Showing 57001 words to 60000 words out of 145230 words

Chapter 20 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

266

komawa ameera sabo cos yau ita kadai ta wuni, gashi da musassara ta wuni ga ciwon kai dana Mara, duk abin duniya ya isheta, bakin gate taje tayi knocking,

" meye?" Suka tambayeta, cikin kuka tace

"Dan Allah Ku kiramin hinde.." Banza sukayi daita,

"Kunji Dan Allah.. Bani da lafiya ne..."

"Kar ki kara aikanmu...darajanki daya da baki da lafiya.. Bari musa akira maki ita" daya daga cikin su ya fada sannan ya kira wani ya aikeshi ya kira hinde.

Bayan kaman minti ashirin sai ga hinde ta shigo gidan , gani tayi ameera durkushe kasa tana kuka hannunta kan maranta

"Lafiya?" Ta tambayeta tana karasowa wajen ta, cikin kuka tace

"Cikina...wayyo..menses zanyi..."

"Meye messes" tafada tana dagata tsaye

"Alada zanyi..." Tafada tana kuka tana yarfa hannuwa,

"Daman haka yake yi maki?" Kai kawai ameera ta daga mata,

"Sannu" hinde ta dinga yimata, ta maidata daki sannan ta dora mata ruwan , bayan yayi dumi ta saka daya daga cikin dankwali ameera ta dinga danne mata cikin ta da bayan ta,, aranan hinde nan gidan ta kwana, banda kuka babu abinda ameera takeyi don a gida in ta fara har Karin ruwa akeyi mata.

๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’›โค

Sai wacegari around 8am tawa ta isa Ilorin, tunjiya ko ruwa bata shaba, kuka ta dinga yi although the way, cikin kwana daya ta rame sosai, ga idanuwanta sun yi ja, bakinta ya bushe, wayan mutane ta dinga amsa tana kiran mami har ta isa, wayan wani bayerabe ta amsa ta kira mami ta sanar daita sun isa park, baa dadeba wasu cousins dinta uku sukazo daukanta, dukkan su kallonta sukayi suna cewa.

"Ga Hausa Yoruba" tawa batace masu komai ba ta shiga bayan helux suka kara gaba, cikin wani babban flat suka tsaya, anayin parking tawa ta fito kasancewan tasan gidan cos mai gidan yayan mami ce, itakadai ce bata juyawa mami baya ba amma sauran 6 duk basu yiwa mami magana wai don ta zani talaka.

Afalo taga mami da yayanta zaune, mami na ganinta ta mike tana mamakin yanda yarta ta koma cikin kwana biyu, tawa fadawa jikin mami tayi tana kuka Mara fita, hankalin mami tashi yayi

"Ife...kiLode?" Tawa bata amsaba tacigaba da kuka, irin kukan da takeyi yasa mami tunanin kilan Salem raping dinta yayi mami with dirty mind. Tawa kneeling tayi ta gaida yan mami da mami, Matan amsawa tayi tana tambayan ta abinda ke sata kuka amma tace bakomai.

Daya daga cikin cousin dinta wanda suke same age mate ta daga ta sukayi wani daki, ruwan wanka ta hada mata, wanka ta shiga tana wanka tanajin kamshin turaren shi, sabon kuka tafara.

๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’šโค

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’š๐Ÿ’›โค๐Ÿ’™๐Ÿ’œ

ยฎzuwairat(ummu maryam)

3โƒฃ9โƒฃ

Tawa na wanka ta kuka, fitowa tayi daure da towel, kayan data cire ta fito rungume dasu, kamshin Salem kawai take shaka, bata ankara ba cousin dinta ta amshe kayan ta wulla cikin laundry basket sannan ta miko mata leggings da shimi,

"Ki ajiye wannan ki bani kayana in maidasu.." Tawa ta fada mata cikin low voice, kallon mamaki tayi mata

"Ya zaayi ki maida kayan daki kayi tafiyan hour ashirin dasu?..."

"Please just give me"

"Freaky one.." Ta fada sannan ta Dauko mata kayan daga inda ta ajiye su. Tawa maida kayan tayi tana hawaye. Daman lokacin breakfast ne, dukan su na zaune kan dinning sun fara cin abinci amma tawa bata fitoba, yan mami kallon autanta mai suna tima tayi ta kirawo tawa, tima bakin gado ta tarda tawa sai kuka take tana shafa kayan jikin ta,

," please sis meke damunki?..you look pale..." Ahankali tawa tace

"Nothing.." Tsoki taja

"Daman ke matsalan ki kenan..zurfin ciki...mom tace kifito kici abinci" tana kaiwa nan tafice, tawa goge hawaye tayi ta fito, mami sai kallon ta take, zama tayi kanta kasa, abinci suka faraci, amma ko chokali biyar tawa bata yi ba ta mike,

"Har kin koshi?..* babban Dan mom maisuna femi ya tambayeta ciki yarensu, kai kawai ta daga mashi, mami kalonta kawai take, tima tace

" something is wrong with you " ta fadawa tawa.

Bayan sun gama breakfast suka falo, tawa da mami tare da mom sukashiga dakin mom, nan mom ta tambayeta abinda ke faruwa, cikin kuka ta fada masu ko Salem waye amma bata fada masu yanda sukayi da Umma Salem ba, mami kallonta tayi

"Tawa ko yayi maki wani abune?" Girgiza mata kai tayi

"No mami... I just love him..and am missing him already.." Mami buge mata baki tayi, mom kallon mami tayi

"Wai meye haka... Kinci saa tawa Dana respect.. Meye na rabata da mutumin da take so..ke an rabakune?... Har iyayenki ki watsar saboda so..to gaskiya ban ga amfani abinda know keyiba" afusace mami tafara cewa

"Aini mutuwa ya rabani dashi amma hausawa don't have respect for marriage.. Kuma mutumin in questions..is beyond us..."

"Ohh stop it!..." Mom ta dakawa mami tsawa

"At least ko bansan Salem a zahiri ba nasan shi a news..I don't think he's a bad person.. Gaskiya kinason kisa yarinya nan ciki wani hali...I don't know why mother take their children's feeling for granted..." Tawa sai kuka take, mom ta cigaba dacewa

"Ni zan nemo contact..." Da sauri tawa tafara girgizawa mom kai

"Mom ki barshi..."

"Why?..." Mom ta tambayeta, kuka ta farayi sosai sannan ta fada masu yanda sukayi da Umma, mami ma kuka tafarayi, rungume tawa tayi tana cewa

"Kinyi kadan da wahalan da kike sha...am sorry for all you have been through.." Tawa ma rungume mami tayi, duk jikin mom yayi sanyi, at the same time tana cewa

"Gaskiya am disappointed in her...sai kace bata da addini?..ai in Allah ya hada, mutum yayi kadan ya raba. Sunfi hour zaune nan, daga baya bacci yayi gaba da tawa jikin mami.

๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œโค๐Ÿ’š

Salem bai sake farkawa ba sai 9pm, lokacin ana yi mashi Karin ruwa na biyu, ahankali ya bude ido ya kalli Abba da Umma, Umma sai kuka take,

" son am sorry... " Salem bai komaiba tacigaba dacewa

"Na yarda ka aureta" Salem lumshe idanuwa yayi

"Umma where is tawa?" Ya tambayeta ahankali,

"Ta tafi gidansu..."

"Bata Kano..." Sabon kuka Umma ta farayi, Salem mikewa yayi zaune tare da taimakon guards dinshi, Abba kallon Salem yayi

"Son ko ta tafi garin su" kan Salem kasa baice komaiba

"Son ya sunan garin su...sai insa a nemo ta" daga kai Salem yayi

"Abba ban San garin su ba..besides tunda Umma ta roki tawa ta rabu dani..bazata Kara saurarena ba..kawai na hakura daita..." Yafada yana komawa, hawaye na zubo daga idonshi

"Son kayi hakuri... Ni zansa anemota...zanje har gidansu in bata hakuri..."

"Stop it Umma... Ki rabani da ita...tawa bazata Kara saurarenaba...tana da bin umarnin manya..." Umma shafa kanshi tayi tacigaba da kuka

"Yanzu ta ya zamu fara Neman ta..." Salem shuru yayi yana tunanin yanda rayuwanshi zata kasance in babu tawa aciki, yasan life will be meaningless, ko yanzu ji yake kaman ya mutu don bakin ciki, shi bai ga laifin ummanshi sosai ba..yafi gani laifin Tawakaltu data gudu daga gareshi, ahankali yafara cewa

"Why...why..me.." Abba rike mashi hannu yayi

"Son tashi ka dan cin abinci sai kasha drugs.." Girgiza mashi kai yayi

"Abba am not hungry..."

"No son..you have to eat.."

"Wallahi Abba bazan iya cin komai ba.." Haka suka kyalleshi, sai around 12am Umma da Abba suka kwanta, yarage daga Salem sai guards dinshi, daya daga kai suka hada ido sai ya wulla masu harara, haushin dukan su yakeji don gani yake rashin kulansu yasa tawa ta samu hanyan fita, cikin ranshi kuma yana tunanin babu abinda zai hanashi ciwa tawa for playing with his heart.

Har garin Allah ya waye bai samu bacci ba tunani kala2 yake, don ji yake inda zai Iya cire tawa daga cikin ranshi da yaji dadi. Duk Wanda ya ganshi sai yasan yana cikin damuwa, don idanuwanshi sun koma ciki, ya fada sosai. Tunda safe Umma tafara calling mutane tana cewa su nemomata yarinya mai suna tawa, abun haushin shine yanda babu mai photo dinta.har daren rana Salem bai ci komaiba, so yayi ya koma abuja amma Abba ya hanashi tafiya. Saida Abba yayi da gaske sannan yasha tea.

๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’šโค

With in kwana biyar kowanne part ya wahala, ita ameera ta jigata sosai saboda menstural pain don ta kara ramewa ta rage haske sosai don babu Wanda zai taba cewa classic ameera mai manicure, pedicure, zuwa spa..ce duk ta koma kalan tausayi, kullum cikin kuka take, yanzu sun shirya da hinde, don yanzu nan gidan hinde ke kwana.

Tawa kan cikin kwana biyar din ta koma kaman ba itaba don wannan hips din da Salem ke mutuwar so sun rage, mami ta kasa gane kanta, yar mom my shekara 22 ta sata gaba tana tambayan ta kasancewan babu Wanda yasan dalilinsu na dawowa Ilorin sai mom,

"Please tawa tell me what's the problem.. Remember we are family.. Matsalarki matsalar mune..." Deeja ta tambayeta, tima dake zaune cikin dakin tana chatting tayi karaf tace

"Anty deeja leave her... Babu tambayan da banyi mata ba..amma taki fadamin... Cikin dare bata barina inyi bacci.. Sai ta rungume kayanta ta dinga kuka..." Tawa daga red eyes dinta tayi ta gallawa tima harara.

"To tunda baki gayawa kawarkiba..ni in fidda ran zaki fadamin kenan" inji deeja, ahankali tawa tafara cewa

"Anty INA cikin matsaln da shuru yafi min alkhairi..." Da sauri tima ta ajiye wayan hannunta

"Meye Dan Allah?" Tawa kara hararan ta tayi sannan yajuya tana kallon deeja tafara bata labarin yanda suka hadu da Salem har ranar da taje gidanshi, baki dukkansu suka bude, da sauri deeja tace

"You mean Salem Yusuf sulaiman popularly known as slim.." Cikin kuka tawa tace

"Ni ban san ana ce mashi slim ba.."

"Kam...dan baki ganin shi asocial media ba...wow..I can believe this.. Kin taba ganin slim?.. Bari in rungume ki" deeja rungume tayi tawa ta gallawa bayanta harara

"Tunda kin taba runguman slim...."

"Anty stop it.." Tawa tafada cikin fada da kishi, dariya sukayi

"Babe kar ki biyewa mami wallahi in kina sonshi.. Kawai ki kirashi yazo nan.." Inji tima, mikewa tayi daga inda take suka bita da kallo ko wannensu tana mamakin yanda akayi tawa tasan Salem dukda gani suke karya take.

Dakin mami ta shiga ta ganta kwance tana bacci, ahankali ta dauki wayanta ta fita daga dakin

Abangaren Salem baka gane shine don raman dayayi, kullum sai anyi mashi Karin ruwa, Abba da Umma suna mamakin irin wannan so, sai sunyi da kyar yake Dan cin abinci, duk hankalin guards dinshi ya tashi, don gani suke kaman yana Iya mutuwa kuma hakan means problem for them.

Duk iyan kokarin da Umma da Abba keyi don su nemi garin su tawa yaci tura don har obasonjo aka kira shima ya yasa mutane su nemo Tawakaltu Lukman amma baa samuba.



Salem na zaune yayi tagumi duk abun duniya ta isheshi, sai tunani yake tawa bata sonshi don yanda ta iya kwana 6 bata ji muryanshiba, su Abdul na tsaye Dan nesa da inda yake, Wayanshi dake hannun majed yafara ringing, da sauri majed ya karasa wurin shi tare da mika mashi wayan,

"Who?.." Salem ya tambaya batare daya kalleshi ba

"No name sir" majed ya amsa mashi, shuru Salem yayi yana sauraron kiran, don baya daukan anyhow call, kaman an chunkuleshi yace.

"Tawa..." Sannan yayi saurin amsan watan, kafawa yayi ga kunne

"Hello.." Yafada cikin sauri, tawa najin muryan shi ta rike baki

"Hello...Tawakaltu is that you?" Tawa najin ya kira sunan ta ta fashe da kuka, mikewa tsaye yayi

"Tawa..the only way I will forgive you for playing with my heart is by telling me where you are..." Yafada afusace har jijiyan wuyanshi na tashi, tawa bata ce komaiba yacigaba dacewa

",I thought you love me...but I was wrong... Wallahi in har baki gayamin inda kike ba...." Hawaye ne yafara zubo mashi,

"What did I ever do wrong to you..." Yafada muryan shi na rawa

"Habibty tell me... Please", yafada ahankali, tawa bata ce kala ba, tari ya farayi sosai,

" am dying for you...wallahi habibty tunda kika gudu kika barni banci komai ba...tell me and I will forgive you..." Ahankali tawa tace

"Ife..am..."

"Don't you ever call me that.. Until you tell me where you are..."

"Am sorry..." Afusace ya kara katseta

"Don't say anything until you tell me where you are..." Tawa batace komai ba ta dinga kuka, hankali Salem yayi murmushin takaici

"So bazaki fadamin bako?.." Tawa bata bashi amsa ba tacigaba da kuka

"OK..ba matsala.. Did you know what I regret most?" Ya tambayeta, bata bashi amsa ba yacigaba dacewa

"That night you spent in my house.. I would have tear you..I would have given you something to remember.. Da bazakiyi gigin guduwa daga gareniba...but you know what?" Ya kara tambayan ta

"I will find you....you know why?..cos I love you.. But that will not stop me from landing you in the hospital the way you landed me..." Tawa kuka tacigaba dayi sosai, Salem ji yayi kafanshi baya daukan shi, wuri ya samu ya zauna, bai gama zamaba yaji wayan ta katse, da sauri yace

"Hello.." Yaji ta katse wayan, with out wasting of time Yayi dailing number amma switch off, tsayawa Yayi yana Tunanin abun yi don yasan he's going insane already, da sauri ya fara shiga cikin contact din wayan, nan ya dinga neman contact masu suna Yoruba, Mr kayode ya gani, da sauri ya kira number, mutumin na dagawa yayi yanason gaida Salem amma Salem ya katseshi dacewa

"Please kai Dan wane garine?" Ya tambayi mutumin

"Sir from osun"

"Please kasan sarki cikin sarkin yorubawa Wanda ya kori yarshi saboda ta zabi wani talaka?" Mutum shuru yayi for a while

"Sir yaushe hakan ya faru?" After few seconds yace

"I think it should be 19 to 20 years ago" mutumin shuru yakarayi da alaman tunani take

"Gaskiya sir I don't know.. Any problem?" Tsoki Salem yaja

"Please help me find out from you family and friends"

"OK sir" cikin few minutes Salem ya kira wayanda yasani yorubawa ya tambayesu amma babu Wanda yasani, sai yace masu please su tambayar mashi, mikewa yayi ya nufi part dinshi na gidan, su Abdul binshi sukayi, juyawa yayi ya kallesu

"Dalla Ku bar bina..sanda naso kuyimin guiding din gidana Baku yiba...kawai kuyi adua in ganta..in ba hakaba you will all be fired.." Ya fada yana kallon su dayan bayan daya, saida yazo kan Abdul ya nuna shi da Dan yatsa

"Most especially you..don duk kai kajamin wannan matsalan.

Salem komawa yayi ya kwanta yana tunanin Allah yasa agane ko waye, bai kai minti ashirin da kwanciya ba wayanshi yafara ringing, da sauri yayi picking,

$" sir ance its oba of kwara state" da sauri Salem ya mike zaune yana saka palm sandal dinshi

"You oba...ehmm...oba sadiku!?"

"Yes sir"

"Are sure?"

"Yes sir"

"Thank you.. " ya fada yana katse wayan, bai dade da katsewa ba yafara ringing kuma picking yayi

"sir ance its oba sadiku of kwara state"

"Thanks" kawai yace ya fita ya nufi side din abbanshi.

๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’šโค

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’™โค๐Ÿ’š

ยฎzuwairat(ummu maryam)

4โƒฃ0โƒฃ

Salem na zuwa part din Abba ya zauna yana haki saboda yanda yayi tafiyan cikin sauri, saida numfashin sa ya daidaita sannan yace

"Abba.. Na gane waye grandpa dinta," da sauri Abba yace

"Really?.. Waye?"

"Can you believe it?.. Oba sadiku of kwara state ne grandpa dinta," kallon mamaki Abba yafara yiwa Salem

"Son are sure of what you are saying.."

"Yes Abba.. Investigation nasa aka yimin" Abba gyara zama yayi

"Wane investigation?" Sai lokacin Salem ya bawa Abba labarin da tawa ta bashi, baki Abba yabude

"Son shine kake cewa har talakawa ce?.. Ai sadikus linage are filty rich..." Dan murmushi Salem yayi

"Ai tawa a restaurant take saida abinci.." Abba shuru yayi for a moment sannan yace

"Ai abinda uwar yarinyan tayi bata kyauta ba..whatever parents come first... I think nasan lokacin da abin yafaru..I was the GCFR a lokacin..."

"To yanzu Abba meye abinyi?.." Salem ya tambayi Abba, Abba shuru yayi yana tunanin abinyi, bayan kaman 40 seconds yace

"Zan yiwa obasonjo magana sai ya rakani muje wurin oba.."

"To Abba inkuje ..." Shuru yayi sannan ya Dan doki kanshi sannan yace

"Abba am confused.. Kasan iyaye maza suke babanta ya kamata su bani ita..." Dariya Abba yayi

"I know.. Kasan am sure yarinya da mamanta basu gidan oba...so zamu shirya tsakanin ta da iyayenta..hakan zaisa mu gane whereabout dinsu"

"Gaskiya hakan yayi... Amma.." Sai kuma yayi shuru,

"Amma me?" Abba ya tambayeshi, yana Dan shafa keyanshi kaman mai jin kunya yace

"It will take a long time.." Dariya Abba yayi sosai, cikin zolaya irin na iyayen zamani yace

"Ka matsu ne?" Salem sunkuyar da kanshi kasa yayi yan dariya,

"Ai kayi kokari...35 ba wasa bane..in badai kana..." Da sauri Salem ya girgiza mashi kai

"Never.. Abba" yafada kanshi kasa, saida kunyan tadan sakeshi sannan yace

"Amma Abba there is one more problem.."

"OK..na meye?" Ahankali Salem yafara cewa

"Abba maminta bata son hausawa" dariya Abba yakarayi

"Me hausawa sukayi mata"

"Wai Abba cewa take basu da rike aure..." Dariya Salem yafara yana

cewa

"Yau aure gobe babu" yafada a irin muryan mami, Abba dariya yayi.

"In-law to be dinka kake yiwa shakiyanci ko..babu ruwana..amma maganan ta ba karya bane..saidai ba duka aka taru aka zama dayaba.. Besides we are not hausas"

"Ai Abba dukkan mu Hausa ake cemana"

"To ba matsala bane, zamu nuna masu muma muna da rikon aure"

"Insha Allah" mikewa yayi ahankali,

"Abba inason in goma gidana na nan" kai Abba ya girgiza mashi

"Kayi zamanka nan tukunna"

"OK" yafada amma badon yasoba, donshi mutum ne maison privacy, har ya kai bakin kofa Abba yace.

"Mijin Yoruba..ka kokarta kafara cin abinci don kar ayi tunanin wani ciwo gareka" murmushi jin dadi Salem yayi

"Insha Allah Abba" sannan yafita, yana fita yaga majed ya taho da wani work phone

"Sir wani nason magana da kai" fuska daure Salem yace.

"Waye?"

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login