Showing 24001 words to 27000 words out of 145230 words

Chapter 9 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

239

kam tunani yake

_"Anan princess dina ta rayu...ranakun wahalanki a numbered"_yafada cikin ranshi, gani yayi wata mata tafito daga cikin dakin, sauka yayi daga kan kujrean dayake ya durkusa ya gaidata cikin girmamawa amsawa tayi da murmushi fuskanta har iyayenshi ta tambaya ,sannan ta juya zata koma ciki Dan kara juyawa tayi ta kalleshi sai ta lurada yanda hannuwanshi da kafafunshi suke fari kal sai tayi tunanin kilan wahalan rayuwa ne yasa fuskanshi baki.

Bata dade da shiga dakiba tawa ta dawo, maltina yaga ta ta fiddo daga cikin ledan hanunta, Dan murmushi yayi sannan yace

"Irin wannan tarban haka.." Murmushi kawai tawa tayi tashiga kurya ta dauko wani plastic cup ta Juye maltinan sannan ta durkusa ta mika mashi, amsan cup din yayi tare da hadawa da hannunta, da sauri ta janye hannunta saboda wani taushi da shocking dataji.

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’™โค๐Ÿ’›

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค

ยฎzuwairat(ummu maryam)

1โƒฃ9โƒฃ

Tawa komawa tayi ta zauna har lokacin bata dainajin shocking ba, Salem murmushi yayi ya kai cupin bakin shi, wani irin daci yaji don tunda yake wannan ne karo na farko daya sha maltina, hadiyewa yayi, sai yaji makogaron shi nayi mashi zafi, cikin ranshi yafara cewa

"Allah yasa kada wannan abun ya zama ajalina" da kyar ya kara sha akaro na biyu fuskanshi kaman na mai shan giya. Gefe ya ajiye, tawa kallon shi tayi

"Sir ka shanyeshi.."

"Indai bakison daukan gawata kin barni haka nan" yafada cikin ranshi sannan yadan harareta

"Nagode" saida ya Dan goge bakin shi da bayan hannunshi sannan yace

"Oremi dauko pen Muyi list din" mikewa tayi tashiga ciki, few minutes later ta dawo da pen da paper. Zama tayi kasa a gabanshi zata fara rubutawa yadan taba kafadanta ta daga kai, alama yayi mata dasu tafi waje, girgiza mashi kai tayi , shikuma yace

"Please" da ba kowa zaijiba, mikewa ta karayi tashiga ciki tacewa mami sun tafi kasuwan

"Ku dawo lafiya" yaji mami tace cikin hausanta mara fita, tawa tafito

"Mu tafi" ta fada mashi murya chan kasa, kaman yana jira ya mike har ya rigata fita tabi bayanshil.

Yana fita ya bude mata murfin mota Amman taki shiga

"Ki shiga mana" ya umarceta,Dan girgiza mashi kai tayi

"Ka rufe in bude da kaina" Dan daria yayi

"Laifine mutum ya budewa budurwan shi mota.."

"Ni ba budurwan ka bace.." Ta katseshi tana murmushi

"To laifine mutum ya budewa friend dinshi mota?"

"Ai ka girmeni.."

"Nasani Amman inason bude maki cos you are a lady" gyara tsayuwanta tayi

"To mu kwana anan" bashi da choice dole ya maida ya rufe ya zagaya yashiga cikin ranshi yana tunanin

"Daman haka suke kodai she's just kidding with him" shiganta cikin motan ya katse mashi tunani.

Kallon ta yayi

"Oremi please taimakamin zakiyi..kiyimin list din abubuwan da mace kamanki zata bukata in ita kadai ke zaune kuma bata fita" tawa kallon tuhuma tayi mashi sannan tace

"Ban gane ba?" Dan murmushi yayi

"Sister ta nakeson yiwa siyayya"

"But kace boarding school zata" dan shafa keyanshi yayi don ya mance daya fada mata hakan,

"Oh sorry..Ashe hakana gayamaki..daman aure zatayi to mijin bashi da ko sisi so sai nayi niyyan siya duk abubuwa dazata bukata" baki tawa ta bude don sai ya burgeta

"Amman gaskiya kana da kirki".

" kafin kisanabinda zanyi da kayan kenan" yafada cikin ranshi

"Meyasa kika fadi hakan" ya tambayeta, ahankali tace

"Ai naga kaima hustling kake Amman kasan ciwon yan uwanka" murmushi yayi tawa yacigaba dacewa

"To kayan abinci kawai zamu rubuta?.."

"Aa..dukkan kaya harda nasawa..Amman masu sauki na talaka"

"OK" kawai tawa tace sannan tasake cewa

"Bari mu fara da kayan sawa..atampa bawa zan rubuta" Salem shuru yayi kaman mai tunani

"To..ki rubuta shida..Amman kar kudin su yawuce

2k" ba musu tawa ta rubuta sannan tace undie nawa

"Uku each" tawa ta rubuta pant da bra uku,

"Gyale fa" ta tambayeshi, Dan girgiza kai Salem yayi

"Ai cikin gida take babu inda zata"

"Ok..zaka saya da shadda da lace ko materials?"

"Gaskiya bani da kudin.."

"Turare fa?" Tasake tambayanshi

"Matan kauye basu shafa turare sai Ku Matan birni" yafada

"Matan birnin ma sai masu halin" tawa tafada cikin ranta

"Kayan kwalliya fa?"

"Bandasu"

"Amman at least ka sayamata man shafawa ko?"

"To rubuta mata Wanda kike shafawa indai bashi da tsada"

"Cocobutter ne kuma karamin 600"

"Rubuta mata babban" ta rubuta

"Yan kunnefa?" Ta sake tambayanshi

"Nawa kudin na kunnenki?" Ya tambayeta yana nuna bariman dake kunnenta

"250"

"Babu Wanda kudin ta bai kai hakaba?"

"Da akwai mana..har na 70 naira da akwai"

"Kirubuuta na 70 guda biyu" ta rubuta.

"Mun gama da kayan sawa now kayan aikin gida..set din tukunya zamu rubuta?" Ido Salem ya zaro

"Me zatayi da set..kawai rubuta kwano, cup , spoon, pot, knife,.. Hmmm saime kuma..rubuta bibbiyu " duka tawa ta rubuta su

"Yarda broom da dustbin ko?"

"Eh yauwa na mance su..".

Haka tawa ta dinga lissafa mashi kayan aikin gida suna rubutawa,

"Sai su gado da kayan daki" inji tawa

"Wane irin gado..kawai rubuta student foam sai ledan daki sai curtains masu sauki don ba kudin gareniba" ta rubutasu

"Sai abinci" tawa ta fada mashi

"The fun part" ya fada cikin ranshi, kallon ta yayi sannan yace

"Kaman ke kina iya cinye buhun shinkafa cikin wata hudu?" Ya tambayeta, ido ta zaro

"Kam ina hauka?..gaskiya bazan iyaba...why do you ask?" Dan jinginawa yayi sannan yace

"Ai don insan irin yawan rice din da zan saya mata,..lissafamin kayan abinci in gani..ki dinga rubuta su"

"OK" ta amsa mashi sannan ta fara rubutawa tana cewa

"Rice, macaroni, spaghetti, indomie.." Da sauri Salem ya katseta dacewa "banda indomie...ni ban ciba balle in sayawa wani...cigaba" Dan murmushi tawa tayi sannan tacigaba

"Garin tuwo, kuskus,.." Salem ya kara katseta

"Nifa ba kayan birni nace ki rubuta ba..kawai rubuta irin garin danwake, alkubus.." Kayan gargajiya Salem ya dinga lissafawa kaman yana cinsu itakuma sai rubutawa take.

"Sai kayan miya..." Ta fada mashi bayan ta kammala rubuta kayan abinci

"To ki fadesu inji" Salem ya amsa mata yana kallon bayan wuyanta da ya dana bayyana, wasu kananun gashi yagani kwance har bisa gadon bayan ta, sai yaji tana cewa

"Kuka, egusi..tasshi, maggi, gishiri,albasa..." Suma haka ta rubuta su, data rubuta mai tsada Salem yace ta gogeshi don bashi da kudin siyansu.

"Mun gama..." Ta fada mashi,

"Kawo su in gani" ya fada mata yana lumshe sexy eyes dinshi kaman mai jin bacci, mika mashi tayi, amsa yayi ya kara hadawa da hannunta, wannan karinma janyewa tayi da sauri, saiyaga ta hada giran sama sana kasa

"Sorry..mistake nayi" yace mata, batace komaiba, kallon list din yayi

"Wow..kina da fine handwriting..ki gama uni ne..?" Kallon shi tayi for few seconds sannan ta sada kanta kasa

"Ka taba gani degree holder yana saida abinci a restaurant?" Shuru yayi bai bata amsa ba tacigaba dacewa

"Ka taba ganin talaka yayi degree?" Salem saiyaji jikinshi a mutu

"Nayi maki alkawarin zaki gaji da karatu" ya fada cikin ranshi sannan yace.

"Ai with Allah komai ma is possible" yafada ahankali

"Hakane" ta amsa mashi sannan ta kara cewa

"Amman kai kayi karatu sosai" dan murmushi yayi sannan yace

"Kin taba ganin degree holder yana tukin taxi?" Tawa dan daria tayi

"Ai Nigeria kenan everything is possible..Amman seriously kayi karatu"

"Meyasa kike ganin kaman nayi karatu?" Ya tambayeta

"Ai naga turancin ka mai dadi" nikam nace dan baki ganshi a office ba.

"Ai yau da gobe..yanzu lissafamin kudin kayan nan da wayanki" yafada mata don abar maganan cos shi mutum ne Mara son karya kuma in ya fada mata baiyi karatuba karyan kara yawa zaiyi tunda doctorate gareshi.

Kara amsa tayi tafara calculating da wayanta don dukkan kayan ta rubuta harda kudin su, bayan kaman minti goma ta daga ta gan yanda ya kurawa bayan wuyanta ido, ahankali ta maida gyalenta daya fadi daga kanta sannan tace

"Gaskiya kudin dayawa" ahankali Salem yace

"Nawa" yafada kaman mai rada

"72k" wara idanuwa Salem yayi kaman Wanda bai taba ganin irin wayannan kudin ba

"Gaskiya oremi.. Duka kudina 70k..suma na kusa shekara ina tarasu" ahankali tawa tace

"Yanzu me zamuyi?" Ta tambayeshi kaman its her problem

"Mu rage wasu kayan.." Dan daria tayi

"Ai dukkan kayan are important.. Wane kake ganin zamu rage" kallon ta yayi eyeball to eyeball sannan yace.

"Underwears" da sauri tawa ta kauda kanta

"anya wannan mutumin ba dan iskabane?..."

"I heard you" ya fada mata ido tawa ta zaro don atunaninta maganan zuci tayi,

"Kasan basai mun rage komaiba..ina da kudin da nake tarawa saboda kudin hayanmu...zan baka 2k sai ka kara.." Mamaki ne kwance kan fuska Salem don kasa boyewa yayi

"In lokacin biyan kudin yayi kuma ban baki bafa?" Ya tambayeta yana karajin sonta cikin ranshi

"Ai insha Allah zan samu wasu kafin time din..." Shuru yayi yana tunani kala2 cikin zuciyanshi

"OK" yace mata.

Fita tayi daga cikin motan ta shiga gida, bayan kaman minti biyar ta fito da kudin, saida ta shiga motan sannan ta mika mashi, amsan kudin yayi yaga yan Dari bibbiyu ne guda goma

"Thanks... Zan biyaki..I promise"

"Ba sai ka biyaniba...so yanzu zamu tafi kasuwane ko yaya?" Shuru yayi ya kalli waje yaga yanda rana ke shining yasan ko kashe shi zaayi bazai Iya shiga rana ba

"Kawai ki barshi da yamma zan shiga kasuwa tunda yanzu zuhr ya kusa"

"Amman cemin kayi bakasan kasuwa ba" kara shafa kanshi yayi

"This gal is smart" yafada cikin ranshi

"Ai wannan abokin nawa zansa ya rakani"

"To shikenan" ta fada feeling disappointed don har lokacin bata gaji da ganinshi ba.

"Rubuta min number ki bayan takardan" yafada mata don yasan da zaran ya fidda wayanshi asirinshi zai tonu. Ba masu ta rubuta mashi kasan list din sannan sukayi sallama, ko wannensu da tunanin dayake.

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค

Ranar da Salem yabar gidansu ameera dad ya maidata gidan kanwanahi dake sharada, duk yanda mom tayi yabar ameera gidan ki yayi

"Bari in kai yata inda zaa bata kulawan da amare ke bukata" yafadawa mom. Suna isa gidan dad ya ajiye ameera ya koma, kanwa dad irin wayyanyun Matan nan ne, don tun ranar tafara durawa ameera kayan mata masu kyau da tsada sabanin wayanda tasha abaya,

"Yarinya kisha kiyi tatul don daya dandanaki bazai kara shaawan wata ya mace" inji anty Sadiya kanwar dadi.

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค

Salem dawowa daga gidansu tawa, Abdul ya kira ya mikawa list din tare da cewa

"Alh inaso kayi typing din wannan ka turawa agent dina...ka gaya mashi ya sayi dukan kayanan ya ajiyesu cikin wannan gida...and tell him ban yarda akara ko arage wani abu ba"

"Yes sir" abdul ya amsa mashi. masjid ya wuce, yana dawowa yashiga shiga bedroom dinshi wayanshi yafara ringing, murmushi yayi don yasan ummanshi ce

Yana picking yaji tana cewa

"Son what's happening??" Ahankali yace.

"First love ban ganeba..meya faru?" Cikin fada Umma tace

"So you are asking me ko?" Ahankali yakara cewa

"Umma bansan abinda nayiba ko" yafada cikin shagwaba,

"Mutane nata kirana da abbanka sunayi mana congrats wai zaayi aurenka this coming Saturday!?" Salem baki ya rike sannan yafara kalle2 cikin dakin kaman mara gaskiya.

_Nagode kwarai da irin kulawanku, Allah yasaka maku da alkhairi_

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค

ZAKISAN KONI WAYE

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’™๐Ÿ’œ๐Ÿ’š

ยฎzuwairat(ummu Maryam)

2โƒฃ0โƒฃ

Dan daria karfin hali yayi

"Umma aurena kuma?..."

"Kai wallahi kasa na sauka garin Kano yau ranka sai yafi nakowa baci...wato maganan daria na fada maka..." Tafada cikin fada, daka ji muryan ta kasan ciki tension take kuma dajin muryan ta kasan Matan nan ne masu tsiwa, ahankali Salem yace

"am sorry first love.. Amman in zanyi aure baku zakuyimin aureba?...ta yaya zanyi aure bada saninkuba?..please Umma ina kika samu wannan labarin?" Ya fada yana kwalo idanuwa, daka ganshi kasan ko kadan bashi da gaskiya, Umma Dan ajiyan zuciya tayi sannan tace

"Habibi nasan its impossible,..tunda safe mutanen Kano ke ta kiranmu sukayi mana murna ...cewa suke anata sanarwan auren Salem Yusuf sulaiman..."

"Amman Umma mutane da gulma suke...ni kadai ne Salem Yusuf sulaiman? Ai Umma da akwai masu irin sunana da yawa..so just relax" yafada yasauraron abinda ummanshi zata ce next

"I know don abbanku ma baudamu ba..Amman son kazo yola wannan week end" shuru yayi yana tunanin tawa don yanzu ya dauki aniyan zuwa wurin ta kullum har sai ya gama gwadata

"Kaji habibi..I want you in yola Friday night" yaji muryan ummanshi nacewa

"Amman first love ina da aiki dayawa fa.."

"I said I want you here Friday night... You can go back to your duties by Monday?" Ta daka mashi tsawa

"Yes Umma" yafada, Amman da jin muryan shi kasan bayaso. Katse wayanshi yayi , yana kumbure2 kaman agaban ummanshi yake, yana ajiye wayan yafara wani ringing, dauka yayi yaji ana cewa

"Congratulations sir...." Bai ce komai ba ya katse wayanshi, bai gama katsewaba dayan wayan yafara ringing, dubawa yayi yaga Khalid

"Guy how far" yafada bayan yayi picking

"Ango.. Ango..zancen aurenka ya bade Nigeria harda ketare..."

"Wai wake yadawa?" Salem ya tambayi Khalid

"Wai a gidan radio...wasu course mate dinmu suka kirani suna son jin party da zamuyi..." Dariya Salem yayi

"Ashe party.." Shima Khalid dariya yayi

"Eh mana..at least kabamu dama mu girgiza waist da yanmatan mu..."

"Wallahi ka sake kayi organising wani party to karshen friendship dinmu..." Wani darian rainin hankali Khalid ya karayi

"Dalla haka kake magana kaman bazaka yi sex da yarinyan ba..." Murmushi Salem yayi tare da cije lebenshi na kasa

"Ai gara dakace sex don kasan da akwai banbamci tsakanin sex da love making.. Kuma ina tabbatar maka.. Ko itace karshen mata..."

"Haba kana fadi ne kawai...yanda kake fama da shan magunguna sai kasamu mace kaki biyan bukatanka?" Salem banza yayi dashi Khalid yacigaba dacewa

"Wallahi guy ai babu abinda zakayi mata ta dinga kuka sai sex every now and then.."

"Dalla in baka da abun cewa get off my phone... Yarinya data kirani son of a bitch zan taba...yarinyan datacemim motanta zai sayi uwata da ubana zan taba..Ni kasan ba Mara zuciya bane...wallahi ban da niyyan auren ta kawai narasa hanyan mallakanta ne..." Shuru Khalid yayi sannan yace

"Ai yarinyan nan bakai kadai ta taba ba..Ni ma haushinta nakeji...let's forget about her and say something important... Ya yar Yoruba" dariya Salem yayi sosai don wani sanyi yaji cikin ranshi

"Yanzu na baro gidansu..munyi list din abubuwan da wannan shaidaniyan yarinyan zata bukata...kasan guy in bansami Tawakaltu ba sai rijiya.." Cikin daria Salem yace

"Really in love ko?" Salem kwantawa yayi tare da lumshe idanuwa, yafara bawa Khalid labarin yanda tawa ta bashi 2k, daria kawai Khalid yake Salem yacigaba dacewa

"guy inason biyan yarinyan nan in cash and in kind...guy oremi is so beautiful... Bansan da akwai beauty cikin bakaken mataba sai yanzu.." Shuru yayi Khalid yace.

"Yace daman black beauty special suke..." Salem ya kara cewa

"Best duka jikin ta da akwai wasu gashi kwantattu..." Daria Khalid yayi da karfi

"Guy ya akayi ka gan gashin jikin ta.. Kodai kana shan minti.."/

" kai Aa Amman gaskiya yarinyan tana tadani dayawa..ban tabaji ina bukatan aureba sosai sai yanzu.. " ahankali Khalid yace

"Allah yasa su Umma su yarda"

"Hmmm in basu yardaba ai sai dai su dauki gawata...she's the best part of me"

"Nidai mu bawa malamai kudi sufara yimana aduan amincewan Umma don kasan yanda Umma take.." Salem shuru yayi da dan lokaci sannan yayi ajiyan zuciya

"Nima itakadai nake tsoro... Nasan Abba bashi da case...Amman zanji yola this weekend.. Zanyi mata maganan inji abinda zatace.."

"Am wishing you best of luck" ahankali Salem yace

"I will need it" katse wayanshi yayi sannan ya saka hannu cikin aljihunshi ya fiddo kudin da tawa tabashi ya bude wani briefcase mai dauke da mint na 1k da dollars ya saka kudin daga gefen jakkan.

Fita yayi daga dakin ya koma waje ya samu Abdul yana typing din list din daya bashi, amsan list din yayi ya rubuta number tawa cikin wayanshi sannan yace

"Alh. Kar ka rubuta atampopin..anjuma zan baka 12k ka shiga kasuwa ka sayomin yan 2k kusa 6"

"OK sir " Abdul yace mashi sannan ya koma ciki.

Kwantawa yayi tare dayin rub daciki sannan yafara dailing number tawa.

๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’œโค๐Ÿ’™

Ameera ce zaune cikin wasu kawayenta da suka ziyarce ta gidan anty Sadiya, shewa kawai suke

"Amman ameera na tausayawa Salem yanda baki da mutuncin..." Zeenat bata gamaba ameera ta tari numfashinta

"Ke banson kutumar burouba...ubanme nayi na rashi mutunci...wallahi..." Bata idaba anty Sadiya ta kawo mata wani magani cikin cup, amsa tayi ta shanye, dariya kawayenta sukayi wata tace

"Shegiya ameera sai zukan magani kike ko tsoron abinda zai biyo baya bakiyi" baki ameera ta tabe

"Me zai biyo baya...banda first

night" daria zeenat tayi

"Ke irin tsoron da amare keyi sam bakiyi...kuma ance first night wahala akesha" dan lumshe idanuwa ameera tayi tana imagining yanda ranan zai kasance cos kaman ta jawo ranar take ji, don tunjiya da antyn ta tafara bata wasu special magani takejin kaman wani abu na yawo cikin wandon ta, ahankali tace

"Karku damu angona will be romantic.."

"Yanzu ya zancen karatunki?" Daya daga cikin kawayanta ta tambayeta,

"Wane karatu zanyi bayan ga already made guy...daman dan kudi ake karatu nikuma yanzu am the wife of the richest man in Africa...so to hell with school" wata cikin kawayenta dan hararanta tayi, irin kawayen nan masu bakin ciki da karuwan dan uwansu. Saida ta gama wulla mata dirty look sannan tace

"aini abinda ke bani haushi wajen wannan auren shine babu wani party ko shagalin da zaayi..." Wani irin disgusting look ameera ta watsa mata

"Meye najin haushi kaman auren uwarki zaayi..."

"Ke ballagaza karki zageni dan nazo wurin ki.."

"Naje na zageki kuma wallahi kiyi min maganan banza in kulleki da uwarki da ubanki don ba ameera da

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login