Showing 36001 words to 39000 words out of 123508 words

Chapter 13 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

533

Zayn ya bisu da kallo. Maa tayi murmushi kafin tace,

"Ai sun saba sosai. Waheedah ta zama babbar kawar sa. Kwana biyun nan na huta da fitinar sa." Ta karasa fada hade da daga kai sama tana tunani. Can ta mayar da kanta kan notepad ta cigaba da rubutu.

"Maa list din menene kike yi...?*

"Na bikin nan da zaai. Saboda kar na manta ban inviting wasu ba. "

Kada kai yayi can ya nisa yace,

"Maaa . Dama inason magana da ke..."

"To ni kuma?"

Ya 'daga kansa kafin yace,

"Eh .."

"To Allah yasa muji alkhairi....."

"Aamin .."

"Ina sauraron ka .." Ta ajiye biron da notepad din a gefe.

Ta bashi nutsuwar ta baki daya. Zuciyar ta nata waswasi akan zancen da zai fada... Ta kasa gano koma menene..Don tabbas ta lura baya hayyacin sa.

A hankali kuma a nutse yace da ita,

"Maaaa... Dan Allah a fasa auren nan."

Shiru tayi tana nazarin sa. Can ta nisa kafin ta bashi amsar maganar sa,

"Kai ma kasan abune mai wahalar yiwuwa. Wanda ba zaa fasa a kan ka ba. You know that, don't you?"

"Yeah I know right Maa. But ku duba zancena pls . Infact ba wanda na samu akan zancen nan sai ke "

"Eh saboda ni ce marainiyar wayon ka ko? "

Dariya ya kyalkyale da ita kafin yace,

"Maa gaba daya kin koma cikakkiyar bahaushiya wallahi "

Itama murmushin tayi kawai ta gyara zaman gilashin fuskar ta.

"Eh inada gaskia. Meyasa ba ka samu Wanda suke a samana ba? "

"Allah, Maa naje har sashen Abiey na kasa gaya masa. Dama kune options dina shi da kuma ke. Nasan idan na gaya miki zaki sanar masa. Shi kuma ya gayawa Ummimi. Please "

"Toh ai Zayn. Zancen da kazo da shi kasan ko ni bazan amince da shi ba. Ballantana naje har wajen Abiey dinku na same shi da maganar. Ka zauna kayi tunani. Dangi na kusa dana nesa sun fara hallara saboda taron bikin ku ba? Kai kadai zaa yiwa auren ko kuwa sauran duk suna raayi ne? Tambayar ka na ke?"

Ya girgiza kansa kawai yana sauke zuciya.

"Maa ban gama fuskantar Ahlam ba."

"Yo kai ai ko gaba daya lokacin zaa baka ba zaka amince ku fuskanci juna ba. Yarinyar da gaba daya bata gaban ka. Kullum ranka a hade kana muzurai tamkar wani shugabanmu. Kama dauke maganar nan. Maganin kar ayi kada a so ma kaji na gaya maka."

Ya saka hannu ya shafo keyar sa da saman goshin sa.

"Maa. Yarinyar nan is too lazy wallahi. Gashi ta baci da kashe kudi. Beside idanunta sun bude Maa. I can't stand her. Ita smooching a wajenta ba wani abu bane...."

Haj Hameedah ta karasa sauraron sa. Can tace,

"Toh idan ka aureta sai ka tankwarata. Kayi kokarin nuna mata dai dai da akasin haka. Ka mata wa'azi da jan kunne akan haramcin taba wanda ba muharrami ba. Ka wayar mata kai. Sannu ahankali zata dena...."

Ya sake sauke zuciya a karo na takwas kafin yace,

"Dole ne auren dangin nan ne Maa? "

"Dole ne. Kana gani ai ba akan ka farau ba. Junan ku kuke aure, Mutum yanaso ko bayaso haka ze hakura dole yayi. Haka kuma ba kai kadai za'a aurar a wannan karon ba kai da wasu daga cikin yan uwa zaa aurar. Na menene zaka janyowa kan ka ka janyo mun? Salon ace ni na hana ka saboda ban taba aurarwa ba sai akan ka. ..."

"Maa ni fa bansan yadda ake kaunar mace ko so ba. Bantaba ba wallahi "

"To ka fara akan Ahlam... Sai Allah yasa albarka a abun "

"Maa please...."

"Tashi ka fita Zayn. Zan saba maka idan har ka sake tarata da makamancin zance irin wannan wallahi, Kaji na gaya maka "

Dai dai sanda Waheedah suka shiga itada Moha. Nadra na biye da su.

"Tashi ka fita Zayn " ta fada a tsawance

Da sauri ya mike ya fice. Waheedah tabi bayan sa da kallo. Mamakin ganin dazu sunata hira yanzu kuma ga akasin haka .

Ta cigaba da rubuce rubucen da take a notepad. Su kuma suka haye sama.

Dakin Nadra suka shiga. Dakinta mai dauke da kayan gado da furnitures komai purple and white.

Suka zauna akan wasu sofas. Moha yanata tsalle tsalle. Nadra can ta nisa tace,

"Auren su zaai kinsan.!"

"Oh haba?"

"Allah... Shi da Ahlam."

"Allah sarki Allah yabasu zaman lapia."

"Amin... Kinsan mu bama auren bare sai iya cikin dangin mu kawai. Ko kanaso ko baka so ."

"Masha Allah... Allah ya kara muku zumunci "

"Amin. Nima an mun miji . First cousin dina ne .. Dan yayar Abiey dinmu yana Istanbul "

"Masha Allah. ALLAH sa albarka. Amin"

"Amin .. Ahlam ita yar yayan Abiey dinmu ce."

"Kuna kama ma ...."

"Tohm shi yayan namu bayaso. Kuma shine auren farko da zaa fara na dan dakin mu. Kuma ba yadda zeyi sede ya hakura. "

"Tab... Allah sarki ."

"Hmm! Kede bari wallahi. Allah yabamu saa duka kawai "

"Amin.."

"Yauwa na manta..." Ta bude drawer dinta ta dakko wani material ja daya sha dinkin gown da dankwali harda mayafin sa baki sabo ta ajiye wa Waheedah akan cinyar ta. Ta sake ciro laffaya sabuwa pink me torches black ta ajiye mata "

"Na menene wannan?"

"Kayan fitar biki ne .. Na Zayn and Ahlam."

Waheedah ta girgiza kai kawai. Ta kasa ma magana.

"Meye size din takalman ki?"

Waheedah ta sauka daga kan kujerar ta zube akan gwiwoyin ta. Hawaye daya na bin daya na farin ciki.

"Na rasa bakin godia..."

"Kar ma ki soma sis."

"Nagode Ya Nadra.. Allah ya saka miki da mafificin alkhairn sa. Ya biya miki dukkanin bukatin ki na duniya da lahira "

"Bar kuka please. "

"Ahhh Waheedah ." Moha ya rungume ta shima zeyi kukan

"Ga yaron ki nan zeyi kukan shima.dan Allah ki dena wannan kokekoken meye haka? Ai an zama daya "

Waheedah kuwa sai da ta tabbatar ta karasa godia. Ta sauka kasa wajen Maa nanma ta shiga nuna mata tana godia. Ita dai Maa murmushi kawai take. Ta dakko wani material da ba a dinke yake ba wanda tayiwa dukkanin ma'aikatan da ke karkashinta su. Ta hada da debo kudi yan dari biyar biyar guda 5 ta mika mata wai na dinki.

Nanma Waheedah ta cigaba da godia. Again Nadra ta sake bata takalmi sabo dal. Ranar haka Waheedah ta wuni agidan nan tana farin ciki .

Mai kunshi datazo yi har ita akayiwa. Nadra kuma ta wanke mata kanta ta mata stretching ya sake tsayi.

Sai yamma lis ta koma gidah da tarin kayan. Umma Hadiza ta Yaba sosai ita dasu Kamal.

Har kwanciyar bacci Waheedah bata dena godia ba. Tayi sallar nafila rakaa biyu tanata shararawa su Nadra godia. Da fatan dacewa a rayuwa.

××××

Kamar ko da yaushe a al'adun bukukuwan bikin su. Daurin aure ne yake zuwa farko. Bayan sunje sunyi gwaje gwaje komai nasu kalau zasu iya auren junan su

Ranar alhamis akayi bridal tea party a wani eatery dake kan nassarawa GRA. Iya kawaye mata kawai

Ranar jumu'ah bayan an sakko daga masallaci. Dubban mutane. All the who is who. Suka hallara wajen daurin auren amare da angwaye

Ango Zayn Adams Nasseer da amaryar sa Ahlam Nouh Nasser. Sai amarya da ango na biyu wato: Jannat Adams Nasser da angonta Zaid Nouruh Nasser.

'Yayan Yaya da kanne. Biyu daga yaran professor Adams. Saia daya a yayan su wato Nouh Nasser. Sai daya ta kani gare su wato Nouruh.

Aka daura auren a babban masallaci. Akan sadaki mafi daraja. Daga nan akayi reception a farfajiyar dakin taro da ke gidan na farfesa Adams. Anci an sha anyi hani'an. An kuma yi addoin zaman lapia ga amare da kuma angwayen su....

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:29_


_____


Tuni mayukan shafawa. Da shower gel na wanka harda night cream da face mask da Nadra ta bawa Waheedah. Sunyi matukar karban jikinta. Kalar fatar ta ta kara haskakawa . Ko'ina luwai luwai na jikinta tamkar kifi tarwada. Very smooth and clear. Gashi cimar da suke ci ta the Adams family ta matukar kara gina jikin su . Dukkanin su sun maro akan da da suke a kandare saboda yunwa.

Ranar jumu'ah din da aka daura aure za'ayi mother's eve. Shine wanda zasu saka red material dinnan.

Don haka tun da safe Waheedah tayo wanka. Ta shiga tsaftace komai da killace su zuwa inda ya kamata.

Tana zaune akan kujerar zama. Tana wanke wanke. Marka ta fito daga dakinta. Ta saki wata bahaguwar miqa tana gantsarewa sosai.

Tayi kan Waheedah tana tafa hannuwan ta.

"Wannan kwailin din da kike narasa na menene.... Karfi da yaji sai kin koma baturiya. Kinata bilicin. Da girman Allah Sa'adatu kalli yarinyar nan yadda ta mayar da kanta "

Cewar Marka, Ta juya tana gayawa inna Sa'adatu. Dake zaune a tsakar gidan tana yankan farce.

"Ai lamarin se kallo kawai Marka... A deyi a hankali . Kuma abu duniya a sannu. Kuna bin kwadayi sannu ahankali zaku faada halaka." Inna Sa'adatu ta fada tana yatsina fuska.

Suka cigaba da bin su da zagi da mugayen alkaba'i. Ita dai Waheedah ta toshe kunnuwanta ta hanyar qin cewa komai.

Ta karasa wanke wanken ta kai kwanukan daaka. Ta sharce inda tayi wanke wanken tanata sauri. Don tuni Umma Hadiza ta tafi gidan aikin nata da sassafe dan kama musu wasu aiyukan.

Kayan da Nadra ta bata da material din wajen Maa da aka dinka ta saka a leda don kai wa wajen guga.

Tanata sauri ta fito daga cikin dakin sanye cikin riga da skirt yan kanti sai hijabi babba wanda take zuwa islamiyya da shi.

"A yawo. A yawata...Sai ina kuma zaa sake harbawa. ?"

"Yawan ta zubar m..." Inna Sa'adatu bata karasa fada ba. Waheedah ta daga mata hannu

Idanuwanta sun kawo ruwa sosai. Don abu kalilan ne ke sakata kuka saboda raunin zuciyar ta. Ta saka hannunta daya ta goge hawayen dake tsiyaya a idanunta.

"Ke ni kike dagawa hannu.?" Ta fada cikin fushi da kufulewa .

"Ki dena aibata ni Inna... Ki dena fadan maganganun da ba haka suke ba .. Ya zaki dinga cewa yawon ta zubar za ni?"

Inna Sa'adatu na daga zaune sai ta miqe tana sallallami hadi da tafa hannuwan ta. Bakinta a bude cikin tsantsar mamakin kalaman Waheedah

"Ke da ni kike? Ni ki ke mayarwa martani dan uban ki?"

Waheedah ta sauke zuciya tana kallon gefe.

"Ni ka..."

Kwas!!! Marka ta zuba mata rankwashi a kwanyar kanta da yasha mai da kananun kitson da Najan Isubu ta yarfa mata.

"Karya ta miki? Ba halin uwar ki bane kika gada? Shegiya da idanuwa tsuru tsuru. Gaskia Sa'adatu ta fada. Kin koma mai kwailin. Jikin ki ko'ina ya cicciko bayan da ba ahakan kike ba. Idanuwan ki sun bude. Kina wani gani gani. Duk iskancin da kike a boye zai fito fili duniya tasan ke kike aikata komai."

Waheedah ta sake fashewa da kuka ganin yadda haka kawai sun tsara zancen su suna magana tamkar suna da tabbacin hakan.

"Zaki bar wannan kukan munafurcin ko sai na tashi na hanbare ki? Kayan meye kike sussunnewa a leda?"

Cikin kuka da rawar murya tace,

"Kayan fitar bikin ce zan kai guga."

"To koma 'daka. Babu inda zaki. "

"Dan Allah kiyi hakuri Marka "

"Karki bari na sake magana...."

"Uwar tata ma tun duku duku ta fice daga gidan nan. Ai awajenta ta koya. Gado girman 'da. Hadiza kam watsattsi..." Inna Sa'adatu bata karasa ba Waheedah ta miqe da ga tsugunnen da tayi . Da karfi tace,

"Ya isa !! Ya isheku haka. "

Gaba daya sai suka cika fam da mamakin kalaman ta. Wai yau Waheedah ce ke mayar da martani?

"Wa kike cewa ya ishe su haka?"

Ta saka hannunta daya ta goge hawayen dake zuba .

"Ummanmu ba watsattsiya bace. Sannan uwa ce mai nagarta da jajircewa akan komai. Bisaga addini da al'adun hausa. Umman mu kamilace acikin kamilallu. Tana neman hakkinta ta hanyar halak. Allah shine shahidi "

"Marka... Kinajin abunda yarinyar nan ke fada? Ah lalle dan zaki ya girma."

Marka kuwa tamkar ruwa ya cinyeta ta kasa magana sam. Sai ma sake zubawa Waheedah kallo da tayi."

"Marka Allah ya baki hakuri idan na bata miki rai. Magana ta gaskia ni idona ba a bude yake ba. Sannan mahaifiya ta ba haka halinta yake ba. " Tana kasara magana ta koma daki.

Yayinda Marka ke tsaye sandandan da yatsanta a baka tana gatsawa. Inna Sa'adatu ta ja dogon tsaki tana hararar Marka. Can ta koma cikin dakin ta. Tana kutuntumo ashariya tana saukewa da sunan Waheedah, Umma Hadiza da danginta baki daya.

Zubewa Waheedah tayi akan katifa tana hawaye daya na bin daya. Hakurin ta ya kai makurar da ba zata iya tsayawa bata mayar da martani ba. Duk tarin shekarun nan bata taba cewa uffan ba sai fa yau ta hakurin ta ya kai makura.

Marka ta shiga zaramboto a tsakar gidah . Tayi nan tayi can ita kadai. Ga uban tsaki kamar tsaka.

Can ba dadewa kuwa sai ga Umma Hadiza ta dawo tanata sauri baiwar Allah. Da kular abinci a hannunta. Bakinta dauke da sallama ta shiga gidan . Tanata zabga sauri ganin ba abincin da su Kamal zasu ci na rana.

"Waheedah kina ina ne baki tafi ba? Maza maza ki shirya ga direba nan da ya kawo ni zai dauke ki. Su Nadra suna jiran ki." Ta karasa fada hadi da zare mayafin jikinta ta ajiye a gefe. Tashiga duba kwanukan da zata rabaa musu abincin.

"Ni ce na hanata... Shafaffiya da mai. Ko kina da ja?" Marka ta fada. Ta dasa wani bokitin karfe ta zauna akansa

Waheedah ta fito daga cikin dakin su Kamal ta tsugunna a kusa da Umma Hadiza.

"Gani nan Umma... Sannu da dawowa. Allah ya saka miki da alkhairi."

"Eh muma da bakya fada. Alkhairin Allah kullum cikin sa muke. Makirar wofi."

Da jin haka, Sai Umma Hadiza ta tsame hannunta daga dakko wainar da take ta fuskanci Marka. Cikin ladabi tace,

"Kiyi hakuri ... Bansan tayi lefi ba. Allah ya huci zuciyar ki. Marka."

Ta waiga ta dubi Waheedah dake tsugunne tana karta tsinken tsintsiyar kwakwa a kàsa .

"Me kikai mata waheedah. Je ki nemi gafarar ta "

"Umma na bata hakuri... Wallahi ba abunda nayi ."

"Laaa masalli ila. Ke ni zaki dubi tsabar idanuna ki ce ba abunda kikai mun? Yarinyar nan ba dan na matsa ba da bugu zata kai mun dazu. Ga Sa'adatu nan idan karya na ke...."

"Haka akayi. Don sai da na tura ta daki saboda yadda ta hayayyako wa Marka. Da girman Allah da yarinyar nan yau nima ta dake ni. Don banason jan magana ne shi ya sa na shige daki."

Umma Hadiza tayi shiru. Tama rasa abun cewa, Sarai tasan ba halin Waheedah bane. Dukkanin abunda suka fada karairakin su ne kawai suka shirya don kawowa waheedan suka.

"Kin bi bayanta kenan... Ko?" Marka ta sake fada tana kwafa. 'hum'

Umma Hadiza ta rausayar da kai. Hadi da sake mayar da kanta wajen Waheedah.

"Ki basu hakuri Waheedah.... Marka, Sa'adatu.. Dan Allah ku gafarceta. Allah ya tausashi zukatan ku."

Tayi gurfane agaban su. Yayin da Sa'adatu ke wani munafukin murmushi. Ita kuma Marka ta shiga jijjiga kai tana kada kafafun ta.

"Marka Allah ya baki hakuri..... Inna Sa'adatu Allah ya baki hakuri "

Tana gama fada ta shige daki. Ta kwantar da kanta akan katifa yayinda gangar jikinta ke a kàsa. Hawaye ne ke zuba a idanunta. Ganin karyar da suka shirya bayan ba ayi hakan ba. Tasa bayan hannunta ta goge hawayen alokacin da Umma Hadizan ta shiga daki hannunta dauke da plate da waina akai da miya dataji nama.

"Zauna ki ci.... Kinji."

Idanunta sukayi rau rau. Ta dago ta dubi mahaifiyar ta su, Cikin baki innocently tace,

"Wallahi Umma ba'ai haka ba....." Ta kwashe dukkanin yadda sukayi ba tarage komai ba ta gayawa Umman ta su.

Umman ta sauke nannauyar ajiyar zuciya kafin tace,

"Duk nasani Waheedah. Nasan ba halin ki bane. Amma ki dai na mayar da magana idan sunayi ko da kuwa kece da gaskiya ko akasin haka. Sun haife ki koda kuwa babu yan uwan taka a tsakani. Kinji?"

"Insha Allah Umma..."

"Maza kici abincin."

Umman zata tashi kenan sai ga shigowar Nadra gidan. Tanata doka sallama

"Abbas ka tabbata nanne?" Ta tanbayi direban dayayo musu kwatancen zuwa gidan na su Waheedah.

Nadran ta kira direban ya waya akan rashin dakko Waheedah da baiyi ba. Nan ya ke shaida mata tun dazu daya sauke Umma Hadizan yana jiran Waheedah a kofar layin bata fito ba.

Shine Nadran ta saka dayan direban bisaga kwatancen Abbas daya kai Umman . Aka tuka ta aka kawota kofar layin. Da tambaya suka gane gidan na su Waheedah saboda bashida wuyar ganewa. Da kace gidan Nalado ba wanda baisan yan gidan ba baki dayan su...


❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login