya bar dakin, yana fita waje ya hangi ameera zaune kan dinning table da alaman ta gama breakfast, Dan kura mata ido yayi for a few seconds

"Ayya wannan yarinyan ba aljana bace?..." Ya fada cikin ranshi, wurin ta ya nufa yaga ta sadda kanta kasa, yana zuwa ya zauna , da sauri ameera ta fara kokarin mikewa

"Sis I need to talk to you.." Yafada sounding so calm, juye2 ameera ta farayi don batasan ko daita yakeba, kuma bata tabajin muryan shi so cool ba

"Am talking to you.." Ya fada yana nuna ta da dan yatsa, sunkuyar da kanta kasa tayi gabanta na faduwa,

"Kilan sai yanzu yayi niyyan bani takardan.." Ta fada cikin ranta, gyara zama Salem yayi Sannan ya fara cewa

"An baki sakona?.." Ya tambayeta calmly, ahankali ta girgiza mashi kai,

"Ok..daman na riga na rubuta takardan sakinki na bada a baki...." Ya fada yana kallon fuskan ta don ganin reactions dinta, gani yayi fuskan ta look very calm,

"You are not surprised?.." Ya tambayeta, Ahankali ta girgiza mashi kai

"Why?..." Ya kara tambayan ta cikin sanyin murya, gabanta na faduwa ta fara cewa.

"Daman you promise to divorce me..." Tafada tana kokarin daidai ta muryan ta.

"Good.." Ya fada atakaice, shuru yayi for a moment, ameera kam komai tsaya mata yayi, ahankali Salem yacigaba dacewa

"Aisha..." Ya kirata, bata amsa ba ta daga kanta ta kalleshi, shima kallon ta yayi

"Nasan abinda kika yimin was very rude and disrespectful... Amma nima abinda na yi maki was in called for.. So am asking for your forgiveness... Ki yafemin..cos nobody is above mistake.,.." Ahankali ameera ta fara girgiza mashi kai hawaye na zubowa idonta, batamasan yana zuba ba saida taji dumin hawayan a fuskan ta

"No... Baka yimin komai ba..." Ta

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login