Showing 45001 words to 48000 words out of 145230 words

Chapter 16 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

250

tsale tayi tana ihu ta fada jikin mami, mami mikar daita tayi tafara rawa

"Wayyo Allah na..alhamdulillah.. Alhamdulillah.. Alhamdulillah" tawa ta dinga maimaitawa,

"Mami..Allah yaamshi aduan mu..Allah yashare min hawaye na.." Tana fadan haka ta fara kuka, mami rungume ta tayi itama ta fara kuka

"Mami in karya ne fa?..mami in karyane sun dauki alhakina..." Girgiza mata kai mami tayi

"Insha Allah.. Babu karya cikin wannan maganan"

"Mami ya zanyi inje abuja..ban san kowa abuja ba..." Bata gama magana ba wayan ta yafara ringing tana dubawa taga Salem, da sauri ta dauka, zatayi magana Salem yayi saurin cewa

"Habibty abuja zani..Abdul zai shigaba da zuwa amsan abinci..." Tana exaggerating tace

"Me zakayi abuja?"

"Wani abokina ne Mtn sukayiwa kyauta shi...." Bai karasaba ta ce

"Sir nima yanzu aka kirani" tafada tana daka tsalle,da sauri Salem yace

"Me akayi naji kaman you are rejoicing?"

"Sir Mtn sunce sun bani 25m da...." Wani irin ihu Salem yayi kaman baisan abinda ke faruwa ba

"Habibty am happy for you..you are such a good person and Allah have reward you" har lokacin tawa bata bar tsalle ba

"So when are you redeeming your price?" Ya tambayeta, shuru tayi for a while sannan tace

"Kuma Mtn office sin zaku?"

"Yes..nan da hour daya zamu tafi da abokina don cewa sukayi yazo kafin su rufe"

"OK bari inyiwa mami magana zan kiraka"

"OK" yafada yana murmushi.

Tawa komawa tayi jikin mami tana cewa

"Mami wannan mutumin mai zuwa nan "

"Eh"

"Shima yanzu nan zai kai abokinshi abuja amso kyautan" mamaki ne ya kama mami

"Ashe suma sun samu"

"Eh..yanzu mami ya zaayi in he abuja?"

Mami shuru tayi

"Ko zaki bisu?" Mami ta tambayeta, ido ta zaro

"Mami yaufa zasu tafi"

"To ya kikeso?..so kike ke kadai kije?... Tunda chan zasu kawai ki bisu..and kinsan cewa bani da lafiya da zan bikI" tawa shuru tayi tana tunanin abinyi...don ko kadan batason ta kadaita da Salem ko kadan

"Mami sunce sai gobe zasu dawo...INA zan kwana?"

"Ki kirashi kiji inda zasu kwana mana" tawa kiran Salem tayi bayan yayi picking tace

"Sir inkuje abuja INA zaku kwana?" Mami ta kasa kunne don taji abinda Salem zaice

"Gidan brother na zamu kwana"

"Yana da family?"

"Eh mana..yana da yara da maranshi biyu" tawa kallon mami tayi, ahankali mami tace mata

"Tell him Zaki bisu" ahankali tawa tace

"Sir..In motan bai cika ba zanbiku" Salem runtse idanuwa yayi don dadi

"Mami zata amince?"

"Eh..ita tace in biku"

"OK..to ki shirya ..nan da 30 minutes zanzo daukan ki..kinsan abuja da akwai nisa.." Da sauri tawa ta kashe wayan ta shiga wanka, mami kuma na shirya mata bag sin dazatayi tafiya dashi.

Salem mikewa yayi yana cewa

"Lokaci yayi da ZAKISAN KONI WAYE" Abdul ya kira, yana zuwa yace

"Pack my things.. Yau zan bar Kano" Abdul zaiyi magana Salem yajuya ya koma dakin shi yana balla button din riganshi,Abdul dinshi yayi ya fiddo kayan dake cikin wardrobe, Salem kallon shi yayi

"Me zakayi dasu?"

"Sir cewa kayi I should pack your things"

"Banda kaya..just pack my shoes, wristwatches, perfumes da sauran important things"

"OK sir" cikin 10 minutes Abdul ya gama cika Nike traveling bag da Salem accessories, shima Salem designer polo shirt da jean ya saka, Abdul fitowa yayi da bag zai saka cikin jet Salem yayi mashi umarnin ya sakasu bayan taxi, babu musu ya sakasu

"Ka kulle koina ka fito mu tafi" yabawa Abdul umarni. Babu musu ya kulle ya dawo gefen Salem dake zaune a driver seat ya zauna, sai tunanin abinda ke faruwa yake, gashi babu dama yayi tambaya

"Sir what about the jet?"

"Zansa pilot yazo daukan shi" ya amsa mashi sannan ya tada motan suka bar gidan bayan Abdul ya kulle gate.

Da sauri tawa tafito daga bathroom, without wasting of time ta shirya cikin wrapper skirt and blouse, powder ta shafa sai kwali tare da wet lips,

"Tawa"

"Yes mami"

"Ki kula da kanki...don't let anything happen to you.. Kisan Allah yana kallon ki..kuma dakin dawo saina dubaki" Dan daria tawa tayi

"Mami don't worry...insha Allah nobody is going into my pant"

"Nadai fada maki..yanzu ya zamuyi da abincin mutumin?"

"Sir Salem yace zai aiki wani daukan abincin.. "

"Ga dubu goma cikin kudin jiya..ki rike in case zaki bukaci wani abu"

"Thank ma" tafada tareda amsan kudin, wayanta yafara ringing ta dauka

"Habibty ki fito mu tafi time is not on our side" yafada sannan ya katse wayan,

"Mami yazo" mikewa tayi ta dauki Vail dinta, itama mami bin bayan ta tayi da bag din da ta shirya mata. Suna fitowa waje Salem yayi sauri fitowa ya gaida mami, bayan ta amsa tace

"Please take care of my daughter.."

"Yes ma"

"Ka tuka motan ahankali"

"Insha Allah" jikkan hannun mami ya amsa, itakuma mami hugging tawa tayi tare dayimata kiss sannan tayi mata bye.

Tawa bayan motan ta bude ta zauna, Salem sai kallon lustrous lips dinta ta mirror yake. Suna Zuwa zoo road yayi parking

"Alh Abdul kazo ka amshi motan don hannuna ciwo yakeyi min"

๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’›โค๐Ÿ’š

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’™๐Ÿ’›โค๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

ยฎzuwairat(ummu maryam)

3โƒฃ2โƒฃ

Baya ya dawo kusa da tawa ya Abdul gaba shi kadai, kallon shi tayi don shigan shi na yau ya sha different da sauran dressing da yakeyi, ita atunaninta don zaiyi tafiya ne, dan kallon shi takarayi, shima ya kalleta suka hada ido tare da sakarwa juna murmushi,

"Habibty sorry for boarding you with my personal problem.." Dan murmushi tayi batare data kalleshi ba

"Don't mind ...what are friends for" Dan harara ta yayi

"Ni friend dinki ne?..kodan yanzu kinzama millionaire kike..."

"Please.. I don't mean it that way"

"Apologies accepted" juya zamanshi yayi yana fuskantanta

"Miss..let me interview you..me zakiyi da 25m?" Tawa shuru tayi kaman mai tunani

"Gaskiya I don't want to get my hopes up..zan jira sai da gaske ne cos har yanzu ban yardaba" dan murmushi Salem yayi yana tunanin

"Come on..you are rich already" azahiri yace

"Just kiyi tunanin an baki kudin yanzu...me zakiyi dashi?" Lumshe idanuwa tayi sannan ta fara cewa

"First of all zan fara kai mami hospital.." Surprisedly Salem yace

"Is mami sick?" Ahankali tace

"Yeah..tana da chronic asthma...".

" oh sorry.. Then what next?"

"Then I will open a medium supermarket for mami da yaran da zasu dinga taimaka mata..." Kallon shi tayi tadan sakar mashi murmushi

"And zan baka 3m kafara business.." Baki Salem yabude kaman yana murna

"Are you kidding me?" Girgiza mashi kai tayi

"Am serious" Abdul dake sauraronsu yayi murmushi yana tunanin

"Nima kabani mai sona don Allah koda iyamurace" Salem yace

"Amman habibty I will be the happiest man on earth.. With 3m I can make it"

"Insha Allah"

"Then what next..."

"I will go to school"

"And"

"Shikenan" kallon mamaki Salem yayi mata

"Baki gamaba..continue"

"Shikenan nidai" tsaya kallon ta yayi

"Banji kinyi maganan auren mu ba" tawa murmushi tayi

"Aure a wannan stage din?..nifa adolescent ce.. Ba yanzu zanyi aureba"

"Waike meyasa da anyi maki maganan aure sai kice you are a child"

"Karya nayi?"

"Hmmm.. Habibty many of your age are married with a child or children"

"Hausawa kenan..mu bamu haka" Salem kauda kanshi gefe yayi tare da daure fuska kaman bai taba daria ba, kara kallon ta yayi

"Amman habibty baki sona kaman yanda nake sonki..if you love me you will want to be with me" tawa dai shuru tayi batace komaiba, haka suka cigaba da tafiya babu Wanda ya cewa Dan uwansa magana, Salem sai kallon ta yake, itakam relaxing tayi tana lumshe idanuwa, tunanin abubuwa da dama cikin ranta.

Wayan shi yafara ringing, dan murmushi yayi don yasan Umma ce, for the first time ya fiddo wayan shi gaban tawa,

"My wonderful first love.." Cikin fada Umma tace

"Wai kana ina ne?" Pretending yayi kaman bai san plan dinta ba

"Umma INA Kano"

"To..inason kaje gidan Hajiya ummi ka amsomin wani abu" ahankali yace

"Umma ina kan hanyan abuja..na gama abinda nake Kano" Umma katse wayan ta tayi, itakam tawa kurawa wayan ido tayi don wayan kaman glass yake, sannan statement dinshi na karshe ya tsaya mata arai, shikam bai kalleta ba yayi dailing number majeed, bayan yayi picking Salem ya

"Alh clean the mansion next to mine...and get a wonderful ready made dress..medium size..tell the cook to prepare something fascinating" daga chan bangaren majed yace

"Sir su FINA da mima sunyi decorations agidan wai zasuyi celebrating birthday dinka..."

"If I find anything disliking you all are fired" tawa kasa kunne tayi tana jin abinda yake cewa, tunda take bata taba jin muryan shi so commanding ba,

"Who is this man..he talks as if he's the boss" tafada cikin ranta, tsoro ne ya fara kamata, ahankali tace

"Sir ina abokinka da zamu tare dashi?" Salem kallon ta yayi don yasan many things will be going through her head right now, kuma da gangan yakeson bata hint don bayason tazama too speechless in sun isa abuja

"Habibty gashi nan yana tuki" da sauri ta kalleshi

"Amman kuma dazun you said shi zaizo daukan abinci.."

"Smart gal" yafada cikin ranshi

"Ni nace maki haka?" Kai ta daga mashi at the same time tsoro da bayyana fuskanta

"Ni ba haka nace ba..I said abar abinci yau tunda zan raka abokina abuja" tawa Dan girgiza kai tayi

"Ba haka kace min ba"

"Habibty banajin dadi in kina kiran makaryaci" ahankali tace

"Sorry" daria yayi, kallon yanda ta saka hannuwanta cikin cinyanta yayi, hannunta ya kara kallon yaga still gashin kwance a hannunta,

"Hmmm..wonders shall never end" yafada cikin ranshi,

"Habibty do you trust me?" Ahankali ta daga mashi kai Amman ba dan ta amince dashi ba

"Then relax"

๐Ÿ’šโค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’™

Ameera saida taci kukanta ta koshi sannan bacci yayi gaba daita, hinde kam tana tsakar gida tana aiki, Dan wake ta kwaba, dataga yayi yawa taje gidanta ta dauko katon tukunya ta Dora dashi, sai wajen 11 yayi ready, itakuma ameera sai 11:30 ta tashi tana fitowa taga hinde na soya man da zaaci dashi, kallon katon tukunya tayi

"Me akayi da wannan?" Tafada tana nuna tukunyan

"Yata.. "

"Please ki bar cemin yarki..sunana Aisha..ko ki kirani da ameera"

"To..ameera Dana kwaba Dan wake naga tukunya yayi kadan shine na dauko tawa daga gida"

"Thats the problem with low class.. Give them an inci they will take a mile" tafada kasan makocinta

"Do you mean danwake kikayi?"

Tafada tana karasaba wajen bokitin da ta tsani danwake aciki

"Eh" ameera dubawa tayi

"Kan buhun ubanan..wazai ci wannan abun da yake kama da kashin akuya?...gaskiya bazan ci ba..sannan nasan wannan tukunya da kika dafa abinci dashi ya dade baiga sabulu ba"

"Yanzu me zan dafa maki" dan tsaki taja

"Dauko tukunya ki koya min jelof din taliya" da sauri hinde ta sauke man kan wuta sannan ta shiga kitchen ta dauko tukunya

"Zakiyi da daddawa ko?...don yafi dadi" harara ta balla mata

"Shiyasa kuke wari... Stupid baboon.. Kiyi sauri ki kai wancan kazantan gidanki kizo" tafada tana nuna mata bokitin danwaken, hinde cikin gudu2 tafita dashi don yau take sallah gidanta.

Bata dadeba ta dawo suka dora abinci, cikin 40 minutes suka dafa taliya mai romo, ameera ci tayi cos she don't have any choice.

"Ni zan tafi" inji hinde

"Please karki tafi yanzu..this loneliness is killing me" shuru hinde tayi for a moment

"To wani Abu zanyi maki?" Ameera shuru tayi don tanajin kunyan abinda takeson cewa, kaman an tsunkureta tace

"Dan Allah idan mutum yasha kayan mata yayi yawa meye maganinta" hinde tsaya kallon ta tayi, saitaji ta tausayawa mata

"Ke ba Matan aure bace?" Kwalla na taruwa Idonta

"Eh...ni Matan aurece"

"To ki kwanta da mijinki..sai kisamu biyan bukatanshi shima ya biya naki..."

"Banda wannan.. Gayamin wata hanyan"

"Gaskiya ban San wata hanyaba" tsaki taja

"To kije gida ki ci abinci sai ki dawo ki tayani wuni"

"Shikenan"

๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œโค๐Ÿ’š

Haka Abdul yacigaba da tuki, itakuma tawa banda tsoro babu abinda ke ranta, sau biyu mami na kiranta,

Sai to 7 suka shiga abuja, tawa sai lulumshe idanuwa take kaman mai jin bacci, Salem duk ya kasa daina kallonta, duk dagakan dazatayi saisun hada ido, wani irin kayataccen unguwa taga sun shiga, duk unguwan babu gidan mai karamin hali, gaban wani katon gate taga Abdul yafara horning, mai gadin fitowa yayi yana kallon motan, da sauri ya koma ciki ya bude gate, shiga Abdul yayi, gaban tawa mugun faruwa yayi don gidajen gidan tsoro suka bata, Salem sai kallon reactions dinta yake, da sauri ta matsa kusa da Salem, muryan ta na rawa tace

"Ife..inane nan?" Ahankali ya kama mata hannu

"Gidan brother na" itama rike hannunshi tayi gam, tawa cigaba da kallon wurin tayi tana juye2, Abdul parking yayi, da sauri guys 5 suka taho wurin motan, tawa kara rike mashi hannu tayi sosai

"Ife...who are this guys"

"He's bodyguards" budewa Salem motan sukayi don ya fita Amman tawa kara matsawa tayi kusa dashi tare da rikeshi sosai

"Ife...am are afraid...please let's go back" kallon fuskanta yayi yaga yanda eyes dinta suka fito don tsoro

"Habibty...calm down... Ko kinason in kaiki hotel?" Ido tazaro kaman zatayi kuka

"Ka maidani Kano...banason kudin" dariya Salem yayi, sai kara shisshige mashi take

"To ina family din brothern ka?" Cikin daria Salem yace

"Suna abroad..." Fashewa tayi da kuka

"Wallahi bazamu saukaba..ka maidani Kano.. Ko ka kaini wani gidan mai mutane" Salem kam sai daria yake

"Wayan nan ba mutane bane?" Su majed sai kallon juna suke,

"Ki bari mu fita sai in kaiki wurin neighbors dinsu" sai lokacin tabari ya fita, yana fita itama ta fito da sauri ta kara rike mashi hannu, duka guys gaida Salem sukayi cikin respect, amsawa yayi hannunshi cikin na tawa, itakuma sai boyewa take bayanshi don gani take kaman muggan mutane ne, part din dake kusa da dashi yayi daita, sai taka mashi kafa take don yanda ta shige mashi jikin, suna zuwa ya bude suka shiga , tawa kallon ikon Allah kawai take,

"Habibty ki shiga bathroom kiyi wanka sannan ki chanza kaya, kiyi sallan, dinner will be serve" rikeshi tayi sosai

"Wallahi baka barina nan wajen..." Sai

"Please stop... Ki zauna..babu abinda zai faru...besides ina nan..kawai zanje inyi wanka in chanza ne" cikin kuka tace

"Tsoro nakeji... Mutafi tare" kura mata ido yayi

"Mu tafi muyi wankan tare?" Da sauri ta girgiza mashi

"Then wait here..zansa akawo maki abinci..in kina bukatan wani abu.. Just call me" da kyar ya cire hannunta daga jikin shi ya fita, tawa kam sai kuka take don gani take yaune rananta na karshe aduniya.

Bayan fitanshi wani ya shigo ya jera mata abinci kan dinning, tana takure waje daya.

Shikuma Salem fita yayi yana jin wani irin dadi cikin ranshi don ji yake inama ace ya riga ya aureta

๐Ÿ’™๐Ÿ’œโค๐Ÿ’š๐Ÿ’›

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’œโค๐Ÿ’š๐Ÿ’›๐Ÿ’™

ยฎzuwairat(ummu maryam)

3โƒฃ3โƒฃ

Salem na komawa part dinshi ya goge fuskanshi sannan ya shiga wanka, yana gamawa yayi alwalla sannan ya fito sanye da jallabiya fari tas, fitowa yayi ya samu guys dinshi suna jiranshi su tafi masjid, shi kuma cook sai jera abinci kan grass carpet yake, kallon majed yayi

"Ka kaimata kayan danace ka sayo?"

"No..sir"

"Hurry ka kaimata sa samemu kan Hanya" majed part dinsu ya tafi ya dauki kayan

Tawa kam banda kuka babu abinda take yi , da taga kai ta kalli katon falon sai ta kara fashewa da kuka

"Wayyo.. Na aminta da yan yankan mutane" take ta fada cikin zuciyanta, wayanta ta dauka ta so kiran mami Amman tasan yin haka na nufin kashe maminta da kanta, kuka take taji an bude kofa, da sauri ta mike tsaye don gani take kaman wanda zai yankata ne ya shigo,

"Ma'am you dress" majed ya fada mata sannan ya ajiye kayan ya fita, yana fita takoma kasa inda take ta cigaba da kukanta.

Suna dawowa daga masjid direct inda aka jera abinci suka wuce suka fara cin abinci, Amman Salem babu abinda yake sai kallon side din da tawa take, kawai tunanin abinda zai faru yake, yana tunanin shin zata amshe shi cikin murna dukda ya boye mata koshi waye? Bai wani ci abincin kirki ba har lokacin sallan ishai yayi. Masjid suka koma sannan suka dawo, direct mansion din da tawa take ya nufa, yana zuwa ya rasa courage din shiga, duk sai ya rasa abinda zai fada mata, yafi minti biyar wajen sannan yayi karfin halin knocking, sau biyu yayi knocking dukda yasan ba response zai samuba, ahankali ya bude ya shiga, ganin ta yayi takure kusa da wani kujera tana kuka, tana ganinshi ta mike, kura mashi ido tadanyi tayi saurin dauke idonta tana tunanin kilan brother shi da yake magana ne

"Meyasa bakici abinci kiba?" Ya tambayeta ahankali, da sauri takara daga kai ta kalleshi

"Please take your bath, change, pray then eat..." Da sauri tace

"Please ina sir Salem?" Dan murmushi yayi

"Do what I said.. Zan gaya maki inda yake" Dan kura mashi ido tayi for a moment

"Please WAYE kai?".

" kije kiyi abinda nace ZAKISAN KONI WAYE " kuka tacigaba dayi

"Na koshi..nidai please ka Kiramin sir Salem" gani yayi kozai kwana rokonta ba zatayi abinda yake so ba, Ahankali yace

"Ifemi please eat..its your first time in my house" tawa tsaya kallonshi tayi, bako kiftawa

"Please" yakara cewa

"Please who are you?" Bai ce komaiba ya tunkareta, itakuma ta tsaya tana ganewa ko Salem dinta ne, bata ankaraba taji ya riketa ya zaunar daita kan kujera, shima zama yayi kusa daita,

"Ni Salem" da sauri ta girgiza kanta tare da matsawa baya

"Ba kai bane Salem dina" Dan murmushi jin dadi yayi

"Nine..I am Salem" deep down tana tunanin shine cos da idanuwa da muryan duk nashi,Amman she can believe Salem dinta is as handsome as the Arabs, runtse idanuwanta tayi tana girgiza kanta

"No..you are not" da sauri ya rike kanta

"Stop it habibty kanki zaiyi maki ciwo.. Nine Salem.. Its me

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login