Showing 39001 words to 42000 words out of 145230 words

Chapter 14 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

249

mata

"Yaushe muka taba tuwon shinkafa nan gidan?" tawa tsuru2 tayi

"Ai mami tunda yau ina gida, so nake in yi maki ki ji dadi" mami kallon tuhuma tayi mata

"Ai kinsan bai dameniba..dawo kawai ki zauna" jikin tawa sanyi yayi don bata Iya gayawa mami cewa Salem zata dafawa don tana Iya cin ubanta,

"To mami bari in sayo kayan sai in yiwa kaina"

"Tawa...ina kikeson zuwa?"

"Wallahi mami kayan miya da shinkafa tuwo zan sayo.." Mami kura mata ido tayi na dan lokaci sannan tace

"To kar ki dade...banson gantali...kullum kina yawo..yau dake ranar hutunki basai ki hutaba?...Aa kinfison gantali" tawa daukan gyalenta tayi

"Mami ba gantali zan niba...yanzu nan zan dawo" ta fice, tana hanya ta kira Salem, ta gaya mashi karyan data yiwa mami, banda daria babu abinda suke, data tambayeshi inda suke sai yace basu kusa zuwaba don kilan sai dare zai iso. Alhalin lokacin yana kwance kan gado yana hutawanshi.

Tawa bata dadeba ta dawo da yan kayanta m, cikin hour daya da rabi ta hada hadadden tuwon shinkafa da miyan ganye.

Salem kiran ummanshi yayi

"First love Good evening" sai da ta gandama sannan tace

"Evening.. Yanzu Salem Dan nace kar ka auri Yoruba shine ka yadani...yanzu ka nuna min tafini matsayi kenan ko?" Ahankali Salem yace

"Umma babu wacce zata taba kaiki matsayi balle ta fiki...amma Umma it hurt me Ashe you don't trust my choice.. Am 35 am old enough to make my decisions..."

"Shut up there..." Tafada tare da zaginshi da fillanci sannan ta cigaba dacewa

"Habibi..kazo zan baka yarinyan da bazaka yi Dana saniba..."

"Umma please.. I love tawa..." Kat ta katse wayan ta. Salem ya kwanta yana tunanin abinda zaiyi next.

Ameera tana farkawa daga bacci ta fito waje, ji tayi ana kiraye2 sallan asar don rana yayi nisa sosai, wani irin matsiyacin ciwon kai take har lokacin, bakin gate taje ta tsaya ta kwankwansa

"Dan Allah Ku bude min ..." Wani irin daria masu gadi sukayi

"Ke wuce ki koma inda sir ya ajiyeki..baa bamu umarnin mu bude maki gate ba..."

"Dan Allah Ku taimakamin.. Wallahi yunwa nakeji" banza sukayi daita, fara buga kofan tayi, tana bugawa tana kuka, still banza sukayi daita, kallon gidan tayi yaga wani dutsi ta dauka tafara bugun kofan da karfi, duk yan kauyen dake area din suna jin bugun da take, tana kuka tana cewa

"Jamaa Ku tai makeni..kasheni zasuyi" kunsan yan kauye da iyayi, nan take suka cika kofan gidan, suna cewa

"Ku bude mata mana ko Ku yan yankan kanu ne?" Ameera najin abinda suke cewa ta cigaba da kuka sosai, tana

"Ku taimaka min..yankani zasuyi" wata tsohuwa cikin yan kauyen tace

"Daman daga ganin wannan gidan bana arziki bane.. Gida da tsawo kaman husumiyan babila?..to Ku budeta ko musa matasan mu su suburbudeku yanzu nan" masu gadi najin ance zaa suburbudesu suka fara cewa

"Aa bar mu kirawo Wanda ya kawomu gadinta" daya daga cikin su ya kira agent din daya basu aiki ya sanar dashi abinda ke faruwa, shikuma agent ya kira Salem,

Har lokacin Salem bai mike zaune ba, yana ganin kira agent yayi tsoki

"What did he want" ya fada sannan yayi picking tare da cewa

"What?" Ahankali agent ya fada mashi abinda ke faruwa

"Send me the number of the security men" yafada tare da katse wayan shi, ko minti biyu baa yiba number ta shigo mashi, kiran number yayi, ana picking yaji hayaniya sosai

"Hello" a tsawace Salem yace

"Put the phone on speak.. I want to talk to those idiots"

"Yes sir" mutumin yace sannan Salem yaji suna cewa

"Jamaaku saurara..Wanda ya kawota zaiyi maku magana" nan take sukayi tsit kaman ruwa ya cinye su, Salem yace

"Kuma jina?" Abinka da China phone maganan kaman saurin yayi ta

"Wannan yarinyan dake cikin wurin matatace... Maza takebi shiyasa na kawota wurin nace kar abarta ta fita...yanzu dana barta ta fita zata koma karuwanci..."

"Subhanallahi!!" Yaji suna ta maimaitawa, Salem sai dariya zuci yake, yacigaba dacewa

"Yanzu kun ga laifina?" Duka su kace

"Aa" sai yaji wata tace

"yazamuyi mugane gaskiyar ka?" Baki Salem ya tabe sannan yace

"Abudawa mata uku daga cikin Ku su shiga su gani..babu kayan abinci da babu..in yankata zaayi zan saya mata kayan abinci?..Kuma nasan da anbude zatayi kokarin guduwa don ta koma karuwancinta kuma inkun barta ta fita alhaki kanku " yafada kaman zai tuntsure da daria.

Daga chan bangaren suka zabi manyan mata guda uku mai gadi ya bude masu har lokacin Salem bai kashe wayan shi ba. Itakam ameera batasan yanda akayi duk mutanen kofan gidan sukayi shuru ba don batajin abinda Salem ke cewa Amman yaji ana

"Subhanallahi... Subhanallahi" tana ganin an bude kofa tayi kokarin fita , nan Matan dake shigowa suka kamata suka maidata cikin gidan, Salem kam yanajin ihun ameera ya tuntsure da dariya Amman bai bari sukajiba, yaji daya daga cikin Matan na cewa

"Wallahi da gaske yake...da ganinta mutuniyar kirki bace" suka kara shakumota sukayi ciki daita, ameera sabon ihu tafara tana cewa

"Stop touching me with your filthy.. Stinking hand.. Kar Ku kara tabani da karamin hannunku..." Tas Salem yaji wata ta buge mata baki tare dacewa

"Kull...yara basu zagin manya nan wurin" ameera takara fashewa da ihu tana rike bakinta, har lokacin maigadin bai cire wayan daga speaker ba, Salem yakara cewa

"Kuci mata uwa...bata da tarbiya"

"Ai mungan alaman hakan" suka amsa mashi, daya daga cikin Matan ta zagaya gidan sannan tashiga kitchen taga lodin abinci, baki ta bude

"Amman wannan yarinyan baki da kirki... Ga kayan abinci kaman shago... Kai ko shagon dalha bai da kayan abinci haka" ameera kam sai kuka take tana kokarin kwacewa daga rikon daya dagacikin Matan, gashi babu bakin magana balle tayi zagin data saba.

Matan fita sukayi mai gadin yabisu ya maida gate ya rufe har lokacin Salem bai kashe wayanba, Matan dasuka shiga suka tabbatar masu cewa ba gidan yankan kai bane. Salem yakara cewa

"Yanzu kun yarda da magana ta?"

"Eh..." Suka amsa mashi sannan yacigaba dacewa

"to inason Ku sami wacce ta fi kowa kazanta ta dinga zuwa koya mata abinci zan biyata duk karshen wata" duka suka ce

"Ai indai kazama kake son ta koya mata abinci sai hinde..tafi kowa kazanta nan unkuwan"

"To daga gobe ta dinga zuwa tana koya mata abinci" sannan yayi was masu gadin umarnin su rage volume din wayan, bayan mutumin ya kanga wayan ga kunne Salem yace

"Ku dinga barinmace daya tana shiga gidan ...sannan ban daita ban amince Ku bar wata ta shigaba" katse wayanshi yayi yana shuumin daria

"We're are just getting started.. Bitch" agent dinshi ya kara kira ya gaya mashi ya saka CCTV cameras cikin koina na gidan ayi mashi recording din abubuwan dake faruwa cikin gidan.

Aranan ameera kam rana bata kara cin abinci ba, sau uku tana shiga kitchen Amman bata iya sarrafa kayan abinci ba, kuka tayi har daga baya hawaye suka bar zubo mata, bayan sallan ishai ta koma ta zauna daga bakin gate inda zata dinga jin motsin mutane, adua take mutuwa yazo ya dauketa kawai ta huta.

bayan sallan ishai Salem yaje gidan su tawa, cikin dakin su suka zauna suka sha hiransu, banda kallon ta babu abinda yakeyi don gani yake in har iyayensu basu yarda suyi aureba yana Iya dauketa ya maida ta wata kasan a daura masu aure don yasan babu abinda zaace dazai hanashi auren ta saidai wani iko daga rabbi, dazai tafi tabashi tuwon shinkafa cikin cooler, mamaki ne kwance kan fuskanshi donshi har ya manta da maganan tuwon.

Aranan ne yasani cewa abinci basai da nama, kifi, kayan ciki etc yake dadi ba don kashine cikin miyan Amman it's the most delicious tuwon shinkafa daya taba ci, yana ci yana waya daita yana yi mata santi

๐Ÿ’š๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’™โค

ZAKISAN KONI WAYE"

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค

ยฎzuwairat(ummu maryam)

2โƒฃ9โƒฃ

Wacegari bayan ya dawo daga masjid ya kwanta yana tunanin abinci tawa, shidai in so samune ta cigaba dayi mashi abinci dukda ya kuduri aniyan ya kusa gaya mata koshi WAYE don yanzu hutunshi sauran sati uku ta kare,

"Daman ana samu mace mai hali, kyau , sanin ya kamata?...ko dai kina da wani halin da ban saniba?..you have all the qualities.. You have the perfect shape perfect body... " ya fadawa kanshi, zama yayi yana tunanin yanda zaiyi ya dinga sa tawa dafa mashi abinci batare datasan shi takewa ba, yafi minti goma yana tunani sannan ya saki dan kasaitaccen murmushi, wayanshi ya dauka yaga 6:15am, number tawa yayi dialing yana cewa Allah yasa bani zan tadaki daga bacci ba, bayan ringing uku ta dauka da sallama, dajin muryan ta kasan ta dade da tashi kuma jiya kusan 1 na dare suna hira awaya, gaidashi tayi kaman yanda ta saba shima ya amsa sannan yace

"Princess kinsa me yafaru dasafen nan?"

"No sir"

"Dazun naje daukao uban gidana daga Aminu Kano airport...shine yake fadamin yana Neman wacce zata dinga yi mashi abinci.. Ya dinga bata 15k kullum tana siyan kayan sannan ta rike sauran...kuma yace zai bada 200k ta sayi kayan aiki" saida ya kai aya sannan tawa tadan saki daria

"Amman ifemi you are very funny.. Ka taba ganin inda mutum yaci abinci 5k arana balle 15k?" Dan murmushi yayi don yasan da akwai elegant restaurant dake abroad, zama daya sai yaci 3000$

"Ai mutumin yana da naira...kuma na fada mashi nasan wata yarinya data iya abinci sosai" tawa shuru tayi for a moment sannan tace

"Gaskiya bazan iyaba..tsoro nakeji...kuma nasan da kyar mami ta amince"

"Tsoron me?"

"Kar mutumin ya zama dan yankan kai" daria Salem yayi

"Kina tsoron kar mutumin ya yanke maki beautiful head dinki...well relax..ban dan occult bane sannan babu ruwanki dashi cos ni Zan amso kudin sannan ni zan kai mashi abinci so kinga babu ruwanki dashi..."

"Hmmm gaskiya mami bazata yarda ba...kuma ko ta yarda ina tsoron kar inyi disappointing dinka cos kilan baya cin anyhow food"

"Don't worry about that.. You are a wonderful cook..kawai talk to mami yanzu nan..inta amince ki kirani sai in amso kudin"

"So soon?"

"Yes mana...bayason son cin abinci anyhow.. Kuma kema kin huta da wannan katuwar madam din nan" daria tayi

"OK...let me talk to her"

"Good.. Call me inta amince.. Kuma please ki nace har sai ta yarda" daria ta karayi sannan ta katse wayan ta.

"Indai ba cikin wahala take sonkiba ai ta amince" yafawa kanshi yana dailing number Abdul, bayan yayi picking yace

"Call me the makeup artist" sannan ya katse wayan shi.

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค



Ameera batayi bacci ba har garin Allah waye, tana ganin hasken wayewan gari ta rarrafa ta koma cikin dakin ta kwanta kasan carpet tana tuna daddy, nan hawaye ya fara zubo mata, mom ta kara tunowa ya kara fashewa da kuka,ba karamin sauro ya cijeta ba, don duk jikinta kaikayi yake mata,, bata dade da kwantawa ba taji anacewa

"Salamun alaikum" banza tayi bata amsa ba, saida aka maimaita kusan sau uku sannan ta mike jiki ba kwari don azaban yunwa da takeji, ahankali ta fito waje, wata mata ta gani kaman aljana saboda muninta

"Inna lillahi waina ilaihi rajuun!" Tafada da karfi tare da komawa cikin dakin, matan wace green teeth dinta tayi sannan tace

"Ke dawo..nice hinde..ni..." Ameera bata saurareta ba ta dinga kwala ihu, matan binta tayi daki, ameera kamewa tayi waje daya tana kallon ta don kayan jikin ta wulik don dirty, Matan tacigaba dacewa

"Nice akace in dinga koya maki abinci..." Ameera kuka ta kara fashewa dashi tana kalle2 inda zata samu abinda zata jefawa matan, bata ga komaiba ta cire takalmin kafanta ta jefawa matan

"Ki tafi...mahaukaciya kawai..ubanwa zaici abin hannunki...dirty, disgusting creature" Matan Dan scratching gashin kanta tayi kaman mai lice aka

"To shikenan.. Tunda baki son in koya maki" tafada tana daria kaman na morons, juyawa tayi ta fita, da sauri ta ameera ta mike ta bi bayan ta, har matan ta kai bakin gate tayi saurin cewa

"Kin iya dafa abinci?" Da sauri hinde tace

"Sosai" ameera tana ganin hakoranta ta sartar da yawu sannan tace

"Kina Iya tsayawa daga nesa ki koya min?"

"Eh" ameera kallon ta tayi tana tunanin bata da zabi don tasan in bata ci abinci ba tana iya mutuwa, nuna mata itacen tayi

"To ki huta wuta" ameera ta umarceta, da sauri hinde ta dawo ta dauko murhu ta saka itace, ameera sai kallon ta take, tana gamawa tace

"Ina ashana?"

"Tsaya inda kike indauko maki" tafada tana shiga cikin kitchen dinta , cikin kayan ta duba ta dauko sashana ta wullawa hinde, babu bata lokaci wuta ya kama

"Kawo tukunya in Dora" hinde ta fada mata

"Ubanwa zaki dafawa abinci?.. Dan matsa baya ki gani" ta fadawa hinde, matsawa baya tayi daga inda wuta yake,ameera kitchen ta koma ta dauko tukunya,

"Me zan fara sawa cikin tukunyan?" Dan takowa hinde ta farayi

"Dalla tsaya inda kike ki fada min abinyi" ameera ta daka mata tsawa, daga nesa Matan ta tsaya tana gaya mata steps din da zata bi, cikin kankanin lokaci abinci ya dahu, ameera kitchen ta shiga ta dauki kwano ta zuba ta fara ci, kaman wacce bata taba cin abinci ba , haka ta dinga ci ,dukda dadin abinci bai kai Wanda ta saba ci ba, tana ci tana zagin Salem, hinde ta nan daga tsaye, ameera ko kallon inda take batayiba har saida ta koshi sannan ta kalleta

"Ke ki tafi mana" ta fada mata,

"To" hinde ta amsa mata kuma daga gani ranta ya biya, Amman ameera bata kalleta ba, kuma abinci na da yawa. Sauran abinci ta kai kitchen sannan ta nemi sabulun wanka da soso, sabulun wanki ta gani, sabon kuka tafara, idanuwanta sunyi mugun kumburi, ahaka tayi wanka da sabulun wankin, mai cocobutter ta dauka, tabude Amman ta maida ta rufe don warinshi ma takeji.

๐Ÿ’š๐Ÿ’œ๐Ÿ’›๐Ÿ’™โค

Umma Salem zaune tana waya, ji nayi tana cewa

"Kina nufin baa taba bude office dinshi ba?"

"Eh..guys din cewa sukayi kwata2 babu alaman shi akano don cewa sukayi duk binciken da akayi ya nuna cewa tunda shi ba boyeyyen mutum bane zamanshi a Kano ma bazai boyeba.." Matan ta fada mata daga chan bangaren, shuru Umma tayi kaman mai tunanin wani Abu,

"To me hakan yake nufi kenan?"

"Gaskiya inajin bai Kano"

"To shikenan, but please keep on finding him cos nasan yan Kano,..tunda nasan bayayi min karya"

"To hajiyata..da akwai daya daga cikin yarona Wanda yake aboki da wani bodyguard din Salem, zansa shi ya kirashi muji in suna Kano..."

"Ok ..haka ma yayi..make the call right away".

" yanzu nan insha Allah "Umma ta katse wayan tare da kara kiran kawanta dake abuja ta jadadda mata akara tsaro wurin duba gidan Salem. Don yanzu babu abinda take so kaman tasa tawa a idonta

โค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’š๐Ÿ’™

"Tawa wace irin abinci zaki dafawa mutum a 15k kuma kullum?" Mami ta tambayi tawa

"Mami nidai ban saniba...cewa wannan mutum dake zuwa wurina yace mutumin mai kudi ne" mami shuru tayi tana tunanin maganan tawa

"Hmmm..kina ganin da gaske yake?"

"Eh mami don bai cika karyaba..ko yanzu ma cewa yayi inki yarda zai koma gidan mutumin ya amso kudin"

"Kuma yace babu inda zakishi zai kawo kudi yazo ya amshi abinci?"

"Yes mami..ni kawai indafa abinci shine nawa"

"To kina gani zaki Iya dafa kalolin abinda zai gansar da mutumin?"

"Insha Allah"

"To shikenan.." Bata idaba tawa ta mike ta dauki wayanta ta kira

Salem tana tsale tana cewa

"Ifemi.ta yarda" karaf sai kunnen mami, don tunda take kirnashi ifemi mamiba tabajiba

"Tawa me kika kirashi?" Tawa dauke wayan tayi daga kunnenta Amman bata tuna ta kashe wayan ba don yanda jikin ta ke rawa

"Mami...ba..komai..," tafada kaman zatayi kuka, duk abinda suke cewa a kunnen Salem

"Tawa Hausa kike cewa ifemi.. Tawa..."

"Mami sorry" mami bata sauraretaba ta nufeta

"Tawa Hausa kike cewa ifemi" kunnenta takama da karfi, daga chan bangaren Salem yaji ihun tawa sai hakuri take bawa mami, ji yayi ranshi yayi mugun baci

"If you don't want it the easy way...we will do it the hard way" yafadawa kanshi, har lokacin bai bar jin ihun tawa ba, yaji mami tana gayawa neighbors dasuka shigo ceton tawa da hausanta Mara fita

"Wai wannan yarinyan Hausa take so..bata ganin abinda suke yiwa Matan su?..yau aure gobe babu" hakuri aka dinga bata, tawa share hawayenta tayi

"Mami I love him.." Salem dake jinsu ya lumshe idanuwa kwalla na taruwa idonshi, mami kunnen tawa takara kamawa, banda ihu babu abinda takeyi, sai ka rantse yankata akeyi kuma kunnenta kawai mami ke kamawa.

A lokacin anayiwa Salem Chanjin fuska, ture artist din yayi ya mike ya koma daki ya kwanta, har lokacin wayan bai katseba, yaji tawa nacewa

"Mami he's not a bad person" mami kara kama kunnenta tayi da karfi sosai, wannan Karin da karfi tarike don da kar aka kwace kunnen tawa daga hannunta, Salem kaman yashake mami yakeji, daga baya wayan ta katse, dagani kudinta ne ya kare.

Salem kwantawa yayi yana juye2.

Bayan kaman minti talatin ya kirata bata dagaba, kara kiranta yayi, saida ya kusa tsinkewa sannan tayi picking, muryan ta chan kasa tayi mashi magana, pretending yayi kaman baisan abinda yafaruba

"Princess na amso kudin inzo mutafi?" Ahankali tace

"Ka bari saida yamma kaina ke ciwo"

"Ayya sorry.. In sayo maki magani?"

"Aa"

"OK..I love you" bata amsa ba ta katse wayan ta.

Da yamma yazo gidan, yau mami bata yi mashi faraa ba.

๐Ÿ’š๐Ÿ’œโค๐Ÿ’™๐Ÿ’›

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’š๐Ÿ’œโค๐Ÿ’™๐Ÿ’›

ยฎzuwairat(ummu maryam)

3โƒฃ0โƒฃ

Falonsu yazauna kanshi kasa, mami amsa gaisuwan shi tayi babu yabo babu fallasa, daki ta shige, baa dade ba tawa ta fito, daganin idanuwanta kasan tasha kuka, tana kallon shi ta sakar mashi murmushi karfin hali, kura mata ido yayi

"Tawa ciwon kai din ne yasa idanuwanki kumburi?" Ahankali ta daga mashi kai hawaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login