Showing 114001 words to 117000 words out of 145230 words

Chapter 39 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

281

shiga ciki, kan dinning suka tadda tawa tana breakfast, gefen ta ya zauna bayan yayi mata kiss, ameera kam a falo ta zauna taki cin abinci cos ita gida kawai, duk yanda Salem da tawa sukayi don taci abinci ki tayi. Salem tea kawai yasha, kara kallon agogon hannun shi yayi, kallon tawa yayi

"Baby anya zan Iya I can come back yau?... Yanzu 12:30...Nigeria will be 5:30.." Ahankali tawa tace

"Take your time..." Mikewa yayi itama ta mike kallon wayan daya ajiye kan cushion yayi

"Yauwa baby replace this phone with yours..."

"Thank you " kawai tace, ta nufi wurin ameera, itama ameera mikewa tayi suka rungume juna, sai tawa ta fashe da kuka, Salem ne ya rabasu ya rungume ta for a while, ameera fita tayi, bedroom ya kaita ya zaunar daita bakin gado

"Princess ki huta ..you deserve it..." Yafada yana kwantar da ita, kuka tacigaba dayi

"Yanzu maidata zakayi da gaske?..."

"Please princess we have been over this..." Yafada yana manna mata kiss Sannan ya fito tare da Jan kofan, magana yayi wa Mrs Samuel kan ta zauna da Tawakaltu har ya dawo kuma ta amince.



Yana fita ya hau jet ameera tabi bayan shi.

Around 9pm suka isa gidan shi na Kano dama ya fadawa Abdul ya jirashi da motan shi, suna sauka babu bata lokaci Abdul ya maida kaya cikin mota suka kama hanyan gidan ameera su ameera. Salem sai kallon ta yake ita kam kaman motan bai gudu takeji.

9:40 suka isa gidan, sai Salem ya tuna lokacin da ya fara zuwa gidan, kaman jiya, horn Abdul yayi mai gadi ya bude don ganin waye, yana ganin ameera zaune bayan motan yayi saurin wangale gate, shiga Abdul yayi ya parka motan gefe daya, da sauri ameera ta fito tana cewa

"Daddy!... Mommy!... Affan!..." Ta dinga kira da karfi tana shiga ciki da gudu.

Acikin falo dad ne da affan, mom kam tana upstairs,

"Dad kaman ana kiran sunana...." Inji affan, dad banza yayi dashi, da gudu suka ga ameera ta shigo, dukkan su mikewa sukayi, batayi wasting time ba ta fada jikin dad, at that moment sai dad da affan suka zama motionless, don gani suke kaman mafarki suke, da sauri affan ya hau sama yana kiran mommy,

"Mommy... Ga anty ameera nan...." Zumbur mom dake zaune kan praying mat ta mike

"Ina?.." Ta tambayi affan

"Downstairs..." Mom bata kara cewa komaiba ta fita dakin da sauri affan ya biyo bayanta, har lokacin ameera na rungume da dad tana ganin mom tayi saurin sakin dad ta fada jikin mom sai ta fashe da kuka, mom rungume ta tayi kaman zata maidata ciki

"Baby daga ina kike?..." Ta tambayeta, cikin kuka tace

"Mom tare muke da sir Salem..." Da sauri dad ya fita don zuwa shigo da salem, baa dadeba suka shigo tare, durkusawa yayi ya gaida Umma dukda yasa in tayi gudun tsiya ta kai 40, zama yayi,Umma sai kallon ameera take, affan zuwa yayi ya tsaya kusa da Salem bayan sunyi shaking hands, Abdul ne ya fara shigowa da kaya, Salem shuru yayi yana kallon ameera dake lafe jikin mom tana, kan dad kasa shi ga boss a gidanshi, bayan Abdul ya gama shigo da kaya Salem ya kalli affan,

"Little bros...excuse us..." Ya fadawa affan,

"Ok sir... But remember my promise.." Ya fada yana hawa stairs, dariya Salem yayi

"Don't worry.. Am a man of my word..." Ya fada, bayan affan ya tafi ya kalli mom don itace main concern dinshi, as for dad he can goto hell,

"Hajiya da akwai maganan da zanso fada maku amma ina ganin is late already..." Bai idaba dad ya katseshi dacewa

"Ai in baka takuraba shikenan..." Salem murtuke fuska yayi Sannan ya fara basu labarin abinda ya faru tsakanin shi da ameera har izuwa yanzu daya kawota gidan, ya kara dacewa

"So ina Neman yafiyanki amatsayin ki na mom dinta...nasan na shiga hakkinki...ki yafemin...kuma Allah ya bata mijin da dayafini...." Tunda ya fara magana dad ya sadda kai kasa, sai lokacin yafara danasanin tarbiyan da ya bawa ameera, hawaye ne ya gangarowa mom, Ahankali ta goge Sannan ta fara cewa

"Alhamdulillah... Allah na ganin I tried my best in bata tarbiya na gari..amma inayi dad dinta na rushewa...nagode wa Allah dayasa ka zama sanadin shiryanta...ko kadan raina bai baci ba..Allah ya saka maka da alkhairi... Don nasan inda aljani ko wani mugun mutum tayiwa haka bazata kai labari ba...so once again thank you.." Tafada tana kuka, itama ameera kuka ta dingayi sosai, kneeling tayi tafara cewa

"Mommy am so sorry... I promise to be a good a girl..." Da sauri mom ta rungume ta, Salem sai ya tsinci kanshi da tausayi da kuma jindadi, dad kam hawaye ya farayi amma babu Wanda ya gani cos kanshi na kasa,Salem yakara cewa

"Babu idda akanta..." Duk sun gane abinda yake nufi,

"Samun irin ka a mazan zamani zaiyi wuya... Mungode..." Mom tayi adding, mikewa yayi

To nima nagode for your understanding...zan wuce sai na sake zagayowa.. " ya fada yana takawa ahankali, ameera mikewa tayi tabi bayan shi, har bakin kofan motan ta rakashi, juyawa yayi ya tsaya yana kallon ta, itama tsayawa tayi kanta kasa, hannu ya bude mata, Ahankali ta taka ta fada jikin shi rungume ta yayi casually Sannan ya saketa,

"I will miss you..." Yafada mata cikin whisper, shuru tayi batace komaiba, cikin mota ya shiga Sannan yace

"Yauwa na mance wannan iPad din is for affan.. And kibani number ki..so that mu dinga gaisawa, " pin dinta ta bashi Sannan ta matsa kusa da motan

"Sir please take care of Tawakaltu.. She's a good person..." Dariya Salem yayi

"I will insha Allah.." Yafada waving dinta yayi itama tayi waving dinshi Sannan suka bar gidan.

๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’š

ยฎzuwairat( ummu Maryam)

7โƒฃ0โƒฃ

Salem relaxing yayi cikin mota duk jikin shi ba dadi don sai yanzu yasan ko baka son mutum rabuwa bata da dadi. Har suka koma gida bai ce komaiba. Suna zuwa yayi wanka ya rama sallolin da ake binshi Sannan ya hau gado yayi ya cire number Khalid daga blacklist Sai lokacin yake ganin messages din Khalid, sunfi talatin, dariya kawai yayi ya fara waya da matarshi.

Itama ameera sam jikinta ba dadi don tasan yanzu babu ita babu Salem,

"Hmmm...I will definitely miss you..." Ta fada cikin ranta daidai lokacin da ta shiga parlour, jikin mom ta kara fadawa dad kam har lokacin yana zaune kanshi kasa,

"Habibty kinga riban wulakanta mutane ko?... Na fada maki amma Sam bakiji.... Ko alhakin maaikatan gidan nan ya isheki...yanzu look what happens..." Mom ta fada tana shafa kanta, ajiyan zuciya tayi

"Mom am sorry... Zan nemi yafiyansu duka...." Tafada cikin sanyin murya,

"Duk baki da laifi...laifi nane.. Duk ni da ja maki..,am sorry daughter..." Inji dad, da sauri mom da duk jikinta yayi sanyi tace

"Alhaji.. Allah ya kaddara hakan zai faru..."

"Dad ka bar daurawa kanka laifi...it was destined to happen" inji ameera data koma wurin dad. Mom mikewa tayi ameera ta mike ta bi bayanta suka hau upstairs,aranan basuyi bacci ba din hira suka dingayi har da affan, shi kanshi affan yaji dadi yanda anty ta chanza don a da bai isa ya tsaya kusa daita ba balle suyi hira.

First thing in the morning ya kama hanyan yola, gidan Khalid ya sauka, Khalid na ganin shi, ya hade gabas da yamma,

"Daman kai haka kake bansani ba?.... Allah yaisa tsakanina dakai..." Salem dariya kawai yayi ya samu wuri ya zauna yana kallon Khalid dake huci, Khalid yacigaba dacewa

"Wallahi Allah ya taimakeka...I intended to take this later to Umma and Abba...."

"Kace masu me?..." Salem ya tambayeshi atakaice

"Kasan sauran..." Baki Salem ya tabe

"Ai is your word against mine....banza Mara hankali..." Salem ya fada yana dariya, tsaki Khalid yaja

"Dalla ina yar mutane?..."

"Tana gidansu...." Afusace Khalid yace

"Haka mukayi da kai?..lallai ka isa dan bakin ciki...don kaji nace inason ta shine ka tashi ka kaita gidansu ko?...no problem.. I will find my way..." Yafada cikin fada, Salem tabe baki yayi

"See dalla relax let's talk like two matured men..." Salem ya fada mashi, Khalid baice komaiba ya dinga girgiza kafa, Salem ya cigaba dacewa

"Please in kasan ba auren yarinyan nan zakayi ba kawai just let her be..." Hararanshi Khalid yayi

"Look who is talking... Kai da ka aureta ka ajiye ta cikin sambiza fa?... Ai kasan ni na fi karfin wannan..." Dariya Salem yayi don shi ko kadan bai daukan abun da zafi kaman yanda Khalid ke ta tada jijiyoyin wuya,

"Ni dai rokonka nake...if you know you are lusting after her then just forget about her..don wallahi if you tries anything stupid zan manta da friendship dinmu in ci burouban ka.."

"Sannu dad..." Khalid ya fada mashi

"Wallahi ba da wasa nake ba...ba dan ban sonta na rabu daita ba...don ko makaho yasan da ameera..." Tsaki Khalid yaja

"Kana sonta ubanwa yasaka rubuta mata saki...kawai in kana bani address dinta kabani and stop all this Bullshits..." Salem bai kara cewa komaiba ya mike

"Ni zanje gaida su Umma kafin in koma..." Yafada yana nufan bakin kofa, da sauri Khalid ya tari gabanshi

"Haba guy...why are you doing this to me...wallahi yarinyan nan son ta nakanyi..." Salem dariya yayi don yanda Khalid yayi maganan,

"Wallahi am serious... Please just give me her address... I promise to take good care of her...kaji daddy..." Salem dariya ya karayi

"Please help me.." Khalid ya kara cewa, kallon manyan idanuwanshi Salem yayi

"In ba karya ba ka taba ganin inda mutum yayi falling in love da wacce bai taba ganin koda pic dintaba?..."

"AI kullum cikin imagining face dinta nake, yanda kayi describing dinta ma ya isheni..."

"Naji...tell Abdul guard dina ya rakaka gidansu..." Da sauri Khalid ya dan rutsuna

"Thank you Abba..." Salem banza yayi dashi ya fita

"Abba kajira in saka kaya muje gaida su Umma mana..." Banza yayi dashi yayi tafiyan shi.

Salem family house dinshi yaje inda Umma da Abba suka nemi jin actual reason dinshi na zuwa Nigeria yayi masu karya da wani emergency meeting ne ya kawo shi, zama yayi ya cika cikin shi Sannan yayi masu ban kwana, karfe twelve ya bar Nigeria.

Ameera kam gari na wayewa ta shirya ta sauka downstairs ta shiga kitchen da masu aiki tare sua dafa abinci, Sai mamaki suke, kallon su tayi Sannan tace

"Sahura" wacce ta kira ta amsa mata tana kallon ta,

"Talatu..." Ta kira daya itama amsa mata tayi Sannan ameera ta fara cewa

"Dan Allah, ina neman yafiyanku kan abinda nayi maku abaya...Dan Allah Ku yafemin..." Dukkan su biyu shuru sukayi suna kallon juna,

"Dan Allah fa nace...ba kaman ke talatu nasha marinki batare da kin yimin komaiba... Dan Allah Ku yafeni..." Da sauri sukace

"Mun yafe maki...Allah ya yafemana..." Cikin jin dadi ameera tace

"Ameen nagode..." Tafada tana rungume su biyu lokaci daya, Allah yasa ba mafarki suke ba, don sun San ko cup din ameera babu wacce ta isa ta taba cikin su ba tare da tacin uwarsu ba. Bayan sun gama jera breakfast kan dinning ameera ta fita waje taje wurin masu wankin mototaci da sauran maaikanta maza ta nemi yafiyansu, suma duk yafe mata sukayi, tambayan tsohon data fesawa pepper spray tayi daya daga cikin su yace

"Ai tunda wani yabashi kudi ya bar gidan nan..." Inji daya cikin su

"To Dan Allah kunsan inda yake yanzu?..." Ta tambayesu cikin sanyin murya

"Eh...yana sabuwar gandu...."

"To Dan Allah zuwa gobe zaka rakani wajen shi...."

"To Hajiya karama..." Suka amsa mata Sannan ta bar wajen, duk abinda take yi a idon mom dake tsaye bakin window upstairs, kara godewa Salem tayi tana yi mashi adua. Sama ta hau ta kira mom da dad su sauko breakfast.

Suna kan dinning take basu labarin su hinde da yaranta, ba karamin dariya dukkan su suke ba ba kaman mom dake kallon ameera With adoration

"Wallahi mom sanda na fara ganinta nayi tunanin zombie ce..." Tafada tana dariya

"Sai gashi ta zama the most important person in my life at that time... Ashe mom mutum Rahama ne?...I was willing to give all the money sir Salem gave kawai don a barta ta shigo..." Tafada tana dariya sosai, dukkan su dariya suke, mom bata taba jinta cikin kwanciyan hankali ba kaman yanzu, don bata da matsala kaman rashin respect din ameera ga mutane

"Ai ina fada maki... Ko trillion zaa baki a hanaki zama da mutane an gama da kai...don mutane are very important in our lives... No matter how dirty... Poor...ugly they are..." Inji mom

"Hakane wallahi...." Ameera tayi adding, hira suka cigaba dayi har suka gama breakfast. Ameera ta tattare plates ta kai kitchen, ta dawo ta tadda mom dake zaune falo looking very relaxed, kusa daita ta zauna

"Yanzu mom inason inje gidan su zeenat..."

"No baby...ki je kiyi wanka ki kwanta... Just call her...nafison ki maida jikin ki sosai kafin kifara fita..."

"Ok..amma mom in fada mata gaskiya abinda ya faru tsakanina da sir Salem ko...." Ta tambayi mom, shuru mom tayi for a while Sannan tace

"If you trust her...don banason mutane suji ainahin reasons din daya maido ki gida...kawai a fada masu rabuwa kukayi is better than a fada masu komai...don bakasan mai farinciki kan problems dinka ba..."

"Mom I trust zeenat... Bazata fadawa kowaba...she's the only friend I trust... Ai ranar da muka fara haduwa da sir Salem muna tare daita..."

"Ok..." Kawai mom ta fada mata Sannan ta mike ta hau upstairs.

Kayan da sir ya saya mata ta jera cikin wardrobe dinta ta fiddo wasu da yawa don ta badasu, wayanta ta dauka ta saka sim card dinta, tana kun nawa taga message kaman haka,

_"The ugly taxi driver is saying good morning... Ki gaida mutanen gidan...na tafi..."_ dariya tayi Sannan tayi saving number Salem.

Zeenat ta kira, in one word tace

"Babe am home..." Wani irin ihu zeenat tayi

"Am flying over right now..." Zeenat ta fada Sannan ta katse wayan ta.

Wanka tashiga tafito ta shirya cikin daya daga kayan da Salem ya saya mata, ba karamin kyau tayiba, tana komawa down stairs taji an bude gate, da sauri ta fita don tasan zeenat ce, ko parking lot zeenat bata kai motan ba ta fito da gudu itama ameera da gudu suka rungume juna, kaman yara suka dinga ihu suna jumping, kallon ta zeenat tayi

"Amma babe kin Dan rame..."

"Hmmm..sis kedai bari...naga rayuwa"

"Kodai ciki ne?...." Dariya ameera tayi,

"I have gist for you... Amma muje ciki in baki ruwa ki sha..." Wani irin dariya zeenat tayi

"Shegiya ke zaki bawa mutum ruwan sha?...wonder shall never end..." Dukanta ameera tayi

"Sis ki bar ruwa...just give me the gist...." Zeenat tayi adding. Wuri suka samu nan waje suka zauna ameera ta fara bata labarin komai, zeenat baki kawai ta bude tana sauraron ta, saida ta kai karshe Sannan zeenat tace

"Ikon Allah... Am I dreaming..."

"No dear... Its real..." Ameera tayi assuring dinta

"Daman na dade ina warning dinki amma bakiji...nasha fada maki duk abinda kike takama dashi da akwai Wanda yayi doubling dinka...in kudi ne..motan da wani yake hawa ya sayi komai naka... In kyau ne.....ko kafan wani baka kamaba...in ilimi inda naka ya kare nan na wani yayi starting... Look now for instance jet din Salem ya sayi duk abinda dad ya mallaka..."

"Kedai bari...now I know better....sis da akwai dukiya inda take... Kar kiso ki ga gidanshi na abuja...estate guda

..."

"Ai kinyi loosing... Wait ya matanshi?.." Zeenat ta tambayeta

"Wallahi Matan is very nice... Har kuka take wai kar in tafi..."

"You mean tanason Ku zauna tare?..."

"Seriously.. I was surprised.. Yanzu we're friends..."

"Hmmm...sis anya har yanzu ke ba matar Salem bace?..tunda kince kina period lokacin da yayi sakin?..."

"Ai babu abinda ya taba shiga tsakanina dashi...so babu aure.." Hira suka cigaba dayi kaman sun shekara basu haduba,

"Sis enough about me...ya zancen auren ki da Mahmud..." Ameera ta tambayeta

"Sauran two months wedding... Yanzu tunda Allah ya kawo ki Sai mufara choosing wears din da zamuyi amfani dashi..." Tsalle ameera tayi don jindadi, zeenat ta fiddo wayanta, tana cewa

"Bari kiga kayan da yaya sultan ya yimin order..." Tafada tana bude gallery din wayan ta, kusa daita ameera ta dawo tana cewa

"Yaya sultan ya dawo daga Madrid ne?..."

"Aa..Sai next week... Shima don Abba yaci ubanshi..." Dariya sukayi, zeenat nuna mata wasu elegant kujeru da gado tayi, baki ameera ta bude

"Wooowwww...babe na kasa rufe bakina.... Please ki tayani rufeta..." Tafada tana daria, dukkansu Dariya sukayi

"Amma yaya sultan ya iya choosing... Gaskiya yayi kokari..." Inji ameera,

"Yo sis baki San wani abu ba...set uku yace zaiyi Abba ya hanashi..."

"Kam...Ashe daman yan kwallo suna da kudi haka?..." Inji ameera

"AI weekly aka basu kudi kuma ba kadan ba....amma abun haushi wai baturiya zai aura... Abba ya hana..."

"Tofah...amma da sun barshi ya auri wacce yakeso...." Bata idaba zeenat ta galla mata harara

"Haba sis...Sai kice babban wanmu ya auri kafira?...Aa wallahi..."

"Allah ya zaba mashi wacce tafi alkhairi..."

"Yanzu kikayi magana...".

Haka suka cigaba da labartawa. Sai bayan magrub zeenat ta koma gida.

๐Ÿ’œโค๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’›

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’™๐Ÿ’šโค๐Ÿ’œ๐Ÿ’›

ยฎzuwairat(ummu Maryam)

7โƒฃ1โƒฃ

_One week later_

Ameera ta maida jikin ta sosai don har haskenta ya dawo, Sai gulma ake wai Salem ya saki ameera daga auren beyerabiya, su kam ko ajikinsu tunda sun san gaskiyan maganan, kawayen ameera datake wulakantawa Sai Allah shi kara suke yimata, wasu har kiran number ta suke su zolayeta, amma ko uffan bata ce masu, itadai alhamdulillah she's a changed person.

Ameera da zeenat tare da daya daga cikin masu aikin su sunje gidan wannan tsohon da ta taba fesawa pepper spray, har yau tsohon bai gani sosai saida glass, shikuma mako ya hanashi ya dauki kudi daga cikin kudinda Salem

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login