Showing 75001 words to 78000 words out of 145230 words

Chapter 26 - Zakisan Koni Waye Complete

01 Nov 2025

273

ta koma bedroom ta shiga wanka, few minutes later ta fito da alwallah Sannan tayi sallah.

Undies tima kallon ta tayi tace

"Sis wallahi kina da bikini body... Irin wannan shape haka..." Bata kalleta ba, Arabian gown data dauko ta zura sannan ta yafa falo tayi zamanta, tima binta tayi ta tsaya tana kallon ikon Allah,

"Ke tashi muje ko light makeup ne ayimaki..." Ahankali ta girgiza mata kai

"Ban zuwa..." Janta tima tayi sannan tace

"Ai ba anan zaki zauna ba...corridor nake next to palace zamu zauna mu jira kiran kins men..." Dan tsaka taja sannan ta mike, suna fita yayi daidai da shigo wansu Salem daga inda compound masjid yake, kaman ance ya daga, aikam daga nesa ya hango tawa, yana tafiya yana kallon ta, sai mamakin yanda ta koma yake, don ba karamin kyawunta ya ganiba, sannan ya ga ramanta, kaman yaje ya dauketa yakeji, yana tafiya yana tuntube, itakam tawa batasan yanayi ba don kanta kasa tima na rike da hannun ta, yanda Salem ke kallon wurin yasa su Abba da uncles maida hankalinsu wajen, Dan murmushi Abba yayi sannan daya daga cikin uncles dinsh yadan bugi bayan shi, Salem daria yayi ya kauda kanshi, tima dai ta gansu Dan murmushi tayi

"Kai..babe wancan kaman sir Salem.." Gaban tawa mugun faduwa yayi, da sauri ta daga kanta don ganinshi amma har sun shige, cikin ranta tace

"Me zai kawo sir Salem nan". Cikin balcony da su Salem suka bi suma sukabi sai ta tsinci kamshin turarenshi wurin, waige2 tafarayi sosai, babu kowa wurin sai suka shiga inda sauran yan matan ke zaune mai kwalliya tana yi masu kwalliya, zolayanta suka fara as usual, ko kallon su batayiba ta zauna, mai kwalliya wurin ta tazo zata fara yimata kwalliya, girgiza kanta tayi

" kaina ke ciwo"

"Sorry.." Suka cemata dukkan su sannan deeja tace

"Ai dole a dan shafa maki ko wet lip ne..." Bata kara cewa kala ba Matan tafara shafa mata makeup, amma har cikin ranta batason kwalliyan.

Sul Salem na komawa oba yasa aka kirawo daya daga cikin yanmatan, Salem dake tunanin ganin tawa sai yaga wata tayi kneeling amma kanta kasa, cikin zolaya daya daga cikin kins men yace

"Wannan itace?.." Ahankali Salem ya girgiza kai, daria dukkan su sukayi sannan yarinyan ta mike ta bar wajen. Watace takara shigowa aka sake tambayan Salem yace no, cikin zuciyanshi sai cewa

Wannan wane irin iskanci ne...ai wannan rainin hankali ne..." Ya fada cikin zuciyanshi, watace takara shigowa aka tambayeshi itace still ya girgiza masu kai, haka yanmatan suka dinga shigowa har yazo kan tawa, itadai tawa saita tsinci kanta da mugun faduwa gaba don bata taba irin wannan abun ba, jikin ta na Dan rawa tashiga ciki, ko tsakiyan bata kaiba tayi kneeling tana jiran a sallameta, Salem na ganin ta ya saki ajiyan zuciya, mutumin kallon shi yayi

"Wannan itace?.." Ahankali Salem yace

"Yes.." Yana kallon yanda tawa ta Dan zaro ido don tawa tunani take ko muryan Salem ne taji, hankali ta bai tashiba saida taji muryan oba yana kiran sunan ta, kasa amsawa tayi

"Tawakaltu.." Ya Kara kiranta, batare data daga kantaba ta amsa mashi, oba nuna Salem yayi abun sarauta dake hannun shi sannan yace

"Grandchild... Kinsan wannan mutumin dayazo Neman auren ki?..." Tawa jitayi kaman heart dinta zai bude kirjinta ya fito don ba karamin bugawa takeba, ahankali ta daga kanta ta kalli inda oba ke nunawa, karaf sukayi ido hudu da fabulous Salem, da sauri ya kashe mata ido daya tare da sakar mata murmushi, da sauri ta sunkuyar da kanta kasa tadan dora hannun ta kan kirjinta for 2 seconds sannan tayi saurin sauke hannun ta, tunanin maganan mami

"Ashe mami tasan Salem ne zaizo shiyasa ta yi min warning?..." Tafada cikin ranta, tunanin alkawarin datayi wa ummanshi ta farayi, _"kiyi min alkawarin zaki fita harkan Salem..."_ taji muryan Umma a kunnenta

"I..promise" ta tuna statement dinta,dukkan mutane sun maida hankalinsu kanta sunason jin amsanta, especially salem daya tsinci gaban shi na faduwa, ji tayi oba ya maimaita ta tambayan, ahankali ta daga kanta tana kallon Salem hawaye na taruwa idanuwanta sannan ta fara girgizawa oba kai.

,

๐Ÿ’™โค๐Ÿ’›๐Ÿ’œ๐Ÿ’š

ZAKISAN KONI WAYE

โค๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’š๐Ÿ’›

.

ยฎzuwairat( ummu maryam)

4โƒฃ8โƒฃ

Dukkan mutane wurin mamaki ne kwance kan fuskansu, banda oba donshi yasan hakan zai faru, Salem kura mata ido yayi da idanuwanshi da suka chanza kala, kaman ya hadiye rai ya mutu kawai yake, kallon tawa data sunkuyar da kai hawaye juna zuba yayi, duk Ilahirin jikin shi shaking yake, amma kam rasa yawu yayi cikin bakinshi, oba baki ya bude yayi niyyan sallaman tawa OBJ yayi saurin cewa

"Daughter.. Ki daga kanki ki kalleshi da kyau...baki sanshi ba?.." Tawa bata samu courage din kara kallon Salem ba, kawai hawaye ne ke zuba fuskanta kaman tap,

"You can go...$" oba ya fada mata, ahankali ta mike kanta kasa ta fita daga wurin, tana fita ta fashe da kuka sosai tana gudu ta nufi part dinsu.

Salem ji yayi iska na Neman yi mashi kadan

"She deny me..." Ya fada ahankali, kaman an tureshi ya fita daga wurin ko takalmi babu kafanshi ya fita da sauri, yana fita ya hangi bayanta ta shiga part dinsu, mami tana ragube upstairs dake opposite inda part dinsu yake, tana kallon abinda ke faruwa, da gudu Salem ya bi bayanta, tana shiga ta zube kasa tana kuka, Salem shiga yayi har falonsu, wani fixga yayi mata ya daga ta tsaye ya wanka mata wani mahaukacin mari

"Ni ke baki saniba!?" Yafada kaman numfashin shi zai dauke, tawa rike hannun wanshi tayi tana kuka, fixge hannun shi yayi ya kara zuba mata wani mari, cikin ihu yace

"What have I done to you?...why me..." Rike mashi hannu ta karayi ya kara fixgewa,

"I said uban me nayi maki?...why are you killing me slowly..." Yafada hawaye na zuba daga idanuwanshi, tawa kara kokarin rike mashi hannu tayi ya fixge ya rike shoulders dinta da hannuwanshi biyu ya fara girgiza ta sosai yana cewa

"Tell me what I have done to you to deserve this humiliation...Tell me abinda nayi maki kika yi insulting dina kikayi insulting parents dina...tell me why you want me dead..." Duk furucin dayayi sai ya girgiza ta kaman zai karyata, yana kuka tana kuka, da karfi ya kara rike shoulders dinta, tawa ta rike mashi hannuwa,

"Tell me...ki fadamin or zan kashe ki in kashe kaina...then we can continue in hell..." Da karfi ya kara girgiza ta

"I said tell me why you deny me..in front of my parents..." Yafada cikin murya kaman na mayunwancin zaki, tawa data fara fita hayyacinta saboda irin girgiza da yakeyi mata ta fara cewa

"Umma.. I promise... Umma.. To..leave you... Alone..." Tafada kaman numfashin ta zai dauke

"Fuck you..fuck your promise.... Umma has given her...blessings..." Yafada cikin kuka kuma he don't care if the whole world is watching, a hankali tawa ta girgiza mashi kai

"She...made...it..clear.. She..don't want...you...to marry...another... Language..." Da karfi ya kara girgiza ta

"I said Umma have given her blessings!" Ya fada cikin tsawa, turata yayi gefe ta fadi kan kujera, shima ji yayi kafanshi bata daukan shi, ahankali ya zame ya zauna kasan carpet yana kuka, tawa mikewa zaune tayi, ta dawo kasa kusa dashi, kafa yasa ya tureta daga wurin shi ya cigaba da kuka kaman anyi mashi albishir da jahannama.

Acikin palace kam dukkan su cikin tension suke, kanin Abba yaso ya bi bayan Salem amma OBJ ya dakatar dashi, Abba kam tunani yake kilan wannan yana Iya zama sanadiyan mutuwan Salem don yasan irin son da Salem ke yiwa Tawakaltu. Dukkan su babu mai bakin magana, Obj ne yayi gyaran murya sannan ya fara cewa

"Nasan there is something behind what happened... Naga sonshi a idanuwanta..." Shuru yayi ya juya wajen da oba ke zaune

"Your royal highness.. Ko kana da masaniya kan abinda ke faruwa?.." Oba gyara zama yayi sannan yace

"Gaskiya nafiku bacin rai kan abinda ya faru cos babu abinda Salem zai nema wurina in hanashi saidai nasamu labarin ummanshi batason ya auri wata yaren..." Abba shuru yayi yana sunkuyar da kanshi kasa don Sam baida kwarin jiki, oba yacigaba dacewa

"Kuma uwar dabance..in har batason Abu..to wannan abun baya albarka..." Da sauri Abba yace

"Your royal highness maganaka gaskiya ce, amma wallahi umman Salem tayi realising mistakes dinta...she has given her blessings,..." Yafada cikin sanyin murya, OBJ mamaki yayi sosai

"Gaskiya in hakane...auren ba mai yuwa bane..amma tunda kace ta bada blessings dinta..maybe if possible kuzo tare daita..don gaskiya bamu yarda a hada auren da uwanda bata so..." Ahankali Abba ya gyada kai alaman understanding, sai tunani yake daman haka mutanen nan suke? ...don yasan da kyar a hana aure a arewa don uwa bataso. Abba sai tunanin inda Salem yake yake.

Salem kam hada kai yayi da gwaiwa yana kuka sosai, da kyar tawa ta Iya kara mikewa ta rarrafa inda yake, cikin kuka tace

"Please... Ife..." Afusace Salem ya daga kanshi

"If you ever call me that again.. I will strangle you to... Death...baki sona...baki taba sona ba..." Kurawa juna ido sukayi hawaye na zubowa daga idon kowanne su, cikin shessheka ta kara cewa

"Please... Tell.. Me...have Umma given... Blessings..." Salem murtuke fuska yayi ya mike ahankali ya goge hawayen fuskanshi, sannan ya juya gareta ya nuna ta da dan yatsa

"Ko kece autan mata..na hakura dake....ko sonki zai kasheni...na hakura dake....amma Allah yaisa tsakanina dake...I will not forgive..." Da sauri tawa ta rike mashi kafa sannan ta mike ahankali, wani irin kallon juna suke, Salem yana tunanin yasan bazai iya rayuwa bada itaba, itama tana tunanin no body is taking away this man from her, she has the right to love and she loves him

"Am not letting you go..." Ta fada mashi, tana kaiwa nan tayi hanyan waje.

Mami na gani Salem ya Dade part dinta bai fito ba ta sauko, adaidai bakin palace ta cikaro da tawa data koma kaman baitaba, duk idanuwanta sun chanza color, fuskanta ya kumbura, rike mata hannu tayi, Salem ma fitowa yayi ya nufosu.

"Habibty were are you going?... What happened to your face..." Ta jerawa tawa tambaya, amma tawa bata saurareta ba ta fixge hannun ta daga hannun mami ta shiga cikin palace da gudu, da gudu Salem ma ya taho, mami tsaya kallon ikon Allah tayi, yanmatan gidan har dasu tima da deeja suna tsaye tsakar gidan suna kallon su, don dazu da suka wuce sun gansu, kuma yanzu sun san sir Salem ne, tima so tayi tashiga part din mami amma sauran yan Matan Suka hanata.

Tawa shiga cikin palace tayi, tundaga bakin palace din tayi kneeling tafara rarrafawa har gaban oba, su Abba da OBJ kallon ikon Allah kawaisuke, Salem na tafe bayan ta, tafiya yake ahankali yana kallon yanda take kuka tana crawling kasa, cikin shessheka tafara cewa

"Grandpa.. Nasan shi....I know him...and... I love him... Am...sorry..." Yanda take maganan kaman ranta zai fita yasa oba daga mata hannu, amma batayi shuru ba ta cigaba dacewa

"Grandpa... I love.. Him..." Kai oba ya gyada mata alaman I understand, mami na tsaye bakin fada tana jin abinda tawa take cewa, duk mutanen wurin jikin su yayi sanyi Abba kam kaman zaiyi kuka yakeji, OBJ kam baki ya saki don tunda yake bai taba ganin event din da ya bashi tausayi irin wannan ba, Salem har lokacin bai bar hawaye ba ahankali shima yayi kneeling bayan ta, saida ya goge hawaye shi ya daidai ta murya sannan yafara cewa

"I promise... To take care of her...i will make sure she's happy.... She will be the only gueen of my heart... I will do everything.... For her...." Mami duk tana jin abinda yake cewa oba daga kai yayi ya kalleta

"History is repeating itself..." Oba ya fada cikin ranshi, kallon tawa da Salem yayi

"Ni ba dangin uban Tawakaltu bane...am amatsayin na na sarkin gari da kuma grandpa dinta...na baka Tawakaltu..." Da sauri OBJ da sauran mutane suka kwanta kasa suna godiya, shima Salem kwantawa yayi, duk yanmatan gidan suna tsaye bakin window suna kallon kuma suna jin abinda ake cewa, dukkan su ihu suka fara suna tsalle, tima hannu tasa bayan kunnenta kaman tana sauraron wani few seconds later tace

"I can hear a wedding bell ringing.." Dukkan su ihu suka karayi, jikin mami ba kwari ta bar bakin palace ta koma part dinta, dukkan mutanen komawa sukayi suka zauna, ahankali Salem ya mike yakara kneeling, har lokacin tawa bata tashi ba, ahankali ta juya zamanta ta fuskanci Salem, cikin rawan murya tace

"Am sorry..." Girgiza mata kai yi

"No...am sorry for hitting you..." Yafada cikin whisper yana kallon yanda ya bar hannun shi kan fuskanta. Ahankali ta mike shima ya mike, tafiya ta farayi amma kaman iska na kadata, da kyar ta kai baki palace, Salem na bin bayanta don inda babu Abba awajen da daukan ta zaiyiko gaban uban waye, tana fita yanmatan suka rungume ta ta fada jikin su tana kuka, dukkan su tsaya kallon sir Salem in flesh and blood sukayi, Dan murmushi yayi sannan yace

"Excuse me ladies..." Dukkan su daria sukayi suka sakar mashi tawa. Hannunta ya rike suka kama hanyan part din mami, har sun kai bakin kofan tawa tadan tirje tana girgiza mashi kai, shima girgiza mata kai yayi sannan bude kofa, mami ce zaune sai hawaye take, babu abinda take tunawa sai irin tsangwaman datasha wurin family mijinta, gani suke ita tasa ya juya masu baya wai don tana princess. Ahankali Salem ya saki hannu tawa ya zauna gaban mami, ahankali yafara cewa

"Mami... Nasan bani ke bakiso ba...halin mutanen mu da kika zauna dasu ke bakiso...Ni ina daukan maki alkawarin zan kula da yarki kaman yanda zan kula da kaina..." Mami goge hawayenta tayi sannan tace

"Allah ya ba ikon kula da yata... Dan Allah duk laifin dazatayi maka..please kar ka saketa...ka hukuntata...please" dan murmushi yayi

"Sakin mata baya cikin dictionary dina...insha Allah I will show you that we are not all the same..." Kai kawai ta gyada mashi

"Kam irin wannan wahalan Dana sha kanta zan saketa?... Ai intayimin laifi ubanta zanci mu shirya.." Yafada cikin ranshi. Mikewa yayi ya bar dakin, tawa kam rakubewa tayi jikin bango don gani take mami zata cimata for going against her order. Mami mikewa tayi ta koma bedroom dinta, da sauri tawa tashiga nata bedroom din ta kwanta tana jin dadi.

Salem na fita ya hangi yanmatan zaune cikin balcony suna ganin shi suka fara kus2 kuma maganan shi suke, kallon white leg dinshi mara takalmi sukayi, har ya Dan wucesu ya dawo wurin su,

"In-laws.. Can I know the names of these beautiful ladies?..." Ya tambayesu sounding so naughty, da sauri suka fara introducing Kansu dan murmushi yayi yana godewa Allah da bada Khalid yazo ba don yasan babu abinda zai hanashi flirting dasu in yana nan, bayan sun gama

"Lovely names.." Yafada yana saka hannu cikin aljihunshi, ATM ya fiddo sannan ya fara cewa

"Ga ATM ...Ku shiga cikin gari Ku nemawa princess dina the most expensive phone... Sannan each and every one of you should spend 200k..." Ihu suka farayi suna Neman tada palace din,

"For us?.." Suka fada gabaki dayansu, murmushi yayi yana daga gira daya

"Yes..babies...you know money is not the problem..."

"We know handsome!" Suka fada in chorus, wacce tafisu shekaru mai suna mufida ta amshi ATM din sannan ta kalli sauran

"Sis Ku kirani nan in dauko car keys.."

"OK" kawai suka amsa mata, Salem wani murmushi yayi ya kama hanyan cikin palace.

Su Salem na barin palace OBJ ya kalli oba sannan yace,

"Tunda an gama wannan sai Ku bamu list da kuma ranar introduction.." Oba dariya yayi

"So soon haka?" Abba dadi yaji yanda OBJ yasan abinda ke cikin ranshi

"Meye na wasting time kuma?... Kawai mu gama mu dauki yarmu.." Dukkan su dariya sukayi sannan oba yace

"To yanzu zan aikawa iyayen yarinyan maza...zuwa next two weeks kuzo sai Ku amshi list..." Kai OBJ ya Dan girgiza

"Ranka shi dade two weeks yayi mana yawa...ka Dan rage mana..."

"OK...bakomai... Ku dawo zuwa next week..."

"Godiya muke.. So ranar zaayi fixing din ranar introduction ko?.." wani uncle Salem ya tambayi oba

"Insha Allah..."

Salem na shigowa ya zauna kanshi kasa, acikin zuciyanshi kam dadi yakeji Mara misaltuwa.

Yanmatan sa suka tafi shopping kam basu dawoba sai 5:30pm lokacin su Salem sun dawo daga masjid suna zaune palace, hira kawai su Abba da oba suke, shikam so yake ya kara komawa wajen tawa su danyi hiran wedding preparations, hakuri yayi tunda ba yau zasu koma ba, da sun koma government house zai sabe ya dawo.

๐Ÿ’œ๐Ÿ’™๐Ÿ’›๐Ÿ’šโค

ZAKISAN KONI WAYE

๐Ÿ’›๐Ÿ’š๐Ÿ’™๐Ÿ’œโค

ยฎzuwairat(ummu maryam)

4โƒฃ9โƒฃ

Tawa najin anbude kofan dakinta tayi saurin mikewa zaune, mami tagani tashigo jikinta duk babu kwari, gaban tawa ne yafara disco cos gani take mami dukanta zatayi, mami batace komai ba ta zauna gefen gadon, tawa rakubewa tayi jikin bango, mami tafi minti biyar zaune batace kala ba, sai daga baya tayi ajiyan zuciya sannan tafara cewa

"Yanzu tawa duk maganan danayi maki saida kika nuna kin sanshi?.. " tafada cikin sanyin murya, tawa bata ce komai ba tafara sabon kuka, hannu mami ta daga mata alaman tayi shuru, nan take ta hadiye kukanta

"Yanzu tawa har kinyi girma da bazaki bi umarni na ba?... Ko kina ganin farincikin ki ke banaso" shuru tayi for a moment sannan tacigaba dacewa

"Sam ba haka bane...kawai banason abinda zsai tabamin ke..kuma banason ki sha wahalan Dana sha...yana making promise wai zai yi this and that... Its all lie.. There is something he sees in you..the moment ya dauki wannan abun zai ajiyeki gefe ba fata nake maki..." Tawa ji tayi gaban ta na faduwa don gani take maganan mami gaskiya ce ba kaman in ta tuna yanda yake maganan sex cikin waya, taji mami nacewa

"Kuma tunda ummanshi bata sonki koshi baiyi aureba dole zata aura mashi mata yarensu lokacin zaki koma..." Shuru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login