Showing 3001 words to 6000 words out of 145230 words

Chapter 2 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

268

koface suka gani mai cikin wardrobe room din, ahankali mimi ta bude wurin, wani irin wagegen bathroom suka gani,

"shidai slim komai nashi extra large.." inji fina.

Girman bathroom din abin mamakine don wani katon swimming pool ne wurin sai wata plasma a tsakiyan ceiling din. Daga gefe kuma wani mirror ne wanda shake yake da bath perfume kala2 sai shower gel suma kala2 , daga dayan gefen kuma wani rank ne mai dauke da towel manya da kanana.

Wata kofa suka bi sai gasu a bedroom, wani fridge duka bude sai ga exotic wine amman ba mai giyaba, daya suka dauka tare da cup guda biyu, kan wani mini dinning mai dauke da kujera biyu suka kioma suka zauna suna shan wine din kiowacce tana tunanin yanda zatayi slim ya zama mallakinta.

Shidai salem dan tsohon shugaban kasane amman baya cikin yara masu dogara da arzikin iyayensu don yanzu shine shugaban NGO na Africa gabaki daya, shine babba agidansu sai kannenshi biyu mata wanda yansu suna gidan mazajensu.

Salem yana da kirki sosai don duk shekara sai ya biya mutane dari kudin hajj sannan yana da kungiyan tallafawa talakawa a garuruwan arewa sanna duk begger daya cikaro da slim kaman yanda friends suke ce mashi saboda yanayin jikinshi ya warke ko da a gidansu talaucin duniya ta kare. Shidai Salem yana daga cikin the most eligible bachelor da muke dasu a duniya don yan mata da suke sonshi basu irguwa amman abinda basu saniba shine babu abinda yafi damunshi kaman true love.

Bashi da babban aboki sai Khalifa dan governor na garinsu wato Adamawa, sannan ya dauki bodyguards dinshi tankar abokai don yawanshisu zasuyi shekaru daya.

Saidai wani hanzari ba guduba baya tolerating immorality don mutune mai tsanani amman in ka gane zama dashi yana da saukin kai sosai. Yanzu dai he's 35 years old. Wanna shine short and brief history na Salem.

Bayan ya gama waya da ummanshi yayi relaxing, kaman an sunkuereshi ya mike yana cewa

"subhanallahi!!" donshi ya manta da su mimi a bedroom dinshi, da sauri ya kama hanyan bedroom din yana cewa

"those abuja girls with evil character.. " yana shiga dakin ya hangesu zaune feeling at home har sun kusa shanye wine kwalba daya. Suna ganinshi suka mike tare da nufoshi, kallonsu yayi

" wai ku in dare yayi baku san hanyan gidajenkuba?" yace masu, ahankali mimi tace

"slim ba sauri mukeba..sannan ai dazun kai kace zamuyi maka wani abu ko ka manta?"wani irin kallo ya wasta mata sannan yace

"oh... Na mance,..daman inners dina naso ku wanke min... Amman tunda dare yayi ku tafi" wani irin lustful look suka dinga jefa mashi, yasan maanan kallon amman ya basar yana cewa

"kuyi sauri ku tafi... "mimi da fina kallon junansu sukayi sannan suka nufoshi. Bayanshi mimi ta tsaya, itakuma fina ta zagayo gabanshi, tsayawa takayi daf dashi don boobs dinta yana taba kirjinshi, nan take tsigan jikinshi ta tashi amman sai yayi karfin halin cewa

"meye haka... " bai karasaba fina ta zagaya hannuwanta biyu bayan keyanshi tare da kai bakinta saitin kunnenshi sannan tace

"sli.. You can have us both... " tafada muryanta na fita ahankali, itama mimi tafara shafa gadon bayanshi itakuma fina ta kai bakinta saitin bakinshi ta fiddo harshenta ta lasan bakinshi, nan take ya chafke bakinta yana kissing dinta kaman his life depends on it. Mimi sai shafa gefen cikinshi take, with out wasting of time ya fita hayyacinshi, hannuwanshi biyu ya zagaya kugun fina dasu, yana nishi kaman wanda yayi hour daya yana gudu.bai ankaraba yaji hannun fina kan joystick dinshi.

Nan take ya turata tare da ingiza mimi yayi sannan yayisaurin zama kan kujera, mimi da fina kallon juna sukayi sannan mimi tace

"what's wrong Slim...." ahankali ya daga red eyes dinshi ya watsa masu disgusting look sannan yace

"you both should get out of my house " dan murmushi fina tayi sannan tace

"common slim... Let's have fun " Salem lumshe idanuwanshi yayi sannan yace

"i can't " sake kallon juna sukayi snnan fina tace

" haba slim.. You can't ko you won't.. Nasan you are not impotent don yanzu na taba joystick dinka. .." bata karasa ba ya katseta dacewa

" ban taba zina ba... Kuma bazan faraba yau. Kuma ko ina zina nafi karfin inci leftover irinku...so leave my house before I call my guard to force you out..." tsayawa sukayi suna nuna mashi boobs dinsu, afusace ya mike yana tafiya yana rike gaban jallabiyan dake jikinshi don kar suga girmanshi.

Wani intercom dake jikin bhango ya dannja sannan yace

"guys come and bundle those second hand bitchies fr... " bai karasabha kowacce ta dauki hanbag dinta don a ganinsu abun kunyane suna yayan ministers asa bodyguard su fiddasu.



Suna fita ya tafi wajen wani cabinet ya bhude ya dauki wata magani, wajen fridge ya nufa ya dauki foreign juice yasha maganin sannan ya koma kan kujera, lumshe ido yayi yana tunanin halin matan yanzu, yanda suka koma basu da wani tunani sai na yin mugun abu saboda connection

"anya mu da bamuyi aureba zamu sami matan aure kuwa..don 99% na matan yanzu are bitchies..ya rabbi ina kara rokonka, yanda ban tabha kusanta zinabha kar kabani mata mazinaciya...ya allah yanda nake da tawakali ka bani mata mai tawakali... Ya azizu yanda nake son talakawa kabani mata waccfe zata soni don ni bha dan wani abu nawaba.. " haka ya dinga adua kamar yanda ya saba donshi babu abinda yakeso kaman aure cos yana samun matsalan hornyness.

Ahankali ya mike yashiga bathroom tare dayin bubble bath sanna yafito sanye da kayan bacci. Kwanciya yayi tare da rage hasken dakin. Har ya mance da maganan da Abdul ya fada mashi.

Around 3am yayi firgit ya tashi da adua bakinshi da alaman mafarki yayi, ji nayi yana cewa

"ya Allah ka sauwake wannan mafarkin... Me taxi driver... Kuma ina kuka..." kunna hasken dakin yayi ya dauki wayanshi kaman zaiyi waya kuma kome ya tuna oho ya maida wayan sannan ya mike yashiga bathroom ya dauro alwallah yafara sallan nafila.

๐Ÿ’›โ™ฅโค๐Ÿ’š๐Ÿ’œ

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›โ™ฅ๐Ÿ’œ

ยฎzuwairat(ummu maryam)

4โƒฃ

Wacegari baiyi breakfast da guards dinshi ba. Aside dinshi yasa cook ya kai mashi abinci, bodyguard dinshi sai tsoro suke don basu san abinda zai biyo bayaba mussanman Abdul don gani yake ya riga ya rasa aikinshi.

Kaman kullum yafito, cikin girmamawa sukร  gaidashi, ya amsa masu a takaice. Ba kaman yanda ya saba ba.

A office kam sai ya tsinci kanshi da tunanin abinda Abdul yace, shuru yayi for a while sannan yace

" it can't be possible.. It's only possible in movie ". Aranan baiyi aikin kirkiba don banda tunani babu abinda yake yi Amman abinda yafi bashi haushi shine yanda Abdul ya rasa abinda zaice yayi sai taxi driver. Kaman ya kira Khalid Amman yasan shegenta babu abinda zaiyi mashi.

Atakaice dai bayan kwana uku abun ya zame mashi kaman disturbia, don tunda Abdul yayi wannan maganan bai Iya bacci batare dayayi marfarkin yana tukin taxi ba. Wani lokacin ya ganshi zaune cikin mota da wata cute lady amman baya ganin fuskanta, kuma tun ranan yabar zama da bodyguard dinshi balle yakara jin abinda Abdul zaice.

Dazun ya kira Khalid yana gaya mashi abinda ke faruwa amman daria ban haushi ya dinga yi mashi yana cewa nasha gaya maka ka bar bari bodyguard dinka suna ganin girmanka don irin wannan amman bakaji. Maganan Khalid haushi ya bashi don basu gama maganaba ya kashe wayanshi.

Yau yayi daidai da sati daya da maganan, ji yayi kaman he's going insane. Bayan ya dawo daga sallan ishai ya zauna falonshi sannan ya kira Abdul,

" meet me now!" Yace MASHI bayan ya dauki wayan.

Jikin ba kwari Abdul ya shiga falon kasancewan yasan password din kofan. Da sallama yashiga Salem ya amsa Mashi, bayan ya zauna Salem ya kalleshi sannan yace

" Abdul wane irin charm kasa abakinka kafin ka bani shawaran kwanaki baya?..." Da sauri Abdul yace

"Sir wallahi babu wani asiri...sir am sorry..." Daga mashi hannu Salem yayi sannan yace

"Yanzu ba lokacin bada hakuri bane...inason ka yimin bayanin plan din..." Dan girgiza kai Abdul yayi before saying

"Sir da ka bar maganan kawai..."

"Abdul am not a patient person so don't play dumb with me..." Ya fada afusace, jikin Abdul na rawa yafara cewa

" sir... Gani nayi tunda kanason samun mata dazata soka don Allah...shine nace ahaka bazaka gane masoyiyarka na gaskiyaba...." Salem ya katseshi dacewa

"Nasan wannan part din...I want you to hit the nail at head and stop beating around the bush" Abdul dan gyaran muryan yayi sanna yace

"Sir cewa nayi kayi pretending kai talakane for a while..." Salem ya sake katseshi da cewa

"Abdul banda abinka kawai daga nayi pretending ni talakane said in gane mai sona?..." Dan girgiza kai Abdul yayi sannan yace

" ai sir ba haka nake nufiba...Ina nufin kayi pretending ka maida kanka taxi driver.... " daga kai yayi ya kalli reactions din Salem sannan yacigaba dacewa

" na Dan lokaci nasan insha Allah zaka hadu na mai sonka ba don abinda hannunkaba" Salem kura Mashi ido yayi for a while sannan yace

"Yanzu Abdul kasan cikin kasan nan daidaikune basu sanni ba sannan kasan in na fita ko hour day a bazanyiba zaayi kidnapping dina...ko ka manta saboda tsaro nake daku?" Ahankali Abdul yace

"Sir...ai ba a haka zaka fitaba dolene zaka danyi disguising kanka yanda bazaa ganekaba tunda kasan in har kafita a haka ko ba mota babu Wanda zaiyi maka kallon talaka cos everything about you look rich.." Maganan Abdul dariya tabashi don saida yadan dara

"Wai everything about me look rich..." Shima Abdul dan daria yayi, Salem shuru yayi acikin ranshi yana tunanin this might be fun cos sauran sati biyu ya fara annual leave dinshi kuma wata uku zaiyi, da yayi niyyan zaije yola yayi masu sati daya sannan ya wuce San Francisco daga nan ya wuce ummura Amman yanzu zaibi shawaran Abdul at least ko bai samu mataba zai samu more experience akan rayuwa.

Kallon Abdul yayi sannan yace

"Alh Abdul wane gari zamu..." Da Sauri Abdul yayi murmushi tare dacewa

"Sir duk garin da kakeso..."

"Ka bar cewa duk garin da nakeso cos kaima you are involved... So ka zabamana inda zamu" shuru Abdul yayi kaman mai tunanin sannan yace

"Sir muje Adamawa garinku tunda suna da beautiful ladies..." Dasauri Salem y girgiza Mashi kai

"Kai alh forget about beauty wane dare jemage bai ganiba...sannan kasan ba disguise ba ko ubanme zanyi bai hana first love sanin ina garin...so choose again" shuru Abdul yasakeyi for a moment sannan yace

"Muje garinmu" kallonshi Salem yayi sannan yace

"Na mance wane garinema?"

"Kano" Abdul ya amsa mashi, I do Salem ya kwalo sannan yace

"KANO?!!"

"Yes sir" Salem shuru yayi kaman mai tunanin wani Abu

"Kaima alh Abdul ina zan Iya taxi a garin Kano tunda ba sanin garin nayiba ...wait a second meyasa ka nacewa taxi driving alhalin dakwai wasu aikinyi kaman ...." Sai yayi shuru don baisan example din da zai badaba, cikin zolaya Abdul yace

"Kaman sharan titi..." Dariya suka farayi sannan abdul ya cigaba dacewa

"Ko kwasan toilet...." Bai karasabha Salem ya jefeshi da pillow da ke kusa dashi yana daria, saida suka sami nutsuwa sannan Abdul yace

"Sir abinda yasa ka ga na nacewa taxi driving shine yana bawa mutum daman samun address dinmutum sannan karka damu wurin gane garin cos I will be besides you all through the way"

๐Ÿ’šโ™ฅ๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’š๐Ÿ’›๐Ÿ’™โ™ฅ๐Ÿ’œ

ยฎzuwairat(ummu maryam)

5โƒฃ

"Subhanallahi" wata beautiful mata dake zaune balcony din saman bene ta fada lokacin da ta ga abinda ke faruwa cikin tsakar gidanta.

"Inna lillahi waina ilaihi rajuun" ta kara fada tana mikewa tana komawa daga bakin balcony don kara tabbatar da abinda idonta ya gane mata, don akasan benen wata yarinya ce wacce bazata wuce shekara 18 ba ta watsa wani mutum dake wanke wani jeep ruwa ajiki.

Afusace Matan tace

"Me nake gani haka...what's happening?" Tambayan data jero masu kenen Amman yarinyan bata juyo ba balle ta amsa mata sai nuna mutum da ta watsawa ruwan take tana cewa

"Yanzu ya kaji ajikinka?...don dabbanci Ashe karasa abinda zaka wanke sabon murano dina sai detergent?. โ€ฆ" ahankali mutum Wanda zaiyi shekara 40 yace

"Allah ya huci zuciyanki...wallahi car wash ne ya kare...Ku..." Bai karasa ba ta katseshi da cewa

"To sarkin jahilai data kare agidan nan sai ya kare a kasuwa ko?..to wallahi...." Bata karasaba Matan saman bene ta kara cewa

"Wai badaku nakeba?!" Tafada atsawace. Mutum Wanda sai rawan sanyi yake a sanadiyan ruwan sanyin da aka zuba mashi ya daga kanshi ya kalli Matan dake saman bene sannan yace

" Hajiya don na wanke motanta da klin shine ta watsamin ruwan klin din a jikina" yafada kaman zaiyi kuka, Matan komawa baya tayi da alaman kasan bene zata sauko , yarinyan tana juyawa taga babu Matan saitayi saurin komawa cikin don kar matan tarisketa, itama matan sauri take don tasan halin yarta, lokacin daga suka hadu afalo

"Ameera da gaskene abinda umar yafada?" Ta tambayi yarinyan fuskanta babu alaman wasa, Dan matsawa baya tayi sannan tace

"Mummy he wash my brand new jeep with..." Bata karasaba Matan ta sharara mata mari Wanda yasa kunnenta tsaya jin, yarinyan dafa kunnenta tayi tana kuka tana kiran daddy.Matan tacfigaba dacewa

"Maimaita abinda kikace..." Yarinyan batace komaiba sai kiran daddy take

"I said repeat what you said" ta daka mata tsawa, da sauri tafara cewa

"Mommy kiyi hakuri...ruwan klin na watsa mashi..." Wani Marin Matan ta kara mata, wani irin rikitaccen ihu ta saki still tana kiran daddy

"Ameera kika zubawa age mate din ubanki ruwa?..ameera rashin hankalinki ya kai haka? ...ni like son jawa zagi a garin?...." Cikin kuka tace

"Ni ba saan ubana bane..." Wani irin mutum duka matan ta kaimata, aikam nan yarinyan ta kwanta kasan ta rolling tana kuka tana kiran daddy na...ihunta yasa wani mutum tahowa daga saman bene da gudu don har neman silbewa yake don sauri

"Ameera daddy meya faru?" Ya tambayeta, tana ganinshi ta tashi da gudu ta fada jikinshi, riketa yayi ya sake cewa

"Ki gayamin abinda ke damunki" dakaji yanda yake magana kasan yana cikin tension kuma kasan bai hada wannan yarinyan da kowaba. Matan bata kalleshiba tashigaba dacewa

"Ameera ba baki nayi makiba Amman ke macece kuma in har baki bar wannan halin ba shi zai jamaki wahala" wani dan saurayi ne Wanda bazai fi shekara 12 ba dake zaune kan dinning da alaman yana homework Yayi saurin cewa

"Mommy jiya ma dan tace ya siya mata Mtn na 1k ya sayo na 5 hundred guda biyu tayi ta zaginshi tana cewa jakki jahili..." Ran Matan kara baci yayi ta nufe, ameera bayan daddy ta boye, shikam daddy ya hada rai sannan ya kara cewa

"Wai me kika yi take dukkanki kaman jakka?" Ya fada afusace, cikin kuka ameera tafada cewa

"Daddy wai dan umar mai wankin mota ya wanke motata da klin na zuba mashi ruwan ajikinshi shine mommy take dukana" afusace babanta yace

"Wai dan ki nunawa mai aiki Laifinshi take dukanki?" Cikin shagwaba ta dagawa ubanta kai, mutumin jiyawa yayi ya kalli Matan , itakam Matan ko kallonshi batayiba ta banbare ameera daga jikinshi zata kara dukanta mutumin yayi saurin rike mata, yana cewa

"Wai meye haka...ki bar dukanmi daughter don ta nuna..." Bata bari ya karasa ba tafara cewa

"Wallahi alh ka barni in hukunta yata tunda bakai zaa zagaba...nice uwa kuma nice zaa zaga..haka wannan yar iskan yarinyan tajtaza zana tattoo kaman wata karuwa amman ka hanani hukunta..." Mutumin Dan daria yayi sannan yace

"Hajiya banda Africa mentality.. Daga tattoo sai yarinya tazama yar iska?..kullum INA gayamiki yarainta ke damunta...watarana ko ance tayi bazata yiba...so...." Cikin fada Matan tace

"Ba wani yarinta...kawai kana goya mata baya..yanzu Aisha bata ganin uban kowa da gashin arziki...to wallahi gidan nan ni dakene..ko ki chanza ways dinki ko kuma in hallakaki dan wallahi bazan haifi yar dazata jamin tsinuwa ba..." Tana kaiwa nan ta hau stairs tabarsu, ameera cikin kuka tafara cewa

"Daddy ka kaini gidan anty Safiya...mommy bata sona" dan rarrashinta daddy yayi sannan ya haura daita dakinta, wani irin harara ta watsawa yaron

" affan zan kamaka" tacewa yaron.

Ameera dai irin yanmatan nan ne dabasu ganin kowa da gashin arziki mussaman in kana karkashinsu, daka ganta saika rantse yar barikice don komai nata irin nayan bariki, don har tattoo gareta abayan wuyanta, a bangaren samari kam babu namijin dazai ganta ya kauda kai, amman wulankanci kam kaman daita aka hallinceta don zagi kwando2 taiya kuma dad dinta is hundred percent behind her, kyakyawa ce na gidan karshe . Tana 200 level a b.u.k She's the first born sai kaninta affan Wanda Sam ba halinsu dayaba

๐Ÿ’›โ™ฅ๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’›โ™ฅ

"Ma-mi am going.. Kuma insha Allah in aka bani kudi yay zan sayo maki inhaler dinki" inji wata yarinyan da ke tsaye ratayi da dan tsohon handbag, da ka kanta kasan ba bahaushiya bace, yarinyan tana da kyau Iya gwargwado don bakace, Amman inda zata sami hutu zatayi kyau fiye da yanda take, mata dake zaune kan wata tsohuwar kujera tace

"Tawakaltu..." Yarinyan ta amsa tana rusunawa kusa da Matan sannan Matan tasake cewa

"Ki dawo lafiya" ahankali yarinyan yace

"Ameen mami" yanda take maganan ya nuna tana da respect, dan rungume matan tayi sannan ta fita daga dakin room and parlour, tana fita tsakar gidan naga ashe gidan mutane ne dayawa don dakunan dake gidan zasuyi takwas kuma da ganin duk ciki da falone, wata mata dake wankeke ta gaida cikin girmamawa sai naji matan tace

"Toyin ..zaki tafi" sunan da aka kirata ya tabbatar min cewa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login