Showing 102001 words to 105000 words out of 145230 words

Chapter 35 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

251

baby me!..." Ta daka mashi tsawa

"Baby you are taking this whole thing in another way....Dan Allah ki bani just a little chance to explain..." Banza tayi dashi ta ida cire kayanta ta wurga mashi afuska ya rage daga ita sai pant, juyawa tayi tashiga bathroom da sauri Salem yabi bayanta

"Habibty please what are you doing?... Please let me explain..." Bata saurareshiba ta dauki wet gown dinta ta fara maidawa jikinta, da sauri Salem ya riketa, wani irin turawa tayi mashi sai gashi ya kusa kaiwa kasa

"I will not let you use me and dumb me...." Girgiza kanshi kanta kanshi kanshi

"Wallahi ba haka bane...." Ko kallon shi batayiba ta gama saka kayan da ruwan Salem tsaye yayi ya kasa kara tabata, tana kuka tazo wucewa inda yake tsaye, da sauri yayi kneeling tareda rike mata hannu still fixgewa tayi ta fice. Da gudu ta fara sauka kasan bene shima da gudu ya fara binta,

"Habibty were are you going?.." Ya tambayeta yana binta da gudu cikin kuka tace

"Far away from a lier like you..."

"Please stop... Ki tsaya...baki San kowaba...please.." Bata saurareshiba har ta bude kofan down stairs bai kamata ba, gani yayi da gaske take don gudu take kaman wata yar race, gudu yake da dukkan karfinshi da kyar ya cimmata ya kamata ta baya, wani irin naushi ta dinga sakar mashi ta baya amma bai saketa

"Please... Stop.."

"No...bazan Iya zama da kaiba...ka maidani wurin uwata..." Tafada tana haki at the same time tana kuka kaman ranta zai fita

"Please.. Am..sorry... " ya fada kaman numfashin shi zau dauke saboda gudun da yayi

"Please ki saurareni...in har baki gamsuba zansa pilot ya dawo ya maidani...please calm down" kai ta girgiza mashi

"Duk abinda zaka fadamin yanzu karyane...na rokeka ka fadamin in da akwai something I should know about you... Amma kace min babu..na taba tambayar ka kana da aure kace min Aa....yan news sun tambayekร  kace ร ...kawai don ka sameni ka using dina kayi dumbing dina...you such a big liar...can be with a cheat and a liar..." Kukane yaci karfin ta tayi shuru, rungume ta yayi ta baya

"Am sorry... Wallahi ba hali na bane....ki bari in fada maki komai...."

"No!... I hate you.." Tafada tana son kwacewa daga rikon da yayi mata

"Stop it!!!" Ya daka mata tsawa

"No!!!" Itama ta daka mashi tsawa, kokarin kwace wa tacigaba dayi. Abun sai ya zame masu kaman fada don duk yanda yake kokarin maidata cikin gidan ya kasa don gani yake kaman ma ta fishi karfi...sunfi minti arbain suna Abu daya , Salem ya kasa maidata cikin gidan itakuma takasa kwacewa daga rikon da yayi mata,

"Allah yaisa sakanina da kai..." Ta dinga maimaitawa Salem kam duk ya gaji don banda nishi babu abinda yakeyi, hakuri yakebata amma ko saurareshi batayiba

"Tell me what you want me to do..." Ya tambayeta cikin sanyin murya

"Ka maido matanka...ka sakeni in tafi..."

"Wallahi ban dauke ta a..," bai idaba ta kara kokarin kwacewa, kara riketa yayi

"Na saketa already...." Yafada cikin tashin sense don tunda yake bai taba shiga matsala kaman na yanzuba

"Please..ba matata bace...yarinyan data mareni ce..."

"More lies..." Tafada cikin shessheka

"Kawai bring back your wife.. Daman duk Dan ...da baijin maganan iyayenshi yana cikin nadama...mami ta fadamin amma son...nakeyi maka ya hanani gani...wallahi I hate you..." Salem hawaye ya farayi don gawayi ta fi zuciyanshi haske.

"Kar ki bari shaidan ya tarwatse happiness dinmu..."

"Kaine shaidani...." Bai Kara cewa komaiba yayi ta maza ta dauketa ba karamin duka tayi mashi ba don baisan tana da masifa ba sai yanzu da hannun biyu ta dinga dukan shi tana cewa

"Drop me.." Bai ajiye ta ba har suka shiga ciki gani yayi zata kifa mashi baki shoulder da sauri ya direta ya koma ya kulle kofa, takalman kafanta ta cire ta fara wulla mashi ya kaucewa

"Ka bude min kofa...wallahi ka bude min ..shuru2 ba haukabane..." Baice komai ba sai mamaki yake cos she's taking it very bad, wannan tana iya kissan kai in ranta ya baci, bai ankaraba ta dauki wani beautiful vase dake zaune kan wani table ta wulla mashi Allah ya taimakeshi ya kauce nan take ta tarwase

"Wallahi ka bude min...ban zama da kai..." Tafada tana daukan wani decor dake zaune kan dinning table shima wurga mashi tayi ta fashe, gani yayi in ya kyaleta zata Iya bata dukkan abubuwa dake dakin, kafin ta kara daukan wani Abu yayi sauri kamata kaman mage ya yagesgi a fuska gashi tayi fixing nails, bai ji ciwo ba amma fuskanshi yayi ja sosai, kaman mahaukaciya ta koma sai kuka take babu alaman gajiya tattare daita, da kyar ya samu ya danneta kasa sai kuka yake yana cewa

"Am sorry.. Please don't hurt your self... Wallahi..."

"Kar ka fadamin komai... Ka aure yarenka ka wulakanta ta balleni...."

"Please just let me explain....I married her to take revenge on what she did to me...." Yafada cikin kuka, tawa shuru tayi bata ce komaiba yacigaba dacewa

"I married you for love... Ban taba son kowaba sai ke...."

"Lies!..." Tafada cikin husky voice,

"Ok..in baki yardaba I know what to do...zansa akawo ta..ta fada maki gaskiya abinda ke tsakanin mu... Please is nothing... Forgive me for not being truthful to you..."

"Stop... Talking... Liar..." Tafada cikin sanyin murya

"I hate you.. I regret knowing you... Ka gama da wancan ka saketa zaka dawo kaina ko?....Allah ya isa tsakani na da kai....kuma kazani I can't stay with the man I don't trust..." Salem hawaye kawai yake, baisan nemesis will caught up to him this soon ba,

"Am sorry.. But your words are hurting me.." Tana cikin kuka ta fashe da dariya

"Really?... Well welcome on board... You wanted to ruin my life.. Kuma wallahi letting me go zai fi maka sauki..."

"Please stop my love... am sorry.. bansan zaki dauki abun da zafi ba..da tuntuni na fada maki gaskiya..."

"Karya dai...please free me jare..." Ta fada tana tureshi da karfi, gefe daya ya koma yana hawaye baisan something very cute can be violent ba, kai ta hada da kwaiwa tacigaba da kuka. Ahankali ya mike ya hau saman bene, bedroom yashiga ya dauki wayanshi dake wurge kasa yayi dailing number pilot dake kan hanyan koma Nigeria, daman in yana abroad gidan iyayenshi ake maida jet in case zasu bukaceta, pilot na picking yafara cewa

"Go straight to abuja you will met majed...ka dauko min yarinyan da majed zai kaika wajen ta...and please be fast...its urgent"

"Yes sir..." Mutumin ya amsa mashi, Majed ya kira ya fada mashi ya shirya zai raka pilot wurin yarinyan nan.

Komawa yayi ya zauna bakin gado ya hada kai da kwaiwa yanzu babu Wanda ya tsana kaman Khalid, gani yake he's the cause of his predicament.

Yana barin wurin tawa tayi kokarin bude kofa amma kulle take, komawa tayi ta zauna kasa tana kuka, mami ta dinga kira tana bubbuga kafanta da kasa, sai ta tsinci kanta bata jin haushin auren sai sakin Sannan irin maganan dataji yana fada kan waya, jitayi cikin kankanin lokaci an cire mata son Salem, gani take daga shaidan babu Wanda ta tsana kaman Salem

โค๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’œโค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’š

ยฎzuwairat( ummu Maryam)

6โƒฃ3โƒฃ

๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ *alhamdulillah am becoming a celebrity ..nagodewa wacce ta hada pic din nan Allah ya saka da alkhairi.. Ko kadan raina bai bacci ba cos nasan ina da masoya thousands, kuma of course ni ba bahaushiya bace likewise am not a Yoruba, ai tun daga first novel dina na fadi am not hausa amma tunda an haifeni a garin Hausa har naiya reading and writing da Hausa alhamdulillah don ko come ban Iya da yarenaba....wacce ta hada pics din nan inayi maki godiya...da nayi niyyan rounding up wannan novel amma yanzu zan kara tsawonshi saboda nuna jin dadina for making me more popular... Love you* ๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹ *Hausa novel kam yanzu muka fara insha Allah don sai ya kaimu ga fin inda muke biizinillahi taala.*

Salem yafi minti ashirin sama Sannan ya sauko Ahankali kaman Mara lakka, har lokacin kanta kasa tana kuka ahankali ya karasa inda take

"Please baby change the clothe..kada sanyi ya kamaki..." Banza tayi dashi tacigaba da kukan ta on ko muryan shi batason ji,

"Please..." Yafada yana kokarin rike ta, fixge kanta tayi daga rikon shi ta mike har lokacin kayan jikin ta jike yake duk ya like mata ga jiki, Salem sai mamaki yake don tamkar baita da suka shigo gidan in peace bace, duk ta chanza in in less than two hours, hanyan stairs tayi Salem ya bi bayanta keeping his distance, tana shiga bedroom ta dauki wayanta, Fitowa tayi har lokacin tana kuka, hanyan down stairs tayi tana tana dailing number mami sai shessheka take, Salem sai bin bayanta yake kaman bodyguard, number mom na na picking ta fashe da sabon kuka

"Mami..," yafada tana kuka, hankalin Salem kara tashi yayi, kafin ta kara magana ya kwace wayan daga hannun ta ya kashe nan ma dukan shi ta farayi

"Wallahi ka bani wayata,..." Tafada tana dukan shi da hannu biyu, afusace ya wurgar da wayanta ta tarwatse, wurin wayan taje ta duka tana kuka don sam bai haduwa saboda yanda tayi kwasa2.

Mikewa tayi afusace ta shiga ciki bedroom din downstairs cima gyare yake amma bai kai na upstairs haduwa ba, kan gadon ta kwanta, dakin Salem ya shiga ya zauna bakin gadon

"Am sorry... Ko Allah anayiwa laifi kuma yana yafewa...wannan abubuwan da kike ba zai Sani in maidaki gida ko ince zan rabu dakeba....I promise mami babu saki tsakanina da ke cos I love you... Kuma yarinyan in question zata zo nan ta fada maki gaskiya tunda baki yarda da magana ta..." Tawa rufe kanta tayi da pillow yanda bazataji abinda yake cewa ba, magana Salem ya dingayi mata Ahankali cikin ruwan sanyi amma ko kadan bata jin shi. Sunfi hour daya aka daga baya Salem ya mike ya shiga bathroom yayi alwallah ya dawo ya fara sallah saida ya idar yaje inda take kwance, hannu ya dora bayanta kasancewan tayi rub da ciki kuma har lokacin bata bar kuka ba, buge mashi hannu tayi,

"Kije kiyi sallah..." Ya fada mata atakaice Sannan ya bar dakin, saida ya fita da kaman minti talatin Sannan ta mike tayi alwallah.

Salem kam yana falo ya rabka uban tagumi, don duk abun duniya tayi mashi tsaye, Allah Allah yake pilot ya zo da ameera ko in ta fada mata gaskiya alamarin komai zai wuce, baisan tana Iya rikice mashi hakaba ,

"Where is the love she has for me?..โ€ฆ why is over reacting?...." Door bell da ya fara ringing ya katse mashi tunani, jiki ba kwari ya yaje ya bude Mrs Samuel ce tsaye yana budewa ta rungume shi, shima rungume ta yayi for just a moment Sannan ya saketa, gaisuwa sukayi tashigo ciki don dama in yana nan sau uku take zuwa tayi breakfast, lunch da dinner,

"Where is your bride?...." Ta tambayeshi tana kallon yanda falon ya hargitse

"She's taking a nap..." Ya amsa mata atakaice daji kasan karya yake, kunsan turawa da bin diddigi, saida ta gama kallon koina Sannan tajuya gareshi

"Is everything alright?..." Salem dake zaune yayi tagumi ya daga red eyes dinshi ya kalli Matan da akalla zatayi 40 ya saki ajiyan zuciya,

"Sir you don't look alright...." Tafada tana karasawa inda yake zaune a bakin stairs

"I know ban haifeka ba amma INA da younger ones kaman ka....kanada kirki I don't want to see like this... Please share it with me..," ta fada tana zama gefen shi, hawaye Salem ya fara yana bata labarin haduwanshi da ameera da irin abubuwan datayi mashi da irin revenge daya taking kanta da yanda tawa ta Sani sai ya kara da cewa.

"And she's taking it badly..." Dan dukan shoulder shi tayi Sannan tace

"If I were in her shoe I will go and never comes back... You can't build a healthy relationships on lies...and that revenge you took on that girl is dangerous... What if something bad happens to her..." Cikin kuka Salem yace

"What am I going to do...I love my wife...I don't want to loose her..." Dafa kafandan shi tayi

"So now literally you have two wives...." Da sauri Salem ya girgiza mata kai

"I told you I have divorce her..."

"Does divorce work that way?..."

"Yes..."

"Hmmm...and do you think bringing her here will solve all this problems... Cos I don't think is a good idea..."

"I don't know... Am just confused..." Rike mashi hannu tayi

"Go and rest...."

"I can't... I need to calm my wife first.."

"No...you need to give her some free space..now she hates you and staying close to her will only make matter worst..kawai katafi sama ka kwanta...ko bakayi bacci ba just lie down... I will prepare something for you guys..." Salem bai kara cewa komaiba ya mike ya dan leka dakin da tawa take gani yayi tana zaune kan praying carpet tana kuka, maida kofan yayi ya kulle Sannan ya hau upstairs ya shiga bedroom ya kwanta yana kallon agogon, yasan zuwa ten na dare pilot zai dawo da Aisha.

Abangaren Khalid kam yana ganin message din Salem ya daka tsale yana rawa koda Salem ya sake kiranshu yaji kama Salem na ihu baki ya tabe

"Chan Ku gane..." Yafada yana jona wayanshi da computer don printing message din. Saida ya gama ya fiddo takardan ya linka ta ya ajiye agogon hannun shi ya kalla

"Kai anya zan Iya zuwa abuja yanzu kuma in jira har agent dinshi ya rakani kauyen da wancan shegen ya ya ajiye har mutane?..." Dan girgiza kai yayi

"Zan bari sai gobe..first thing in the morning zantafi..." Ya kara fadawa kanshi yana daukan takardan daga katon falon dayake.

๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค

Abangaren ameera tana zaune tana jiran takardan ta har magrub, taji shuru har ishai bataji daga gareshi ba komawa tayi ta kwanta tare da fidda ran tafiya

"Kilan ma ya manta dani..." Ta fadawa Zainabu

"Kiyi hakuri.. Kilan zuwa gobe zaa kawo maki...ko kuma ya fasa baki takardan.. " Dan baki ameera ta tabe, bata kara cewa komaiba ta kwanta har lokacin bata ci wani abun kirki ba don da kyar hinde ta samu tasha tea.

Around 9: 15 tana kwance har ta fara bacci su kuma hinde sun kurawa TV ido as usual cos gen kunne yake sai sukaji kaman karan wani Abu waje, da gudu suka fita chan waje banda ameera dake bacci, Zainabu na ganin jet kofan gidan kasancewan da akwai babban fili wajen, da gudu ta koma cikin gida tana cewa

"Yazo...yazo...ameera tashi yazo ..." Cikin bacci ta farka tare da dafa kirjinta don ba karamin faduwa gaban ta yayiba. Da sauri ta mike zaune tare da daukan dankwalinta ta daura tana sauraron shigowanshi. Baa dadabe majed ya shigo da sallama nan ya fadawa ameera ance ta taho zaa kaita gida, yayi mata karya, wani sanyi taji cikin ranta nan fa hinde da family dinta suka fara kuka itama ameera kuka tafarayi don kamar kar ta tafi takeji,

"Zanzo ganin Ku..," ta fada masu tana kuka Sannan ta warware dankwalin ta ta rufe kanta dashi ta fito ta shiga cikin jet har lokacin bata bar kuka ba. 9:30 daidai jet ya tashi.

๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค

Salem kam koda ya kwanta baiyi bacci ba cos tunanin yanda zai shawo kanmatarshi kawai yake, har lokacin asar yana nan kwance bakinshi ya kurkure yayi sallah yana gamawa Mrs Samuel ta kirashi ta fada mashi food is ready ce mata yayi ta kira matarshi inta fito tayi mashi magana,

Tawa k tana nan zaune kan praying mat har lokacin asar kuma har lokacin bata bar kuka ba don idanuwanta sun kumbura ba kadan ba itama sallah tayi takoma ta zauna still kan praying mat ta cigaba da kukanta tana jin an bude kofa tayi tunanin salemne don haka ko kallon kofan batayiba ta cigaba da kuka ta kanta cikin kwaiwanta,

"Excuse me ma'am..." Taji an fada mata, da sauri ta daga kanta tare da goge hawaye, introduction Mrs Samuel tayi Sannan ta kara dacewa

"Food is ready..."

"Am OK.." Ta fada mata cikin voice dinta da bai fitowa sosai. Mrs Samuel komawa tayi ta sanar da Salem abinda tace, shima Salem gyara kwanciya shi yayi bai je cin abinci ba

๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’›โค๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ

ยฎzuwairat( ummu Maryam)

6โƒฃ4โƒฃ

*The more enemies you have the more you progress.. Makiya kaman fertilizer suke they make you grow fast* ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ๐Ÿ’ƒ

Har magrub babu Wanda yasha ruwa cikin su, Salem bai kara komawa inda take ba, duk idanuwanshi sun koma kaman garwashi don yanda sukayi ja, har party da friends dinshi sukayi mashi organising aka fasa, sai yanzu yasan ba kowa ke daukan simple mistake likely ba, he hates himself, he wish he can turn back the hands of time da bai boye mata komai ba

"Gosh..." Ya fada yana juyawa kan gado, kallon flowers dake kan gadon yayi

"I wanted this night to be memorable... I never see this coming.." Ya fada kanshi. Yana nan yana sake2 har lokacin sallah ishai tayi. Wanka ya shiga ya fito tare da alwallah. Sallah yayi yana idarwa Mrs Samuel ta kara kiranshi kan food is ready, Ahankali ya mike ya fita falon shi Sannan ya sauka down stairs.

Tawakam tunda ta zauna gurin batashi ba sai lokacin sallan magrub ta shiga bathroom ta sake alwallah tayi sallah da kyar idanuwanta ke buduwa saboda kuka rabonta da abinci tun Wanda shuwa ta bata da safe amma abun mamaki ko kishin ruwa bataji don gani take ko ruwa bata Iya hadiyewa, salivanta ma is bitter, sai ajiyan zuciya kawai take, she can believe somebody you love so much can turn into somebody you hate in just an instance tana zaune har sallan ishai tana idarwa ta kwanta nan kasan carpet, lokacin ba kuka take ba amma sai shessheka take, dana sanin rashin jin magana mami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login