Showing 33001 words to 36000 words out of 145230 words

Chapter 12 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

272

mahaukaciya nace inaso kema zaki sota..." Dan goge hawayen fuskanshi yayi sannan yacigaba dacewa

"Umma ban taba ketara umarnin kiba...banson karanta doctor kika yi forcing dina..I never complaint.. Banson karatu a Europe..har na samu admission a Oxford Amman kika ce dole sai peacock still I don't complain... Umma banason rayuwa a Nigeria Amman kika yi forcing dina na zauna...you choose friends for me...You choose everything for me...but am not going to let you choose my life partner...no problem tunda kinfi son family fiye dani...Amman let me make one thing crystal clear... Nobody will stop me from marrying Tawakaltu.. I love her and she's my choice.." Yana kaiwa nan ya fice daga cikin dakin

"Salem come back here now" Umma ta fada a tsawace , Amman bai juyawa ba yacigaba da tafiya, hannu yasa cikin aljihunshi yafara Neman wayoyinshi Amman bai gansuba, tsakar gidan ya tsaya ya kwallawa pilot dinshi kira sai ga guy din ya fito daga cikin wani party da gudu

"Get your things.. We are leaving.. Kuma check if my phones are in the jet" Da sauri guy din ya koma ciki ya shirya cikin sauri, shima Salem part din abbanshi ya koma ya gayamashi yanda sukayi da Umma sannan ya kara dacewa

"So Abba zan wuce abuja..I will call you"

"Amman I wish you can stay more" Abba ya fada mashi, ban kwana sukayi sannan ya fito, direct cikin jet ya wuce ya zauna sai yaga Ashe nan ya bar wayoyinshi, family phone ya dauka sai yaga 46 miss calls. Budewa yayi yaga duka tawace ta kirashi, lumshe idanuwa yayi wasu sabbin hawaye na taruwa idanuwanshi, pilot din tada jet din yayi.

Umma najin antada jet ta fito da sauri, kafin ta fito waje har sun tashi sama, ranta kara baci yayi

"Wace yarinya CE dana yakeson fifita ta kaina?..Salem always obeys me...dole in san yarinyan" tafada sannan ta koma ciki rai bace, Abba yana kallon ta ta window, Abba irin mutanen nan ne masu sanyi don Umma kadai ke making 80% of the family decisions, don ko kannen Salem biyu ita ta zaba masu miji.

"Sir where are we going?" Pilot ya tambayeshi

"Abuja" ya amsa mashi har lokacin muryan shi bai dawo daidai, waya ya daga zai kira tawa Amman yasan daya kirata zatasan da abinda ke damunshi, dole ya ajiye wayan, baiyi 15 second da ajiyewa ba tafara ringing, dubawa yayi yaga itace, dan murmushi yayi sannan yayi gyaran murya yayi picking

" my choice how far?", wani irin ajiyan zuciya yaji tayi

"Ya akayine?" Ya sake tambayan ta, ahankali tace

"Wallahi oremi hankalina ya tashi, tundazu inata kiranka ba amsa..so..."

"Sai kikayi tunanin na mutu..? Dariya tayi, yacigaba dacewa

" in wani abu ya sameni ya kenan" ahankali tace

"Sai in kashe kaina...I can imagine life with you.." Salem lumshe idanuwa yayi

"I love you.. And no obstacles will stand in the way of our love.." Yafada muryan shi na rawa

"Oremi what's the problem?" Dan daria karfi hali yayi

"Haba habibty ban fi karfin oremi wajen kiba?...Gaskiya ki chanzamin suna" yafada don ta bar maganan

"Ifemi...what's the problem..your voice is down" darian karfi hali ya karayi

"What's the meaning of ifemi" shuru tayi for a moment sannan tace

"Abin sirrine"

"Please tell me"

"I said sirri ne..har yanzu baka fada min abinda ke damunka ba" ahankali yace

"Missing dinki nake..my choice in har ban samekiba. Zan hadiye zuciya in mutu.."

"Hmmm"

"Is that all you could say...hmmm?" Daria tayi

"To me kakeso ince...anyway yasu first love da sauran yan gidan?"

"Suna lafiya..habibty anya zan Iya kaiwa Monday ban ganiba..yau Friday and am missing you die.."

"Nima jinake kaman nayi wata ban gankaba"

"Zan dawo gobe..."

"Aa...kar ka dawo..wahalan zama mota zaiyi maka yawa..sannan su first love zasu iya fushi da kai..."

"Alright.. Zan kiraki later"

"OK...bye" kiss yayi blowing cikin wayan sannan ya katse wayan.

Relaxing yayi yana tunanin abin duniya.

Suna zuwa abuja yayi sallan magrub, sannan ya koma gida, sai yaga Sam gidan baya yi mashi dadi,gidan sai yayi mashi mugun girma,

"Allah kabani tawa ta shikamin gidan nan da joy and happiness.."

Guys dinshi murna wurin su baa magana. Amman Salem baibi ta Kansu ba. Direct bedroom dinshi yawuce ya kwanta yana tunanin maganan Umma.

Yauma kusan kwana sukayi suna waya da tawa, duk yanda yaso tawa ta fada mashi maanan ifemi ki tayi, wani manager dinshi ya kira ya tambayeshi meye ifemi sai mutumin ya gayamashi my love kasancewan mitumin Yoruba ne.

Wacegari Saturday yaso yayi surprising tawa ya koma Kano don kwata2 abuja batayi mashi dadi Amman sai ya tunani yau zaa kawo ameera, tunda wuri agent dinshi ya rakashi ya gano gidan, yafi minti 30 yana daria don exactly yanda yakeson gidan haka yake, don ko cement baa shafa cikin gidan ba, kuma dubawa yayi yaga anzuba dukan abubuwan daya ce azuba, wani gefen gidan ya kalla yaga itace lode da murhu, wani sabon daria ya karayi, kallon agent din yayi

"Kasamo min guys guda biyu suyi guarding gate din nan.. And make sure you get them before 4pm"

"Yes sir"

๐Ÿ’™๐Ÿ’›โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’š

๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’›โค

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›โค

ยฎzuwairat(ummu maryam )

2โƒฃ5โƒฃ

Yau Friday da misalin karfe biyu aka daura auren ameera da Salem kan sadakin 100k Wanda dad dinta ne ya bada, duk wurin babu wani dangin ango ko daya amma still wurin ya shika sosai, Amman yan gulma sai magana suke wai aure ba dangin ango ko daya acikinsu har yanuwan dad wanda basu shiri, shikam dad cewa yake

"Yan bakin ciki saidai Ku mutu"

Around 4pm jet yaisa gidansu ameera, yan gidan baki suka bude suna kallon ikon Allah, ameera tasha gayu cikin Arabian gown mai duwatsu from head to toe, tana wurin mom tana bata shawara kan zaman aure Amman tanajin ance jet yazo babu kunya babu tsoron Allah ta mike, kallon mamaki mom tayi mata

"Saurin meye haka?" Mom ta tambayeta, karaf anty Sadiya dake gefen ameera tace

"Ki kyaleta...ta biye maki dare yayi masu?..ki tunafa Lagos zasu daga nan su wuce" haka anty Sadiya ta rike mata hannu ta fidda ta daga cikin dakin. Wani daki suka shiga sai sauri take ta hada mata wani Maganin jaraban ta bata, kafa kai tayi ta shanye, sannan suka fita wajen jet, agaban jet Abdul da pilot ne sai aka budewa ameera bayan ta zauna, Abdul kallon ta yayi ta cikin madubi

"Anya wannan kyau sir yana Iya aikata abinda yayi niyyan kusa?" Yafada cikin ranshi. Mutane sai bye sukewa ameera Amman don girma kai ko kallon inda suke bata yiba, bakin kofan affan ya tsaya daga nesa, suna hada ido da ameera sai yayi mata gwalo, nace affan ko kasan abinda zai faru ne. Pilot daga jet yayi sakuyi sama.

Mom dake kallo ta window ta fashe da kuka, don tamkar ta yarda yarta takeji gashi bata da bakin magana.

Baa bata lokaci ba sukazo gidan Salem na Kano akayi landing, ameera sai kallon ikon Allah take don atunaninta straight to lasgidi, su Abdul na fitowa suka bude mata kofa ta fito, gaban taxi dayayi ready yana jiran su shiga ayi gaba Abdul ya tafi ya bude mata, ameera tsayawa tayi kaman batasan abinda yake nufiba

"Ma'am ki shiga mu kara gaba..." Wani irin ashar ta saki tare da watsa mashi irritating look

"Kana haukane?.. Ya zaayi kace in hau wannan dirty..disgusting.. Crippy looking car" dan daria Abdul yayi

"Ma'am please ki shiga time is not on our side..muna da long journey ahead.." Ameera bata kalli inda yake ba koma ta zauna cikin jet sai lokacin ta tuna da bata dauki wayanta daga gidaba.

Abdul yafi minti ashirin yana magiya Amman banda zagi na uwa da uwa babu abinda takeyi mashi, shikam Abdul yasan da umarnin Salem zaibi da tuni an wuce wurin don cewa yayi

"Drag her ass to abuja" Amman Sam Abdul bayason taba Matan da ba nashiba, komawa yayi cikin motan ya dauki wayan shi ya kira Salem

"What?" Salem ya ce mashi sanda yayi picking

"Sir she is not cooperating"

"What do you mean" ya tambayeshi, ahankali Abdul yace

"Sir taki shiga taxi..." Bai idaba yaji Salem nacewa

"Who the fuck give you the order of asking her?..Abdul kafara ketara umarni na ko?..in baka kiyayeniba zaka rasa aikinka...and don't forget to come along with the makeup artist" yana kaiwa nan ya katse wayanshi.

Ahankali Abdul yafito daga cikin motan ya nufi inda ameera ta kame cikin jet kaman na ubanta yace."ma'am Dan Allah kiyi hakuri ki fito mutafi...sir yana chan yana jiranki...babu mai cikin jet..kuma nan da hour 4 jirginku zai tashi... Please we have to go" ameera zama tayi kaman mai tunani sannan tace

"Ka sake wani motan don kallon wannan motan yana sani jin amai.." Dan tabe baki Abdul yayi Amman bai bari ta ganiba

"Kiyi hakuri ranki ya Dade, dukkan motocin suna abuja kuma babu time da zaa zo daga abuja daukanki..please muje kar sir ya koreni daga aiki" yakara yi mata wani karyan.

"Ai hakan zai fi cos you look worthless" tafada tana fitowa daga cikin jet, bakin motan ta tsaya tana jiran abdul ya bude mata, babu musu ya bude mata ta shiga sannan ya maida ta rufe.

Shiga Yayi gaban motan yatafara tuki sannan yace

"Ma'am kiyi hakuri zan dauki pilot din dazai yi tukin jirgin" ya kara dapka mata wani karyan.

"Go to hell its not my business kawai take me to my husband" shidai baice komaiba ya jata suka tafi yabi ta gidan makeup artist ya daukeshi, shima saida ya amshi rabonshi na zagi gurin ameera.

๐Ÿ’š๐Ÿ’›โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’™

Aranan kam tawa basu samu zamaba a restaurant saboda gari daya cika saboda bikin da ake, Allah Allah take ta amshi wayanta daga gurin shaji dake kusa dasu ta kira Salem tabashi labarin abinda ke faruwa, sai wajen karfe uku mutane suka Dan rage shagonsu ta amshi wayanta ta kunna, number Salem ta kira

"My angel meyasa number ki baya shiga tunda safe?" Salem ya fada,

"Wallahi ifemi badi da battery shine na kai chaji kuma tunda safe bamu zauna ba.." Ahankali Salem yace.

"Saboda me habibty"

"Hmmm...ifemi..dan former President yayi aure yau...kaji labarin auren?" Murmushi yayi.

"Ina talaka kammani zaiji labarin auren dan tsohon shugaban kasa?..."

"Ifemi ka bar cewa talaka kamka...ai talaka shine Wanda bashi da cin yau balle na gobe..."

"Hmm habibty you always know the right thing to say...yau kin gaji sosai kenan"

"Sosai.. Kaman inje in kwanta nakeji" Salem lumshe idanuwa yayi yana imagining dinta kwance kusa dashi

"Sorry my love..kin kusa daina wannan wahalan.. "

"Hmmm Allah yasa"

"yama sa"

"Saboda me kace haka?" Ta tambayeshi, Salem shuru yayi don ya rasa karyan da zai shirga mata, sai few seconds later yace

"Nayi mafarkin nidake cikin daula Mara iyaka..." Karaf itama tace

"Nima nasha irin wannan mafarkin."

"Wane iri kenan?" Ahankali tafara cewa

"Tuntuni nake mafarkin gani cikin wani babban gida" daria Salem yayi

"Allah ya maida maki shi gaskiya"

"Yadai maida mana" haka suka cigaba da hiransu har sanda madam ta kirata. Acikin ran Salem kam saiji yake inama tawace zaa kawo gidanshi yau da babu abinda zai hanashi angwancewa yau.

๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค๐Ÿ’™๐Ÿ’š

Sai goma saura su Abdul suka isa abuja, ameera har bacci tayi ta farka, Abdul kiran Salem yayi yasanar dashi isowansu, Abdul ya hadashi da agent dinshi yayi masu discription din inda zai kai ameera.

Duk kwatancen da agent din yayi wa Abdul bai ganeba, cos ba sanin garin yayi ba sosai, kuma wurin wajen garine, Salem ya kira.

Abangaren Salem kam ya kame kan wani kujera na alfarma yana jiran Abdul ya fada mashi ankai ameera, yana ganin kiran Abdul yayi picking

"Kun isa?"

"No sir..ban gane wurin ba.." Shuru Abdul yayi kaman mai tunani sannan yace.

"Ka kawota estate.. Ka kaita dakin baki, shikuma Artist din ka kawomin shi"

"Yes sir" ya katse wayanshi sannan ya mike ya tafi bedroom dinshi yayi kwanciyanshi.

10:50 suka isa gidan, yana shiga yayi parking ya bude mata mota tafito tana kallon gidan, dukda darene gidan kaman rana, don koina kal yake , ita amarya bude baki tayi tana kallon wannan aljannan duniya.

"Ma'am follow me" yace mata, kallon shi tayi kaman mai gani kashi sannan tabi bayan shi, wane part na gidan ya kaita yabude mata kofan,ameera kallonshi tayi

"Idiot does this place looks like an airport?"

"No ma'am.. Sir ne yace kin gaji abari sai gobe zaku wuce" tsaki taja

"Ina ogan"

"Zan kirashi yanzu"

"No entity kawai" tafada sannan tafara kallon wurin.. Abdul na fita ya saki ajiyan zuciya

"Na dai kusa gama aikina...duk ni najawa kaina wallahi" yafada lokacin daya iso wurin artist dake tsaye jikin mota yana karewa slim estate kallo,

"Muje " Abdul ya fada mashi sannan ya dauki bag dinshi sukayi mansion din Salem.

Kofan falo yabude suka shiga sannan yaisa bakin kofan bedroom yayi knocking, Salem daya fara bacci ya dauki wayanshi ya mike ya bude kofa ya fito sanye da three quarter tare da armless.

Baa bata lokaci ba guy din ya chanza mashi kamanni kaman yanda ya saba, fita sukayi, shikuma Salem yabi bayan su, yana tafiya cikin kasaita.

Ameera kara kwantawa tayi kanwani doguwar kujera, Sai matse kafafuwa take, Salem na budewa ya hangeta kwance, kara takawa yayi kusa daita ya kura mata ido

"Ga kyawun fuska Amman babu kyawun hali," yafada cikin ranshi, kallon yanda fuskanta ke kyali yayi sannan ya kalli kafanta sunsha nails ga leglace, kallon yanda take ta faman Matse kafafuwa yayi, hannu ya daga ya sharara mata wani mahaukacin mari, nan take tafarka tare da faduwa daga kujeran datake, hannunta kan cheeks dinta tafara karewa Wanda ya mareta kallo, gani tayi fuskanshi na Wanda ta taba mari Amman daga kwaiwanshi kasa tas

"Surprised?" Salem ya tambayeta hannuwanshi biyu cikin aljihunshi, har lokacin ameera bata dawo normal ba don gani take mafarki take, Dan dukan kanta tayi ko zata farka daga bacci, Salem daria yayi

"Do you think you are dreaming?... Well you are not.. This is reality" ameera kara ware idanuwa tayi

"Remember me?" Yafada yana kara tunkaran inda take, ameera ta fara ja da baya, tana tunanin abinda ke faruwa, ahankali tace

"Please WAYE kai" har lokacin hannunta na kan kumatunta

"The bitch can say please... Well am Salem Yusuf sulaiman" idanuwa tazaro

"Kaine ka taba zuwa gidanmu?" Daria Salem yayi

"Nine Wanda kika mara..nine Wanda kika watsawa ruwa a jiki...please in tambayeki meye cikin abinda kika watsa min" ameera kuka ta fara tana yarfe hannuwa, daria Salem ya karayi

"Why are you crying...answer my question.. I don't have all night" cikin kuka ameera ta fara cewa

"Pepper.." Da sauri tayi kneeling tana kuka ta cigaba dacewa

"Don Allah kayi..."

"Wato kin zuba min yaji don ki Kashe min ido kaman yanda kika kashewa maigadin gidan Ku ido"

"Don Allah kayi hakuri bansan kai bane.."

"Eh dakin san nine bakiyin haka..da kin boyemin halinki na gaskiya.."

"Wallahi sharin shaitan ne...ba halina bane" tafada tana kuka kaman ranta zai fita, daria Salem ya karayi

"Gaskiya ba halinki bane..Amman bakijin tsoron ki daga hannu ki mari Wanda ya girmeki..."

"Shaidan ne...please kayi hakuri"

"haba young lady it's too early to apologize.. Zan baki dama ki bada hakuri...Amman sai nan da shekara daya..." Yana kaiwa nan ya juya, da sauri ameera ta kama kafanshi

"Please forgive me.. Wallahi bazan karaba..." Bata idaba Salem yayi ball daita tayi rolling daga inda take, barin dakin yayi tare da jawo kafan. Ameera mikewa zaune tayi tana kuka, bayan kaman minti biyar ta goge hawayenta sannan tace

"Nasan with time zai huce..."kara kallon dakin tayi

" ko me zakayi min bazai hanani bearing Mrs Salem Yusuf ba"

๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค๐Ÿ’š๐Ÿ’™

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’™โค๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›

ยฎzuwairat(ummu maryam)

2โƒฃ6โƒฃ

Ameera komawa tayi tsaye tana kallon kofofin dake dakin, daya daga cikin dakin ta bude ta shiga ta ga wani katon gado dayasha expensive bedsheets, takawa tayi ta kwanta sai lokacin shaawa ya kara taso mata

"Kin cuceni anty Sadiya... Wayyo na shiga uku" tafada tana Kara matse kafafuwanta, shafa bedsheets din tayi tana cewa

"Ko abinda ke gidan nan yaisa debemin kewa...do what ever you want.. But am not letting you go" hamma tayi, sai lokacin ta tuna cewa rabonta da abinci tun pepper soup din nama da anty Sadiya ta bata tun safe shima na magani ne. Ji tayi cikin ta na ruri don yunwa, mikewa ta karayi

"Nasan baa rasa abinci cikin wannan katon gidan.." Bata karasaba wutan side din da take ya dauke, kamewa tayi waje daya tafara kuka don babu abinda ke sata cikin damuwa kaman duhu. Ahankali ta taka taje bakin window gani tayi dukan estate din da akwai wuta Amman banda inda take.

Salem yana komawa ya bada umarnin akashe wutan part din datake, zama yayi palour yana son jin muryan tawa, gashi bayason kiranta saboda tace mashi yau ta wahala wajen aiki. Zama yayi yana tunanin hanyan dazai tsayar da wahalan rayuwa tawa, bai gama tunanin ba tayi mashi flashing, kaman yana jira ya dauki wayan ya kirata

"Habibty bakiyi bacci ba?" Dan daria tayi

"Ifemi na kwanta Amman na kasa bacci.."

"Why? my choice"

"Saboda banji muryan ka da Daren nan ba...kasan kasaba min jin muryan ka ko wane dare...da in mami ta yimin tausa sai inyi bacci yanzu kam kotayimin ban iya bacci sai naji muryan ka.." Tunda ta fara magana Salem ke cije lower lip dinshi mussanman datace tausa, Dan daria yayi

"Ashe har tausa mami take yi maki?" "

"Eh mana...agajiye nake dawo wa daga wurin aiki.. In bata yimin ba ban iya bacci".

" kice INA da aiki kenan..don na kusa hutar da mami...tawan in fada maki wani abu? " ahankali tace

"Eh.."

"You are special.. You are lucky....kinsan tunda nayi kissing dinki ban bar jin bakinki cikin nawaba?..."

"Zaka fara ko?" Da sauri Salem yace.

"No please.. Am just

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login