Showing 36001 words to 39000 words out of 145230 words
telling you how I feel... I still feel your body in my arm.." Shuru yayi itama tawa shuru tayi ta rufe idanuwa tana sauraron shi, Salem kwantawa yayi kan dogon kujera yana samun desires
"Habibty I love you..in ni my kudine ranar dana aureki sai na bawa mutane hamsin kujeran Mecca... Sai nabawa talakawa hamsin 2 million each.." Ahankali tawa tace
"Please stop it..."
"Why..I want to say it out loud"
"But you don't have such money..besides iyayenmu bazasu yardaba.." Da sauri Salem yace
"Kina nufin mami bazata yarda in aurekiba?"
"Gaskiya bazata yarda yarta daya ta bawa bahauce ba..gani take wata rana yana iya juya mata baya..."
"Haba...habibty in mami bata amince ba ke baki cewa saini?..don ni babu Wanda yaisa hanani zabina.."
"Koda iyayenka sunce basu so?"
"Eh mana?"
"Gaskiya hakan babu kyau..zai zama disrespect.. Ni in mami batason abu ban iyayi.." Sai duk jikin Salem yayi sanyi
"Nasan mami zata Iya kine Dan bani da naira..."
"Ohoo please stop talking about money.. Besides money is not every thing... Sannan mami is not a money person... Don in kasan waye baban mami zakayi mamaki..."
"Tell me more" yafada yana jin dadi hiran
"Grandpa dina shine oba na garin su.." Da sauri Salem yace
"You mean grandpa dinki sarki ne?"
"Yes sir" ido Salem ya kwalo
"What happens?" Ji yayi tawa ta kara kwantar da murya da alaman batason wani yaji labarin dazata bashi
"Lokaci da mami take budurwa ta kamu da son bami, kuma bami dan talakawa ne..sai grandpa yayi2 ya rabasu Amman mami taki tace saishi..sai grandpa yace ta zaba tsakanin shi da bami daita zabi bami sai grandpa yace ta tafi kar ta kara dawowa.."
"Hmmm..ashe princess ceke? Shiyasa kike da nobility.. Wane garine?" Don babu sarakunan dabai saniba
"Bazan fada makaba..Amman he's a very powerful king in the west"
"Meyasa mami bata komaba?"
"Nima ban saniba kuma the annoying part shine tunda bami ya rasu basu nemanmu..."ahankali Salem yace
" karki damu zasu nemeki..yanzu habibty kinsan mami tabi so shine ke kike cewa sai abinda mami tace..."
"Ina amfani hakan?..kawai mutum yabi maganan iyayenshi yafi..."
"To naji..nasan when we get to that bridge we cross insha Allah.. Yanzu gayamin meye abinda zaki fiso a wurin namiji dazaki aura?" Tawa shuru tayi don batasan abinda zatace ba
"Please love am listening.." Ahankali tafara cewa
"Inason mutumin my addini, mai tsoron Allah, respect, intelligent, truth worthy,..I think shikenan."
"Baki fada ko kinason mai jiki ko mara jiki ba sannan kyau...fari ko baki..sannan dogo ko gajere?" Tawa daria tayi sosai
"Gaskiya ban son mai jiki, kyau yana gushewa, inason fari Amman kilan bazan samuba tunda ni bakace sannan banason dogon over ko gajere over" Salem daria yayi yana kallon hannuwanshi da suke kal kaman jini zasu fito
"Wai bazata samuba tunda ita bakace...anyway ni ki tambayeni abinda nakeso jikin mace" tawa shuru tayi bata tambayeshi ba,
"Am waiting.." Kin tambayan shi tayi don tasan yana iya baro magana babu ruwanshi,
"To bari in fada maki tunda baki tambayan ta, na daya inason figure 8 ..mai up and down..." Daria tawa ta farayi sannan ta katse wayan ta batare data ji karashen abinda zai ceba, shima mikewa yayi yana daria, kallon joystick dinshi dake tsaye yayi sannan yace
"Am disappointed in you.." Yafada tare da kaiwa wurin dan duka, nan take ya saki Dan kara yana rike wurin har lokacin bai bar daria ba.
Haka ya kwanta yana juye2 duk desire na damunshi, nikam nace ango kaje wajen amarya tabaka hakkinka mana.. Wani irin dirty look ya watsa min sannan ya mike ya balli magani daga first aid box yasha sannan ya samu bacci.
Amaryakam haka ta kwana rakube jikin window saboda hasken dake reflecting wajen, batayi bacci kirkiba Ga yunwa ga tsoro sannan ga son sex.
Salem na dawowa daga masjid ya shiga swimming pool din bathroom dinshi yayi swimming har kusan hour daya sannan yayi wankan sabulu ya fito, shiryawa yayi cikin Gucci suit sannan ya fesa turaruka masu dauke hankali, saida ya tsaya yayi selfie ya saka Instagram sannan ya fito, wasu BMW MRI guda uku ne tsaye sakar gidan suna jiranshi, yana zuwa ya shiga cikin daya majeed yashiga cikin Wanda yashiga daga gaba sai driver, dayan Abdul da Jibril sai na karshen isah da Mahmud , Salem kallon Majed yayi
"Alh kaje sasshen baki ka fiddo yarinyan dake gurin" Abdul fita yayi ya tafi, Abdul kallon shi yayi tacikin mirror
"Allah ya kiyayeni..kaje abaka na karyawa...saidai majed bashi da mutunci" yafada cikin ranshi.
Ameera tashi tayi tashiga bathroom sannan ta fito falo adaidai lokacin da majed ya shiga falon
"Kan buro uban nan... Kai wane irin kafirine baka sallama?... Ku jimin jakki..$" bata karasaba ya karaso inda take ya rike hannunta yayi waje daita don shi baisan Matan oga bane sannan koya Sani umarnin oganshi yake bi,ameera salati ta fara tana burma mashi zagi, suna fitowa waje Allah ya bata saa kwace hannunta aikam bata bata lokaci ba ta daukeshi da mari, shima tabkeken hannunshi ya daga ya sharara mata mari, nan take wuta ya dauke mata ,Salem na zaune cikin mota yana kallon abinda ke faruwa, daria ya farayi, shikam Abdul dake cikin dayan motan cewa yake
"Ai wannan ba irina bane mai daukan raini"
Majed ya dinga cewa
"You dey cry?..you dey mad?..who be your father for Niger?...who born you?..." Salem Dan fitowa waje yayi sannan yace
"Alh majeed drag her to that taxi" yana kaiwa nan ya koma cikin mota, itakam ameera har lokacin hannunta na kan cheeks dinta, don tunda take wannan ne karo na biyu da babban mutum ya mareta, nafarko Salem yanzu kuma wannan, haka yashaida mata daakwai matsala.
Ingizata majeed yafara yi, batayi musu ba tafara tafiya Amman dukda haka bai bar ingizata ba, kaman prisoner haka ta koma, tana zuwa wurin motan bata tsaya aka bude mata ba ta bude ta shiga tana kuka
"Dakin tsaya an bude maki" inji Abdul dakeji kaman yau salla, majed har ya taho Salem ya kalleshi yace
"Ka biyomu da wannan shaidaniyan yarinyan"
"Yes sir"
๐โค๐๐๐
ZAKISAN KONI WAYE
๐๐๐๐โค
ยฎzuwairat(ummu maryam)
2โฃ7โฃ
Suna tafiya Salem na sauraon wakan breathless na ward Shayne, magagganun Umma sai dawo mashi suke
_"Indai nice saidai kar kayi aure har ka mutu Amman bazaka kawomin Yoruba ta haifamani jikokiba"_ kauda kanshi gefe yayi tare da lumshe idanuwa, sannan maganan tawa ya faraji cikin kunnenshi shi
_"Yin haka disrespect ne..nidai in mami batason abu ban yi.."_ kara maida kanshi yayi dayan gefen
"Kardai ashe bazan auri tawaba..." Da sauri ya kauda wannan tunanin tare dacewa
"No" har saida driver yace
"Sir ka yimin magana ne?"
"Kaji sunanka abakina ne?" Shima ya amsa mashi.
Sunfi hour daya suna tafiya, kuma har lokacin ameera bata bar kuka ba, majed daya juyo sai ya daka mata tsawa sai tayi shuru don wani irin tsoron shi takeji don ko kamanninshi ka kalla yaisa ya baka tsoro don yafi dukkan guard din Salem tsawo da kwari.
Suna zuwa gidan sukayi parking, aka budewa Salem kofa ya fito yana gyara button din gaban suit dinshi, abakin gate din wasu guys ne guda biyu suna gadin wurin, suna ganinshi suka mike tare da bude gate din, daganin katangan gidan mai tsawo kana iya tunanin da akwai katon gidan acikin ta, Amman da an bude zaka ga tamkar kango don ginin ciki bai da tsawo sosai, har lokacin ameera bata fito daga cikin motan ba, Salem kallon majed yayi.
"Bring her out" yafadawa majed, ameera tana ganin yayiwa majed magana tayi saurin fitowa tana sauri ta nufi inda Salem ke tsaye Dan har ta mutu bazata yi marmarin wannan mutumin ya kara tabata ba, Salem na ganin ta taho ya Yajuya ya shiga ciki, da sauri tabi bayanshi, kallon gidan tayi tana tunanin kilan wani abu zaiyi sannan su wuce, saida suka shiga Dan falon mai dauke da ledan da labule kawai sannan ya juya, gani yayi ameera tanayiwa wurin disgusting look, tan ganin ya juyo tayi saurin chanza yanayin fuskanta,
"Daman baki taba janzawa cos it runs in your blood" yafa cikin ranshi sannan ya hada giran sama Dana kasa yace
"Welcome home.." Ido ameera tazaro sabbin hawaye na zubowa daga idonta
"Duk abubuwan dazaki bukata da akwai shi cikin gidan nan..." Bai karasaba tayi kneeling tare da rike takalmin shi
"Kinsan kina gigin tabani sai na balli buroubanki...stop touching me with you filthy hands" da sauri ta cire hannunta ta Amman tana nan durkushe
"Dan Allah.. Dan annabi...nasan nayi laifi..Amman wannan hukuncin yayi min yawa...wallahi I will not survive here...dan Allah ka yamemin ka maidani gidanmu..." Kuka yaci karfinta tadan goge hawayenta ta cigaba dacewa
"Please I promise to be a good person.." Salem tsaya kallonta yayi Amman ko kadan babu alaman tausayi a zuciyanshi ,ameera ta cigaba dacewa
"Please forgive me..."
"Ke please don't waste my time.. Yanzu kishiga kitchen..." Ya nuna mata dan akurkin da aka gina in the name of kitchen sannan yacigaba dacewa
"Ki dafawa akalla almajirai ashirin abinci.. Kuma na baki hour daya..in ba haka ba in hada ki da guards dina.." Yana kaiwa nan ya juya zai tafi..da sauri ta kara rike kafanshi
"Wallahi ban iya girkiba...ban taba girkiba...wayyo na shiga uku..nidai ka maidani gidanmu.." Ta fada tana kuka kaman ranta zai fita don har juwa take gani don yunwa.
"Baki iya girkiba kike kiran kanki mace?..dalla ki sakarmin kafa kar itakaki...."
"Wallahi ka kashe ni...Amman ban zama wannan gidan"
"Haka kikace?..then wait...majed" ya kira da karfi, ameera na ganin majed tayi saurin sakin kafanshi, daria Salem yayi hannunshi cikin aljihunshi
"Bakince kina son mutuwaba...da kin bari kin ga aiki da cikawa...kuma wallahi na kashe banza...now ki shiga kitchen before I count three.." Tana shesheka tafara cewa
"Please zanyi..Amman Dan Allah.. Kubani abinci.. Wallahi rabona da abinci tun shekarajiya..." Daria Salem yayi
"In kin dafa kici" yajuya yafara tafiya, cikin kuka sosai tace
"I beg you in the name of Allah..ka bani abinci ...please am dying" tabe baki yayi ya fice daga wurin.
Wurin masu gadin gate yaje
"Kun ga wancan ta cikin gidan?"
"Yes sir" sukace da sauri, Salem ya cigaba dacewa
"On no account zaku barta ta fita, sannan ban yarda kuyi magana daitaba..karta aikeku..I repeat ban yarda ta fita ba...do I make myself clear?"
"Yes sir"
"Good.." Cikin mota ya shiga ya dauko 1k yabawa daya daga cikin masu gadin yace
"Wane irin abinci ake saidawa nan wurin?"
"Sir da akwai Dan wake..awara, taliya da mai da yaji, soyayyen dankalin Hausa. ." bai karasaba Salem ya katseshi dacewa
"What ever...ka saya mata talaiya na 200.."
"OK..sir" Salem shiga mota yayi escort dinshi suka shiga suka bar wajen.
Ameera kaman ta hadiyi zuciya ta mutu , yanzu tasan Salem uwarta zaici don da tayi tunanin abin wasa ne kuma gani take ko sati bazata yi cikin gidan nan da raiba.
๐๐๐โค๐๐
Umma Salem ce zaune Sam fuskanta babu walwala, daka ganta kasan babu farin cikin tattare da itako kadan, yau rabon da ranta ya kirata tun ranar Friday, gashi yau lahadi.
"Wannan shine kashi na farko da dana ya iya kwana biyu bai ji murya ta ba...all because of a girl...a Yoruba for that matter... Dole in san ko wacce irin yarinya ce..sannan dole ta fadamin da bakin ta" tafada tana daukan wayan ta, wata number da aka rubuta hjy ummi kano tayi dialing, few seconds later akayi picking, daga chan bangaren akace
"Hajiya ta ta kaina ya kike ya kwana biyu?" Ahankali Umma tace
"Alhamdulillah..ya yan gidan.."
"Lafiya lau suke...ranan asabar akayi wannan auren..wallahi duk garin sunyi tunanin Salem ne..."
"Manta da wannan ba shi bane Amman ina cikin matsala..." Da saurin matan tace
"Hajiya wane matsala kuma?" Ajiyan zuciya Umma tayi sannan tafara cewa
"Hajiya ummi narasa Dana..."
"Subhanallahi! Hajiya meke faruwa ne?"
"Ranar Friday Salem yazo nan da maganan auren wata beyerebiya dan nace Aa shine Salem yajuya min baya...can you imagine that?...Salem da bai iya hour uku baiji murya taba yayi kwana biyu bai nemeniba..."
"Hajiya beyerebiya fa kika ce.. Ai an gama dashi...ai babu masu asiri kamansu...Amman Salem baiyiba..ga yara nan birjit cikin family sai ya kwaso wani abi waishi Yoruba?.. Gaskiya da akwai matsala babba...yanzu meye abinyi?" Shuru Umma tayi na Dan lokaci sannan ta fara cewa
"Shine dalilin dayasa na kiraki..inasin ki sa guys su dauko min yarinyan.. Nan Kano take..."
"Yanzu Hajiya har sai an dauko maki ita? Kawai agama ...."
"Please stop... Ni bawani abu zanyi mataba..kawai zan roketane ta kunce asirin datayiwa Dana..kuma kar ki bari a tabata..kawai akawomin ita" ahankali Matan tace.
"Yasunan ta"
"Naji yace Tawakaltu..."
"Kin San sunan unguwarsu?"
"No..Amman shi Salem yana Kano...so guys din subishi zaiyi leading dinsu wajen ta."
"To madallah..zakiji daga gareni zuwa gobe" tafada ranta baisoba ..don ita kawai a fidda tawa daga way.
Umma wata kawanta tasake kira ta gaya mata abinda ke faruwa sannan ta fada mata tasa guys su dinga duba shiga da fitan Salem in case zaizo da wata yarinya. Hmmm masu kudi ko kadan wasu basu san kaddaraba.
๐๐โค๐๐
Kan hanya Salem wani dake south Africa ya gaya mashi ya turo mashi number shugaban mtn.
Suna isagida number na shigowa,
Kiran mutumin yayi suka gaisa sannan Salem yace.
"I need a help?"
"Anything for big guys like you" Salem tabe baki yayi sannan yafara cewa
"Da akwai wata yarinya dakeso kuyiwa kyautan 25m.." Dasauri mutumin yace
"Wa zaiyi kyautan?"
"Ni zanyi Amman da sunanku..."
"That's a good business...so tell me what I should do"
"There is a house in maitama"
Yabashi address din gidan sannan ya cigaba dacewa
" I want your people to paint it yellow.. Before next week then call me on this line its my direct line and I will tell you what to do next.."
"OK..I will call them right" ji yayi wayanshi na ringing yana dubawa yaga tawa, katse wayan Dan Mtn din yayi batare da sunyi ban kwana ba sannan yayi picking
"Princess of Yoruba land how are you.."
"Good morning sir"
"Morning ma...har kin tashi?"
"Eh wallahi.. Har nazo wajen aiki..."
"Tunda dazu nake son kiranki in baki wata labari" da sauri tace
"Please wane labari?"
"Wani abokina ne ya kirani dazun yacemin Mtn sun bashi million ashirin da biyar da katon gida" tawa daria tayi
"Congratulations to him in ba karya yayi makaba...please let's say something important.. Yaushe zaka dawo"
"Yanzu habibty maganan abokina ba abun important bane?.."
"No sir bahaka bane..kawai gane nayi kamar karya.."
"Love nine makaryaci?..."
"Ohhh..ifemi...yau kana jin fada..ba da kai nakeba...kaman abokinka karya yayi maka...Amman sorry if you are angry" Salem ceje lebe yayi yana daria ahankali
"Nima ba fushi nayiba..Amman da gaske ne..Mtn suna bawa masu luck kyauta"
"Naji...yaushe zaka dawo?"
"Yau... ina hanya..me zaki ajiye min tunda kin isheni da tambayan" daria jin dadi tawa tayi
"Na meye wannan darian?" Salem ya tambayeta
"Haka nan..yanzu me kakeso in ajiye maka?" Karaf Salem yace
"Kanki..."
"Zaka farako...bari in kashe wayata..."
"Sorry.. Sorry habibty karki kashe..bani da kudin kiranki..kiyi min tuwon shinkafa da miya...kina iyawa?" Daria tayi
"Sosai kam"
"Kina da kudi?" Ahankali tawa tace
"Ranar da akiyi bikin Dan President madam ta bamu bonus din 1k zai isheni tunda da kai da mami kawai zanyiwa..."
"Har kin bar aiki ki koma gida ki daga tuwon shinkafa da miya?"
"Kwarai kuwa"
"To shikenan... I love you"
"Love you more"
โค๐๐๐๐
ZAKISAN KONI WAYE
๐โค๐๐๐
ยฎzuwairat(ummu maryam)
2โฃ8โฃ
Ameera na zaune tana kuka wanda aka aika ya sayo abinci ya kawo cikin bakin Leda, daga kai tayi ta kalleshi da red eyes dinta
"Ubanmeye wannan?" Bai amsa mata ba ya juya abun shi
"Dan uwarka ba da kai nakeba?" Mutumin juyowa yayi yana kallon ikon Allah
"Me nayi maki kike zagina?" Da sauri ta girgiza mashi kai
"Kayi hakuri...Dan Allah" tafada tana kuka,
"Banza karuwa.. Ai Maganin Ku kenan.." Wani sabon bakin ciki ne ya tur nuketa
"Wallahi ba karuwa bace ni...Dan Allah Ku barni in tafi ko nawa kukeso zan Baku" wani irin dariya rainin hankali yayi
"Yarinya baki da abun badawa" daga chan waje dayan yace
"Magana kake daita ko?...har ka mance abinda sir yace?" Da sauri ya bar wajen ya koma bakin gate.
Ameera tana ji tana gani aka maida gate aka rufe, tayi kuka ta gaji, ahankali ta dauko ledan ta buda taga taliyace da mai da yaji, sabon kuka ta fara
"Allah yaisa tsakanina da kai...wallahi bazan taba yafe makaba..mugu macuci" tafada tana deban abinci, don tasan in har bata ciba tana iya mutuwa,tana ci ta tsinewa Salem, cinye abinci tayi tas, ta mike tafita, kitchen ta shiga taga duk an ajiye kayan abinci Amman babu wani abun fast food cikin su, wasu yan container ta bude taga da tashi da su daddawa,
"Amman duk ubanda ya sayi kayan nan matsiyaci ne...da Wanda ya saya.. Da Wanda ya saida...Allah sai ya tsine maku.." Tafada tana kuka, wani katon tulu tagani ta bude taga cike yake da ruwa, cikin kayan ta dauki wani cup ta dibi ruwan, tana sha tana kuka, komawa tayi cikin ta kwanta kanta nayi mata mugun ciwo, bata dade da kwanciyaba bacci yayi gaba daita.
Baa dade ba Abdul ya kara dawowa ya ajiye mata kayan sawanta da aka mance baa ajiye ba, yana ganin tana bacci ya ajiye ahankali batare daya tada taba.
๐๐๐๐โค
Da yamma Salem ya hau jet ya koma Kano , ko tuna ameera bayayi hankalinshi kwance don gani yake one mission is accomplished, sai zancen tawa kawai ne gabanshi da kuma yanda zaiyi ya shawo kan ummanshi.
Around 4pm tawa tayi wanka ta shirya , mami sai kallon ta take ba tare data ce komaiba, saida ta gama sannan tace
"Mami inason insayo kayan miya inyi maki tuwon shinkafa da miya" mami kallon mamaki tayi