Showing 81001 words to 84000 words out of 145230 words

Chapter 28 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

262

farincikin har ya mance.

Abdul ne da sauran guards dinshi suka shigo suka yi mashi congrats sannan Abdul yace

"Sir..yan jarida na son magana da kai..."

"Just tell them subar interview Sai ranar wedding.."

"OK" kawai Salem yace sannan ya fita.

Sai dare Salem ya koma abuja, aranan ma soyewa sukayi da tawa don hiransu na rana ya kasance ta yanda zasu tsara rayuwansu.

_

_The following Saturday__

From Sunday zuwa yau Saturday Salem da tawa suna cikin farin cikin sosai don basu hour basuyi video call ba, acikin satin oba yasa aka kira yan uwan Baban tawa aka fada masu abinda ke faruwa. Kuka suka dingayi suna Neman yafiyan mami da tawa, sai lokacin ta tabbatar da maganar Salem dayake cewa kar ta damu family din babanta zasu nemata when the time is right.

With in one week Salem da tawa suka maida jikin su ba kaman tawa da killer hips dinta suka kara fitowa.

Ameera kam tunda taji zancen auren Salem ta kara shiga damuwa, don Sam yanzu bata samun nutsuwa kaman yanda ta Dan samu cikin ya kwanakin baya, yanzu ta tabbatar da tana son Salem, gani take ko ata hudu zata Iya zama dashi. Yanzu damuwanta yanda Sai kasance. Adua take Allah ya huci zuciyanshi ya barta ko anan gidan ne.

Yaune su Abba sukaje kwara amsan list.. Hmm auren Yoruba Sai mai hali don harda saa biyu, da kwayoyin doya guda 300, Sai abinci da su man ja da sauransu, kuma aranan kasa ranar engagement wata daya kawai sannan suyi traditional wedding Sai daurin aure, atakaice daurin auren ya rage sati biyar. Bayansu Abba sun kawo list gida abun mamaki ya bawa Umma don akwati daya kawai suka bukata a yimata amma duk sauran babu nata cikin, murmushi Umma tayi

"Ai Sai munyi akwati 24..don mu daya yayi kadan wajenmu"

_*๐Ÿ’™โค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’š

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค๐Ÿ’™๐Ÿ’š

ยฎzuwairat(ummu maryam)

5โƒฃ1โƒฃ

_Please fan inason kusani cewa wannan book din na riga na tsara kayana daga farko har karshen shi, duk masu cewa in ya saki ameera sun daina karantawa.. Kuna iya daina karantawa tun yanzu...likewise masu cewa in bai saki ameera ba su daina karantawa.. Suma suna Iya daina karantawa ...Sannan masu cewa in aka saki ameera novel ya lalace you will be surprise.. And masu cewa nabawa Yoruba power cikin novel din da yawa har suna cewa koni Yoruba CE..to am not Yoruba.. Amma na zauna da Yoruba likewise Hausa so its the reality of what am seeing that am writing.. So kowa yayimin hakuri yaga karshen novel din nan.

Thanks for the love and affections._

_

๐Ÿ’™โค๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

Salem dake zaune gaban Umma daria yayi sannan ya amshi list din daga hannun Umma yana dubawa shima dariya yayi

"To wannan akwati daya na meye hope ba lefe suke nufi ba..." Daria Umma tayi

"Hmm..so kona meye nidai 24lb zanyiwa daughter in-law..." Salem murmushi jin dadi yayi yana tunanin

"In sunje chan zatayi shopping kayanta na Nigeria Dan kanta" Abba kara amsan list din yayi ya dinga dubawa

" kayan nan doubling dinsu zamuyi..like tunda sunce 300 tubers of yam akai 600.. Rice akai 10bags, komai linkawa zamuyi.. Cows kuma tunda sunce biyu Sai akai biyar..ko ya kika gani?.." Ya fada yana kallon Umma

"Hakan yayi..don naji yarubawa da akwai cin nama a occasions....so ana iya karawa da raguna uku" daria Salem yayi

"Kam..Umma duk cin namansu sun cinye cows biyar?..."

"Ko basu cinye ba..mudai zamu kai..in ya rage su rike..." Salem mikewa yayi

"Umma bari inje inyi calming nerves dina...nagaji..." Hararanshi Umma tayi

"Abba ka dayaje kwara state saiyace me" Salem daria kawai yayi ya fita ya bar Abba da Umma zaune, Umma wayan ta ta dauko tana cewa

"Bari inkira Hajiya hannatu ko containers din kayanta sun iso... Sai muyi siyayyan daga wurin ta kawai tunda ba lokacin da zamu je Dubai yanzu"

"OK..hakan ma yayi.. Make sure you buy correct things..." Inji Abba, Umma daria tayi tana cewa

"you know me..."

Ahankali ameera ta shiga kitchen taga babu sauran abinci gashi kudin hannun ta sun kare, hinde da yaranta sunyi shurko2 suna jiran abinda zaayi, ameera fitowa tayi ta bugi gate, masu gadin budewa sukayi don atunaninsu hinde ce ko yaranta, suna gani ameera sukayi saurin maida gate, baki ta tabe tare da Jan tsaki

"Malam ba fita zanyi ba..kawai Ku kira sir Salem Ku fada mashi bani da sauran abinci..." Tafada tana jinginawa da gate, masu gate banza sukayi daita, saida ta kai minti ashirin basu ce mata kala ba, kara dukan gate din tayi

"Kunsan wallahi Ku kirashi ko kuma in tara maku mutanen garin nan...kun San karamin aiki nane..." Daya daga cikin su ya dauki wayan shi yafara dailing number sir Salem.

Salem na komawa side dinshi na family house ya kwanta tare da rungume pillow yana lumshe idanuwa ahankali kaman mai jin bacci, yanajin wayan shi tafara kara yayi tsaki tare dacewa

"Can't someone have a nice and quite time?.." Yafada yana daukan wayan, yana ganin number Mara suna ya Dan saki murmushi don most of the time sisters din tawa suna kiranshi suna zolayanshi, picking yayi daga chan bangaren akayi mashi sallama, amsawa yayi sannan yace

"Waye?.." Daga chan bangaren mutumin yayi mashi bayani ko shi waye kaman yanda ya saba, bata rai Salem yayi don har ga Allah mancewa yake daita mussanman tunda komai ya daidaita da tawa, shuru yayi for a moment sannan yace

"Bata wayan.." Da sauri aka mikawa ameera waya, Salem komawa yayi ya kwanta ya bar wayan on hands free, ameera don daidai ta muryan ta tayi

"Good afternoon..." Tafada with strong and firm tune, Salem dan kallon wayan yayi don yanda ya ji muryan ta so strong da firmer don babu alaman karaya cikin muryan ta, Dan tabe baki yayi

"Son of a bitch speaking... Me akayi?" Yafada batare da ya amsa gaisuwanta ba, ameera lumshe idanuwa tayi tare da zama kasan inda take don wani irin masculine voice dataji

"Sir...wai daman abinci na ne yakare..."

"Are you insane... Ya zaayi kice dukkan uban abincin da aka ajiye har sun kare?" Yafada afusace har yana mikewa zaune, ameera shuru tayi tana tura kanta cikin cinyanta, saida ya kai aya Sannan tace

"Sir..."

"Don't sir me... I said ya akayi dukan abincin yakere..and don't play dumb with me...filthy fool" ameera kuka tafara kokarin yi

"I don't have time.." Dasauri ta daidaita muryan ta Sannan tace

"Bani kadai keciba..."

"What!... Kunjimin shegiya.. Da abincina kike good Samaritan?... Na ubankine?...kina son ki nuna min you are now charitable ko?... Karyanki..cos people with deadly habit don't quit easily" ameera kuka tafarayi tana cewa

"Am ka yafe..."

"Keep am not done talking... Kilan kin mance abinda kikayi.. Well let me remind you.. Kinga wannan tsohon da kika fesawa pepper spray a ido?..har yau ban bar imagining how he feels and curse you ba..." Yanda yake magana kaman yanzu abun ya faru don muryan shi Sai fita yake da wani irin bitterness, kuka ameera tafarayi sosai

"Ka sakeni inje in nemi yafiyansu..please.." Baki Salem ya kara tabewa

"Hmmm..don't you think is a little to late to cry when the head is cut off?.." Ameera kuka ta dingayi kaman ranta zai fita, don tasan Salem ya gama ganin bakin haka ya tabbatar mata she don't stand a chance when it comes to having her love,

"Kuma da kike cewa in sakeki..just relax..in the next 5 weeks you will be a free bitch...kuma kika kara sa aka kirani bazan sakekiba Sai nan da wata biyar..." Cikin kuka ameera tayi saurin cewa

"Sir..abincin fa..." Dariya ne ya kufcewa Salem don a tunanin shi bazata kara maganan abinci ba

"Ban saniba.." Hannu yasa zai kashe wayan yaji tana cewa

"Duk yau banci komai ba... Am starving.." Tsaki yaja Sannan ya kashe wayan

"This girl will never change" ya fada yana dailing number agent dinshi, nan ya sanar dashi ya aika yaro ya kai 500k chan gidan kuma Wanda ya aika ya tsaya ya saya mata duk abubuwan da take bukata.

Komawa yayi ya kwanta tare da kashe wayan gabadaya.

Sai bayan asar aka kawowa ameera kudin kuma saurayin cewa yayi ta aikeshi yayi mata siyayyan kayan datake bukata. Alokacin ameera tayi kuka har tagaji don gani take Salem bazai sa akawo kudi ko abinci. Iyalen hinde kam duk sunsha tagumi. Ana kawo kudin kowa ya warware amma banda ameera cos Sam bashine matsalan taba. Nan take ameera ta tambayi hinde cinkafa buhu nawa zai ishesu har sati biyar? Nan suka fara list har da kayan lashe2 da sabulan wanka da wanki mostly for hinde s family. Duk uban siyayyan da sukayi saida suka samu chanjin kusan 270k.

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’™

Tawa na zaune falo, daka ganta kasan tana cikin kwanciyan hankali cos yanzu tayi mugun kyau, gashin kanta ya sha gyara sosai Sannan skin dinta look so radiant (who say black is not beauty), yanzu kamanninta da rihanna ya kara fitowa sosai. Komai nata moderate, Sai yanzu naga abinda Salem ya gani daya like mata. Suna Zaune kan gadonta tayi ganmo da kafanta Sai temple run take cikin wayan ta, bude kofa akayi ta daga kanta, mamice ta shigo da wata babban mace data sha speck, daganin matan mai halice cos she looks glamorous, nunata mami tayi

"She's the bride tobe.." Tawa taji mami ta fada mata sannan ta fice daga dakin tabar tawa da Matan, da sauri tawa ta ajiye wayan hannunta ta sauka daga kan gado ta gaida Matan cikin girmamawa. Bayan Matan ta amsa ta dauki kujeran gaban mirror ta zauna ta fuskanshi tawa Sannan tafara cewa

"My daughter how old are you?"

" 18..going to 19" tafada kanta kasa, murmushi Matan tayi,

"Alhamdulillah.. Tunda Allah yasa zakiyi auren wuri..to da akwai lectures da yakamata in dinga baki for two weeks, acikin lectures din da akwai Wanda zaku dauka tare dashi groom..." Tawa dai kanta kasa batace komai ba, Matan tacigaba dacewa

"Sannan zan kula da abinda ya kamata kici, abinda ya kamata kiyi, Sannan zan koya maki traditional dance steps for your introduction and traditional wedding.." Gaban tawa yafara faduwa cos ko daga kafa bata iyaba indai rawa ne. Sai kafkafta idanuwa take kaman Mara gaskiya,

"So from now har lokacin wedding dinki kina under my care.." Bata idaba mami tashigo , key ta mikawa Matan

"Ga makullin wurin Dana nuna maki dazun.." Matan amsa tayi mata godiya Sannan ta kalli tawa

"Nuna Mani inda kayan sawanki suke in yi maki parking..." Da sauri tawa ta mike

" No...no" Matan tafada tana daga mata hannu

"Don't do that.. You are a princess and a bride to be...komai naki yazama cikin ruwan sanyi"

"Ikon Allah.." Tawa tafada cikin ranta,kuma tana mamakin inda zasu da zaayi mata parking

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’š

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’œ๐Ÿ’›โค๐Ÿ’™๐Ÿ’š

ยฎzuwairat(ummu maryam)

5โƒฃ2โƒฃ

Yanuwa kunsan dukkanmu ba sanin kamu mukayi, social media ta hada mu and I love all of you, kuma yanda kuke comments ko kuma reply comments din wasu ke nuna in kai literate ne ko kuma illiterate, so those that have good manners congrats cos yana na kyau da kuma riba...those that lack manners kuma can easily hug transformers cos it will be better.

Kuma please Ku Dan yimin uzuri don zaku jini shuru for a while.

HABIBA MOHD, I LOVE YOU DIE ALLAH YABAR MU JONE

โค๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›๐Ÿ’œ

Tawa komawa tayi ta zauna gabanta na faduwa, saida ta nutsu Sannan ta kara kokarin mikewa amma wannan Karin ba da irin saurin datayi ana farko ba, Matan kallon ta tayi

"And were are going?" Matan ta tambayeta

"I want to pack up..." Matan Dan girgiza kanta tayi

"Bride to be ..in har kina son mu zauna lafiya you do as I say..cewa nayi ki nunamin inda kayan ki suke..I will pack up for you" jiki ba kwari ta nunawa mata wall wardrobe dake dakin, wurin Matan taje ta bude nan ta cikaro da beads din saurautan da yake symbolizing ita royalty ce, Matan daukan su tayi ta komo wajen tawa tana cewa

"I don't want to see you without your royalty beads..ki tabbatar kullum kina sakasu.." Ta fada tana saka mata na kafan, Sannan ta rataya mata na gaban goshinta, hannun hagunta ta kama ta saka mata sannan ta juya ta duba wardrobe din sexy dresses din da suka siya da tima kwana kin baya ta fara fiddowa , tawa Sai kallon ta take, saida ta gama kwasan enough Sannan tace

"Your bag.." Ta tambayeta, tawa nuna mata bag dake saman wardrobe, Matan daukan bag din tayi sannan ta zuba kayan,

"Your perfumes.." Ahankali tawa tace

"Ban..." Bata idaba Matan ta bata fuska

"You mean as a princess or should I say fiancee na the richest man in Africa baki da perfumes?... Gaskiya is very bad...bakisan perfume na defining personality ba...as a princess duk inda kikaje ya kamata ki bar kamshin perfume dinki behind.. That's what we call a a lady with a class.." Dan tsaki taja Sannan tace

"Your cosmetics.." Tawa shuru tayi ta sunkuyar da kanta kasa don banda kwali da faran powder bata da komai, su tima sunyi2 su kaita cosmetic shopping taki

"Gaskiya we need some changes around here... Cos I can't believe that person with such personality will behave like this.." Tawa taji Matan tana cewa, Ahankali tawa tace

"Zan je wurin mami in amshi kudi.. " da sauri Matan ta katseta dacewa

"Are you kidding me?...ba kisan aladanmu bane?...well ba kwari mami zata baki kudin kula da kankiba..your fiance zai bada..now pick up your phone and call him..tell him you need money for shopping.."

"Kambu.." Tawa ta fada cikin ranta, don tasan bazata iyaba, shuru tayi kuma bata dauki wayanta ba, Matan kara repeating tayi, cikin sanyin jiki ta dauki wayan tayi dailing number Salem,jikinta sai rawa yake, tana tunanin yanda zata bude maki tace ya bata kudi, tanajin ance switch off ta Dan saki ajiyan zuciya,

"Ma...is switch off.." Ta fadawa mata, kallon rashin yarda tayiwa tawa,

"Dail the number and give me the phone.." Matan ta fada mata. Dailing tayi ta mika mata, itama jitay switch off. Kallon fuskan wayan tayi taga ifemi, dariya tayi

"Wai ifemi.. That's outdated..$" tafada tana wulla mata wayan. Zipping bag din tayi sannan tace

" let's go.. And make sure you walk like a princess.. "

"Am in trouble..." Tawa ta fada cikin ranta.

Suna fita falon tawa ta kalleta

"Ma'am can I speak to my mami?.."

"No.." Ta amsa mata atakaice. Suna fita taga tayi wani part na gidan, tunda tazo palace bata taba zuwa wurin ba cos babu kowa ciki. Kofa ta saka key ta bude, katon falone Mara tarkacen kaya da yawa, gani tayi an gyara dakin don babu alamun dust ko kadan wurin. Bedroom biyu ke da akwai wurin daya daga cikin su Matan ta kai bag din tawa ta fidda kayanta ta fara linkasu tana sakawa cikin wardrobe tawa na tsaye Sai kallon ta take, har cikin ranta mamakin abinda ke faruwa take. Tana gamawa akayi knocking, tawa juyawa tayi da niyyan bude kofa Matan ta dakatar daita

"Sit here.." Tafada tana nuna mata bakin gadon, ta fita tabude kofan, kayan abinci kala2 da su fruits and vegetables. Amsan kayan tayi ajiyesu inda ya kamata Sannan ta shiga dakinda tawa take, direct bathroom tashiga tahada mata ruwan wanka mai dumi Sannan tafito

"Ko and take your bath.." Ta umarceta, tawa kam ko hour daya batayi da wanka ba cos tana gamawa tayi sallan zuhr, amma who is she to say a word, kayan jikinta ta cire ta shiga wanka. Falo Matan ta koma ta hada fruit salad cike da bowl ta ajiye kan dinning Sannan ta koma dakin tawa ta dauko mata vest da bump short ta ajiye mata kan gado. Tawa da fitowa taga vest da bump short, tsaya kallon kayan tayi cos bata taba saka su kadai ba, tafi minti goma tsaye tana tunani, saitaji Matan tana cewa

"Time for lunch.. A princess does everything in time.." Da sauri ta saka kayan, kallon kanta tayi cikin mirror taga pecky boobs dinta da chocolate colour laps dinta, fita tayi ta zauna kan dinning mata ta ajiye mata uban fruit salad

"Finish it.." Ta umarceta, cokali biyu tagani kan plate, daya fuck Sai Normal spoon, Sai kallon spoons din take don batasan Wanda zata daukaba, Matan ta kura mata ido, tagane matsalan tawa

"Use the spoon" ta fada mata, spoon ta dauka ta fara ci. Mata tana kallon ta tafaraci aikam Sai ta hauta da fada wai bata Iya cin abinci kaman princess, wai dole ta dinga taunan abinci kaman tanav. tausayawa abinda takeci, tun lokacin tawa tasan da akwai matsala, tana gamawa tasata ta shanye karamin bottle water daya Sannan sata tayi taki talatin cikin dakin tana gamawa ta kalleta

"Go and take a nap.." Ta fada mata ba musu tawa ta shiga bedroom tana tunanin yanda zatayi tayi baccin rana don tunda take in tayi baccin rana to bata da lafiya ne, amma Sam bata saba ba. Kwantawa tayi Matan ta rufa mata blanket tare da dauke wayanta. Tawa kwantawa tayi tana juye2, abun mamaki ko minti ashirin batayi da kwanciyaba bacci yayi gaba daita.

๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’šโค๐Ÿ’œ

Salem kam tunda ya kashe wayan shi ya kwanta bai farkaba Sai daf da asar, da sauri ya mike tare da adua Sannan ya shiga bathroom yayi wanka tare da alwallah, yana fitowa ya ya saka jallabiya ya tafi masjid. Yana dawowa ya ya dauki wayan shi ya kunna, agent dinshi ya kira ya tambayeshi ko ya aikawa ameera abinda yace mutumin ya amsa mashi da yes.

Number tawa yayi dailing yaji switch off, Dan murmushi yayi tare dacewa

"This is unlike you.." Yafada yana ajiye wayan.

Tawakam ba karamin dadin baccin taji ba cos bata tashiba Sai bayan asar kuma saida Matan ta tadata, tana mikewa ta mika mata ruwa nan take ta shanye ta mika mata cup

"How do you feel?" Matan ta tambayeta, Dan murmushi tayi

"I

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login