Showing 120001 words to 123000 words out of 145230 words
nice.."
"To Allah ya shige mana gaba..."
"Ameen" ta amsa Sannan ta shiga dakinta, tana shiga wayanta ya fara ringing, sunan Wanda ta gani yasata sakin murmushi, picking tayi tare da sallama, daga chan bangaren Salem yace
"Babe ya kike?..."
"Lafiya lau...ya sis Tawakaltu?..."
"Tana lafiya...she's sleeping... Yasu affan?..."
"Duk suna lafiya..."
"That's good to hear... Meye labari?..." Ya tambayeta sounding naughty,
"Babu...labari" Dariya yayi
"Anya?... You sound as if you are lying..."
"Da gaske babu labari.."
"Nidai ki fadamin ko wani ya ganemin mata..." Dariya ameera tayi
"Wacce Matan kuma?..." Ahankali yace
"ke mana.." Ameera shuru tayi batace kala ba
"Kinyi shuru..." Ya fada ahankali
"Me zance?..."
"Ki fadamin mana in wani ya ganemin ke inyi Maganin shi..." Ahankali tace
"Aini ba matarka bace..." Dan Dariya yayi
"Ke matata ce mana...ko kin manta?.."
"Ni ba matarka bace..."
"You are my wife..." Yafada cikin whisper,
"Hmmm nidai Aa..."
"Daman nasan baki sona...amma you are still my wife... Na daya kina period when I divorced you... Na biyu ban taba fada maki saki nawa nayi maki ba I only told you na sakeki...." Ameera dai shuru tayi tana sauraron ikon Allah. Salem yacigaba dacewa
"Ke matata ce..."
"Please sir can we stop this conversation?..."
"Stop calling me sir...ai you are not working under me..."
"Naji..amma can we stop this conversation?..."
"Yes...for now...ki gaida min su momcy..."
"Zasuji..."
"Ki turomin account number dinki...let me send you some money in case zaki bukaci wani abun..."
"No thanks... Bana bukatan komai..."
"Bye then..." Ya fada Sannan ya katse wayan shi. Da sauri ta kara komawa wurin mom ta fada mashi abinda Salem yace.
"Just forget about him...yanason wannan yarinyan so ko da akwai aure a tsakanin Ku yanzu bazaiso ki yanda yake son matarshi ba...so fatana shine Allah ya baki Wanda zai soki fiye da yanda yake son matarshi..."
"Ameen... Mommy.." Ta fada Sannan ta kara komawa dakinta.
๐๐๐๐โค
ZAKISAN KONI WAYE
๐โค๐๐๐
ยฎzuwairat(ummu Maryam)
7โฃ3โฃ
Sultan kam har yanzu bai yarda ameera is a divorcรฉ ba, yana ganin zeenat ta dawo ya kirata har part dinshi na cikin gidan, tana zuwa ya kalleta
" sis please fadamin everything about ameera and her marriage... " kallon mamaki zeenat tayi mashi, cos tunda tasan wanta he never looks this serious on anything except for football,
"Yaya ai she's my friend kuma nayi mata alkawarin babu Wanda zan fadawa sanadiyan rabuwanta da slim..." Tafada tana Dan turo baki,
"Come on sis...ni ba wani bane...ai ba fada mata zanyi ba..." Yafada yana rike hands dinta, kallon shi tayi
"Yaya why the sudden interest in ameera.. Kodai..." Tafada tana daga mashi giranta, dungurin goshinta yayi
"Am I your mate?..." Da sauri ta girgiza mashi, Dan marairace fuska yayi
"Please tell me.. Zan chanza maki mota...that's if you tell me the whole truth..."
"Really?.." Ta tambayeshi sounding very excited
"Eh mana..." Cikin sanyin murya zeenat tace.
"But yaya she's my friend.. Babu kyau cin amanan Wanda ya aminta da kai...."
"Don't worry sis this won't take you to hell...just tell..."
"Yaya how did you know?..kasan ko INA gama fada maka in mutu yanzu nan...kaga na mutu munafuka..."
"Spare me the sermon and tell me... Please.." Atakaice da kyar sultan ya shawo kanta ta yarda ta fada mashi abinda ya faru tsakanin ameera da Salem #tagtruefriendship.
"Amma that guy is a jackass..." Sultan yafada, baki zeenat ta rike
"Yaya sir Salem din ne jackass?..."
"Ke bacemin da gani.." Ya daka mata tsawa, da sauri ta mike ta bar part dinshi, Dariya nayi nace kin gama gulma kuma an koreki amebo number one. Sultan zama yayi yana tunanin ameera, he's surprised by his sudden feeling for her, daman he's looking for a classy lady da zai aura, anashi tunanin bazai samu yarinyan da zatayi fitting international class dinshi that is why yaso auran Lizzy amma yanzu he knows Africa have the most beautiful and elegant woman, kuma from the story zeenat ta fada mashi it seems she's a virgin.
"Hmmm....can't wait wify..." Yafadawa kanshi yana murmushi, zaiso ya fadawa Abba amma ya fi karfin ace bai kulla soyayya da yarinya ba ya tura iyayenshi.
_A week later_
Around 4pm Tawakaltu ce zaune kan cinyan Salem, sanye take da wasu arnan Jordan half vest Sai wandonshi mai kama da pencil jeans, a wurin boobs dinta a rubuta Jordan Sai kuma baya wurin bombom dinta still an rubuta Jordan, tayi haske sosai amma fa ta rame, Sai cije lebe take,
"Sannu.." Salem yace mata, tunda safe take ciwon ciki Dana Mara, daman one week da gama period dinta akayi wedding dinsu, so she's expecting it, amma abinda ke bata mamaki shine wannan ciwon cikin, normally bata mestral cramp, kuma daman period dinta take jira ko ta huta da matsalan Salem dukda yanzu tafara Dan sabawa da halin shi amma still ba Sosaiba,
"Wayyo..." Tafada kaman zatayi kuka at the same time tana makale bayan wuyanshi da hannayenta dake zagaye ga shoulder dinshi,
"Sorry princess.. The doctor will soon be here..." Yafada yana shafa bayanta
"Ka dubani mana..." Tafada tana kokarin kuka
"Please bani da equipment... Kuma when it comes to you am vulnerable... Ki bari doc yazo...amma ina tunanin menstral cramp ne..." Cikin ciwo ta girgiza mashi kai
"Banayi....Kaine ka jamin ciwon... Ciki..." Salem dariya yayi
"Amma sorry kinji...." Kaman anyi pitching dinta ta rike cikinta, ta fara kuka
"Wayyo.. Cikina.. Mutuwa zanyi..." Tafada tana sauka daga kafan Salem, kasa ta sauka ta durkusa kaman maiyin sujjada ta rike cikin ta Sai kuka take, Salem komawa yayi wurin ta yacigaba dayi mata sannu, suna cikin haka akayi ringing bell, da sauri ya bude kofan wani young doc ya shigo, doc kallon yanda Tawakaltu ke kuka yi,
"I think she will need an ambulance..." Yafada yana kira hospital, ko minti goma baayiba ambulance yazo, tare sukaje hospital, har lokacin bata bar kuka ba duk hankali Salem ya tashi don da baidauki abun serious ba. Dukda yana doc bai bar turawan sun barshi ya shiga daita ba, daga waje ya tsaya, dube2 akayi mata, injections akayi mata bacci yayi gaba daita.
Thirty minutes later doc ya fito suka shiga office da Salem,
"Mr Salem your wife is three weeks pregnant... But right now bamu saniba ko zai zauna ko zai zube cos with any slitest mistake she can miscarried it..."
"I never see that coming...alhamdulillah..." Ya fada sounding extra excited,
"So doc...she will need a bed rest?..." Salem ya tambayi doc
"Exactly..." Doc ya amsa mashi,
"Then doc why is she having such abdominal pain?... Am a doc but not on such aspects.." Inji Salem
"The pain is as a result of the instability of the pregnancy... That's why I said with any small mis doing...she will miscarried it..." Salem dai shuru yayi saida doc ya kai aya Sannan yace
"What type of misdoing?..." Ya sake tambayan doc. Nan doc ya dinga lissafo mashi abubuwan da bazatayiba, ciki har da sex don shine yake ta maimaitawa especially rough one. Godiya yayi ya fita wurin cashier ya bada credit card akayi debiting. Shi har yanzu he can't believe he is becoming a father, bai bata lokaci ba ya shiga inda take, kallon ta yayi tana bacci hannuwanta biyu kan cikinta karasawa yayi ya dora hannun shi kan nata
"We're are becoming parents.." Yafada mata dukda baji takeba, yana nan tsaye wayanshi ta fara ringing, dasauri yayi picking don kar yayi waking dinta, gaisawa sukayi da Umma,
"Ina Tawakaltu?... Bata wayan..." Umma ta fada mashi, shuru yayi
"Bakaji nane?..."
"First love...Tawakaltu bata da lafiya.. Yanzu ma muna hospital..."
"Subhanallahi... Meke damunta?..." Salem shuru yayi,
"Kai banason wannan shuru da kakeyi... What's wrong with her?..."
"She's three weeks pregnant..." Yafada kaman an fixgi maganan daga bakinshi, kuda Umma ta farayi
"Alhamdulillah... Masha Allah.... Wow...so soon?... Kai alhamdulillah... Yanzu meye matsalarta?..."
"Ciwon ciki take..."
"That's bad...ka maido min ita mana..." Da sauri ya girgiza kai
"Ance she should not travel a long distance..."
"Ok...then take very good care of her..." Hira suka danyi Sannan sukayi sallama.
Kiss ya dinga jerawa sleeping face dinta yana cewa
"A child with Yoruba mother and a Hausa Fulani father... Awesome..." Yafada yana kissing cikin ta.
With in one week ameera da Khalid suka shaku sosai, suyi video call, chat, itadai ameera can't say she loves him amma she definitely likes him, he's funny, bai bata daman tunanin rayuwa, he make her feel like an angel, har yanzu bata bashi amsan da yake nema ba. Daman yace he will come for the answer in a week time kuma that is today, Visitors room tasa aka gyara suka dafa abinci kala2 don Khalid babu kunya cos ya fada mata ko breakfast bazaiyiba kafin ya bar yola, so ta ajiye mashi abinci, yana daga cikin abinda yasa ameera ke dan ji dashi, he's straight forward.
Kafin karfe biyu suka jera abinci cikin dakin saukan baki,. Sai karfe uku ya iso, yana ganinta yaga kaman ta kara kyau don yau ta danyi kwalliya, Sai kamshi ke tashi ta duk inda tabi, itama ba karamin kyawunshi ta gani cos shi da Salem Allah kadai yasan Wanda yafi wani kyau, dakin bakin ta kaishi bayan sun gaisa,
"Wai baki kaini in gaida su mom?.. Kafin in loda cikina?" Ya fada in a funny way, murmushi kawai tayi batace mashi komaiba.
Abinci yaci sosai kaman a gidansu, Sai bayan nan ya kura mata ido Sannan yace
"Nazo amsan amsata.." Yafada mata still staring at her like a mirror, shuru tayi for a moment kanta kasa
"Please you need to tell me if am accepted or not.." Dan murmushi tayi Sannan tace
"You don't know anything about me.. "
"I don't care...kin sace zuciya..."
"Kodani bazawarace?..."
"Yes" ya amsa mata without thinking about it cos he already knows
"Da gaske nake...na taba aure...."
"I don't care..ko sau goma kikayi aure...am in love with you... Please accept me..." Ya fada mata, har lokacin ameera tunanin inda ta sanshi kawai take
"You know what?..." Da sauri Khalid ya girgiza mata kai
"You look familiar...." Tafada mashi , murmushi yayi
"Am a social figure... Maybe Mun taba haduwa...forget about that and answer me.. Please"
"How can I accept the person I hardly know..."
"Don't worry you will know very thing you want to know about me..." Shuru tayi for almost minti biyar Sannan ta daga kanta ta kalleshi
"Accepted..." Tafada kanta kasa tana murmushi, Khalid relaxing yayi kan kujeran da yake zaune Sannan yace
"Alhamdulillah....naji dadi..I promise you will never regret this..." Dan gyara zama yayi
"So will you marry me?.." Ya tambayeta, kallon shi tayi
"Marriage tun yanzu?..."
"Yes mana...AI ba friendship nazo yi ba.."
"AI it's too early.. Let's get to know each other better..." Shuru Khalid yayi donshi har ga Allah bai taba jin yana son yayi aureba kaman yanzu
"If you say so...amma please kar ya dade... Am dying for you already..." Ameera Dariya tayi, hira suka cigaba dayi har lokacin sallan asar tayi, cikin bathroom dake wurin yashiga yayi ablution ya fito, tare suka fita compound da ameera, yabi masu gadinsu da affan suka tafi masjid, itakuma ta shiga ciki donyi sallah.
Bayan minti ashirin suka dawo, bai shiga dakin bakin ba ya zauna waje cikin canopy, yana zama ameera ta fito, nan suka zauna suka cigaba da hiran masoya, around 5pm wata Peugeot fractal ya shigo gidan,
"Dad ne ya dawo?.." Khalid ya tambayi ameera, lokacin da bugaggen motan ba tashigo ciki,
"No bashi bane.." Tafada tana kurawa motan ido don bata san mai irin motan ba kuma the car look extra classic, zeenat ce ta fito daga passenger seat, da sauri ameera ta mike tana murmushi, zeenat takowa tayi suka iso wurin juna, cikin whisper zeenat tace
"Babe wannan handsome guy fa?..."
"Shine Wanda na fada maki..." Itama ta fada yanda babu Wanda yaji.
"Woowww...Allah ya baki white blood... Kina samun handsome guys... " tafada tana dariya
"Tare muke da yaya sultan..."
"Allah?.."
"Wallahi"
"To muje ki gaisa da Khalid kafin yaya ya fito" inji ameera, karasawa sukayi wurin Khalid suka fara gaisawa da zeenat.
Sultan kam tunda ya shigo ya hangi ameera zaune da wani yaji kaman yajuya
"Yarinyan da bata fi one month da rabuwa da miji ba har ta fara Tara samari.." Yafada in a jealous tune. Zama yayi ya kasa fitowa, gani yayi har su ameera sun nufoshi, ahankali ya bude motan ya fito, duk yaso sakin fuskanshi don kar su gane wani Abu kasawa yayi.
"Yaya ina wuni..." Ta gaidashi,
"Lafiya...lau..." Ya amsa mata yana kallon eyeballs dinta, da sauri ameera ta dauke kanta don yanda taji gabanta yayi mugun faduwa.
"Ina su mommy..." Zeenat ta tambayeta
"Suna ciki... Ku shiga bari in dauki excuse wurin Khalid..." Maganan ta kara batawa sultan rai yayi ya kara daure fuska Sannan ya fara tafiya ya nufi hanyan falo, hannun Khalid ya daga mashi amma yayi kaman bai ganshi ba
๐๐๐โค๐
ZAKISAN KONI WAYE
๐โค๐๐๐
ยฎzuwairat(ummu Maryam)
7โฃ4โฃ
Ya shige falo yana biye da zeenat, Khalid kura mashi ido yayi yana ganin kaman dan kwallon nan ne da ya Sani Sannan ya ganin shima saurayin ameera ne cos yaga yanda yayi behaving,
"I have a rival...and a footballer..." Ya fada cikin ranshi, ameera dawowa tayi gurin shi, murmushi yayi Sannan yace
"Hmmm ...dayake ni ba ayi trusting dinaba shine ba abari in shiga cikin falo gaida su mom..." Yafada yana marairace fuska, Dariya ameera tayi
"Not at all..." Dan hararanta yayi
"Wane irin not at all... Gashi wancan ya shiga...." Yafada kaman dan yaro, Dariya ameera tayi tana tunanin wannan mutumin is an ajebota daman haka ya nuna ajikinshi,
"Wancan is family... Ba saurayina bane...."
"Hmmm we have been hearing such things since 1857...." Itadai ameera Dariya take don he's sounding very funny
"Wallahi da gaske nake...ba saurayina bane..."
"Naji...ni zan tafi...kilan in dawo da dare ko kuma tomorrow morning kafin in koma kauyanmu..." Dan hararanshi tayi da vibrant eyes dinta
"Yola ke kauye?..."
Eh mana..." Ya amsa mata yana mikewa, takawa ya farayi tana biye dashi, har waje sukaje taga ya nufi wani Lamborghini, har bakin motan ta rakashi
"Da ka shigo da motanka ciki ai..."
"Nasani ko bazaki yarda ba?..."
"Why not..."
Yauma tare suke da Abdul don har yanzu bai iya zuwa gidan shi kadai cos bai iya gane hanya,
"Daman tare kuke da wani shine baku shigo tare ba?..." Tafada tana kallon Abdul dake zaune driver seat.
"Eh abokina ne..." Ameera Dan matsawa tayi kusa da inda yake zaune ta gaidashi, daga kai yayi yana amsawa, karaf sukayi ido hudu, kallon Khalid tayi ta kara kallon Abdul, confirm wannan shine Wanda sukazo tare da pilot ranar da aka za daukanta Sannan shine yayi mata karyan Salem na jiranta su tafi, tasan yanayiwa Salem aiki, he's bodyguard to be precise,
"To meye hadinshi da Khalid..." Ta tambayi kanta cikin ranta, murmushi ta saki Sannan sukayi sallama, komawa tayi cikin taga har sun zeenat sun fito.
"Kayyyy sis har kun fito?..." Ta tambayi zeenat, kawai ta kalli sultan Sai taga ya galla mata harara,
"Eh.... Wani wurin zamu...yau yaya zumunci yakesonyi,..."
"Ko ruwa bakushaba kilan..." Inji ameera data kasa kara kallon sultan,
"Ai baki zo kika bamuba...you were busy with your boyfriend..." Sukaji sultan ya fada, duk Wanda yaji yanda yayi magana yasan he's jealous, murmushi sukayi, ameera tace
"Yaya sorry.. Muje in Baku...."
"Kidaije ki dauko min insha tunda bansha Wanda aka bamuba...." Yafada sounding serious,
"Ok.." Ta fada Sannan ta shiga ciki, kallon ta yake babu blinking, kallon shi zeenat tayi tana tunanin ko yayanta na son ameera,
"Kilan" tafada cikin ranta cos tun last week yake damunta ta kaishi yawo sai su biya gidansu su ameera ya gaida abokin Abba, zeenat dai mamaki take don yayanta in ya zo Nigeria bai fita koina har ya koma. Kallon shi tayi suka hada ido
"What?..." Ya tambayeta, murmushi tayi
"Nothing.." Ta amsa mashi. Kurawa ameera ido yayi har ta karaso da juice da cup. Zubawa tayi ta bashi, amsa yayi ya hada da yatsanta na kasan cup amma yayi kaman bashi ya rike mata yatsan ba, da sauri ta zare hannun ta batare da zeenat ta ganeba, Dan shan juice din yayi
"Is too sugary..." Ya fada yana maida mata cup din. Mota ya shiga itama zeenat ta shiga, juyowa yayi ya kalleta ya kashe mata ido daya. Basarwa tayi amma cikin ranta tana tunanin kilan dan iskane
"Daman Wanda ya zauna kasan turawa dole yayi iskanci..." Ta fadawa kanta tana shiga falo.
Tun five Tawakaltu bata farka ba sai 9pm, Ahankali ta bude idanuwanta, kallon Salem dake massaging kafanta tayi, yana ganin ta bude ido ya bar kafanta ya dawo wurin kanta,
"My angel.. Ya jikin?..." Ya tambayeta yana kissing hannun ta,
"Da sauki..." Tafada tana magana Ahankali,
"Me doc yace?..." Ta tambayeshi, murmushi yayi har lokacin yana kissing hannun ta
"Yace ki huta...kar kiyi komai...and you know what?..." Yafada yana kallon idanuwanta, Ahankali ta girgiza mashi kai Sannan yace
"Yace I should stop riding you for a while..." Idanuwa ta dan kwalo
"Really?..."
"Yes...har kinji dadi ko?..." Batace komaiba ta Dan saki murmushi,
"Ya akayi ya san abinda ke faruwa?..." Ta sake asking
"Because... You..,..are... Pregnant....." Yafada yana spelling out the word one after the other, idanuwa ta kara kwalowa ta kalli cikinta tare da tabashi
"Da gaske?..." Da sauri ya daga mata kai, murmushi ta saki
"So am becoming a mother?...." Bata idaba ya katseta dacewa
"And me a father..." Yafada yana dariya,
"Amma da wuri haka?...daman ana samu da wuri haka?.." Dariya Salem ya sakeyi cikin jindadi
"Kilan na first night dinmu ne..." Yafada in a funny way, ahankali ta Dan daga hannun ta ta dokeshi, hannun ta ya rike ya cigaba