Showing 42001 words to 45000 words out of 123508 words

Chapter 15 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

527

daga kai ta dubi Zayn kafin ta sauke da sauri

"Eh na san shi ..... Umman mu na aiki a wajen su." Ta fada kai tsaye batare da wani karya ko sauya zancen ba.

Zayn yaja kasan labban sa. Duk sai yaji kunya ta dubibiye shi. Ya dan daki kafadar Dawud

"Ta sanni na santa... Infact ni na kawo ta wajen bikin yau. Tare mu ka zo "

Waheedah tayi shiru kanta a kàsa. Tana mamakin ashe yana magana haka?

Dawud ya sake dashare hakora yana gyada kai,

"Komai yazo cikin sauki..... Saboda kai zaka zamo mun tsanin da zan hau katanga na shiga zuciar Waheedah. Ke na ke so ba usulin ki ba. Ba duk wani abu daya shafe ki ba. Da aure nake k...."

Bai karasa ba Zayn ya kware. Dawud ya hau masa sannu. Idanun sa har sun sauya saboda wuya yace.

"Yarinya ce fa Dawud... Me zakayi da wannan? Idan ba reno ba "

"Reno ...?" Waheedah ta maimaita acikin zuciyar ta. Wannan wane irin cin mutunci ne?

"Kai kake ganin ta a yar reno... Ni idanuwana da zuciya ta ganin cikakkiyar mace suke mata wallahi...."

"Lalle fa...." Zayn ya fada yana kauda kansa. Ji yake tamkar ya rufe Dawud da duka haka kawai

Dawud ya sake yin kasa da muryar sa. Ya langwabar da kai hadi da karyar da shi. Cikin muryar tarairaya da lallami yace,

"Dan Allah ki ban number din wayar ki...please! Kinji pretty Waheedah ..?"

Zayn yaja dogon tsakin da shi kansa bai san na meye ba ,

"Waheedah ... Kiyi magana mana . Ko nayi lefi ne uhmmm? Please ..."

Yadda yake karya harshe da lankwasa shi ne yasa Waheedah yin murmushi. Dawud din shima murmushin yayi. Ya sake cewa,

"To me zanyi aban number wayar nanne eh?"

"Allah banda waya...."

"Kina emmata baki da waya. Wait a wane school kike?"

"Ina ss2..."

"Ah dai dai kenan. .. Ashe mun kusa kammala school dinma ko?"

Ta gyada masa kai da sauri tana murmushi . Zai sake magana kenan. Nadra ta kwalawa Waheedah kira

"Zo nan sis zamu shiga ciki."

Waheedah ta amsa da sauri. Don dama tsaiwar dole take agaban su. Ta ketare ta gefen Zayn zata wuce. Awawwaton hannunta ya riko zaren aikin hannun rigar sa .

Ta juya da sauri. Yayinda shima juyowar yayi. Karen hancin su saura kadan ya hadu. Yayin da numfashin junan su ya shiga haduwa a tare.

Kamshin turaren jikin ta dana Zayn suka hadu suka bada wani ni'imattaccen kamshi mai wuyar fassarawa .

"Sorry...... " Ya fada kasan maqoshi. Yayinda ya daga hannun sa ahankali yana zare zaren daga jikin awawwaron nata .

Waheedah tayi tsit. Tana sauraron bugun zuciyar sa da ke bugawa da sauri sauri. Irin bugun nan da zuciya keyi idan tana cikin farin ciki ..


#FARHATAL QALB
(FARIN CIKIN ZUCIYA)



❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:32_

===

Gaba daya ji Zayn yake yi tamkar babu laka ajikin sa. Saboda yanayin yadda jikin nasa yayi laushi ya kasa zare zaren. Jikin sam ba karfi.

"Sorry...." Ya sake maimaitawa yanata kiciniya.

Nadra dake jiran Waheedah ta karasa . Hannu daya ta saka ta yage awawwaron zaren ya fita daga ciki.

"Ya Zayn . Ahlam na jira fa..."

"Gani nan... " Ya amsa ta yana sauke kai.

Wasu masu serving abinci zasu shige ciki ya dauki ruwan roba daya daga cikin ledar sa. Nan da nan ya shiga kwankwada. Sakamakon wani zafi dayaji yana taso masa.

Abokan suka karasar da shi wajen Ahlam. Ta kama hannuwan sa acikin nata. Yayinda kafadun su ke gugar na juna. Ya juya ya kalleta. Ta dan daga tsayinta zuwa kunnen sa ta rada masa,

"I've the right hubby ...... An daura ai ko?" Ta karasa ce masa tana murmushi.

A haka suka shiga cikin marque din ango Zaid da amaryar sa Jannat sune a farko. Sunyi matukar kyawu ta saka wata riga baka gown me flowing da wasu stones masu glittering farare tas.

Sai shi ango Zaid da yayi shigar alfarma shima cikin wagambari fara data sha aikin baki. Yayi bala'in kyau ba kadan ba. Shi da amaryar tasa sun bada color .

Sai couple na biyu. Ango Zayn dayayi shigar wagambari baka data sha aikin kala fara. Sai amaryar sa Ahlam data sha kyau itama cikin farar gown mai glittering (kyalkyali) na stones baki.

Ba kadan ba sunyi kyau. Kyawu irin wanda alkalami yayi kadan wajen fassara shi. . ..

Gaba daya kowa sai da ya miqe a cikin marque dinnan in honor of the couples. Har sai da suka zazzauna awajen zaman su. Tukun sannan kawayen amare da abokan angwaye suma aka sakar musu speaker rawa suka dan tattaka. Kafin su koma wajen zaman da akayi musu na musanman suka zazzauna.

Daga nan aka kira wata babbar malama. Ta bude taro da addua. Sannan gayshe gayshen yan uwa da abokan arziki. Sanarwar zuwan manyan baki na musanman. Bada tarihin amare da angwaye daga abokanai da kawaye. Sai kuma refreshments.

Abinci ne kala kala babu irin wanda babu. Menu aka bawa kowanne yayi ticking abincin da yake so. Dik wanda ka zaba shi din ake kawo maka. Nadra da kanta ta zabarwa Umma Hadiza. Aka kai mata. Yayinda Waheedah ta zabi wanda take so.

Karar kwanuka da cokula kawai kakeji sai slow music da ke tashi. Amare da angwaye ma an saka su dole su ci. Bisaga jagorancin Ummimi da tace jikokinta ba zasuyi jidalin yunwa ba. Bayan kowa ya take ciki yana cika cikin sa.

Aka saka dariya baki daya. Ahlam ta juya ta dubi Zayn da ke danna wayar sa.

"Hubby .. abincin fa?"

"Na koshi..." Ya amsa yana kallonta

"Ya zaka ce ba zaka ci ba...? Bayan Ummimi tace duk mu ci. "

"Banacin abincin wadanda bansani ba gaskia. Wanda na sani dinma rarely nake ci."Ya karasa yana cigaba da danna wayar sa.

Ahlam ta juya ta kalli su Zaid da Jannat. Suna feeding junan su suna hirar su kasa kasa. Wani tuququn bakin ciki ya tsaya mata a makoshi. Ganin ita natan yayi biris da ita waya ce ma agaban sa. Ko irin lallashin nan nata baya yi.

"Zayn...."

"Naam .. Ahlam"

"Ba zaka ce naci abincin ba?"

"Tohm Waheedah ki ci abincin ."

"Waheedah Kuma?" Ta tambaye shi cikin tsantsar kulawa.

Sai a sannan Zayn ya gano baranbaramar da yayi. Yayi saurin fuskewa hadi da mayar da wayar sa aljihu. Kasan zuciyar sa tunanin Waheedah yake tabbas. Amman harshen sa daya ambata sam baisan dalili ba .

"Look Ahlam...."

Ta katse shi.

"Babu zancen look ... Zayn I'm i that unimportant? "

"Noo . .. Kinaji Dawud ne ba kinga dazu na je wajen sa ba...!"

"Eh...."

"Toh maganar Waheedah din yake mun . Yana son ta "

Ahlam ta sauke gauruwar ajiyar zuciya. Amman duk da haka ta sake tambayar shi da,

"To meyasa zaka kira ni da Waheedah? Tun da ai ba awajen bane. Yanzu ni da kai ne a zaune "

Ya sosa keyar sa yana murmushi.

"Yes I'm all ears Zayn .. saboda me zaka kira sunana da Waheedah?? Sunana bashida matsayi a zuciar ka ne ko kuwa?"

"Da shi muke magana ta WhatsApp ... Kingan shi da can wayar sa a hannu."

Ya nuna mata Dawud da yatsa. Nan taga Dawud din wayar sa a hannu yana dannawa. Hankalinta sai ya kwanta. Ta danyi murmushi lallausa

"Na yadda .."

"Yauwa.... " Ya amsata yana murmushi

"Abincin fa?"

"Ki ci...."

"Ka bani.... Feed me pls"

Ba yadda ya iya. Ya debo fried rice da patoosh salad a spoon ya saka mata a baki. Ya zuba ruwa a cup ya bata.

Kawayen amarya na ta awwwwn.. Waheedah ta dube su cikin kulawa. Suna birgeta kwarai matuka da ka gansu kasan su din suna kaunar junan su .

Ya dakko tissue ya goge mata baki.

"Thank you hubby...."

"Anytime...."

Yana daga kai suka hada idanu da Waheedah . Ya janye idanun sa da sauri yana saisai ta kan sa.

Haka aka cigaba da gudanar da shagalin bakin ranar. Yan uwan juna gaba da baya. Kamar ko da yaushe. Babu wasu bare sai yan gayyata da wasu tsirarru na daga kawaye ko abokai dama makota da sauran su

Anyi 'barin kudi ranar tamkar bishiyun kudi ne da su suke zazzaga su.

Dukkanin iyalan Ummimi matan su 3 anko sukayi gwanin shaawa. Cikin wani dandatsetsen lace mai dan karen kyau da kyalkyali. Yayin da mazan suma sun zuba wata gezna shadda mai madaukakin tsada da kyau

Lamarin sai wanda ya gani ya kuma halarci taron kawai. Anci an sha anyi hani'an.

Zayn yayi excusing kan sa ya fita daga cikin marque din. Ya tsaya a tsaye yana mai furzar da iskar bakin sa.
Kansa sai wani sara masa yake yi .

Yanayin jikin sa baki daya ba dadi. Ya kuma tabbatar da hakan nada nasaba da wannan bikin. Gaba daya ya rasa wane tunani ma zai kama da zai fitar masa da mafita.

"Zayn... Ka dawo ciki zaa dauki pictures." Cewar Awais abokin sa.

Gyada kai kawai yayi alamun toh. Ya koma ciki. Aka shiga daukar hotuna ta ko'ina photographers nata haskakawa da aiyukan su.

Sannu ahankali wadanda aka gayyato suka fara tafiya inda suka fito. Ciki har da Waheedah da Umma Hadiza. Daga karshe kuma bayan yan uwan sun gama warkajami. Aka tashi daga taron sai kuma na washegari idan Allah yayi da rabon ga ni....

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:33_

=====

*GIDAN MALAM NALADO*


*DA* sallama a bakunan su, Suka shiga cikin gidan na su. Marka na kwance akan shimfidar tabarmar ta. Saitin gefenta daga dama kuwa fitila ce ta wuta mai lagwani.

Bata amsa sallamar ba. Sai ma dago fitilar da tayi don ganewa idanun ta.

"Wohoho. Fito nan mai sunan malam. Ai na gayan ka."

Nan da nan Malam Nalado ya fito daga cikin daki. Ya tsugunna agaban mahaifiyar ta sa.

"Kaga ni ko .....? Wane tsinannen biki ne za'a tafi tun rana tsaka sai dare zaa dawo?"

Umma Hadiza ta fara girgiza kai zata yi bayani. Marka ta hanata. Ta hanyar mikewa jikinta har kakkarwa yake saboda bala'i.

"Dube su ... Dubi kayan jikin Wahidin fisabilillahi... Wannan shiga ta dace? Dubi fatar jikin ta da fuskar ta. Tayi kwailin.. kalli yadda ta kode tsabar bilicin."

"Wallahi Allah bana bleaching Marka .. Mai ne da sabulu Nadra ta bani. Wadda Umma ke yiwa mahaifiyar ta ai..."

"Zaki rufe mun baki ko sai na zo na gabje ki anan?"

"Allah yabaki hakuri ...." Ta fada hawaye sirara na zuba a kyakkyawar fuskar ta...

"Na gaji..... Mai sunan Malam. Yau dai kagani da idanun ka. Ire iren rashin tarbiyyar da suke gudanarwa acikin gidan nan.."

"Wallahi Malam... Ko tashi ba'ayi ba awajen taron muka taho."

"Bikin gidan na uban ku ne dama da zaku zauna?. Ai malam na dauka abun na mutunci ne da arziki da mu ma za'a gayyace mu. Muje mu kashe kwarkatar idanun mu. Amman saboda tsabar akwai kaucewar hanya ai kaga su kadai suka tafi. Sai cikin dare. Kowane gidah sun kulle gidajen su banda mu. Su sun tafi regargadin biki gidan mu a yashare. "

Umma Hadiza ta tsugunna tana jujjuya kai. Idanunta sun kawo ruwa sosai. Cikin muryar ban hakuri da sanyin jiki tace,

"Dan Allah Marka kiyi hakuri .... Wallahi wallahi babu inda mukaje sai wajen taron bikin nan. Kuma acikin gidan yake daga wani bangaren. Kayi hakuri Malam. Dan Allah ku yafe ni."

"Hakuri ... Wohoho ko ba hakuri ba? "

"Eh dan Allah Marka "

"Mai sunan Malam.."

"Na'am Marka ."

"Kace Hadiza ta bar maka gidan ka. "

"Kiyi hakuri Marka .." ya fada a hankali yana kallon Hadiza ta gefen idanu

"Nayi hakuri ?" Ta tambaye shi. Tana binsa da kallo sheqeqe.

"Ehh ."

"Matsa can. Sahoro mijin sahorama. Gidah na waye?"

"Na ki ne Marka."

"Toh wabillahil lazi zaman Hadiza ya kare a gidan nan."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!!" Kamal ya shiga furtawa. Yana takawa dakyar hannun sa dafe da bango

"Matsa can. Gawa taki rami kawai "

"Haba Marka .. Haba Marka." Umma Hadiza ta fada . Hawaye na kwarara a fuskarta sosai jin yadda Markan ke aibata Kamal jikan ta.

"Karya nayi? Ba ragowa bane shi? Kullum akan magani. Nakasasshe, Bushassshe. Kanjamamme. Ai kuwa gawa ce shi din da taki rami "

Kamal yayi murmushi. Ya dafa bango ya zauna yana sauke numfarfashi

"Marka... Ki dena cewa haka ... Tamu kaddarar kenan. Lapiyayyun ma basu da tsimi bare dabara. Kowanne rai Allah ya halicce da dukkanin dik wasu abubuwan da zasu faru agare shi. Don haka wannan cuta da muke fama da ita kankarar zunubai ake mana...Marka mu fa jikokin k .."

"Karka karasa... Kar ka soma karasawa. Bani da tabbacin kudin jikoki na ne ko akasin haka. Mai sunan malam babu yadda banyi ba kar ya auro Hadiza. Amman ya toshe kunnen sa. Yayi kunnen uwar shegu. Hadi da badawa idanun sa kasa. Ya kafe ya nace ya cije kan dole sai ya aurota. Gashi nan ai baki dayan tattalin arzikin sa ya kare akan ku da uwar ku. Dukkanin ku ku ukun ba mai lapia ingatacciya. Ita wannan baki daya ma makanta ce da ita. Sai da temakon gilashi take gani. ..." Ta karasa tana mai sakarwa Waheedah rankwashi .

Waheedah bata ce komai ba. Yayinda kanta ke a kàsa kawai.

"Kai maganganun menene haka ne..? Cikin bacci na ke jiyowa." Cewar Inna Sa'adatu . Ta gantsare tana miqa hade da yin hamma.

"Su wa kika sani? Hadiza da iyalanta ne. Ina magana suna mayar mun. Munata musayar yawu da ni da uwar tasu. ."

"Au wai sai yanzu kuka dawo...? " Inna saadatu ta tambaya tana mai sauke kallon ta bisa fuskar Umma Hadiza .

"Eh yanzu muka dawo Sa'adatu " Umma Hadiza ta amsa ta.

Inna Sa'adatu cikin makirci ta sake cewa,

"Yanzu ku kuna mata ku ka kai wannan tsakar daren awaje? Fisabilillahi biki bana dangin iya ba bana baba ba ? Meyakwan ke Hadiza ki taso keyar ta ku dawo tun tuni."

"Wacce hadizan ce zata ce wa yarta su dawo da wuri? Bayan watsewar ita ke koya mata .."

"Allah ya baku hakuri Marka.."

"Ni fa idan kina gayamun Kalmar hakurin nan ji nake tamkar wuqa kika dabamun a zuciya. Hakurin ubanme zanyi? Kama ki zan na saka a garke na daure ko kuwa? Ai babu abunda ke tsakani na da ke Hadiza. Ba auren 'da na kike ba .... Shekaru masu dadewa."

Umma Hadiza ta tamke idanunta tana dartse bakinta. Baki daya kanta ya mata nauyi. Duk tarin shekarun nan da aka dauka. Bata taba buda baki tacewa yaranta basa tare da mahaifin su ba. So take akwai lokaci da ta ware zata sanar musu idan Allah ya so. Amman baki daya Marka ta tarwatsa mata lissafi. Kusan kullum seta goranta mata. Tayi ta shelan ba aure tsakanin ta da dan ta. Tamkar wani lefi tayi babba da yasa ya saketa. Bayan Markan ce ta saka dole ya saketa babu wata kwakkwarar hujja.

Hawaye sirara suka shiga zuba a idanun Umma Hadiza. Marka ta kalleta tana yamutsa baki.

"Ni fa kukan munafurci ne banaso. Uban me na miki iyye?"

Umma hadiza ta girgiza kai kawai. Hade da saka hannu ta share hawayen ta.

"Babu komai .."

"Toh mai sunan Malam... Yau magana ta kare. Idan Allah ya kai mu wayewar gari. Inason Hadiza ta tattare nata ya nata ta bar mun cikin gida. Kar kuma ta sake tako kafarta kofar gidan nan idan ba da wani dalili ba kwakkwara. Wannan shine zancen da na yanke. "

"Tohm Marka.. Allah ya tashe mu lapia " Umma Hadiza ta fada hade da miqewa tsaye. Ta kamo Kamal ta temaka masa ya shiga daki.

Dan sauran kayan kwalam da suka samu awajen bikin ta juye musu akan faranti ta raba musu shi da Najib.

Sannan ta kunna musu maganin sauro tasa daga bakin kofar daki. Tayi sai da safe ta koma daki.

Waheedah ta cire kayanta ta mayar da na gidah. Wata riga da ta mayar da ita ta bacci. Sai hula da ke kanta

"Baki kwanta ba....? Tara da kwata fa "

"Zan kwanta Ummaa. Yanzun dai bana jin bacci "

Umma Hadiza ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Hawayen da ta ke kokarin zubowa ya shiga tsiyaya . Tayi sauri ta goge . Nan ta fara jiyo sautin na waheedah har da shessheka. Tayi saurin janyo ta jikinta tana lallashinta.

"Bar kuka Waheedah ... Kowane dan adam da tasa kaddarar., Mu ta mu .....

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login