Showing 108001 words to 111000 words out of 145230 words
fada tana goge hawaye da sauri, Salem kura mata ido yayi tausayin ta na kama shi
"You helped me... Ka chanza min rayuwa...you make me understand that human being is far more important than material things.... Ka sa nagane mutane rahamane ko yaya yake...so thank you very much for everything..." Ta fada tana hawaye sosai, Salem komawa yayi ya danyi relaxing da kujeran dinning
"I feel like hugging you right now... Please don't cry.," ya fada cikin whisper, ita kanta batasan kukan da take ba, ta dade tana jiran wannan ranan, hannunshi mai lafiya ya bude ya ajiye kan dinning table da alaman ta saka hannun ta, babu gardama ta saka two hands dinta cikin palm dinshi, ahankali yafara caressing hannun yana cewa
"Am sorry I made your beautiful eyes shade tear.," dariyan karfin hali tayi kuma hawaye na rolling idanuwanta
"Kinsha walaha sosai ko?.." Ya tambayeta, girgiza mashi kai tayi
"Only the bathroom..." Ta fada tana dariya, shima Salem dariya yayi,
"Am sorry..." Ya kara fada mata, kallon hannun shi tayi
"What happens to your hand?..." Salem kallon hannun yayi yadanyi dariya
"Bazan fada maki ba... I don't want you to laugh at me.." Shuru tayi for a moment, lokacin hawayenta ya tsaya, har lokacin hannuwanta cikin palm dinshi
"Ina matarka ne?.." Ta tambayeshi in a formal way, hankali ya fara cewa
"That's the reason I brought you here...I need your help..." Ya fada mata, shuru tayi yacigaba dacewa
"Lokacin da nake rubuta sakin tagani shine take tada ahankalinta wai nayi using dinki nayi dumping dinki, ...so please I want you to help me..." Dan dariya tayi tana kallon hannun shi
"Ita ta karya maka hannu?..." Bata idaba ya cunkuli hannun ta yana dariya
"Please will you tell her?..."
"Yes..." Ta fada
"I owe you one..." Ya fada mata sounding very excited, murmushi kawai tayi batace komai ba, zare hannuwanta tayi, ya kalleta
"Wai har kin koshi?..." Ya tambayeta, kuma dajin muryan shi he cares
"Yes alhamdulillah.." Ta amsa mashi.
"To yanzu muje wurin ta?.." Yafada sounding so earger
"Why not ni kadai inje?.." Tafada tana mikewa tayi
"Ok...sis" yafada cikin zolaya, ameera tafiya n tayi cikin kasaita don ko kadan tafiyan ta babu sauri cikinta, tana tafiya kaman tana tausayin kasa kuma ba wai don tana gaban Salem take tafiya hakan ba Aa daman ko a gida haka take har mom kan ce mata ta fiya nawa.
Salem kura mata ido yayi yana tunanin
"I wish you were nice to me when I first met you..." Yafada cikin ranshi.
Ahankali ameera ta bude kofan dakin tashiga har lokacin Tawakaltu bata taci ba, ba bacci take ba amma idanuwanta rufe, ta kwanta tare dayin rubda ciki, Sallama ameera tayi, jin muryan mace yasa tawa saurin bude idanuwa tare da mikewa zaune, tana juyawa taga wata beautiful lady tsaye itama ameera taga kyauwunta don tana da manyan kyau. Yanayin kumburin idanuwanta bai rage mata kyau ba, itakam tawa gani take in har wannan yarinyan itace Matan da yake cewa ya saka kuma babu abinda yabtaba shiga tsakanin su yayi karya Sannan in har yana Iya sakin wannan glamorous and unique lady to itama she doesn't have a chance of staying with him for ever, dukkan su kurawa juna ido sukayi ko wacce da tunanin da take, ita tawa tana ganin ameera is an angel itakuma ameera tana ganin tawa is gorgeous, da sauri tawa ta saki murmushin karfin hali itama ameera murmushi ta sakar mata Sannan ta karasa bakin gadon ta jawo stool ta zauna, dukkan su babu wacce ta kai 19, gaisawa suka dukda muryan tawa bata fita sosai,
"Nice ex wife... Na mijinki..." Ameera ta fada mata bayan sun gama gaisawa
โค๐๐๐๐
ZAKISAN KONI WAYE
๐๐๐๐โค
ยฎzuwairat(ummu Maryam)
6โฃ6โฃ
*In dedication to anty sis, Allah ya barminke, ya kareki Dan nabiyun rahamati..ameen* ๐๐๐๐
Yanda tayi maganan yasa tawa kallon ta tana tunanin hiring dinta Salem yayi don ta fada mata hakan, cos ko kadan baka tunanin ameera tana son Salem cos she looks cool with what she's saying,
"Hmmm..I know setup ne..." Tawa tafada cikin low voice, kai ameera ta girgiza mata tana tunanin yanda take Hausa fluently
"Aa wallahi... Nice ya aura...AI ya fadamin kece wacce kika taremashi lokacin Dana mareshi...." Tawa kara kura mata ido tayi tana kallon ta, sai lokacin ta tuna she have met her some where,
"Da gaske kike?.." Tawa ta tambayeta,
"Yes...nice.." Dan murmushi tawa ta sake yi
"You have got some nerves..." Tafada tana dariya
"Very..." Ameera ta amsa mata itama tana dariya,
"Amma thanks to sir Salem am a change person..."
"Point of corrections... Your husband.." Tawa tayi adding, ameera girgiza mata kai tayi
"Mijinki dai..."
"Mijin mu...anyway tell me what happens?., " labarin yanda Salem yazo yayi deceiving dad dinta har akayi aurensu babu mutanen shi ko daya har zuwa inda aka kaita gidan Mara kyau... Tana fada tana dariya tawa kam kura mata ido tayi
"Kam...daman ana aure babu iyayen miji?..." Tawa ta tambayi ameera
"Hmmm..AI lokacin nobody was thinking... Remember it's sir Salem and he is dad's boss..." Dariya dukkan su suka karayi
"Amma gaskiya abinda yayi maki bai kyauta ba cos da akwai millions of people da akeyiwa abinda ya fi Wanda kika yi mashi kuma basu cewa komai..."
"AI shi yana da kudi..." Inji ameera shuru suka danyi for a few seconds Sannan ameera tacigaba dacewa
"So kiyi hakuri da mijinki..."
"Our husband..." Tawa ta kara correcting dinta Sannan tacigaba dacewa
"Kuma bazan yi hakuri ba cos na daya ya yimin karya, na biyu ya wulakanta mace yar uwata..." Ameera har cikin ranta taji dadin maganan tawa don gani take ta Iya tsara magana,
"Aa..bai wulakanta ni ba...ai babu abinda yashiga tsakanina dashi...Sannan ni dasu hinde shagalin mu muke fiye da yanda kike tunani..." Dariya tawa tayi
"Ke dasu wa?.."
"Ni da new friends dina...." Tafada tana dariya
"Kice har kawaye kikayi kenan..."
"Wallahi kam..." Ta amsa mata Sannan shuru ya Dan biyo baya,
"Wai ya akayi kike jin Hausa haka..cos wasu daga cikin course mate dina basu jin Hausa..." Ameera ta katse shurun da wannan maganan. Nan tawa ta Dan bata takaitaccen tarihinta,
"Allah sarki.." Ameera ta fada Sannan ta kara cewa
"To ya akayi kuka fara soyayya da sir Salem?..." Ta Kara tambayan ta, nan tawa ta fara bata labarin yanda abun ya fara faruwa tun ranar da ita ameera ta mari Salem, dariya ameera tayi
"Sis kina nufin duk wannan fuskan bai baki tsoro ba?..har kika kamu da sonshi?.." Ameera ta tambayi tawa, itama tawa dariya tayi
"Wallahi kam...ahaka naji wani special feeling akanshi..." Inji tawa,
"Kam...gaskiya dole Salem ya mutu kanki... Kin chanchanci yabo wallahi..." Inji ameera, tawa bata ce komaiba ta cigaba da bata labarin har izuwa yanzu, still ameera babu abinda takeyi sai yabonta kuma har cikin ranta takejin tawa, don kaman sun dade da junansu haka takeji,
"You really tried... That's why sir Salem yake cewa you are the only one for him.." Inji ameera bayan tawa ta gama bata labarin su,
"Kema yana sonki tunda har yaje gidanku for almost three times..." Inji tawa ameera ta katseta dacewa
"Kuma naci buroubanshi ba...." Ta fada tana dariya, itama tawa dariya tayi har da rike ciki,
"So yanzu komai ya wuce..muyi zaman mu mu uku...har Allah ya bamu yara..." Inji tawa, ameera kura mata ido tayi tana mamakin irin halin tawa
"Wai sis baki kishin mijinki?... Har kike cewa na zauna dashi?.." Ameera ta tambayeta, Dan kasaitaccen murmushi tawa tayi
"Hmmm..bawai bana kishin mijina ba..amma tunda Allah yasa hakan ya faru ba sai mu rungumi kaddara ba?... Kuma ina ganin zamuyi zaman lafiya, gamu yara, Sannan mu ajiye kiahi gefe daya, mu rabu da kawaye mu zama aminan junanmu..." Tunda take magana ameera ta kura mata ido, gaskiya Salem yayi saan mata,
"Hmmm...sis kinsan me?..." Ameera ta tambayeta, kai tawa ta girgiza mata,
"Wallahi wannan zaman da mukayi dake for just a few minutes ya chanza min tunanina kan yare..." Gyara zama tawa tayi
"Bangane..ba" tawa ta tambayeta,
"Sis da nifa bana son yare mussanman Yoruba da Igbo..." Dariya tawa tayi
"Why?.." Ta tambayeta da murmushi a fuskan ta
"Nima sis ban Sani ba..amma kawai ina ganin in mutum ba Hausa ko Fulani ba they can go to hell..." Yanda tayi maganan yasa tawa dariya sosai,
"Nikuma ina ganin yin hakan jahilci da rashin wayewa ce...kinsan if you are not expose kana wuri daya haka zaka dinga ganin babu kowa sai naka.. Amma the moment kikayi fita wasu wuraren..kika zauna da mutane kala2 zagi gane we are one...no need to show tribalism..." Inji tawa
"Hmmm...gaskiyane..tunda gashi Dan zaman danayi da ke yasa na samu more light..." Tawa dariya tayi tacigaba dacewa
"Kuma kinsan kilan dani ban zauna Kano naga halin hausawa ba..kilan nima zanki su...amma gani nake kaman yanda na riga na saba dasu bazan iya sabawa da mutane na hakaba..kuma wallahi kiyayyan is from both side amma not with those that are civilized and educated...am just wishing I can bring an end to tribalism"
"Wallahi hakane..." Inji ameera,Sannan tawa tace
"Kinsan...me?..." Ta tambayi ameera
"No sis.." Ameera ta amsa mata cos she enjoying every bit of the discussion
"Wallahi mami bataso na auri Salem ba.." Ido ameera ta gwalo
"Why..."
"Wai cewa take hausawa saurin sakin mata..."
"Hmmm..sis ba karya tayi ba...duk Nigeria.. In short duk duniya babu inda ake saurin sakin aure kaman arewacin Nigeria.. Amma mami ta kwantar da hankalin ta sir Salem bazai sakekiba...kuma ba duka aka taru aka zama dayaba..."
"Hmmm..Allah yasa..." Ta fada ameera ta amta mata da ameen, ameera kallon ta tayi Sannan ta Kara cewa
"Yanzu kin yafewa mijinki for not being truthful?..." Ameera ta tambayeta
"Ni kibar cewa mijina.. Say our husband..." Inji tawa, kai ameera ta girgiza mata
"Ai ya sakeni..." Ta fada kaman bai dameta ba, fuska tawa ta daure,
"Ni bansan wannan zancen ba..kawai ki yarda mu zauna tare ko kuma nima inyi tafiya ta," inji tawa, dariya ameera tayi,
"Da gaske nake...so forget about me and forgive your hubby...don naga har karya mashi hannu kikayi"
"Kam" tawa tafada tana dariya, itama ameera dariya take tamkar bata da damuwa,
"Ki rabu dashi..ni ban karya mashi hannu ba,..he's pretending.. Yana tunanin ban saniba.." Inji tawa, ameera dai dariya kawai take,
"Yanzu sis mu zauna tare..." Inji tawa, dariya kawai ameera tayi bata kara cewa komaiba, dukda tana tunanin ya zaayi mutum ya sowa kanshi kishiya, abinda kowa ke gudunta,
"Yauwa..sis please kinzo da pad?...wallahi period nake kuma I was thinking gida zani so ban dauki extra pad ba.." Kallon ta tawa tayi
"You mean baki da tsarki?..." Tawa ta tambayeta sounding a little bit relieved.
"Eh..wallahi..." Am ta amsa mata not paying attention to her tune
"Kuma kike cewa Salem ya sake ki?... AI na tabajin wani malami yace baa sakin mace in tana haila..kuma ko anyi bata sakuba..." Tawa ta fada da sauri,
"Tofah..." Ameera ta fada Sannan ta kara da cewa
"Ni ban tabajin hakan ba...nidai nasan ance baa son sakin mace sai tana da tsarki.. Anyway let's forget about all that.. Nidai ki bani pad ina samun discomfort already.." Inji ameera
,"naga kaman bakima son sir Salem... " tafada tana danyi kaman zatayi kuka, dariya ameera tayi tana cewa
"Nidai please help me with the pad.."
"Babu amma bari wannan Matan tazo sai ki fada mata..."
"Kedai zaki fada mata.. You are the madam of the house..." Hararanta tawa tayi da manyan idanuwanta
"We shall see"..
Salem kam yayi zaune falo yana jiran fitowan ameera
Amma shuru, gaban shi ne ya dinga faduwa don yaga she's taking too long
"hmmmm.." Kawai yake ta maimaitawa, ahankali ya mike ya taka zuwa bakin kofan, amma ya kasa samun courage din budewa, kafa kunne yayi amma yasan bazaiji komai ba cos kofan sound proof ne, upstairs ya hau hoping to hear good news from ameera, ko minti ashirin baiyi da hawaba Mrs Samuel ta shigo don hada lunch.
Khalid kam tunda wuri ya kama hanyan abuja, yana sauka ya kira agent din Salem suka kama hanyan inda ameera take, Khalid kam ba karamin kyau yayi ba cikin English wears, sai kamshin gaske yake, sai tunanin abinda zai fadawa ameera kawai yake don gani yake dukda bai taba ganin ta ba he knows he's in love with her, don haka nan yake imagining fuskan ta.
Suna isa ya samu bad news kan an dauke ameera, zagi ya dinga burmawa Salem yana cewa
"Ya saki yarinyan kuma ya dauketa Dan uwarshi?...wallahi sai maganan nan taje wurin su first love"ya ya fada yana dailing number Salem, ji yayi not reachable, abinda bai saniba Salem ya saka number shi a blacklist cos a bangaren Salem babu Wanda yake bashi haushi Kamar Khalid don gani yake shine sanadin lalacewan honeymoon donshi.
Khalid kam ya gaji da trying ya rubuta mashi text kaman haka
_" ka maido yarinyan nan tunda yanzu ba matarka bace...in kuma baka maidotaba before the next one week.. Wallahi I will forget about our friendship and take this letter to Umma and Abba.. If you think am joking try me"_yana kaiwa nan ya turawa Salem. Sannan yaja motan shi daga kofan gidan afusace. Gani yake Salem ya rushe mashi plan.
Abangaren mom ameera kam har yau rikishi bai kareba don har yau tana kan bakanta na a maido mata yarta, Sam dad ya kasa gane kanta don ba karamin tsoro take bashi ba, kunsan mai hakuri bai Iya fushiba, itama ta fadawa dad cewa
"In har baka fadawa Salem ya maido min yataba before the next 5 days...wallahi tallahi babu abinda zai hanani zuwa yola wurin iyayenshi... Koda yin hakan zai kawo karshen zama na da kai..." Ta fada Sannan ta hau upstairs tana kuka, dad kam yana zaune yayi tagumi don ba komai ke damunshiba sai halinda matarshi ta shiga tun shekaran jiya da Salem ya fadawa yan jarida bai taba aureba.
๐โค๐๐๐
ZAKISAN KONI WAYE
๐๐๐โค๐
ยฎzuwairat( ummu Maryam)
6โฃ7โฃ
Hiransu suka cigaba dayi kaman wasu best friends da suka dade da sanin junansu, lokacin sallan zuhr yayi tawa ta mike ta shiga bathroom ta dauro alwallah ta fito tayi salla ameera sai kallon ta kawai take har ta ida. Ameera kam sai matse kafafuwa take saboda discomfort da takeji don yanzu ji take kaman jikinta ya bace,
"Sis ki duba mana ko matan ta zo..wallahi duk banajin dadin jikina.." Ameera ta fadawa tawa,
"To muje mu duba ko ta zo..." Tawa ta amsa mata tana mikewa daga kan praying mat, itama ameera mikewa tayi tana kallon jikinta din tabbatar da jikinta bai baciba, falo suka je suka ga babu alaman Salem, kofan kitchen dake bude suka shiga tare looking so united, mrs Samuel suka gani tana chopping carrots, tana ganin su ta sakar masu murmushi, gaisawa sukayi tana kallon both of them,
"Anty please we need sanitary pad..." Tawa ta fada mata,
"Ok ma'am..." Ta fada Sannan ta fita daga kitchen din, ameera da tawa zama sukayi cikin katon kitchen din kasancewan da kawai round center table mai dauke da chairs tamkar dinning table don sai ka zauna wurin kaci abinci, tawa kam sai kallon kitchen din take don bata taba ganin kitchen mai dauke da beautiful and expensive kitchen wares kaman wannan ba, itama ameera sai kallo take don dukda tana yar gidan masu kudi da akwai abubuwa da dama da bata taba ganin su ba,
"Ko me take dafawa?.." Inji tawa tana dan mikewa,
"Ki duba mana..." Ameera ta amsa mata, wurin gas ta nufa daidai da shigowan Mrs Samuel, wani katon Leda ta mikawa tawa
"I bought it when sir ask me to shop for you.." Tafada
"Thanks.." Tawa ta fada tana amsa daga hannun ta, ameera sai dariya kasan makoshinshi take, tawa mikawa ameera tayi ta amsa da niyyan fita amma Mrs Samuel ta nuna mata bathroom dake manne da wurin ameera shiga tayi ta saka Sannan ta fito,
"Mu koma..." Inji ameera, tawa mikewa tayi, har sun kai bakin kofan tawa tace
"Sis why not mu tsaya mu kalli abinda take dafawa,.." Ba musu suka tsaya suna kallon abinda take hadawa, sai hira suke ameera kam da Matan tayi magana sai ta dan kauda kanta tayi dariya, tawa ta lura da hakan
"Sis wai meke damunki ne?..na lura sai dariya kike..." Tawa ta tambayeta, ameera isa tuntsurewa da dariya tayi
"Wallahi yanda wannan Matan ke magana ke bani dariya... Tana magana kaman daga cikin hancintan maganan ke fitowa.." Ta amsa mata tana dariya, itama tawa dariya tayi, Mrs Samuel ma dariya ta farayi dukda batasan abinda ake cewa ba, itakam sai shaawansu take don gani take in har Salem ya hadasu biyu amatsayin mata ya gama holewa din bata ga makusan su ba.
Suna wurin har ta gama lunch kuma duk sun koya tare suka jera abinci kan dinning table,
"Sis muje muyi wanka don mu ji dadin kwasan wannan abinci.." Inji ameera, ba musu tawa ta bita sukayi hanya upstairs.
Salem kam yana hawa ya kwanta kan doguwar kujera bai dadeba bacci yayi gaba dashi suna hawa suka ga handsome face dinshi kwance yana bacci,
"Shhhhh../" tawa ta fadawa ameera tana sa dan yatsanta kan bakinta, cikin sadda suka shiga ciki tawa ta fara wanka ta fito daure da towel Sannan ameera ta shiga, tawa blue din mini gown ta saka ita kuma ameera ta saka pink din gown Wanda ya kai har kasa saidai ya dan matseta.
Ahankali suka fita daga dakin suka sauka downstairs, kan dinning suka zauna suka fara cin abinci su.
Sai bayan zuhr ya tashi bacci, da sauri ya mike tare da yin alwallah Sannan yayi sallah, wanka yayi ya kara chanza kaya, still three quarters ya saka da t-shirt, abinda ke hannun shi ya cire cos