Showing 18001 words to 21000 words out of 123508 words

Chapter 7 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

518



"Ba zaki dago kafa ba sai kin makara ko?"

"Ga ni nan." Ta shiga sassarfa don cinma Umman da tayi gaba abunta .


Sanye yake cikin kaya tamkar na bacci. Wando daya wuce gwiwa. Da kuma wata riga mai dogon hannu. Sai takalma irin na gudu dinnan. Yayinda kunnuwan sa ke sakale cikin earphones.

Gefen dantsen hannun sa kuma wani madauri ne da robar ruwa aciki. Ya hada gumi sharkaf . Yanata gudu da alama atasaye yake. Motsa jiki/exercise.

Bayan sa kuma wani matashi ne shima yake biye da shi. Sanye cikin irin kayan sa. Amman nasa wandon har kasa yake .

Tsabar kwarewa a gudun da suke. Har Wani juyawa suke suna hira da juna. Acikin juye juyen da yake ne yana magana dana bayan sa.

Garaf yaci karo da Waheedah wadda ke dagawa Umma Hadiza hannu zata shiga gidan aikinta .

Yar jarkar ruwan data dura ruwa aciki ta fadi a kàsa. Hakama gilashin ta daya ballo daga idanunta ya fadi kasa

A tare suka kai hannu. Zata dau gilashin shima zai dakko mata. Hannuwan su suka hadu dana juna. Karaf suka daga kayuwa a a tare. Manyan idanun sa suka sauka akan nata. Gashin girar sa da ya kusa hadewa kawai ta ke Iya hangowa. Da jajayen labbansa. Sai lumshe idanu take ta kasa ganin ko wanene saboda matsalar idanun ta

"Waheedah!!" Umma Hadiza ta kira sunanta da sauri. Ta karasa tana janyo ta jikinta hade da goge gilashin ta mayar mata fuska

"Yi hakuri bawan Allah ... Bata gani sosai. Musanman kusa haka "

Kasa magana yayi. Yayinda zuciyar sa ke tsananta bugawa. Bai iya cewa komai ba ya shige cikin gidah da sauri. Dayan saurayin da ke bayan sa ne ya tsaya ya basu hakuri kafin shima ya shige cikin gidan .

Waheedah ta daga idanu ta sauke akan tankamemen signboard din dake jklin gidan da suka shiga wanda ke a matsayin inda Umma Hadiza zata fara aiki wato:. The Adams family.....!!!

*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*


*ZAFAFA BIYAR BACTH A*


1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*


2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*


3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*


1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*


_Duk biyar 1500_

*______________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)*

2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)*

3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)*

4... _INAYAH_
*(Mamu gee)*

5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*



_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*



*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:14_

Ahankali ta janye idanun ta daga kan gate din gidan da suka shiga. Kwantaccen gashin kansa daga baya kawai ta iya hangowa alokacin da Umma Hadizan ta mayar mata da gilashin idanunta

"Sannu baki bugu a wani wajen ba ko?"

"Eh...! Umma "

"Tohm Allah ya tsare gaba. Ungo wannan kya saya ko awara ce idan an taso ku tara (break) " Ta karasa tana mika mata nera talatin.

"Du? Nagode Umma. Allah ya saka da alkhairi."

"Aamin Aamin."

Har kan kwana Umma Hadiza ta raka Waheedah, Sannan ta juya ta shiga gidan aikin nata.

Waheedah na tafe akan hanyar karasawa makaranta tana tunanin gwaren da sukayi da mutumin da bataga fuskar sa ba sai gashin girar sa da na kansa alokacin daya shiga gidan su.

Dan siririn tsaki ta saki kawai a kasan maqoshi tace,

"Allah ya kyauta... Shi da ya bige ni ai sai ya ban hakuri. , Su masu kudinnan dama wasunsu sai ahankali wallahi." Mita ta shiga yi sosai har ta karasa makaranta.


××THE ADAMS RES.××


Sashen da yake a matsayin na mazan gidan ya nufa. Ya shige dakin sa yana buga kofar da karfi.

Gaban mudubi ya tsaya yana kallon kansa, Ya yinda ya saka dayan hannun sa ya shafo kasan keyar sa yana sakin ajiyar zuciya. Bai san musabbabin da zuciyar sa ke wani irin zillo ba da farin cikin daya kasa sanin na menene.?

Knocking kofar dakin nasa akayi. Yana daga tsaye yace,

"Yes!! Come in...."

"Assalamu alaikum… Bross."

"Wa'alaykm Salam! Maza "

"Abunda kayi ba halin ka bane ... Ya za kai haka?"

"What about it? Mena yi ?" Ya karasa fada yana unbuttoning rigar jikin sa.

"Ka fini sanin me kayi ai.."

"Kaga ni wanka zanyi malam "

"Okay haka zaka ce? Fine."

Har ya kai kofa zai fita. Ya saka hannun sa akan handle din zai murda. Ya kirawo sunan sa.

"Basher..."

Dan murmushi basher din yayi ya juya. Kai kana gani kasan jini ne su. Domin suna kama. Sai dai daya yafi daya haske da karan hanci.

"Uhm muna magana .. Ina sauraron ka. Meyasa kai haka? Meyasa ba ka tsaya ka nemi afuwar ta ba bayan kasan kai ne me laifi, faulty . ....Why?? Meyasa Zayn.?"

Wanda ya kira da Zayn ya dan yi murmushi kawai. Yayinda ya dora towel din hannun sa akan kafadar sa. Ya zauna a gefen kujera yana jan kasan leben sa.

"Magana nake maka Zayn "

"Basher. Bansani ba. Bansan meyasa ba. Kawai na tsinci kai na cikin wani yanayi marar misaltuwa. Bansan wane irin yanayi bane basher. Nasan kuma nayi laifi. But wait ai ba da sanayya nayi hakan ba. Beside itama da lefin ta ..."

"Bangane da lefin ta ba. Meta yi? Bayan ance maka bata gani sosai musanman ganin kusa . Short sited ness..."

"Eh ina nufin hankalinta na wani wajen ta tsaya chak. Ni kuma na juyo muna magana da kai, Ai baya bata gani ko? So Allah ya bata hakuri. "

"At least seka tsaya ka bata hakurin acan Zayn. ....."

"Uhm ,"

"Ba uhm ba. Kasan baka kyauta ba "

"Nace Allah yabata hakuri yanzu ai ko. ? Kuma Allah yaga zuciya ta. "

"Kai ka sani , Matsalar ka ce. Mutum sai taurin kan tsiya." Basher na karasa magana ya mike yayi ficewar sa cikin takaicin dan uwan nasa.

Yana fita Zayn ya sauke nannauyar ajiyar zuciya hade da saka hannu ya dafe saitin zuciar sa dake tsananta zillo tamkar zata fado kasa.

"Ya Rabbi...!!!" Ya furta ahankali.idanuwan sa a lumshe.

Bedside drawer ya janyo ya dakko wani memo dinsa da biro yayi rubutu kadan aciki ya rufe.

Bandaki ya shige bayan yayi addua. Shower yasakarwa kansa. Ya dade ruwan dumin na dukan jikin sa. Ya saka hannun sa biyu ya kwantar da gashin sa baya da ruwan yake duka. A duk sanda ya runtse idanun sa hotunan dazu kawai zuciar sa ke hasaso masa na shi da yarinyar nan.

Siririn tsaki ya dan saki yana mai sake sauke ajiyar zuciya a karo na ba adadi. Sihirtaccen kamshin ta da ya do ki kofofin hancin sa. Yayi matukar tasiri acikin ran sa, kwakwalwar sa kai dama gangar jklin sa.

Haka ya karasa wankan nan. Wanda kusan rabin sa duk tunanin Waheedah ne. Ya rasa mai yasa dede da second daya bai man ce ta ba.

Lamarin tamkar almara ya dauke sa. Don shi gaba daya mata basa gaban sa idan ba wanda suke jini daya ba ko yan uwa. Sai gashi, Wai yau shine ya tsinci kansa cikin tunanin mace. Macen ma wadda baisan a wacce duniyar take ba. Uwa uba daga haduwar tsautsayi.

Ya sake sakin tsaki yana kambama lamarin sosai.

"Ko dai ba mutum bace?" Ya tanbayi kansa shi kadai. Don ko da wasa Kwatankwacin haka bai taba faruwa da shi ba.

Haka ya karasa shiryawa cikin kananun kaya riga da wando na jeans. Yabi ya feshe jikin sa da turarukan sa dake jere akan dressing mirror.

Harda shinshina kwalaben ko hancin sa ne. Tabbas lamarin ya fara bashi mamaki. Yadda sosai kamshin ta ke yawo a duk wasu rassa na sa musanman hancin sa da ko kadan bai gushe da kamshin ba.

Ganin zai batawa kansa lokaci da wani shirmen wata yar karamar yarinya da a girme ya girme mata sosai. Hakan ya sashi ficewa daga cikin dakin nasa bayan ya murza key.

Kai tsaye ya wuce sashen mahaifiyar sa. Yana tafe yana yan addoin sa a kasan maqoshi.

Da sallama ya karasa shiga ciki yana dan daga murya.

"Wa'alaykm Salam. " Cewar Umma Hadiza da ke goge jikin dispenser.

"Barka da safiya." Ta gayshe dashi.

"Barka ina kwana?" Ya amsa ta yana kalle kallen inda zai hango mahaifiyar ta su.

Umma Hadiza sam bata gane shine wanda sukayi gware da Waheedah ba dazu, Saboda kayan jikin sa ma ba irin na dazu bane. Kuma dai bata karewa fuskar sa kallo ba dazun.

"Maaaa "

"Zayn., Ga ni nan." Cewar Dr. Hameedah dake saukowa daga saman bene.

Durkusawa yayi har kasa ya gayshe ta. Ta amsa masa hade da saka masa albarka. Ta cigabada cewa,

"Wannan itace baiwar Allah da nake gaya muku. Sunan ta Hadiza. A dayar unguwar suke ta bayan mu dinnan."

"Oh okay Allah sarki....!" Ya fada yana dan kallota da gefen idanun sa. Tamkar itace matar dazu. Don suna yanayi da yarinyar da sukayi gware.

"Ga abincin ka can akan dinning.......


*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*


*ZAFAFA BIYAR BACTH A*


1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*


2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*


3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*


1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*


_Duk biyar 1500_

*______________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*

5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*

1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)*

2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)*

3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)*

4... _INAYAH_
*(Mamu gee)*

5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)*

_Kuɗinsu a yanzu 1k duk biyar_

*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*

_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*

_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*

_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*



_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_

*_07040727902_*

_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_

*_09134848107_*



*_Muna godiya da zaɓin zafafa biyar 😘😘😘🙏🏻_*
[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:15_

××××
 
"Okay Maaa...!" Ya amsa ta cikin nutsuwa da tantsar biyayya.

Har dinning area din ta raka shi. Yana gaba tana biye da shi a baya suka zauna akan kujeru.

"Tea or coffee...?"

"Coffee literally..."

"Tam.... " Wajen coffee maker ta isa dake jone ajin bango. Dake dinning area din kawatacce ne daya ji kaya ya koshi.

Nan da nan cikin kankanin cokali ta hada ta miqa masa. Ta bubbude warmers din da abincin ke cike. Niimataccen kamshin abincin ya gauraye ko'ina.

"Plantain, chips. Doya. Ko yamballs? Ga shredded beef sauce kuma nan da kunu. Nan kuma kosai ne sai wainar kwai."

Dan tsayawa yai yana duban abincin data bubbude murafen su kafin ya girgiza kai kawai.

"Ai kawai Maa bari na sha kununnan ya isa."

"Bangane ba. Kasan sarai kuma dan kai akayi wadannan abubuwan tunda ba cin abincin masu aiki kake ba tun safe nake aikin soye soye ."

"Afuwan Maa " Ya fada ahankali kawai yana sauke numfashi

"Meya faru ne? Naga kaman akwai abunda yake damun ka."

"Bakomai Maa."

"Ai kai taurin kan ka ne yake kara maka ciwo. Kaji da shi "

"Zanci. Aban plantain da soyayyan kwan kawai "

Zuba masa tayi ta tura masa da plate din gaban sa.

"Kullum tamkar wani karamun yaro sai an tsaya akan ka kake cin abinci."

Murmushi kawai yayi. Ya dauki fork yana ci ahankali.

"Nagode Maa. Komai yayi dadi "

"Madalla. ..."

Bai sake cewa komai ba. Ya shiga ci ahankali har ya karasa cinyewa.

"Alhamdulillah...Wai ina su Nassem ne?"

"Suna bacci mana, Anjima kadan zaka gan su. Nadra kuma tana wajen su Jannat. "

"Oh okay. Ni dai ince duk yau banji motsin su ba. "

"Uhm.."

"Bari na tashi zan dan biya site ne."

"Okay Madallah, Allah ya temaka."

"Aamin Yaa Rabbi Maa. "

Tashi yayi ya maida kujerar cikin dinning table din, Sannan ya fice daga cikin sashen bayan ya saci kallon Umma Hadiza da ke shanya dusters ajikin abun shanya.

"Sannu da aiki Hadiza "

"Yauwa sannu Hajia. Na kammala wadan nan akwai wasu aiyukan da zaa tayaki dashi?"

"A'ah sai zuwa anjima. Har yanzu dai ba zaki karba abincin kici ba ko?"

"Allah Hajia a koshe nake. Sai da muka ci yar tsala tukun sannan na taho."

"Ai shikenan, Kyaci anjima. Dawo parlor ki zauna. "

A tare suka fita daga cikin kitchen din zuwa parlor. Hajia ta zauna akan kujera Umma Hadiza kuma ta nemi gefe ta zauna.

"Wannan da ya fita shine babban 'da na fa."

"Ah haba dai? Allah sarki "

"Wallahi shine , Muna kiran sa da Zayn. Sai Nadra  wadda suka kare makaranta a kasar waje inda mukaje.Ita da su  yayyanta yayan wajen kishiyata. "

"Masha Allah. Allah ya raya su. Ya biya bukatu na alkhairi "

"Aamin Hadiza. Bayan Nassem sai Moha, Muhammad kenan, Ita Kuma Nadra ita kadai ce 'yata mace ce. Su kumaa mazan su 3. Ai Ina tunanin tamkar ma ma gaya miki zuwan da kukayi ko?"

"Tabbas kin fadi haka Hajia. Allah ya raya su ya musu albarka Amin..."

"Aamin Yaa rabbi."

"Jira nake 11 ta cika na je asibiti inada wata tiyata 12:30,"

"Allah ya kai mu yasa ayi lapia Hajia . Amin"

"Amin Hadiza "

Suna zaune Nadra ta dawo daga sashen su Jannat . Malami ne yake zuwa ya koya musu karatu .

"Maaa "

"Naam Nadra "

"Ah ina kwana?" Ta dan rissina ta gayda Umma Hadiza.

"Mun kwan kalau? "

"Alhamdulillah."

"Itace 'yata macen da nake gaya miki Nadra ... Dake kafin zuwan ki tatafi can sashen shiyasa baku hadu ba. "

"Allah sarki. Ai kuwa dai ga kamar nan masha Allah. "

"Okay itace wadda kike fada mana ko Maa?"

"Yes ita ce."

"Yunwa..."

"Kije kitchen an kai tun dazu. Amma sai kinyi reheating . Idan kuma na Zayn kike so yana dinning "

"Ah bari naci namun. Abincin akhi sai shi."

Dariya suka sanya baki daya. Nadra ta dubi Umma Hadiza ta shiga cewa.

"Allah shi abincin sa ba yaji kwata kwata, Kuma yana son spices over. Shi fa kullum abinci sai Maa ta masa da kanta yake ci. Idan aka dafa bayacin girkin wani. Sannan ko eateries ba zeje ya saya yaci ba. Ko anyi ordering bayaso. Kullum home cook. Abincin ma wanda Maa tayi. "

Umma Hadiza tayi daria .

"Allah sarki bawan Allah, .."

"Ke Nadra. Je ki kwankwasawa Nassem baccin ya isa haka nan."

"Harda Moha?"

"A'a shi kyale shi "

"Autan ne Moha ko?"

"Eh shine. Ai kinji tace a kyale shi. Dangware shalele ne ai."

Suka sake sakin dariya. Kafin daga bisani Nadra ta miqe ta nufi wani daki dake kasan kafar bene. Ta shiga knocking kofar.

"Nassem.!!! Nasseem!! Nassem!!"

"Naam..." Ya amsa ta cikin muryar bacci

"Ka tashi inji Maa."

"Tohhh. " Ya sake kundundunewa da bargo zai koma baccin kawai ta murda kofar ta shiga kanta tsaye bayan ta saki katuwar sallama

"Oh please ...."

"Ba wani please. Dalla ka tashi inji Maa." Ta kunna wutar dakin.

Ya yamitsa fuska yana mai jujjuya kansa.

"Na ji..."

Ta tsaya kyam a kànsa har sai daya gaji ya miqe ya shige bandaki bayan yayi sallama. Sai da taga ya tashin dagaske tukun tatafi kitchen. Nan da nan ta zuba abincin ta ta koma kan dinning bayan ta hada shayi mai kauri.

Ba jimawa sosai Nassem ya fito daga dakin sa. Sanye cikin jallabiya fara. Gashin kansa a kanannade. Kamar su daya da Zayn.

"Ina kwana?" Ya gayda Umma Hadiza yana rufe bakinsa da tafun hannu. Sakamakon hammar data taho masa,

"Alhamdulillah...."

"Shine Nassem din."

"Allah sarki..." Cewar Umma Hadiza. Tana dan kare masa kallo tamkar shine na wajen nan da suka ci karo da Waheedah .

"Ai kamar shine suka yi gware da yarinyata a waje ko dazu da sassafe."

"Nasseem? Anya kuwa shine. Saboda tun sallar asubah da suka dawo daga masallaci cikin gidah kawai yayo. Dan masallacin ma anan gidan yake. Ina ga dai cikin yan uwansa ne. "

"Maybe Akhi ne... Ya Zayn."

"Oh eh... Yayan su kika gani tabbas, Wanda yazo yaci abinci dazu. Kamar su daya da Nassem din."

"Allah sarki. Sai da kika fada na gano."

"Yarinyar ki makaranta take zuwa anan unguwar..........????


*_ZAFAFA BIYAR COMPLETE DOCUMENTS_*


*ZAFAFA BIYAR BACTH A*


1.. _WUTSIYAR RAƘUMI_ 350
*(Bilyn Abdul)*


2.. _KAI MIN HALACCI_ 350
*(Miss xoxo)*


3.. _BURI DAYA_ 350
*(Mamu gee)*

4... _DAURIN BOYE_ 350
*(Huguma)*

5... _SAUYIN KADDARA_ 350
*(Hafsat Rano)*

_Duka biyar 1500_

*___________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BATCH B_*


1... _DAURIN GORO_ 350
*(Hafsat Rano)*

2... _ALKAWARIN ALLAH_ 350
*(Huguma)*

3... _QAUNAR MU_ 350
*(Mamu gee)*

4... _IGIYAR ZATO_ 350
*(Miss xoxo)*

5... _GUDU DA WAIWAYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*_____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH C_*

1... _MIN QALB_ 350
*(Mamu gee)*

2... _SARAN ƁOYE_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _KIBIYAR AJALI_. 350
*(Miss xoxo)*

4... _ABINDA KE CIKIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _SIRADIN RAYUWAR BILKISU_ 350
*(Huguma)*

_Duk biyar 1500_

*____________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH D_*

1... _ALKIBLA_ 350
*(Huguma)*

2... _DALAAL_ 350
*(Miss xoxo)*

3... _UBAYD MALEEK_ 350
*(Mamu gee)*

4... _MABUDIN ZUCIYA_ 350
*(Hafsat Rano)*

5... _MAKAUNIYAR KADDARA_ 350
*(Bilyn Abdull)*


_Duk biyar 1500_

*____________________________*

*_ZAFAFA BIYAR BATCH E_*

1... _SO DA ZUCIYA_ 350
*(Mss xoxo)*

2... _TAKUN SAAKA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

3... _HALIN GIRMA_ 350
*(Hafsat Rano)*

4... _DAB'IZAR ZUCIYA_ 350
*(Huguma)*

5... _DEEN MARSHALL_ 350
*(Mamu gee)*


_Duk biyar 1500_

*______________________________*


*_ZAFAFA BIYAR BACTH F_*

1... _BAKAR INUWA_ 350
*(Bilyn Abdull)*

2... _RAYUWAR MACE_ 350
*(Hafsat Rano)*

3... _NOOR ALB_ 350
*(Mamu gee)*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login