Showing 87001 words to 90000 words out of 123508 words
ya shiga motar sa ya bar gidan.
Bayan fitar Zayn ba dadewa.. Ummimi ta dubi Haj Hameedah .
"Menene Hameedah?"
"A'ina Ummimi?"
Ummimi ta danyi murmushi,
"Akwai abunda ki ke boyewa. Naga kallon da kika yi wa Zayn shi ya hanashi furta komai akan yarinyar da ya ke so. Shin akwai wata matsalar ne a tattare da yarinyar?"
Haj Hameedah ta girgiza kai. Cikin sanyin jiki ta dubi farfesa Adams da shi dinma ita yake bi da kallon karin bayani.
Ta sauke nannauyar ajiyar zuciya. Kafin cikin sanyin murya tace,
"Gaskia akwai matsaloli Ummimi . Domin na farko ma dai yarinyar da yake ikirarin yana so zai aura. Bata masan yanayi ba. Babu wata soyayyah dake tsakanin su. Ihu yake a ..... A .."
"Ihu a bayan hari" ummimi ta karasa mata.
"Yauwa!ihu yake a bayan hari. Ya sameni da maganar nace masa kada ya kara taso da ita. Domin abune mai wahalar yiwuwa. Bazan bari ya tauye wa yarinya hakki ba. Dubada suna kasa da mu. Tanada damar kulawa ga wanda take so. Kuma yarinyar nan a matsayin wa ta dauke shi. Auren su ba zai yiwu ba ne Ummimi. Idan aka tilasta an tauye mata hakki. Dan ba zata rasa manema da ke son auren ta ba. Wanda suke son ta take son su. Kuma Zayn yarinyar da ya ke so Ahlam ta dauke ta a matsayin yar uwa ta jini. Ta kaunace ta. Ga shi yarinyar nan awaje na akasan ta. Ummimi me kike ganin zai je ya dawo? Kowa gani zai yi ni na shirya hakan. Ni na saka ya auro ta. A dangi yawo za'ayi tayi da ni gani za'ai da hannu na aciki.... Ko da ya same ni da maganar nace masa karya so ma nema na da zancen. Ya je ya nemi wata daban ya auro. Ummimi yarinyar nan ba kowa bace. Fyace diyar Hadiza dake tayani aiyuka. Yarinyar ta dai da muka bawa Ahlam take zaune da su tana tayata aiyuka. Waheedah.... "
Tun da ta fara magana daman Ummimi ta kawo Waheedah ce. Don haka ta sauke zuciya kawai . Farfesa Adams yace ,
"Ummimi ya kike ganin za'ai kenan? Ina tunanin kamar yadda Hameedah ta fada. Maganar nan a bar ta kawai ko? Yaje ya nemi wata daban. "
Ummimin ta dan ni sa kafin tace,
"Idan da alkhairi acikin auren su, Allah ubangiji ya tabbatar da kasancewar hakan. Domin alkhairin Allah ake bukata a komai. Musanman lamarin daya shafi dangartakar aure. Idan ka nemi ka hana idan da rabo sai kuga wanda yayi hani ya rasa ran sa. Kuma Ahlam da ta riki rayuwar auren na su da hannu biyu ta mutunta martabar aure me daraja da dukkanin haka bata taso ba. Zasu zauna kalau. Amman tayi wasarairai. Ta saka wasa da shirme a rayuwar auren.. Yanzu gashi nan a abubuwan da suka biyo baya. Saboda haka.. Ba zamuyi kasa a gwiwa ba. Zamu cigaba da addu'oi na fatan zabin alkhairin Allah ga lamarin. Sannan zamu nemi manyan ita wannan yarinya Waheedah mu tuntube su. Idan batada wani a kàsa da take muradin aure. Za kuma tayi biyayyah ta auri Zayn duk babu matsala. Domin budurwa daman anfi kaunar a zaba mata mijin aure. Ya yin da bazawara kuma ke da ikon kawo wanda take so. Ahlam ita tayi washarere. Ita kuma wannan yarinya Waheedah ta iya yiwuwa kyawawan halayen ta da kokarin aikace aikacen da take musu ne hakan ya sa Zayn nuna kauna agare ta. Ba akan auren su farau ba ko kuwa?"
"Me fa? Ummimi ?"
"Mata dake ajiye duk wasu hakkokin auren su a gefe. Ina nufin kadan kenan daga cikin, Sakacin wasu matan akan bai wa yan aiki ragamar komai na rayuwar aurensu.... Matar gidah ta ajiye duk wasu hakkokin da ke kanta ta dorawa masu aiki ragamar komai. Su ke yiwa masu gidah komai na aikace aikacen yau da kullum. Kowacce zuciya na kaunar me kyautata mata. Don haka Zayn bai yi laifi ba don ya nuna Waheedah a matsayin wadda yake kaunar samu amatsayin matar sa. Hakan zai zamo aya ko iznah ga Ahlam da ma ire iren ta. Mu dai namu addua ce. Sannan ina son manya su shiga zancen nan. Don a san a matsayar da ake."
"Insha Allahu.... Ummimi hakan za'ai." Farfesa Adams ya fada. Cikin girmamawa ga mahaifiyar ta su.
"Karki ji komai Hameedah. Ki cire waswasi aran ki. Idan Allah yayi wannan aure sai anyi shi to fa babu tsimi babu dabara. Ki ma toshe kunnuwan ki da dukkanin surutan da zasu je su da wo. Idan da akwai isashshen da ya isa hanawa sai ya zo mu ga ni. Ni da kai na zan tara kowa na sanar da su yadda ake ci idan har magana ta tabbata. Kinji ko?"
"Toh. Ummimi insha Allah hakan za'ayi "
"Yauwa! To Allah yayi muku albarka baki daya, Amin "
"Amin Ummimi "
"Amin."
Daga nan suka cigaba da tattaunawa akan maganar.
Ko da Zayn ya fita. Kai tsaye ya wuce unguwar shurah ta su Waheedah. Ya samu kansa da faka mota. Ya kwantar da kan sa akan sitiyari. Ya yinda idanuwan sa ke lumshe wa su bude..
Ya samu zuciyar sa da nutsuwar kasancewar hakan. Ji yake tamkar waheedan sa na kusa da shi. Ya yi murmushi kafin ya janyo wayar sa.
Ya shiga kan contact din ta ta WhatsApp suka cigaba da hirar su amatsayin Dawood. Lokaci zuwa lokaci yakan daga idanuwan sa ya sauke akan kofar gidan su Waheedan.
Sun sha hirar su ta WhatsApp yana mai gaya mata kalaman zuciyar sa. Kafin ya kunna motar sa yabar unguwar. Ya wuce majalisar su anan sukayi sallar magriba da ishai kafin ya musu sallama ya koma gidan sa..
Bayan ya karasa kallon news ya yi alwala ya kwanta. Ba dadewa bacci ya dauke shi mai tattare da mafarkai barkatai akan Waheedahn sa.
====
A ranar da Waheedah zata koma gidan su Zayn . Mahaifiyar su Basira ta hai hu. Ta haifo ya mace.
Don haka Waheedah bata koma gidan ba. Sai ma kaya da taje ta dakko ta kara wasu kwanakin. Ran Zayn bai so hakan ba amman dai ya kyale kawai don kada ta harbo jirgin sa.
Waheedah bata koma gidan ba har sai bayan da akayi suna. Yarinya taci sunan mahaifiyar mahaifiyar su Basira (kakar ta) da za'a dinga kiran ta da suna Ilham.
__
Shirye-shiryen bikin Zainab da zahara'u aka shiga yi agidan na malam na lado.
An yanko atamfar ankon kawaye suna ta saya. Waheedah ma Umma Hadiza ta saya mata. Itama ta saya don kada ace bakin ciki suke.
A kuma satin ne Ummimi ta samu Umma Hadiza da maganar Zayn akan Waheedah. Umma Hadizan ta yaba kwarai da kyawawan halayen Zayn din. Sai dai itama tamkar yadda Haj Hameedah ta fada haka ta fada. Kan yarinyar nan Waheedah ta dauki Ahlam da Zayn a matsayin iyaye tunda sune marikan ta. Uwa uba kuma Ahlam din ta zama tamkar babbar yaya awajen ta. Tasan Waheedah ba zata amince ba. Duk kuwa da Waheedah bata da tsayayyen manemin data tsayar a wanda zata aura. Tasan ba zata amince da auren Zayn din ba.
Amman dai idan Allah yayi auren meyiwuwa ne batada ja akai. Ta kuma san manemin auren Waheedahn yanada halayen kwarai da dukkanin kowacce mace zata amince da kokon barar auren sa
Ummimi ta sake zurfafa zancen. Har ya kasance Umma Hadiza ta ce mata zata nemi yayar ta da ke amatsayin uwa agareta. Dukkanin abunda ta yanke idan yayi to sai anemi mahaifin Waheedah a tattauna da shi.
Ummimi ta roki Umma Hadiza da kada ta fadawa Waheedah Zayn ne ke neman auren ta. Ayi komai cikin sirri.
Hakan kuwa akayi . Umma Hadiza ta samu gwaggo haule da maganar. Tashin farko gwaggo haule ta nuna amincewar ta. Don gidah ne da suka san mutunci da darajar dan adam.
Ba tare da bata lokaci ba. Ba kuma da sanin Zayn ba. Su farfesa Adams suka samu mahaifin Waheedah wato malam na lado.
Ya shiga gida ya sanar da Marka. Kan wasu sunzo neman auren Waheedah. Ta amince bugun farko ba tare da bin diddigin su waye ke neman auren ba. Ita dai burinta su rabu da 'kaya.
A kuma lokacin su Alhaji Nouh da Nouruh suka bada shawarar su bada kudin aure kawai. Nan da nan akayi komai aka gama.
Daurin auren zai kasance tare da na su Zainab da zahara'u. Daman saura yan kwanaki.
Gefe daya cikin dabara gwaggo haule ta shiga gyare Waheedah da magunguna na sanyi . Hadi da temakon kayan gyaran fata dana kariya daga sharrin sihiri da ma aljanu. Waheedan nata mamakin gyararrakin da ake sata yi. Ta kuma dau ruwan tofin da take sha a matsayin tofi na adduoin sihiri da kambun baka ..
××××
Ranar wata jumu'ah bayan anyi sallar jumu'ah an idar. Dubban mutane suka sheda daurin auren Bashari da Zainab. Sai Na'Ateeku da zahara'u. Daga karshe kuma Waheedah da angon ta Zayn Adams Nasser. Bisaga sadaki mafi daraja... Auren Waheedah ya kasance cikin sirrin da ba kowane ya sani ba. Ciki har da waheedan kan ta.
Waheedah na bandaki tayi wanka dakyar. Wani zazzafan zazzabi ne ya rufe ta. Ta haura kan katifa ta kwanta daman agidan gwaggo haule ne. Nan da nan tafara rawar sanyi. Idanuwan ta suka shiga kawo ambaliyar hawaye. Gashi yau partyn su Zainab. Bataso tayi latti. So take ta shirya ta tafi gidan su daga can zasu wuce.....
#ZAINUL-WAHEEDAH!!! A FATED LOVE💕
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:59_
_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._
____
*Cikin* matotowar rawan darin da take yi ne Gwaggo Haule ta shiga dakin ita da Umman su.
"Ah'aha... Waheedah? Meya same ki?" Gwaggo haule ta tambaye ta.
So take ta amsa. Amman bakin ta ya gaza, Sai sassarke hakoran ta ta ke yi. Sakamakon gabobin ta da suka dauki rawa baki daya.
"SubhanAllahi... Hadiza taimaka mun dan Allah." Cewar gwaggo haule.
Gwaggo haule ta karasa kusa da Waheedah. Ta tallafota jikin ta ta rungumeta.
"Samu abu Hadiza da ruwa a rage mata dumin jikin. Za kiga panadol akan gefen tv a parlor ki dakko .."
Umma Hadiza ta mike da sauri. Itama jikin na ta sai rawa ya ke. Kasancewar cutar da zata kwantar da Waheedah ba karama ba ce.
Ta ya zasu sanar da ita auren da ke kanta yanzu...? Umma Hadiza ta sauke zuciya kawai
Ta dakko maganin ta kai dakin da Waheedah da gwaggo su ke. Ta koma ta debo ruwa da dankwali. Gwaggo haule da kanta ta shiga tsama dankwalin cikin ruwan ta matse sai ta dora akan Waheedah. Ta shiga matsa mata jiki da haka. Har zazzabin ya dan ragu.
Sannan ta ballo mata maganin da ruwa ta bata ta sha. Ta ke bacci ya dauke Waheedah.
Ganin ta samu bacci. Hakan ya sa suka koma tsakar gidah sukayi zaman curko-curko.
Cikin haka sai ga Najan Isubu ta shiga gidan. Bayan ta kuma fannah da Basira ne kawayen Waheedah.
"Kin dawo Naja'atu?"
"Na dawo gwaggo... Ai badan mun tsaya kan Marka da saadatu ba ma da tuni mun dawo tun dazu."
"SubhanAllahi... Fatan dai komai kalau?"
Najan Isubu ta girgiza kai kawai. Ta zauna akan wata kujerar tsugunno ta sauke zuciya.
"Waheedah bata nan ne?"
"Tana ciki. Zazzabi ta ke .Amman ta samu bacci ma yanzu ya tsurga."
"Allah sarki Allah yabata lapia."
"Aamin.." suka hada baki.
"Wai Najaatu wani abunne ya faru a gidan su Markan? Kinsan gaba nayo ai. Tun ranar da naje dinnan tace wallahi babu lefen da za'a karba a gidan... Yau kinga zasu kawo. Daman ranar daurin aure akace. Niyyata yau na samu Waheedah da maganar batun daurin auren nan fa ba kowa bane fyace Zayn . Da shi aka daura "
"Wai daman Gwaggo ba ku sanar mata ba? Tabbas nasan kince mata wani yazo kan maganar aure an bashi. Amman batun wanene? Da ranar daurin auren shine ba'a sanar mata ba... To yanzu ya kuke ganin zata fuskanci lamarin? Anya bamu shiga hakkin yarinyar nan ba?"
Gwaggo haule ta sauke zuciya kawai. Ta leka ta windown dakin ta hango waheedan nata baccin ta. Ta na mai sauke numfashi ahankali.
"Babu wata tarzoma da zata taso insha Allahu a wannan aure. Yadda aka daura lapia. Ubangiji Allah yasa mutuwa ce zata raba su. Duk wata husuma da sharrace sharrace Allah ya kauda shi. Waheedah bata da matsala. Nasan ba zata taba bijirewa zabin da mukai mata ba.... Insha Allahu "
"Insha Allahu .. Aamin "
"Amin Gwaggo."
"Amin..."
Dukkanin su suka shiga amsa addu'oin Gwaggo. Kafin Najan Isubu tace,
"Ni da Ramman Ukashatu da Hindu ungozoma ne muka karbi haihuwar Deluwa. Don na fito daga gida na kenan zan wuto nan din. Sai ga Ramma da sauri. Shine muka nufi can din baki daya. Allah ya temaka Deluwa ta haifo jarirai mata har biyu, To dai tunda aka shedawa Marka abunda aka samu take kumbure kumbure. Kadaran kadahan. Don na tabbata da ba biki ake ba sai ta saisaye mu da zagi da cin mutunci."
"SubhanAllahi.... Albarkar karuwar haihuwar ce bata so ko kuwa?"
"Hmm ina kai ki Gwaggo."
"Ina sauraron ki "
"Yauwa.... Tayi ta cika tana batsewa. Kinsan Allah kin karbar jariran tayi. Tun dai da ta leka ta gano su da idanun ta. Kum baki gansu ba. Yadda kikasan Markan ce tayi kaki ta tofar gwaggo. Kamar su daya. Har bajajjen hancin nan na Marka da bakar fuska.."
"Wani abun Markan tayi?" Gwaggo Hadiza ta tambayi Najan Isubu.
"Wallahi bata leka dakin Deluwa ta mata barka da arziki ba. Gashi daya jaririyar kwata kwata idanuwan ta a rufe su ke bata bude ba. Numfashin ta wani iri yake fita. Dayar ma bata cika lapiya ba . Amman wallahi ko kadan Marka bata ce kanzil ba. "
"SubhanAllahi.. wannan bakar zuciya ta Marka dai Allah ya yaye mata. Tun kuruciya har tsufa ace baka sauya halayen ka ba? To ubangiji Allah ya yaye ma ta yasa ta gane gaskya."
"Amin. Amin Gwaggo..."
"Amin"
"Amin... "
Suka shiga amsa addu'oin da Gwaggon ta yi. Najan Isubu ta sake karkacewa kafin ta cigaba da cewa,
"Ana cikin haka..... Sai ga shigowar Bashari da wasu abokan sa su biyu. Sallau dan gidan batayya da Harisu dan Malam me gero. Kawai kai tsaye ya dora takarda akan kafar Sa'adatu. Alokacin ta bararraje tana raba abinci. Marka ta shiga tsokanar sa tana ya tsaya su dau hotuna. Zainabu shigowar ta kenan itama gidan ta caba ado cikin wani samfacecen leshi ruwan bula. Iya ganinta sai ya sauya fuska. Ya dage kai zai fita mutane baki daya muka tsaya saroro muna bin su da kallon me ke shirin faruwa. Kai gwaggo kaji tsoron rayuwa. Wato wasu tun a gidan duniya zasu girbi mugayen nufin da suka shuka Gwaggo."
"Ina sauraron ki Najaatu.... Zancen ki haka yake. Wasu a duniya Allah ke fara nuna ishara a kansu. Wasu kuma Allah zai musu talala komai nasu yayita tafiya dai dai. Ya yin da rayuwar su babu wani mishkila aciki. Aganin su hakan sunyi nasara basa duba da mugayen abubuwan da suke yi meyakwan su nemi gafara. To wadannan shine zakiji ana wata shari'ar sai a lahira. Suji dadi a duniya su sha wahala a lahira. Allah ya nesanta mu daga aikata mugayen alkaba'i ya kusanta mu da rahamar sa. Allahumma aamin."
"Aamin..." Suka amsa ta baki daya.
"To na karkare miki zance dai. Takarda da Bashari ya ajiye kowa ya kasa dauka. Basira ce ta dauka ta karanto ko?"
Basira da ke gefe ta daga kai. Kafin ta ce,
"Eh... Fanna ce ta dakko akan cinyar inna Sa'adatu. Saboda Basharin yace a karanta kafin ya fita.