Showing 18001 words to 21000 words out of 145230 words
ameera ya tafi ,nan ya zaiyana mata yanda sukayi da Salem, dad bata gamaba tayi daka tsalle ta fada jikin dad dinta, shima rungumeta yayi.
Bayan dad yafita, kwantawa ameera tayi kan gado tana cewa
"Daman haka Allah yake biyawa bawanshi bukata? Daman duk abinda mutum ke in har kasa abun cikin ranka zaka samu?.. Imagine me as Salem wife , imagine me as surukin former President... Woowww" tafada da karfi tana tsalle kan gado, wayanta ta dauka tafara dailing number zeenat.
โค๐๐๐๐
Bangaren Salem kam hankalishi kwance don yanzu kwana uku da maganan shi da dad ameera, gini kam ana chan anayinta abinka da mai naira har an gama fence din kuma da aka turowa Salem hoton cewa yayi yayi kadan akara tsawon fence din, wani irin dogon fence mai kama da tower akayi sannan aka fara ginin ciki, shima har sunkai tsakiya aka turawa Salem hoton, shima cewa yayi dakunan sunyi girma a ragesu.
Yau yana kwance murmushi ne kwance a fuskanshi.. Kona meye oho, wayan shi ya dauka yasa Abdul ya kira Makeup artist dinshi.
Around 5pm suka bar gidan, suna zuwa daidai inda ameera ta mareshi ya fara kallon wurin kawai sai ya hangi kaman yarinyan data siya mashi cotton wool lokacin da yake nasal bleeding, kallon Abdul yayi kafin yace
"Alh wancan kaman yarinyan data siyamin auduga ko..." Shima Abdul kallon wurin yayi
"Yes sir..itace kuma kaman abun hawa take jira...kilan ta tashi daga wurin aiki" Salem rage gudun abun hwanshi yayi yana cewa
"Wane aiki take?" Abdul murmushi yayi
"Sir bakaji sanda madam din datakewa aiki tana zaginta wai ta kashe mata kudi har da cewa saita biyata..." Shuru Salem yayi kaman mai tunanin wani abu sannan yace
"Sam banjiba ai yarinyan nan tana marina wuta ya daike min Amman naga sanda ta sayi auduga ta baka...Amman baka gayamin aikn datake ba" suna zuwa daidai inda take Abdul nacewa
"Inajin abinci suke saidawa don naji matan nacewa tawuce ta bawa mutane abinci" Salem tsaida taxi yayi inda take, tawa na ganin taxi ya tsaya sai tadanyi baya kadan, Salem dan fiddo kanshi yayi ita kuma ta kura mashi ido tana tunanin ina nasan wannan mutum, Salem zai bude baki yayi magana ta fara cewa
"Lah...Ashe kaine..ina wuni"
"Lafia lau...kinyi tunanin na mutune?" Dan murmushi tayi Wanda ya bayyana one side dimple dinta
"Aa..kawai banyi tunanin kai bane"
"To naji..zo in baki lift"
"Aa nagode..." Kura mata ido yayi for a moment kafin yace
"I insist.. Ko kina tsoron kar..." Dan daria tayi ya dan saci kallon hakoranta
"Meye na tsoro.. Kawai dai nagode.." Shima Salem Dan daria yayi itama tawa tadan kalleshi tayi saurin kauda kanta
"Please ki shigo in ajiyeki" kallon Abdul tayi kafin tace
"wannan passenger da ka dauko fa..kar mu shiga hakkinshi..." Abdul murmushi yayi
"Kar ki damu ni abokinshi ne..." Tawa Dan tsayawa ta yi kaman batason shiga kuma da ka ganta da akwai Dan alaman tsoro tare daita, kara daga kai tayi ta kallesu suka hada ido da Salem, cikin ranshi cewa yayi
"Wannan yarinyan da akwai manyan idanuwa kaman na mage" ahankali ta bude bayan motan tashiga , tana shiga ta dan kwantar da kanta bayan seat da alaman gajiye take, Salem juyawa yayi ya kalleta
"Hajiya ina zaa kaiki?"
"Oh sorry...tukuntawa zaa kaini"
"Babu nisa ma" inji Abdul, Salem fara tuki yayi, yana cikin tafiya yadan saci kallon ta ta mirror yaga sai lumshe ido take ahankali, cigaba da kallonta yayi har ya mance da tuki yake, saida ya kusa bige wani sannan yadawo hankalinshi, bai dade ba yakara kallon ta wannan karin itama ta daga kanta sukayi ido hudu dashi, murmushi yasakar mata kafin yace
"Nagode da taimakonki fa..."
"Haba ba komai...Amman kabani mamaki..." Daga kanshi yayi ya kalleta
"Da nayi me?" Cikin irin jin haushin nan tace
"Da baka rama marin datayi makaba...mazan hausawa da akwai hakuri wallahi da mazan yarenmune da yarinyan nan bata kara marin mace yaruwanta balle namiji" Salem Dan murmushi yayi yana tunanin
"Bakisan abinda ke faruwa don ina tabbatar maki when am done with her ko dabba bazata iya tabawaba balle mutum" dan murmushi yayi
"To ya zanyi tunda ni talaka ne...wai ke wace yaraece?" Ya tambayeta, Ahankali tace
"Yoruba" ido Salem ya kwalo don sam bata kama da yare
"Kambu " yace cikin ranshi sannan yace
"Yoruba? Amman meyasa kike Hausa kaman bahaushiya?"
"Nan aka haifeni"
"Wow..ya ake cewa kina da kyau da yarenku?" Dan daria tayi shima Abdul yayi
"Ni ban iyaba Amman inaji"
"Baki iyaba kwata2? " Dan girgiza kanta tayi sannan tace
"Naiya few words" Dan daria yayi sanda Abdul ya nuna mashi hanyan dazasu bi, saida yabi hanyan sannan yacigaba dacewa
"To ya ake cewa my friend da yarenku?" Ahankali tace
"Ore mi" dan daria yayi kafin yace.
" zaki zama oro mi?" Cikin daria tace
"Ba oro mi naceba...I said ore mi" dukkansu daria sukayi kaman sun wani dade na sanin nuna
"To naji..zaki zama ore mi?" Shuru tayi kaman bada ita yakeba.
Saida ya kara cewa
"Baki bani amsaba?" Kallon shi tayi ta mirror suka hada ido tayi murmushi tare da kauda kanta
"Cewa nayi will you be my ore mi" ahankali tace
"You are funny.. Ka taba ganin inda mace da namiji sukayi abota?"
"Eh mana in kuma babu sai mu zama na farko" tawa shuru tayi bAtace komaiba ba salem ya sake cewa
"So zaki zama ore mi?" Batace komaiba har suka zo gidansu,
"Nan zan sauka" tace mashi, tsayawa yayi ta bude ta sauka sannan tace
"Sakallahu akhaairan..." Murmushi yayi
"Ameen nagode" juyawa tayi ta fara tafiya, Salem yabi bayan ta da kall, cikin ranshi yana
"See hips" Salem da akwai san hips, binta yayi da kallo har saida ta kusa shiga gida sannan yace
"Ore mi..baki gayamin sunan kina?" Ahankali tawa tace
"Tawakaltu"
"Lovely name for a beautiful owner" tawa daria tayi tare da dan girgiza kanta sannan ta shiga gida.
Tun waje Salem kejinmuryan yara suna anty tawa oyoyo. Salem kallon yanayin unguwan yayi sannan yace
"Alhamdulillah" kallon Abdul yayi sanda yake juyawa da motan yace
"Alh yau nasamu mace ta farko da tayi min daria" shima Abdul cewa
"Gaskiya kam..ko mun samu amarya?" Hararan Abdul yayi
"Kanason first love taci ubana kenan" Abdul murmushi yayi
"Sir ai bakasan ikon Allah ba" Dan daga kai Salem yayi kafin yace
"Gaskiya kam Amman kada Allah yabamu abinda yafi karfinmu"
"Ameen" Abdul ya amsa mashi, wuri ya samu yayi parking
"Alh kadawo nan ni nagaji da wannan driving din" ba musu Abdul yafita ya barwa Salem wurin bude Salem ya koma driver seat suka bar wajen, dan yawo suka danyi duk wacce ta tsaida su sai Salem yace kar su tsaya yana cewa
"Alh mu wuce kawai banason shan zagi da yamman nan.
Bayan kwana uku Salem ya stinci kanshi da tunanin tawa ,duk yanda yake kokarin kaudata daga cikin ranshi ya kasa , kwance yake tunanin duniya ya isheshi
" ya Allah koda nafito Neman mata ban fito da niyyan Neman wata kabila ba...why do I want to see her again... Why is my heart always remembering her?...ya rabbi choose the right path for all Muslims " aduan dayake kenan cikin ranshi
"Tawakaltu... Trust in Allah.." Juya kwaciyanshi yayi tare da daukan wayanshi, Khalid yakira, bayan sun gaisa Salem yafara cewa
"Guy wallahi am falling... " da sauri Khalid yace
"From were" daria Salem yayi sannan yace
"In love.. And I think it's love at first sights" ihu Khalid yafara yi yana cewa
"Yeyyy..mission accomplish.. Sai kadawo gida musha shagali..." Dariya Salem yayi, Khalid yakara cewa
"Friend gayamin ya take" ahankali Salem yafara cewa
"Guy bakace, tana da dan tsawo Amman ba sosai ba, sannan tana manyan idanuwa kaman na mage..." Khalid yayi saurin cewa
"Kaman naka kenan" daria Salem yayi sannan yacigaba dacewa
"Tana da dimple sannan ga round face.. In short guy kaman kanwar rihanna" daria Khalid yayi sosai, Salem bai saurareshiba yacigaba dacewa
"Wallahi guy she has the perfect ass..." Wani irin ihu Khalid yayi
"Slim ayya ita kake so...hope ba ass din kawai ya burgeka ba?" Da sauri Salem yace
"Wallahi dukkansu nakeso..dukda hijjab dinta bai bani daman ganin boobs daita ba Amman nasan da akwaisu..wallahi guy the lady is endoured.." Cikin daria Khalid yace
"Wannan kwatancen daka bada bansan yarinyan kake so ko jikinta kakesoba..." Da sauri Salem yace
"wallahi guy I have never wanted something so bad...inason yarinyan nan... I just meet her three days back but am missing her badly"
"Naji...gayamin..yar wacece a garin..." Ahankali Salem yace
"Gaskiya inaji ba yar kowa bace..asalima she's not an Hausa..." Da sauri Khalid yace
"Wace yarece"
"Yoruba" wani irin mugun ashar Khalid ya saki sannan yace
"Shike nan ansamaka wani abu aruwa kasha"
๐โค๐๐๐
ZAKISAN KONI WAYE
๐๐๐๐โค
ยฎzuwairat(ummu maryam)
1โฃ6โฃ
Salem lumshe idanuwa yayi, daman yasan hakan zai faru, Khalid yacigaba dacewa
"Friend am disappointed in you...ace duk Matan duniya ka rasa wacce kakeso sai wata Yoruba?...daman muggan masu asirine, kilan sun baka wani abukaci..."
"Please stop screaming... Kar ka kashe min kunne dalla...don na gaya maka damuwata sai ka tsaya yimin maganan banza?...get off my phone!!!" Salem ya fada cikin fada. Da saurin Khalid yace
"It's not like that... Amman Salem ina kai Fulani ina Yoruba?..."
"Please...ka bar magana kaman jahili mana...Yoruba ba mutum bace..ko matanmu finsu sukayi....wallahi tunda nafito she's the first person da bata yimin rashin mutunciba..."
"Haba slim saboda yarinyan kake kirana jahili?...gaskiya sun kamaka" afusace Salem yace
"Wallahi Khalid ka kara cemin sun kamani zamu bata da kai..wallahi ko maganan ban gaya mataba...kawai nagaya maka don Neman shawaran ka Amman you getting me upset" Khalid kwantar da murya yayi
"Slim am sorry... Amman ka duba wannan lamarin..kana ganin Umma zata yarda?..gaskiya ni ashawarata kar ka gaya mata..." Shima Salem ahankali yace
"Am trying not to say anything.. Amman cikin kwana uku nan Kaman shekara uku..." Ahankali Khalid yace
"Yanzu Salem yanda ka tsani tara mata shine kake shirin yin mata biyu..."
"Kaman ya mata biyu?" Salem ya tambayeshi, cikin zolaya Khalid yace
"Ga wata chan zaka aura kuma gashi har yanzu baka daina neman Matan aureba.." Dan daria Salem yayi
"Ai ita wancan ba aurenta zanyi dan muyi zaman aureba..kaima kasan dalilin dayasa zan aureta...dana gama daita zan maidata wurin ubanta..."
"Karfa daga karshe muji chanjin labari..."
"Kaima kasan ba haka nakeba..I always keep my word...yanzu please best meye abinyi.. Wallahi I think I love that gal" Dan daria Khalid yayi
"Hmmm..ni dai yanzu ban abun cewaba sai ince Allah ya zaba mana abinda ya fi alkhairi" haka suka Dan taba hira kafin suyi sallama.
Salem gyara kwanciyanshi yayi yacigaba da tunani, shi kanshi yasan da kyar ummanshi zata amince da abinda ke faruwa.
๐๐๐๐โค
Abangaren su ameera kam babanta yayi mata order kaya na gani na fada, kuma yar uwan dad mai suna anty safiya ta dauko nauyin gyara ameera don mom kam ko kallo basu ishetaba, da sai gayawa mutane yake zai aurar da yarshi da ance gawa sai yace ga dan tsohon shugaban kasa, da an tambayeshi yaucene bikin sai sai yace jira yake su bashi rana, ko tunanin rashin aikinshi baya yi.
โค๐๐๐๐
Tawa kam tun ranar da Salem ya ajiye ta bata kara tunashi ba sai yau da take kwance gaman maminta tanayi mata ta tanayi mata tausa kasancewan kullum mami sai tayi mata tausa in dare yayi saboda yawan gajiya, zumbur ta mike zaune kaman wacce ta tuna abu ta jiya wajen mami tafara cewa
"Mami kin san wannan mutumin da nake baki labarin shi kwana kin baya?" Cikin magana irin ta wayanda basu jin dadi sosai mami tace
"Wane mutum kenan" da sauri tawa tace
"Wannan mutum da wata yarinya ta Mara..."
"Eh na tunashi..me ya sameshi kuma?" "Ba komai..jekaranjiya na ganshi har ya bani lift..."
"Meye lift?" Mami ta tambayeta
"Ya maido gida kyauta..." Baki mami ta bude tana
"Ah..ah..ah..toyin... Kina hawan motan Wanda baki Sani bako?..." Da sauri tawa tace
"Mami ban taba hawan motan kowaba...shima rokona yayi..." Cikin fada mami yacigaba dacewa
"Rokonki din banza...salan a yanke maki kai?...in badan yaran yanzu Baku da tsoro ba ina ke ina hawan motan Wanda baki saniba..."
"Mami..yi hakuri...bazan karaba.."
"Ke kullum cikin bada hakuri kike..." Tafada cikin fada sannan ta sassauta murya tafara cewa
"Omomi...bawai ina hanaki samun sauki bane..Amman irin abubuwan dake faruwa yanzu ya kamata ko wacce yarinya ta guji mutanen da bata saniba.."
"Mami sorry..."/
" naji..kar ki kara" kai Tawa ta gyadawa mami
"Kwanta in cigaba dayi maki tausan" ba musu tawa ta kwanta tayi rubda ciki, acikin ranta tana tunanin
"Da ganin wannan mutumin ba mugubane..wai oromi...shi dole sai yayi yarenmu" mami sai ganin tawa tayi tadan yi murmushi
"Kini?" Mami ta tambayeta, girgiza kanta tayi sannan tace
"Ba komai"
โค๐๐๐๐
Salem kam yana zaune yana video call da agent dinshi yana nuna mashi yanda gidan yake, daya kalli yanayin gidan sai yayi murmushi don babu abinda yakeyi mashi dadi irin ya tuna ameera zai kai gidan.
"Gaskiya kunyi kokari tunda with in sati daya har kunyi rufi"
"Yes sir...Amman inason in tambayeka" agent din yafada
"Am listening" Salem ya amsa mashi sannan agent din yacigaba dacewa
"Sir a toilet din water system zaa saka? Ko ayishi pit toilet"
"Wane irin water system.. Kawai pit...sannan tunda an kusa gamawa inason..
Forget kawai" yafada kaman Wanda ya tuna wani abu.
Yanzu rabonshi da ganin tawa sati daya kuma shikadai yasan irin kokarin da yake, don so kawai yake ya kara sakata ido koda saudaya ne, kullum in yakira Khalid babu abinda yake kara gaya mashi illah kar ya kuskura ya cemata komai, kawai with time zai mance ta Amman ya lura hakan ba mai yuwa bane
Around 4pm aka chanza mashi fuska ya fita shi kadai, don restaurant din da tawa ke aiki kusa yake da gidan shi.
Bayan ya isawurin yayi parking wani wuri sai ya taka da kafa zuwa restaurant din. Daga nesa ya hangi tawa tana amsan kudi daga hannun wani mutum, hannu tasa cikin apron din dake jikin ta ta fiddo chanji tabawa mutumin tare da Dan runtsunawa. Kallon tayi, sanye take cikin lace Wanda kudin ta bazaifi 3k ba sai dan hijjab Wanda bai wuce kuguntaba,batayiba kwalliyaba Amman fuskanta babu laifi, Dan kara matsawa yayi kusa da wurin , kallon yanda bakinta ke magana ahankali yayi da alaman waka take ji, ahankali ya zo kusa daita, daga kan datayi sai sukayi ido hudu, murmushi ta sakar mashi shima ya mayar mata martani, da sauri ta mike tare da saka hannunta cikin hijjab dinta ta fiddo earpiece sannan tace
"Lah..ina wuni" ta gaidashi
"Oremi ya kike?" Dan daria tayi sannan tace
"Baka mance ba kenan.." Shima daria yayi
"Ya zaayi in mance"
"Inawuni" takara kara cewa wannan Karin har da dan runtsunawa
"Lafiya lau..ya aiki?"
"Alhamdulillah ..zauna " tafada tana nuna mashi inda ta tashi, cikin zolaya yace
"In zauna?..in mai wurin tazo ta tadani fa?" Cikin daria tace
"Sha kuruminka..batanan tayi tafiya" wurin data tashi ya zauna, tawa ta ajiye Wayanta kusa dashi ta shiga cikin inda suke ajiye abincinsu na sayarwa, Salem kallon wayan yayi yaga techno ce Wanda ko 1k bazai iya sayanta ba, earpiece din yadan dauka ya saka cikin kunneshi yaji anacewa
"Dani dake mun dace" da sauri yacire earpiece din daga kunnenshi don kara wayan zata Iya kashe mashi kunne, baijin wakan hausa Amman wakan tayi mashi dadi,
"Dani dake mun dace kam" ya maimaita cikin ranshi, bai ankaraba yaji tace
"Malam bisimillah" sai lokacin ya dawo hankalinshi, daga kai yayi sukayi ido hudu sai yaji tsigan jikinshi na tashi at the same time gabanshi ya fadi, itama tawa Dan daga kirjinta tayi, kuma tayi saurin dauke hannunta, sai yayi karfin halin cewa
"Oremi sunana ba Malam ba..sunana..." Ahankali tace
"Sorry.. Meye sunan ka?" Dan shuru yayi yana tunanin yayi mata karyan sunan shi sai kuma yayi tunanin kar karyan yayi yawa
"Sunana Salem"
"Oga sa..."
"Meye oga kuma...gaskiya banason sunan."
"To sorry...sir Salem" gabanshi faruwa yayi don tunanin ko tasan shi waye yayi, don yasan dukkan maaikatanshi haka suke ce mashi
"Meye kuma sir Salem?" Yayi karfIn halin cemata, Dan murmushi tayi kafin tace
"Ai bazan iya kiran sunanka direct ba.."
"Nima ki kirani da oremi mana" zatayi magana yace
"Please"
"OK..OK..OK...naji oremi kazo kaci abinci" ido Salem ya gwalo
"Ai ba abinci nazo ciba..bani da ko sisi" Dan daria tayi
"Kar ka damu zan saka kudin da kudina..so please kazo kaci" kallon environment din yayi, tunda aka haifeshi bai taba cin abinci a public place ba sannan yasan ko ruwa yayi gigin sha sai ya amayar da dukkan abinci dayaci don shi asalima kyaman wajen yake
"Na koshi" Marairacewa tayi
"Please fa kaci..kaga last time ka rokeni nashiga taxi dinka to nima ina rokonka kaci abinci" shidai yasan yarinya nan is perfect for him
"In na gaya mik gaskiya zaki yarda?" Kai ta daga mashi alaman eh sannan yace
"Azumi nake" Dan hararan zolaya tayi mashi sannan tace
"To shikenan" abinci ta maida sannan ta dawo ta dauki kujera ta zauna Dan nesa dashi, kallonta yayi sannan yace
"Oremi wani taimako nakeso kiyi min"
"Ok...oremi"
"Ance nan Kano da akwai saukin kaya shine nakeson ki taimakamin ki rakani kasuwa inason zan siyawa kanwata kayan boarding school" shuru tawa tayi kaman mai yin tunani sannan tace
"Ok...Amman zan gayawa mami in ta yarda zan rakaka"
G โค๐๐๐๐
ZAKISAN KONI WAYE
๐๐๐๐โค
ยฎzuwairat(ummu maryam)
1โฃ7โฃ
Kallon ta yayi for a moment sannan yace
"To in mami ta kifa?"
"Shikenan.. Bazan rakaka ba"
"Allah yasa ta yarda"
"Ameen" shuru yayi yana tunanin abinda zai ce mata don bayan son tafiya yanzu shikuma ba gwanin fira da mata bane,
"To in mami ta yarda nan zanzo