Showing 69001 words to 72000 words out of 145230 words

Chapter 24 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

276

cikin ranshi.

"Nidai ka yafemin...I will not run away again..." Dan murmushi yayi

"Kima gudu I will be right behind you.." Yafada cikin ranshi

"Wai habibty wannan number mami ce?"

"Eh..."

"Hmmm...ki turo account in sa maki kudi ki sayi waya...for the sake of friendship..."

"Banso...."

"To shikenan... Ai bazan kara rokonki kan komaiba cos you are stubborn..." Shuru tayi batace komai ba yacigaba dacewa

"Kuma zanyi Maganin stubbornness dinki...when the time is right..." Yafada kasan makoshinshi, su biyu shuru sukayi suna sauraron breathing din junan su, ahankali Salem yace

"Habibty kinsan kasan da zanyi honeymoon dina?..." Cikin whisper tace

"No"

"Instabul...INA gida on the mountain view...daga nan zai in wuce Hollywood chan ma ina da gida kuma in kina wurin duk american actors and actress zaki gansu...sai kumaBeverly hills California ..in short zan 12 countries for my honeymoon...." Tawa shuru tayi tana tunanin yanzu inda ummanshi da mami sun amince da daita zaayi wannan yawon ganin duniyan, wasu hawayene ya kara zubo mata, ahankali Salem yace

"Habibty kinyi shuru... Ko jealous din ne...and habibty kinsan in matata ta haihu indai inagida ni zan dinga chanza diapers.. I want to be the perfect hubby..." Ita dai tawa shuru tayi batace kala ba, karaf taji su mami sun dawo sai Neman ta ake a falo, da sauri tace

"Sir I have to go...su mami sun dawo..."

"OK...good night... Love you" bata amsa mashi ba ta katse wayan tana goge hawayenta.

Tana fita falo taga mami na kuka yayanta sai rarrashin ta take, nan take hankali ta ya tashi, da sauri ta karasa inda mami take ta durkusa gabanta

"Mami...menene?.. Why are you crying?" Mami bata amsa ba tacigaba da kuka, mami kallon yayanta tayi tana cewa

"Nasan kilan ya samu labarin ni da yata suna garin nan...yanzu anty in ya koremu ina zani da yarinyan nan... Ban Iya komawa Kano...." Tafada cikin kuka sosai, itadai tawa har lokacin batasan abinda mami ke cewaba,

"Haba.. Kinsan koma meye he's your father... Kawai kiyi hakuri gobe muje muji kiran dayake yi maki...kuma ai ba ke kadai ya kiraba... Dukkan mu ya kira...."

"anty stop saying that.. Kinsan wannan yaron don ni da yata zaayi shi...I think the best option shine in koma garin mijina..."

"No!" Yayanta ta daga mata tsawa, sannan ta sausauta murya tafara cewa

"Ai kina zuwa wajena tun ba yauba...kuma baitaba kirankiba sai ka yanzu...for the past 19 years oba bai nuna yanason ganimki ba sai yanzu..in kika ki zuwa kin kara disrespecting dinshi so kawai gobe muje..." Sai lokacin tawa tagane kakanta ne yakeson ganin mami, ba mamiba har ita gabanta faduwa take, don bata taba ganin shi, hannun ta tasa ta gogewa mami hawayenta tana cewa

"Stop crying"

โค๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’š

Ameera sabon holewa ake don tun rananda Salem ya bargida tasa guard dinshi yayi mata shopping din kayan dadi take shagalin ta, baa kara hura wuta gidanba don dama tun gida Abinci bai dametaba barta kawai da kayan lashe2, Yanzu kullum tana waya da gida kuma ko kadan batayi gigin fada masu abinda ke faruwa ba, kullum mom na fada mata ta turo mata pictures din gidanta sai tace zata turo, ko yanzu waya suke da mom tana cewa

" mom har yanzu baki turo min number zeenat ba..."

"Oh sorry habibty... Bari in kira Hajiyan ta ta fada mata ta kiraki yanzu nan..."

"Yau wa mom nagode.." Dadi mom taji don halin ameera nada Dana yanzu ba daya bane cos yanzu tana kwantar da hankali suyi hira

"Habibty ki gaida mijinki....kuma insha Allah anty Sadiya tana nan tafe..." Dan baki ameera ta tabe don wani haushin anty takeji

"To mom..." Sallama sukayi sannan ta ajiye wayan ta dauki sauran snickers data ci ta rage ta cigaba daci tana korawa da juice.

Bayan kaman minti ashirin wayanta yafara ringing, da sauri ta dauki wayan tana dubawa ta gane zeenat ce don dukda bata haddace digits dinta ba tasan last number, da sauri tayi picking tana cewa

"Shegiya kawas...I miss you die..." Daga chan bangaren zeenat sai jumping take tana cewa

"Babe yaushe kuka shigo kasan?" Ameera kallon gidan da take ciki tayi sannan tace

"Shekaranjiya..."

"Wayyo Allah na...ya amarci...please babe yan mi tori...."

"Ke wallahi banzace...kina nufin..."

"Yes ina nufin ki fadamin yanda first night dinki ya kasance..." Ameera shuru tayi tana tunanin abincewa

"Please babe inajinki..next week iyayen hameed zasuzo...very soon zanyi joining league naku..." Nan take jikin ameera yayi sanyi don ita hameed ya nacewa amma ta nuna ba ajinta bane shi, babu irin wulakanci da bata yi mashi ba, karfin hali tayi sannan tace

"Woww...am happy for you...." Da sauri zeenat ta katse ta dacewa

"Forget... Sis ni kawai tell me...first night da zafi kaman yanda ake cewa?" Ameera shuru tayi hawaye na taruwa idanuwanta, kaman yafadawa zeenat matsala ta takeji amma tasan muddin ta fadawa zeenat tamkar ta fadawa iyayenta ne kuma tasan ko iyayenta sunyi kadan su kwace ta daga hannun Salem.

"Babe..inajinki... Wallahi jikinna har rawa yake...hameed cewa yayi a Hilton zamuyi honeymoon... Allah sai wani irin doki yake..ni har tsoro yake bani..." Ameera goge hawayn daya gangaro mata tayi cikin sanyi murya tace

"babe mu bar wannan maganan sai wata rana..." Da sauri zeenat tace

"This voice is unlike yours...kodai sir Salem yayi maki raga2...ko kuma ince ya koya maki manners of talking.. " ita dai ameera batace komaiba zeenat tacigaba dacewa

"Anyway tunda bakison fadamin... Send me your international photos don na sanki da selfie..." Ahankali ameera tace

"Banyi photo ba..."

"Wallahi kinyi karya...keda koda shop rite muka shiga sai kinyi selfie balle Spain?...please send me jare..."

"Baya bari photo... " tafada kuma dakaji maganan kasan karya take, shuru zeenat tayi for a moment sannan tace

"Babe you are sounding weird... Ko dai wani abu na damunki?.." Ameera kallon wani katon lizard dake jikin bango dan nesa daita tayi da sauri ta mike daga gurin tana cewa

" babe zan kiraki..."

"Ya dawo ne?" Zeenat ta tambayeta

"Eh kawai tace sannan ta katse wayanta.

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’™

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’œ๐Ÿ’™โค๐Ÿ’š๐Ÿ’›

ยฎzuwairat(ummu maryam)

4โƒฃ5โƒฃ

Daki ta shige da gudu ta rufe tana maida numfashi, arayuwa babu abinda take tsoro kaman lizard, lekawa tayi ta window taga yana gurin zaune ko matsawa batayiba, kurya ta koma don gani take yana iya binta, kwantawa tayi ta fara kuka.

"Wallahi nagaji da zama gidan nan...am feed up..." Tafada a tsiwace.

Aranan bata kara fitaba, daga baya ta kira zeenat suka shigaba da hiransu.

๐Ÿ’œโค๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’š

Su Abba sunyi niyyan baro palace yau Sunday amma OBJ yace subari har sai sun ga zuwansu ameenatu, to kawai Abba yace mashi.

Abangaren su mami kam tun wayewan gari ta kara shiga sabon tashin sense, gani take korarta daga garin oba zaiyi, da wuri suka kama hanyan kwara daga Ilorin da mom sai yaranta uku tare da tawa da mami don haka aka ce masu kowa ya zo da family dinshi, daman mijin mom baya kasan. Femi ya dinga tukin mota sai kallon tawa datayi takumi, dayayi tuki kadan daya daga kai ya kalli tawa, acikin zuciyanshi yana mugun son tawa amma yasan Sam aladansu babu zancen auren zumunci, mami da mom suna baya sit din karshe sai kuka take mom na rarrashin ta.

Da wuri suka isa palace, da kyar mom ta fito da mami dake tsoron palace kaman ba gidan ubantaba, itama tawa jiki ba kwari ta fito, ahankali femi ya karasa wurin ta

"sis you look pale...what's the problem?" Ahankali ta juyo ta kalleshi sannan tayi forming murmushi karya

"Nothing... Kawai kukan mami ke tadamin hankali" hannu ya dora kan kafadanta

"Don't worry.. Everything will be alright..." Kai kawai ta gyada mashi.

Cikin palace suka shiga kowa ya nufi inda oba da mutanen sa ke zama, daidai lokacin da Abba da su OBJ suka iso, mami da sauran yanuwan ta suka shiga dukkan su sai kallon ta suke kaman ba yar uwansu ba, itakam mami sai mamakin abinda Yusuf sulaiman Abba Salem yake palace din babanta, don tasan shine baban Salem, itakam tawa batasan Abba Salem ba. Daga nesa oba ya kurawa mami ido, Abba da obj gaisawa sukayi da oba sannan suka zauna, mami sam bata daga kai ba, dukkan yaran kwanatawa kasa sukayi sauka gaida oba sannan suka zauna, Abba sai tunanin anya Salem na iya wannan kwanciya kasan, da juyawa yayi ya hangi yarinyan dake kusa da mami nan ya gane itace yarinyan data sacewa danshi zuciya

"She's adorable..." yafada cikin ranshi.

Ji yayi oba nace addua sannan ya fara cewa

"Alhamdulillah..nasan dukkan Ku kuna mamakin abinda yasa na taraku duka wurin nan..." Shuru yayi sannan yacigaba dacewa

"Kunsan am not a king with many words... Kaman yanda kuka Sani ameenatu bata cikin yarana saboda abinda ta aikata...Wanda nasan dukkanku nan kunsani..." Shuru ya kuma yi a wannan lokacin zucyan mami kaman ya fito don yanda take harvawa, ahankali oba yacigaba dacewa

"To kaman yanda nayi announcing na cireta daga cikin yayana...ta ci darajan wayan nan Nigeria legends din ..." Ya fada yan nuna Abba da OBJ da wani abu na yan sarauta dake hannun shi

"Ni oba sadiku ayodele na maida ameenatu cikin yarana!..." Aikam gabaki daya family kwantawa sukayi kasa suna nuna godiyansu, mami sabon babi kuka ta bude tayi kneeling ta rarrafa har gaban oba ta rungume kafafunshi tana kuka tana cewa

"Pami am sorry... Am sorry...." Bata karasa ba ya jawota ya rungume ta..

"I miss you.. My stubborn princess..." Cikin kuka mami tayi daria, ahankali shima yace

"Am sorry my princess... Mulki yasani son hana abinda Allah ya hada..." Mami tana rungume da jikin tsohon ta ta girgiza kai

"No..pami..." Da sauri oba yace where is my granddaughter, mami Dan janyewa tayi ta kira tawa, ahankali ta karasa wurin tayi kneeling gaban oba, abun hannun shi yadan dora bisakanta ya dinga jero adduoi dukkan yan palace na amsawa da ameen. Abba kallon natsuwan tawa kawai yake acikin zuciyanshi yana

"Alhamdulillah Dana yayi dace...Allah yasa kinada hali na gari" shikam OBJ har Dan guntun hawaye ya goge, oba kallon yara da jikokinshi dake kwance kasa yayi

"Bani zaku gaidaba..Ku gaida wayan nan" yafada yana nuna Abba da OBJ, dukkan su juyawa sukayi daga kwance suka fuskanci inda Abba da OBJ suke sukayi masu godiya.

Bayan kaman hour daya Abba da OBJ suka hau jet aka sauke OBJ a osun sannan Abba yayi hanyar yola.

Murna a family dinsu mami kaman anyi aure don gidan shika yayi da family, gasu masu hali da naira mami da tawa ne kadai suka fita daban cikin su, saukin ma kayan da mom tasa aka dayawa tawa sai man da take shafawa, don ba laifi skin dinta ya danfi da kyau da haske.

Aranan aka sauke su mami da tawa acikin wani 4 bedroom apartment dake cikin palace din, sannan aka bawa mami maidens biyu don su dinga yi mata hidima, mami cewa tayi bata bukatan su amma oba yace dole princess saida maiden. Kuma ranar oba ya sanar dasu cewa ranar asabar mai zuwa zaayi bikin maidawa mami da tawa kayan sarauta.

Abba yana isa gida Salem ya rungume shi babu kunya ya dinga jera mashi kisses a hannu

"Kai baka da kunya ko?..." Abba yafada yana daria, shima Salem daria ya dingayi yana cewa

"Am too excited.. Thanks"

"Ai naga yarinyan... She is so adorable... Gaskiya ka iya zabi..." Salem rufe fuskanshi yayi yana daria

"Abba you mean you saw Tawakaltu?..." Yafada cikin exaggeration,

"Eh mana...yanzu suna palace"

"Thank you so much Abba..."

"Son don't thank me, ka kaiwa obasonjo gaisuwa don ya taimaka sosai..."

"Hmmm..he has always been a wonderful person.. " ya fada yana budewa Abba kofan side dinshi. Abba zama yayi Salem ya nufi fridge ya dauko mashi fresh cow milk da ruwa, ruwan ya fara zuba mashi yasha sannan ya zuba mashi milk din ya mika mashi, Salem komawa yayi a zauna yana kallon Abba ya kasa daina murmushi

"Yanzu Abba next week zamu kwara?" Abba Dan kurban milk din yayi sannan yace

"Bafa wannan week dinba sarkin zumudi...I said next week Saturday..." Salem daria yayi

"To Abba... Da wa zamu?"

"Aa... Ban gane da wa zamuba.. Ga uncles dinka sannan ga friends irin su OBJ" ahankali Salem yace

"Abba kana ganin su uncle bazasu nuna tribalism ba kuwa?.." Abba ajiye cup dinshi yayi sannan yace

"Kaji zancen banza...tribalism na marasa ilimine...ai in mutum yana da ilimi yasan komai na Allah ne...kuma kasan su uncle dinka sunfi civilize saboda sun zauna wurare daban2" Dan ajiyan zuciya Salem yayi yana tunanin yanzu babu wani obstacles gabanshi dazai hanashi auren Tawakaltu, yana cikin tunani ummanshi ta shigo, Abba bude mata hannu yayi ya fada jikinshi ya sumbaceta a goshi, Salem relaxing yayi kan sofa yana kallon iyayenshi cikin shaawa da jindadi

"Umma ina nan fa..." Yafada yana daria, Umma juyowa tayi ta kalleshi tana murmushi, zama tayi gefen mijin ta tana cewa

"Alh ka dawo lafiya?"

"Alhamdulillah.."

"Ya OBJ?" tambayeshi kasancewan batasan asalin dalilin dayasa Abba zuwa kwara ba, suna nan zaune Abba ya fada mata komai gameda tafiyan da yayi, Umma shuru tayi don har cikin ranta batason danta ya auri wata yare sannan kuma har ga Allah bata ga aibun Tawakaltu ba ko kadan ita kawai alada ke batason jikokinta suyi exchanging amma who is she to separate what Allah have joined, shuru datayi yasa Salem kallon Abba da zara2 idanuwanshi sannan ya mike ahankali da niyyan tafiya part dinshi, sai lokacin Umma ta dawo hankalinta

"Son ina zaka kuma?" Ahankali ya juyo ya kalleta

"I want to go..." Cikin sanyin murya Umma tace

"Habibi dawo ka zauna" ahankali ya tako zuwa gaban Umma ya durkusa, Abba sai kallon su yake, Salem dafa gwaiwan Umma yayi

"Umma nasan har yanzu baki son Tawakaltu..." Dasauri Umma ta rufe mashi baki

"Habibi stop saying that... Batawa ke banisoba...its just the language.. Tawa is a lovely girl... Amma habibi I give you my 100% support... You have my blessings..." Da sauri ya mike ya rungume Umma

"Thanks so much...insha Allah ba zamuyi regretting ba..." Umma pointed noise mai kama da nata taja

"Allah yasa Ummas habibi.."

"Argggg... " yafada yana shafa inda Umma ta rike mashi hanci. Haka suka cigaba dari hiransu cikin jindadi, amma fa har lokacin Umma bata bar tunanin Yoruba daughter in-law dintaba...ko ya abun zai kasance?.. Oho....

_One week later_

Kowa na inda yake don ameera kam bata da friends sai lizard don tamkar sunsan tana tsoron su, most of the time tana daki, abun takaici tunda Salem yace kar akara barin hinde ta shigo bata kara shigowa ba, sai tayi kusan hour 10 tana waya da friends and family.

Salem kam ya koma aiki amma komai nashi ya koma shiririta don banda waya da princess tawa babu abinda yakeyi kullum saiya sata tayi mashi kuka hankalinshi yake kwantawa, don kullum cikin zolayanta da sabon amaryanshi yake, he's tormenting her to death and he's enjoying every part of it.

Abangaren tawa kam jiya akayi party basu right place dinsu a kwara, mutane da dama sunzo don har da yan nta da AIT, yanzu sabon rayuwa suke ciki don wata babban fashion artist CE mai dauko designer and qualitative dress ta kawo masu dresses, duk Wanda yaga tawa yasan she's royalty don da akwai bead sakale agaban goshint, sannan da akwai bead a kafafunta biyu kaman leglace sai daya a hannun ta na dama, jikin ta yayi mugun kyau amma kuma ta rame sosai don yanda Salem ke tada mata hankali don har cemata yake in yasan inda take zai kawo mata matanshi su gaisa. Rayuwan palace Sam baiyi mata dadi cos cousins dinta are so expose to life, cikin yan Matan babu mai saka normal skirt da riga saidai kaga an saga skirt abaya sosai ko kuma a gefe, datayi dressing sai su dinga cewa

"Princess toyin.. Omo Hausa" wai yar Hausa

๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’œโค

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’›โค๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’™

ยฎzuwairat(ummu maryam)

4โƒฃ6โƒฃ

Mata dake kawo kayan sawansu ne ta kaya cike da box dukkan jikonki oba su zama saboda ya fada masu zaayi babban bako a palace,

"Duk jikokina yan mata su shirya...ranar asabar mai zuwa zamuyi bako...kuma bakon sananne ne akasan nan...kuma nayi farin ciki daya ga family din mu worthy.. Kunsan aladan mu dole yazo ya nuna mana wacce yakeso cikin Ku.." Oba yafada masu jiya wajen shagalin su mami, hakan yasa Matan ta bus shike da decent kaya, irin su jallabiya da long gowns, don oba ya bata umarnin kar ta kawo kayan banza don yasan halin jikokinshi.

A wani katon falo a juye kayan ko wacce cikin su shida sai zaba suke, sai da suka zaba sai daya ta juya ta kalli tima

"Wai ina toyin?" Sai lokacin tima ta lura da babu tawa awajen, ajiye kayan ta tayi ta nufi part dinsu tawa.

Tawa na kwance kanta kan cinya mami, sai kallon yanda mami ta chanza cikin kankanin lokaci take, daga idanuwanta tayi tana kallon mami, karaf suka hada ido, da sauri mami ta rufe mata idanuwa da hannun ta

"Ife..wayan nan idanuwan suna bani tsoro.." Tawa daria tayi, sai kuma tayi shuru for a moment sannan tace

"Mami" ta kira ta, Ahankali mami tana shafa kanta

"Yes love" ta amsa mata cikin so da kulawa

"Are you happy?..." Mami taji ta tambayeta, mami shuru tayi tana kallon ta, Ahankali ta gyada mata kai

"Yes..am very happy..na dade banji irin wannan farin cikin ba" tafada tana murmushi, tana shafa kan tawa tace

"Habibty.. A you happy?..." Tawa kara daga manyan idanuwanta tayi ta kalli mami, shuru tayi batace komaiba , Ahankali mami takara cewa

"Love are you happy?..." Ahankali ta girgiza wa mami kai, cikin sanyin murya tace

"Why love" tawa fashewa tayi da kuka tana cewa

"Mami..sir Salem is getting married!" Da sauri mami ta daga ta ta rungume

"Don't cry...kilan hakan shiyafi alkhairi.... Koda ni na amince.. Kina Iya auren Wanda ummanshi bata sonki?.." Da sauri ta girgizawa mami

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login