Showing 144001 words to 145230 words out of 145230 words

Chapter 49 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

265

Salem yaso daukanta amma doc ya hana wai the more she walks the better

Ba karamin wahala tasha ba don duk hankalin su ya tashi mussanman Salem don cewa ya dingayi ayi mata cs kawai don wahalan yayi mata yawa, har kuka sai da yayi don Umma hanashi shiga tayi kuma daga baya ya barjin kukanta Sai ya fara tunanin kilan ma mutuwa tayi, buga kofan ya farayi da karfi yana cewa

"Umma meyasa Tawakaltu ta bar kuka?...Umma in mutuwa tayi Ku fadamin...." Da kyar Abba ya jashi daga wurin, kaman mahaukaci ya koma, alwallah yayi ya tafi masjid ya dinga sallah nafila.

Sai bayan magrub ta haifi danta namiji, alokacin bata San inda hankalin ta yake ba don batasan sanda aka karata ba saboda girman dan, duk gidan babu Wanda ya sha ko ruwa saboda tashin hankali, Umma ce ta kira Abba ta sanardashi, Salem dake kwance kasan carpet din Abba najin Abba yace alhamdulillah, ya mike da gudu yayi waje Abba ya bi bayanshi. Yana zuwa bakin wurin yaji kukan jariri,wani irin ajiyan zuciya yayi ya shiga wurin kasancewan Umma ta tafi dauko kayan jariri, ko kallon dan banyi ba ya je wurin Matan da Vicky keyiwa stitching, Sai ajiyan zuciya don ko kuka bata iyayi. Hannu ta ya rike ta bude idanuwanta da suka koma ja ya fara cewa

"Baby am sorry for putting you through such pain...baki kara haihuwa...if we need more kids we will get a surrogate mother... Amma baki kara wannan wahalan...." Bai idaba yaji kukan Dan kaman yana cewa daddy baka yi min magana ba, sakin hannun tawa yayi ya koma wajen Dan, gani yayi dan kaman Dan wata uku cos girman dan yayi yawa,

"Masha Allah..." Ya fada yana duba sex din yaron, kallon doc dake daman aikinta yayi

"What did he weigh?..." Ya tambayeta

"4.5kg..." Ta amsa mashi

"That's why ka wahalal min da mata" ya fada yana daukan Dan.

Jamaa haka ko wacce uwa take wahala kan Dan da ta Haifa amma ka tashi ba ka ganin grima ko darajansu...to Ku Sani duk abinda da yayiwa mahaifanshi zaa yi mashi..so be obedient respective. Allah kasa mu rabu da iyayenmu lafiya.

Kuyi hakuri, mun kusa gamawa don anyi resuming school.

โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’š๐Ÿ’œโค

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›

ZAKISAN KONI WAYE

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’™โค

โค๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™

ยฎzuwairat(ummu Maryam)

8โƒฃ4โƒฃ

* *Alhamdulillah*

*Alhamdulillah*

*Alhamdulillah*

Murna wurin Ameera tamkar ita ta haihu ana fada masu suka kama hanyan family house din Salem kasancewan tunda cikinta ya shiga wata na biyar ta bar ciwo, yanzu garau take, ga haske data kara.

Tawa kam banda bacci babu abinda takeyi, Salem bakinshi bai rufuwa don call kawai yake.

Atakaice ranar suna akayi shagalin fiye da tunanin mai karatu da yaci sunan dad amma ana kiranshi da gidado,

Bangaren Ameera kam Ahankali ta ciga watan haihuwan ta, ranar haihuwa kam taci kwakwa ta haifi danta namiji , suma na karamin shagali akayi ba ranar suna shima dan sunan governor aka bashi ana kiranshi da lamido.

Ahankali lokaci ke tafiya aminci na kara karuwa tsakanin family din Salem dana Ameera, yaran hinde biyu ke yiwa Ameera aiki, dukkan su basu tunawa da abinda ya taba faruwa tsakanin Salem da Ameera, Kuma har yanzu mutane da dama basu San Salem ya taba aure Ameera ba.

Bayan shekara biyu kowanne Family ya kara samun karawan kuma still duk maza.

Yanzu su Khalid sun koma abuja don nan ya gida sabon company.

Salem kam arziki karuwa kawai yake haka soyayyar da yake yiwa matanshi. Dukkan su sun maida zuwa abroad tamkar bathroom.

Admission suka samarmasu a university of abuja inda Ameera take karantan medicine ita kuma Tawakaltu tana Karanta business administration, abun mamaki shine yanda shakuwa ta mussanman ke shiga tsakanin gidado da lamido, most of the time suna tare gashi school daya suke the same class, har ya kaiga suyi sati daya gidan Salem suyi daya gidan Khalid. Kuma ko wanne da kamannin ubanshi don mostly daddys junior Salem da Khalid ke kiran first born dinsu.

Agurguje cikin shekara goma tawa ta haifi yara six four boys Sai two girls amma kowanne da na da mai kula dashi ko ita don sam bayason a takurawa matanshi don har yanzu halinshi na nan babu abinda ya fasa. Tawakaltu business take na kayan kitchen da na gida gaba daya. Ko gobe zaa daurawa yarka aure in ka zo wurin ta zaka samu duk abubuwan da kake buka,.

Bangaren Khalid suma cikin ten years sukayi four kids, three boys and a girl, kuma sunce sun rufe saboda yanda Ameera take shan wahala in tana da ciki.

Yanzu Ameera doc ce kuma ya gina mata hospital inda take aiki.

Yaran sultan da queen Habeeba biyu, suna zaune abroad.

Zainabu ma tayi aure da yaranta uku.

Every part is happy especially mami da ta san cewa ba duka aka taru aka zama daya don duk sanda tawa da yaranta sukaje Sai ta godewa Allah da ya hada Salem da yarta, saidai abinda ke bata haushi shine yanda yaranta basu son zuwa Kwara.

Bayan su Lamido sun gama first degree dinsu daga Cambridge akayi masu aure, lamido da fourth child din Salem mai suna amra Sai gidado da last born din Khalid mai suna afra.

They all live happily ever after

To jamaa nan na kawo karshen littafina.



Na gode na kulawanku.

Mata ga shawara

Ina mai Baku shawaran abar zaman banza, wato zaman rashin aikin yi ko Sana'a, mata da dama suna zaune gida basu da hanyan samun sisin Kansu Sai miji ya bada which is very bad, komai miji, biki miji...anko..miji in short common gishiri Sai miji ya saya, why?... Nasan zakuce Allah ne ya dora masu amma babu Wanda baya bukatan taimako, kullum cikin yar murya kike don abaki kudi, at least in bai bari aiki to kayi Sana'a ko ta cikin gidane don babu abinda ke saurin sa mace ta fita ran mijinta kaman kullum bani, Wallahi duk yanda mijinki ke millionaire watarana dole ya gaji da bani, watarana kiri2 zaice babu kuma babu yanda zakiyi amma the moment kina da abinyi baki jin frustration inya hanaki.

Karki ji na fi karfin inyi kaza da kaza dole Sai kaza wallahi you are deceiving yourself, duk yanda kike takama da kyau da akwai wacce ta damaki tasha. So mata Kar ayi zaman hakan nan, akoyi Sana'a.

Ku kuma masu aiki a dinga taimaka wa mai gida, karkice dole Sai shi kadai zai biya school fees fin yara alhalin kina da halin taimaka mashi, Sai kiji wasu Matan na cewa

" ni zan taimakawa namiji?.. Allah ya sauwake....AI namiji ba Dan goyo bane..in kashe mashi kudina watarana ya kawo min kishiya?..." Well namiji ba dan goyo bane amma in kika yi don Allah zaki ci riba, Sannan in kika taimaka mashi da yaranki tamkar kinyiwa kanki. Kuma kishiya in Allah ya kaddara zaayita babu Wanda yaisa ya hana don haka a dinga taimakawa mai gida don ba karamin aiki suke ba, in kin taimakeshi ya kwareki shi da Allah.

Allah ya sadamu da alkhairi. Sai kunji ni a sabuwa novel dina mai suna *kawarta ce sanadi*

Amma ba yanzu ba cos Sai na gama typing zan fara turowa.

Love you all most especially you my die hard fan.

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login