Showing 72001 words to 75000 words out of 145230 words

Chapter 25 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

245

kai

"No..mami..I can't"

"Good... So ki mance dashi..ki koma school.. Nasan insha Allah kafin ki gama degree dinki Allah zai kawo miji na gari..." Cikin kuka tace

"But mami I love him..."

"Habibty you are too young to know what love is..." Mami tafada tana shafa bayan tawa dake kuka kaman ranta zai fita tace

"Mami.. My heart beats for him" mami dai shuru tayi tana rarrashin ta don tasan yarta da kafiya kan abu, suna cikin hakane tima tayi sallama tashigo ,

"Mami meyasa toyin bata zo daukan kayaba?" Tafada bayan ta gaida mami,

"Oh..na mance... Habibty tashi maza kije ki dauki kaya..." Tawa mikewa tayi daga jikin mami tare da goge hawayenta, tima batace komai ba don ta saba da ganin tana kuka

"Mami na meye kayan?" Daria mami tayi, ta tuna mata abinda oba ya fada jiya, komawa tayi ta kwanta

"Gaskiya mami ban zuwa...." Bata idaba mami ta katseta dacewa

"Kai...Aa ..karki yiwa oba gardama.. Kuma aladanmu dole yan Matan mu su shirya in yar uwansu zatayi introducing Wanda zata aura...." Tawa da turo baki tayi

"To mami in ya nuna wacce yakeso...sauran basu jin haushi?..." Dariya mami tayi

"Haushin me?...ai sunsan ba wurin su yazoba..kawai dai alada akebi"

"To mami yanzu Wanda zaizo wurin wa zaizo?"

"Bansani ba..tunda bamu Dade a palace ba" shuru tayi batace komai ba kuma bata mike ba

"Dalla ki taso mu tafi.." Tima ta fada mata, juyawa tayi ta galla mata harara

"Ban zuwa..."

"Come on..follow her!" Mami ta daka mata tsawa, da sauri ta mike ta bi bayan tima. Suna zuwa duk suka fara zolayanta suna cewa

"Omo Hausa oyoyo..." Tawa Dan murmushi karfin hali tayi Don ko kadan basu bata haushi, kayan ta duba taga wani beautiful Arabian gown black my golden stone ta dauka, batayi wasting time ba ta koma side dinshi.

Around 7pm mami ta tafi side din oba kaman yanda ya bukata ta dinga zuwa suna hiran bayan rabuwa, tana zuwa yana dawowa daga masjid, kneeling tayi ta gaidashi sannan ta zauna suka fara hira kaman yanda suka saba, bayan kaman minti ashirin mami tace

"Yauwa...bami..wai waye zaiyi aure cikin yaran mu?" Oba Dan daria yayi

"Nima nan bansani ba..amma abinda yafi bani mamaki shine yanda akayi Dan Yusuf sulaiman ya ga daya daga cikin jikokina..." Da sauri mami tace

"Pami you mean Salem Yusuf sulaiman ne zaizo ?"

"Eh...ko kin sanshi ne...?" Mami shuru ta danyi sannan ta fara bawa oba labarin abinda ya faru tsakanin tawa da Salem har zuwa lokacin da Umma Salem tasa aka dauko mata tawa ta ja mata kunne ta rabu da Salem, mamakine kwance kan fuskan oba

"Hmmm..wonder shall never end..so saboda yarki sukayi sasanci tsakanin mu?"

"I think so bami" har lokacin oba bai bar mamaki ba,

"Allah mai iko... Ashe rabon ki haifi Matan the richest man in Africa yasa kika bijirewa umarni na..." Mami shuru tayi tana tunanin ko oba baiji abinda tace gameda Umma Salem ba, Ahankali tace

"Bami..gaskiya na yarda yanason ta kuma itama tana son shi... Kuma tunda sunyi kokarin gani zaman lafiyanmu Dana hakura ta aureshi.. Saidai matsalan uwarshi batason danta ya auri wata yaren..." Oba shuru yayi kaman sai yanzu ya saurari abinda mami ta fada da kyau

"Ah ah..kai ai danasan haka zance yake da ban basu daman zuwaba..." Shuru yayi for a moment sannan yace

"Kuma gaskiya aure baya dadi indai uwa ta nuna ranshi son auren..sannan ko kadan bamu son abinda zai hana yaranmu jindadin zaman auren su..." Ahankali mami tace

"Yanzu bami.. Meye abinyi..."

"Kinsan we are people with principles sannan bamu karamin magana don haka bazamu hanasu zuwa ba...saidai dasun zo ta nuna bata sanshi ba...so later I can have a discussion with them..."

"OK pami" hira suka cigaba dayi amma oba sai mamaki wannan abuba.

Sai around nine ta koma part dinsu, afalo ta tadda tawa ta tafka uban tagumi, zama tayi gefen ta, tawa kaman jira take ta kwantar da kanta kan kafan mami, Ahankali mami tace

"Habibty..."

"Na'am mami"

"Inason duk Wanda yazo...da an tambayeki kin sanshi kice Aa..." Da sauri ta daga kanta tana yiwa mami kallon tuhuma

"Mami waye zaizo?"

"Kawai just do what I said" tawa maida kanta tayi ta kwanta, kaman an chunkuleta ta mike zaune sannan tace

"Mami in Salem nefa?" Mami kallon mamaki tayi mata sannan tace

"Ko waye.. After all ko Salem din ne tunda kinsan uwarshi batason aurenku zaki yarda?.." Ahankali ta girgizawa mami kai

"Good" mami ta fada sannan mike tare da rikewa tawa hannun ta kaita bedroom dinta ta kwantar daita tare da rufe mata blanket sannan ta koma nata bedroom. Tawa kam tana dauke da wayan mami kasan riganta. Kiran Salem kawai take jira.

โค๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’›

Ameera kam da tana ganin tunda Salem ya bata kudi zata samu saukin rayuwa amma sai tafi jin dadin zama da hinde kan komai daya bata, gani take zaman kadaici nan zai Iya zama ajalinta, in dare yayi ko fitsari zai kasheta bata iya fita tayishi, kullum cikin kuka take, datayi waya da mom tana Dan samu sauki koma har yau mom tambayanta take abinda ke damunta am sai tace ba komai.

Yau around six taje bakin gate tayi knocking

" ya akayi?" Ahankali tafara kuka tana cewa

"Dan Allah ga 150k Ku kyaleni in tafi.." Shuru sukayi suna kallon juna, ameera adua take Allah yasa su amince, dayan girgizawa danuwanshi kai yayi sannan

"Bamu Iya cin amanan uban gidanmu ba..." Ameera dora kai tayi kan gate tana kuka

"To Dan Allah Ku kiramin hinde...please"

"Oga yace kar akara bari ta shigo gidan nan.. So please ki bar damun mu..." Ameera kuka tacigaba dayi saida takai kusan minti talatin gurin sannan tace

"Please.. Na rokeku... Ku bani number sir Salem...". Wani dariyan raini hankali suka fara sannan daya daga cikin su yace

" bamu dashi" cikin kuka ameera tace

"Wallahi in baku bani number shiba zan kashe kaina..." Wani sabon daria suka farayi ta bugi kofan da stone

"You idiots think am joking?.." ta fada tana dukan gate din kaman zata cire shi, banza sukayi daita, tafi minti ashirin tana dukan gate, gani sukayi tafara tara masu mutane, daya daga cikin su ya koma gefe yayi dialing number Salem.

Salem na dawowa daga aiki ya shiga mansion dinshi ya cire kayan jikin shi ya shiga wanka, yana fitowa wayan shi ya fara ringing, bai daukaba har ta tsinke saida ya ya kara ringing sannan yayi duba, unknown number ne cos bai saka sunan su ba, Dan murmushi yayi don yana tunanin tawa CE take kiranshi da wata number, picking yayi yajinamiji yayi mashi sallama, fuska daure ya amsa

"Waye kai?.. And who gave you my direct number..." Daga chan bangaren akace.

"Sa nine..." Mutumin yayiwa Salem describing kanshi sannan ya fada mashi abinda ke faruwa, tsaki yaja sannan yace

"Ta kashe kanta..." Katse wayan yayi ya ajiye ya koma gaban mirror ya fara shafa mai, ringing wayan ya fara kuma, afusace ya dauki wayan yayi picking

"Kina wasa dani ko!?"

"Sir kayi hakuri.. Wallahi yarinyan nan tana Iya hurting kanta, tafi hour tana buga kanta da gate..cewa take dole yau sai tayi magana da kai.." Salem fursa iska yayi

"Bata wayan" da sauri ya bude gate ya mikawa ameera wayan.

Ameera na amsan wayan tayi kneeling kaman yana ganin ta tana kuka tafara cewa

"Sir Dan Allah... Kayi hakuri ka maidani gidan mu...wallahi am now a good person..."

"Ke!..." Ya daka mata tsawa da sauri ameera ta kama bakinta

"Don't you ever speak to me on phone... Don't test me...ki bar ganin ina yimiki sauki..wallahi zan Iya yimiki abinda har ki mutu bazaki manta mai suna Salem ba....."

"Sir Dan Allah kayi hakuri... Am on my knells... Forgive me so that Allah will forgive you.. Wallahi this loneliness is killing me...."

"Fuck you and loneliness... " har ya kusa katse wayan, ameera cikin sanyin murya tace

"Sir please.. Tell them to call hinde for me...in har kayi min wannan.. I promise to be calm till you free me..."

"Akira maki hinde so that tayi maki asiri...."

"No..no. Sir..I know am bad..but not that bad..." Bata idaba ya katseta dacewa

"Give those guys the phone.. Your voice sounds terrific... Bitch" ameera sabon kuka tafara ta mikawa mai waya wayanshi sannan Salem yayi mashi umarni da kira hinde and ya cigaba da barinta tana shiga gidan, yana kaiwa nan ya katse wayan tare da wullata kan gado ya koma abinda yakeyi.

Bayan kaman minti ashirin hinde ta shigo gidan, yau ameera bata gan kazanta taba ta fada jikin ta tana kuka, wani irin runguma tayi mata kaman her life depends on holding her. Hinde ma rungume ta tayi tana rarrashin ta..

Hmmm haryau kayan da ameera tabawa hinde sune ajikinta kuma da alaman bata taba wanke su amma ahaka ameera ta rungume ta. I think she's progressing.

โค๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’œ

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›๐Ÿ’œโค

ยฎzuwairat( ummu maryam)

4โƒฃ7โƒฃ

Aranan hinde gidan ameera ta kwana kuma another amazing thing is that tare sukaci kayan dadi suka sha juice, imagine ameera eating from the same plate with hinde. Kallon ta tayi tafara cewa

"Ai kwana ki gamo nayi gidan nan" inji hinde dake tura wani katon biscuit cikin bakinta, ameera dariya tayi

"Gamo kuma?.."

"Eh aradu..."

"Yaushe kenan ?.." Ta tambayeta tana bude sabon kwalin biscuit don hinde ta cin sauran data rage,

"Ranan da nazo nan da baki da lafiya fita hura maki wuta...ai Dana fita da gudu ban kara tsayawa koina ba sai gidan babanmu..sai da yayimin aduoi sannan na dawo gida" cikin tsoro ameera tace

"Ya abun yake?.." Ta fada tana zaro idanuwa, hinde daukan kwalin ready to drink custard tayi ta kafa kai, saida ta ji babu saura sannan ta ajiye shi gefe tayi gyatsa ta goge bakinta

"Ai wani Abu na gani fari fat daga kai har katsa...babu Dan Adam mai kyaun wannan abun saidai aljani...kuma kin sanme..." Da sauri ameera tace

"Aa.."

"dana tambayeshi mutum ko aljani..sai yace min aljani..."

"Jikin abune fari kal?..ko yaya?"

"Aa..shaddan jikinshi ne fari.. Sannan shi kanshi fari kaman shaddan..." Daria sosai ameera ta farayi kaman ba itaba, hinde baki ta bude tana kallon ta don tunda suke tare bata taba ganin ta haka ba

"Lafiya?" Ta tambayeta, ameera daria tacigaba dayi har saida ya isheta sannan tace

"Ai wannan ba aljani bane..Wanda ya ajiye ni nan ne.." Hinde baki ta kara wangalewa

"Kina nufin wannan mutumin shine mijinki?.." Ahankali ameera ta girgiza mata kai

"Aa..shine Wanda ya ajiye ni..."

"Kaman ya wanda ya ajiyeki...ba auren ki yayi ba?" Ameera Dan jinginawa tayi da bango tana lumshe idanuwa Ahankali sannan tace

"Ai gwara in bar kiranshi da mijina..saboda daya yi aure rabuwa zamuyi.." Da sauri hinde ta gyara zaman ta

"Wallahi Sam ban gane ba..."

"Ba da chan na fada maki Dan ya dauki fansan abinda nayi mashi ya aureni ba?..." Cikin sanyin jiki hinde ta gyadawa ameera kai, Ahankali ameera tabawa hinde labarin abinda ya faru tsakanin ta da Salem har izuwa yanzu,

"Subhanallahi.." Hinde ta dinga maimaitawa

"Yarnan kinyi wauta...kinci saa ba aljani bane..don da in bai kashekiba da wahalan ki yafi haka...gaskiya ba kyau wulakanci... Ko kadan bashi da riba sai wahala.. Wallahi talakan yau mai kudin gobe ne sannan wani mai kudin yau talakan gobene...gashi yanzu wannan mutumin mai kama da larabawa zai rabu dake..." Tunda hinde tafara magana ameera ke kukan danasani

"Nidai inayi maki adua in zamanki dashi alkhairi ne Allah ya huci zuciyanshi ya yafe maki...in kuma sabanin hakane ina baki shawaran kar ki kuskura ki Kara wulakanta mutane... In kin San wani baki San wani ba..mutum sai Allah.. Wannan ya zame maki darasi da kuma masu hali irin naki" ameera kara fadawa tayi jikin hinde tana cewa

"Wallahi banason zama dashi don ranan dayazo nan...ya nuna min wata ta amshe dukkan zuciyanshi.. Kawai ki tayani aduan Allah ya fiddani gidan nan lafiya.. Kuma Allah ya bani wani na gari" hinde bayan ta ta dinga shafawa tana bata hakuri.

๐Ÿ’š๐Ÿ’™โค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ

Salem kam yana gamawa ya tafi masjid da guards dinshi, suna dawowa sukayi dinner waje kaman yanda suka saba sannan suka koma masjid,bayan sun dawo suka zauna nan waje suna hira kaman bashi na don wani irin annashuwa yakeji in ya tuna ya kusa ganin tawa, sai wajen 9:30pm ya koma part dinshi yana shiga bedroom ya kara wanka ya fito amma wannan Karin bai shafa mai, guys come and see packs fatan jikinshi yafi na fuskanshi haske over, zaune yayi kan gado tare da dora kafunshi har lokacin daure yake da towel wayan shi ya dauka yana cewa

"Let me make you cry a little bit" yafada yana biting lower lip dinshi, bayan ringing kaman sau shida tayi picking da alaman tafara bacci, cikin wani irin sexy voice tayi mashi sallama, lumshe idanuwa yayi sannan ya fara zolayanta, yanda yake magana kaman da gaske yake, sai daria zalunci yake, aikam ko minti goma basu kai da fara wayan ba ta fashe da kuka,

"Yes" Salem yafada kasan makoshinshi kaman Wanda yayi winning jackpot, don he is finding her cry amusing baisan ita she's serious ba, shima kuka karya ya farayi yana cewa

"I can't wait to make you cry under me..." Da sauri tawa tayi shuru tace

"Me kace?.."

"Nothing..." Kuka ta cigaba dayi

"Kukan me kike kuma?.."

"Ai nasan dakayi aure bazamu kara irin wannan wayan ba.." Daria Salem yayi sannan yace

"Da gaskiyan ki..you better cry..don in nayi aure we will be doing something more fun..." Cikin kuka tace

"Kaman me?" Shuru yayi for a few seconds sannan yace

"Kaman tearing each other from Leda.. " ya fada cikin whisper, tawa Sam bata gane inda ya dosa ba

"Who is tearing whom?.." Dan daria Salem yayi

"Me tearing you..." Sabon kuka ta fara don ita tunanin ta bai kai wajen ba, sunfi hour uku suna hira, da ta fara daria don jin dadi hira sai ya takulo maganan da zai sata kuka.

Haka kowa yacigaba da rayuwa cikin jindadi don yanzu ameera ta maido kumarinta sosai don yanzu sai tabawa hinde kudi t sayo masu Kazan Hausa kaman hudu suyi pepper soup suci har da yaran hinde.

Salem kam sun Riga sun kammala shirye2 tafiya kwara kuma su uncles dinshi basu nuna rashin jin dadin zabin Salem ba, don Wanda Abba biyu da kuma kannenshi biyu zasu bisu, Salem taso yaje da Khalid yaga princess dinshi amma ance a wannan zuwan farko baa zuwa da aboki don tafiyan na iyayene sai kuma shi saurayin.

Tawa kam ta kara haske sosai har mami tana tadan ta bar shafa man don duk Wanda yasanta last three weeks inya ganta bazai ganeta, yanzu ta kwana biyu bata shafa maiba amma skin dinta bai bar radiant glowing ba.

_The Saturday_

Da wuri su Salem da Abba da uncles dinshi suka bar yola kasancewan a yola ya kwana, sanye yake cikin white shadda don yawanshi native wears dinshi farareni, sai black cap sannan ya dora siririn corporate speck, ya mugun hadu kuma ga wani annashuwa dayakeyi don har yanzu bai yarda yau zaiga princess dinshiba. Abba ya kira OBJ ya jirasu chan kwara state government house, haka akayi don chan suka tada OBJ da wasu manyan kasa guda biyu, Salem kneeling yayi ya yiwa obj godiya ta mussanman, dagoshi yayi ya rungume shi yana nuna jindadinshi da Salem zai auri yaryarensu, fitowa sukayi daga government house , Salem gani yayi ana zuba manyan wine bayan wani white range rover, kallon mamaki daya keyiwa kayan ne yasa OBJ yi mashi bayanin cewa dole sai an kaiwa surukai drinks da goro a zuwa na farko. Abba godiya yayi mashi.

A palace kam a gama komai har da abincin akayi kala2 don su waina da tuwon shinkafa akayi, wani katon dinning hall mai dauke da dogon dinning table aka jera abincin.

Yan mata kam sunsha kwalliya suna parts dinsu, around 12:30 su Salem suka karasa palace, daka gan wurin kasan da akwai naira awajen don ko kadan bashi da alakada inda talaka ke zama, Dan ajiyan zuciya yayi yana tunanin "yarinyan da gani at the road side tana saida abinci is now leaving here... Alhamdulillah.. Dont neglect people cos some are beyond your expectations.." Ya fada cikin ranshi, daidai lokacin da suka shiga inda oba da kins men dinshi suke hakamce kan kujeruna alfarma, dukan su cire hulunansu sukayi tare da takalmansu Salem speck din fuskanshi ya cire, dukan su kneeling sukayi suna kwansan gaisuwa, cikin murna oba da mutanen shi suka tarbesu kaman ba wata akasa, bayan sun zauna suka kara gaisawa sosai sannan oba ya mike dukkan su suka mike, hanyan dinning hall ya bi suka bi bayan shi, Salem sai Dan waige2 yake ko zai ga princess dinshi tana dan lekosu, zama kowa yayi wasu guys suka fara serving dinsu, Salem kam ba haka yaso, shi kawai yaga Tawakaltu.

Tawa kam suna gama breakfast tayi wanka, ko mai bata shafa ba ta koma tayi kwanciyan ta, bata kara sanin abinda ke faruwa cikin palace ba, harsu Salem suka shiga palace tana chan kwance tana bacci ga azaban ciwon kai da take fama dashi don ba karamin kuka Salem ya Sara ba daren jiya, duk yan mata palace sunyi kwalliya amma banda tawa, sai around 1pm tima ta shigo ta tadata taje ta shirya, hannun tima ta kama ta dora gaban goshinta

"Feel my temperature... Am sick" Ahankali tima ta ji yanda kanta ke harbawa

"Sorry.. Ki zo ki shirya tunda ba wani wasting of time akeba..." Ahankali tawa tace

"Can't I just stay?" Da sauri tima ta girgiza mata kai

"No..it's not allowed.. Please kizo mu tafi don bakin sunzo har sunci abinci sun tafi masjid da su dawo zaa fara kiranmu.." Tawa bata kara cewa komai ba tamike ta dan leka falo taga ba mami

"Ina mami take?" Ta tambayi tima

"Tana cikin main house" bata Kara cewa komaiba

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login