Showing 93001 words to 96000 words out of 123508 words

Chapter 32 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

544

lefunan mutane su sace su.


*******

Kallon kansa ya tsaya yi a gaban mirror. Yana sanye cikin dakakkiyar wagambari da ta sha aikin hannu. Da hular data dace da aikin kayan . Sai hula data sha kari ta zanna bukar. Agogon sa ya hau da kayan jikin sa. Hakama takalman da ke sanye cikin kafafun sa.

Ya yi matukar kyau. Ya dakko turaruka ya shiga feshe dukkanin lungu da sako na jikin sa. Ya goga chappete a bakin sa. Ya gyara zaman zobunan azurfar da ke yatsan sa.

Sannan ya dau wayar sa ya zura a aljihun gaban rigar sa ya fuce daga dakin nasa cikin takun kasaita irin ta angwaye. Dake tattare da farin ciki da annushuwa.

Kamshi ne kawai ke tashi daga jikin sa. Ga wani kyawu daya kara haskaka shi. Yana sauka daga mattakalar bene ya na mai bare ledar chewing gum din hannun sa. Me mint flavour ya jefe a baka yana taunawa ahankali.

Ahlam na zaune a doguwar kujera da wayarta a hannu. Ta dube shi ta watsar. Tun da Ummimi ta zo da kanta gidan ta sanar mata rana i ta yau daurin auren Zayn.. Amman bata gaya mata wadda zai aura ba. Ta ja mata kunne sosai tare da mata nasiha akan zamantakewar aure da hakkokin sa.....

Da harara tabi shi. Yayi murmushin gefen fuska kawai. Ya zauna akan hannun kujera yana kare mata kallo. Ya kasa gane muhimmancin da ta bawa zama da kayan bacci. Ta kwanta ta tashi da su. Da rana ma tayi wanka ta mayar da su.

Ya dan lekar da fuskar sa ga wayar da ke hannun ta hausa novel take karantawa na: zafafa biyar

"Meye zafafa biyar kuma?"

"Ina ruwan ka? Littattafan hausa ne mana.."

"Amma...I'm very sure. Inde littattafan hausa ne suna muku koyi ta yadda zaku dinga kula da tarairayar mazajen ku. Kula da tsaftar jikin ku.. da sauran su. Su kan su ba zasu baku gurbatacciyar shawara ta fatali da ayyukan gidajen auren ku ba ."

Bata bashi amsa ba ta juyar da kanta gefe tana turo baki gaba. Gyara zaman sa yayi ya shiga yi mata nasiha mai ratsa jiki tare da bata hakuri akan dukkanin wasu lefukan da yayi mata a bisa rashin sani. Da kuma wanda yayi da sanin, Ya kuma karkare da batun,

"Game da wacce na auro kuma.... Bata da masaniyar neman auren ta ma ballanta na batun daurin auren mu da ita. Kuma ko da aka sanar mata tanacan tace dole awarware auren nan... Badan komai ba saboda tamkar cin amana ne awajen ki. Duk kuwa da bata kauna ta. Tana mai jin kunyar kasancewar abokiyar zaman ki .. Ahlam!! Wannan ba kowa bace fyace..."

Ahlam ta daga kai da sauri ta dube shi. Gabanta na tsananta bugawa.

Zayn ya kada kai alamun tabbatarwa da zancen sa kafin ya ce,

"Waheedah itace wadda na aura ba tare da masaniyar neman auren ta da nayi ba. Ballanta na kuma daurin auren mu da aka daura yau .."

Kasa magana Ahlam tayi. Idanuwan ta suka shiga kiftawa. Hawaye sirara suka shiga reto a kyakkyawar fuskar ta. Ta mike da sauri tayi sama tana mai fashewa da wani sabon kuka..

Ya dan jima yana sake sake a zuciyar sa. Ya bita saman yana ta roko ta bude dakin taki. Ya sauka fice daga gidan. Kai tsaye ya nufi gidan Gwaggo haule.

*WAHEEDAH....*

Suna tsakar gidah baki dayan su. Ciki harda Waheedah data rufe kafarta saboda soro. Tana mai karanta sakon da ya shigo wayar ta ta lambar Dawood,

"Nikah Mubarak my wife, You are a missing ingredient of my life that has everything..D has now been completed. For me it's not just about showering you respect, you are and always will be my respect, My queen and I honour and respect your family at all times .May Allah give me ability, power and strength to make you happy, for the rest of your life... I love soo much... With every fiber of my being darling...💕" Tana karasa karanta sakon,

Zayn yayi sallama. Sai da aka bashi iso ya shiga. Ya gayshe da su cikin girmamawa. Waheedah ta gayshe shi fuskar ta a kumbure.

Ya karaci zaman sa. Suna hira da gwaggo da yake jefa kalamai daya biyu. Ya musu sallama yana sosa keya ya fuce. Gwaggo tasa Waheedah ta raka shi.

Har waje ta raka shi. Yana gaba tana biye masa a baya. Sun danyi tazarar har zuwa wajen motar sa. Dake ba mutane awajen layin shiru. Hakan ya sanya Zayn rarumo Waheedah tanata ture shi amman yaki sakinta. Ya rungume ta tsam a faffadan kirjin sa. Yana sinsinar wuyan ta dake tashin kamshin da kofofin hancin sa basa mantawa.

"Please Waheedah .. Kyale ni naji dumin jikin ki . Ko kinsan wata rana da muka fara haduwa da ke? A gate din gidan mu. Wanda muka bigi juna har glasses dinki suka cire?" Yana mai goga karan hancin sa akan nata karan hancin ya cigaba da cewa,

"Tun ranar na tsinci kai na da kaunar ki. Kamshin turaren ki. Idanun ki, kyawun ki, nutsuwar ki, kyakkyawar halayyar ki da ma sauran dimbin ladubban ki suka kara ingiza zuciyata da kaunar ki .. Waheedah ke ce FARHATAL QALB na..I remember every second, Your magnificent smell, Your incredible eyes, I remember everything... You are my best present and future Waheedah.. Tun kallon farko ..I always liked you at first glance... Ki sake bamu dama Waheedah. Karki bari a raba auren mu..If only you could give us one more chance"

Kiciniyar kwace kanta take son yi. Zayn yayi nasarar saka bakin sa ya sumbaci gefen wuyan ta. Ta rufe idanunta da sauri jikin ta na ta rawa. Ya busa mata iskar bakin sa a kunnen ta ahankali cikin wata iriyar murya ya shiga rada mata,

"If only you could give us one more chance.... " Yana karasa fada ya samu kansa da saka hannu ya tallabo fuskar ta,

Ya sanya labban sa akan nata. Cikin wani irin yanayi ya shiga sumbatar Waheedah. A hankali kuma cikin nutsuwa,

"What did you hear.....uhm... Me kika ji, ?"

Ta sauke numfashi tana kauda fuska. Ashe dan iska ne? Saboda ya kyaleta tace,

"Naji...."

"No... in english please ..."

"I hear voices of children ...." Ta amsa shi hade da juyawa kadan ta kalli yaran da ke gara taya a tsallaken kwata suna musu ...

"And then....?"

"Kukan dabbobi da tururin numfashin.....

"In English .... Kinji?" Ya karasa fada yana sinsinar bayan kunnenta..

"Crying of animals...And the hint of your breath...."

Rarumota yayi ya rungumeta tsam a jikin sa.

"Ina kaunar ki Waheedah.. I’m in love with you..I love you more than anyone, Fiye da kowa da komai... Meyasa kike son a raba auren mu? Meyasa kike tsane ni haka?..."

"Ka bari ... Ya Ahlam..." Ta shiga zame jikin ta. Tunowa da Ahlam da tayi,

"U're worried about Ahlam... Yeah I knw..But what about us?what about my love for you? Kinsan irin kaunar da na ke miki Waheedah? Bansan so ba sai akan ki. Bansan tacacciyar kauna ba sai da na fara dakon soyayyar ki Waheedah.. " Yana magana yana sake matseta a jikin sa.

Ganin zai iya nasara akanta. Hakan ya sa da sauri ta yage jikin ta daga nasa ta shige gidah. Sun bar tsakar gidan suna dakin gwaggo haule. Don haka fitsari tayi kawai da alwala ta kwanta tana tunano Zayn da ajiye kunyar da yayi a gefe yau. Ta dora hannunta daya akan lebenta tana zagaye su. A haka bacci ya kwashe ta...

×××××

Wasa wasa sai da Waheedah ta kara kwana biyar agidan su kafin Haj Hameedah ta turo a dauketa da kayanta.

Daki wadatacce aka bata asaman gidan na Haj Hameedah kafin komai ya sake sararawa Waheedah ta koma gidan Zayn.

Duk sanda zai zo wasan buya suke. Bata bari su hadu. Ranar daya gaji ya kirata a waya taki dagawa.

Ya tura mata sako da,

"I'm in the car..."

Ta karanta tayi shiru. Ya sake tura mata da,

"Come down! I won't accept no.or I will alert the whole neighborhood .."

Tana karasa karantawa ta kashe wayar baki daya. Zayn ya shiga gidan kan sa tsaye. Yayi hamdala Maa bata nan tana sashen Abiey din su. Da sauri ya haye saman dakin da Waheedah take ya tura kofar ya shiga ya murza mata mukulli. Nufar ta yayi gadan gadan ta gudu bayan kofa ta tokare tana rau rau da idanu, Yayi murmushin gefen fuska kafin yace,

"Waheedah you made a
big impression on me .."

"Ya a Zayn..., Dan Allah ka bari.."

Girgiza kai yayi. Tana baya baya yana kara matsawa kusa da ita. Ta rakube a karshen kofar tamkar zata shige cikinta baki daya. Tana mai rufe bakinta da tafukan hannayenta. Cikin rawar baki ta shiga cewa,

"Sis Ahlam......"

"Shhhhhh!!! I love you more than anyone….. Enta FARHATAL -QALB.…. yes Waheedah ke ce FARIN CIKIN ZUCIYA tahhh..#ItWasAlwaysYouW💕..." Yana karasa fada ya saka hannun sa yana sharce mata hawayen da ke tsiyaya a fuskar ta...

Kafin ya samu kansa da tallabo bakin nata. Ya shiga bata deep and passionate sumba mai ratsa mugudanar jini da bargo..

Yayi nasarar kashe mata lakar jikin ta. Daga shi har ita sun shagala sai bugun kofa suka ji.

"Waheedah kinyi bacci ne?" Suka jiyo muryar Maa.

Waheedah ta tattake iya karfin ta ta ja hannun Zayn ta tura shi abandaki. Ta rufe bandakin da mukulli gabanta na tsananta bugawa. Kunya duk ta dubibiyeta tamkar Maa din na ganin su.

Ta kalli kanta a mudubi gaba daya ko ina a hautsine. Ta juya ta dankarawa kofar bandakin harara sai kace Zayn din yana gani.

Tayi sauri ta gyara ko'ina sannan ta bude kofar. Maa ta shigo tayi hanyar bandakin tana,

"Ashe shower ta lalace sai Nadra ke fada. Haka kiketa wanka da sanyin nan Waheedah? Bari na dau hotan wajen na turawa me gyara sai ya sayo abunda babu..."

Tamkar mota haka Waheedah taja kafafuwa a guje sai gata agaban Maa.

"Ki..ki..ki barshi Maa."

Maa din ta kalleta tayi murmushi,

"Haba Waheedah? Dan Allah ki cire wannan kunyar ai an riga da an zama daya.."

Waheedah ta shiga girgiza kai. Tamkar zata fashe da kuka. Yayin da Zayn dake ciki yanata murmushi da adduar Allah yasa Maa ta bude ta ganshi ta bashi matar sa. 🤣

"Akwai ... Shan..." Ta kasa karasawa tanata rawar murya.

Maa ta yi murmushi kafin cikin kulawa tace,

"Okay ko kin wanke undies ne bakyaso agani? Well kina da gaskia. Ba damuwa zuwa da safe sai ya zo kawai ya gyara. Idan zaki wankan to dan Allah ki fada a kawo miki ruwan zafi ko ki shiga bandakin Nadra . Kinji?"

"Insha Allah Maa. Nagode kwarai."

"Yauwa... Sai da safe."

Tana fita Waheedah ta sauke zuciya. Hannunta akan kirjinta. Yau da Maa ta yi ido biyu da Zayn batasan wacce iriyar kalar kunya ce zata shiga tsakanin su da Maa din ba....


#DESTINED LOVE... #ZAYNUL-WAHEEDAH..
#ITWASALWAYSYOU:W💕

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_

_NANA HAFSATU_
_(MX)_

_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_

_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:61_

___

*Gefen* gado taje ta zauna tana faman sauke ajiyar zuciya, tana sane taki sanar dashi cewar Maa ta tafi yayi ta zama a bathroom É—in ita ba ruwanta. Kafin ta gama zancen zucin da takeyi kawai taga ya fito sukai ido hudu, ta janye nata gefe tana cizon farcen yatsanta.

A hankali ya karasa inda take zaune ya tsaye yana kare mata kallo. Shikam me zai yiwa wannan baiwar Allahn ta yadda cewar shi din yana sonta da gaske ba wai wasa ba? Me zai mata ya tabbatar mata da cewa be aureta dan ya cusgunawa Ahlam ba?

Muryarta yaji tana cewa.

"Yah Zayn zaka danneni fa.." Zayn ya kalleta, gani yai sauran kiris ta fada kan gadon. Maimakon ya matsa sai ya dora kafarsa daya a gefen gadon, Waheedah ta zaro ido, d'an rankwafawa yai ya sata a tsakiyarsa kamar mai san yi mata rada.

"Please Ya Zayn bana so."

Ga mamakinta sai taga ya sake rankwafawa kawai sai ta kwanta akan gadon tare da kauda fuska cikin ranta tana fadin kaci kanka.

"Oh Masha Allah dan naga kin fiso muyi maganar a kwance ko?"

Bata kulashi ba saboda bata san hirar tasu tayi tsayo, so kawai take yabar mata dakin amma bashi da niyar yin hakan. Ji kawai tayi ya kwanta a bayanta tare da rikota ta hanyar sanya hannu ya riko shafaffen cikinta. Waheedah tayi saurin zaro ido kirjinta yana wani irin bugawa, gani kawai take Ahlam tana kallan irin cin amanar da suke yi mata.

Idanuwanta a lumshe sakamakon wani irin yanayi da ta tsinci kanta, murya na sarkewa take faÉ—in.

"Yah Zayn k..."

Tattausan tafin hannunsa taji a saman lebenta, ji tayi yana kokarin juyo da ita wajansa, da sauri ta tirje tana girgiza kai.

"Yah Zayn bazan iya ba, dan Allah kadena tabani bazan iya wannan cin.."

Zayn ya sake katse mata hanzari ta yadda yake goga mata dogon hancinsa da tattausan lips dinsa akan fatar wuyanta, gabaki daya numfashinsa dake fitowa ta hanci da lallausan gashin daya kaawata wajan bakinsa zuwa habarsa sai sake kashe mata jiki suke, banda tsuke kafafuwa babu abinda takeyi. Zayn ya dan rintsa ido yana girgiza kai, husky voice dinsa ne ya daki cikin kunnanta inda yake cewa.

"FARIN CIKIN ZUCIYA tah (My Farhatul qalb) kina tunanin na aureki ne dan wata manufa tawa akanki ko akan Ahlam?"

Waheeda tayi shiru ta kasa cewa komai, Zayn ya dan saki murmushi tare da janyota, gabaki daya sai ta juya suka fara kallan juna tayi saurin rufe ido. Bazata iya kura masa ido sosai ba saboda wasu sirrika dake cikinsu, ya hadiye wani mugun saliva wanda tsagwaran san ya mallaki lips din ta dake ta faman motsawa tamkar wata mai shan sweet. Yaci gaba da cewa.

"Ki cire tsoro da duk wata shakka da kike yiwa Ahlam kizo kiyi biyayyar aure, na dade ina jiranki, zuciyata ta jima a cikin so da kaunarki, ki tausaya min ki shigo cikin rayuwata ko zan samu jin dadi da kwanciyar hankali." Ya karasa maganar yana shigar da fuskarsa gefen wuyanta. Wasu hawaye ne suka dinga bin kyakkyawar fuskar Waheedah, ta shiga girgiza kai tana zamewa daga jikinsa, ganin ya hanata yasa ta fashewa da kuka, Zayn ya rintsa ido kukan ta yana jinsa har cikin ransa, ba zai iya jurewa ba dan haka yai saurin matsawa daga jikinta, muryarsa tana sarkewa yace.

"Ki gaya min abinda kike so nayi wanda zai sa ki kasance a cikin rayuwata ta har abada, sanar dani please but banda saki bana san jin kalmar nan daga cikin bakinki."

Yadda Waheedah taji yayi maganar ne yasa kirjinta bugawa, tunani ta farayi, yanzu me zatayi wanda zai sa ya kyaleta? Share hawayen tai tana fadin.

"Ina so kaje wajan Aunty Ahlam ka tambayeta, idan har ta amince dani a matsayin abokiyar zamanta ina mai tabbatar maka zanje gidanka a matsayin matarka. Idan kuma bata amince ba ina so dan Allah ka rabu dani kaje ka rungumi matarka, dama a duniya ba komai mutum yake samu ba."

Zayn yai mata wani mugun kallo wato sai da ta tabbatar da cewa Ahlam ba zata taba yadda da ita a matsayin kishiya shine tace haka. Bazai mata dole ba hakan yasa shi tashi zaune yana jan dogon hancinsa wanda tsarin yanayin halittarsa ya karawa fuskarsa matukar kyau.

Tsaye ya mike yana so ya kalleta sai dai zuciyarsa na san ta koyi yin hakuri da kasancewa da ita har zuwa lokacin da zatayi hankali ta gane cewa shi din mijinta ne mai tsananin kaunar ta.

"Shikenan zanje, ina san kiyi addu'a ki roki Allah abinda kike so, ni kuma zan tayaki da amin koda kuwa rabuwarmu itace ta ratso tsakanin mu."

Hanyar fita yayi, har ya kama hannun kofar ya murda sai yaji kamar ya koma, ya juya tare da kallanta, tana kwance idanunta a rufe, girgiza kai yayi kawai ya fice zuciyarsa na tsananta harbawa. Yayi sa'a parlorn babu kowa har ya fice daga gidan. Mota ya shiga tare da dora kansa jikin glass door yana jin wani irin yanayi, harga Allah yana matukar san ganin Waheedah a tare da shi, sai dai yaga alamar samunta lokaci guda zai bashi matukar wahala dan yana hango tsoran Ahlam a can cikin idanuwan Waheedan. Dakyar ya iya samun damar kunna motar ya wuce gidansa cike da tunaninta.

Fitowa yayi daga motar hannunsa rike da briefcase dinshi ya nufi cikin gidan kansa tsaye.

Zaune a kasan carpet ya tarar da Ahlam tana waya, ya karasa ya zauna kan daya daga cikin kujerun parlorn, kallanta yai yaga fuskarta tayi wani iri alamar taci kuka har ta godewa Allah. Inda yake zaune bata kallaba ballantana yasa ran zata amsa masa sallamar da yayi. Yanata zama a wajan amman Ahlam bata da niyar katse wayar da takeyi, ran Zayn ya fara sosuwa cikin bacin rai yake kallanta yana fadin.

"Bansan wace irin mata bace ke, kina ganin na shigo har na samu guri na zauna amma baki san ki ajiye wayar ba, a haka kike tunanin zan yi rayuwa dake ke kadai? Bakisan yadda zaki kula da mijinki ba bare ki bashi girmansa na matsayin miji?"

Cikin rashin damuwa Ahlam ta katse wayar tana yi masa wani irin kallan raini take faÉ—in.

"Oh wai kai har yanzu kana tunanin zan yi maka wani abun? Zayn ka manta cewa amanata kaci ta hanyar auro wacce ta gama sanin sirrina? Kun gama cin amanata kake tunanin zan baka muhimmanci?" Ta saki wani murmushin takaici tare da gyada kai tana cizon lebenta na kasa.

"Wallahi indai sai a waje na zaka samu farin ciki zaka dade Yah Zayn, kaje can ita munafukar ta yi maka duk wani abu da kakeso, amman indai nice nagama."

Tana gama maganar ta sake bude wayarta, wannan karan chatting ta ci gaba da yi tana dariya. Wani irin bacin rai ya bayyana a fuskarsa ya mike tsaye yana girgiza kai irin na takaicin nan yace.

"Dama can mekike yi min Ahlam? Tunda mukai aure mekikai min da zan iya nunawa nace naji dadi?"

Bata kulashi ba ya cije lips zuciyarsa na zafi, cikin son ya bata mata rai shima yace.

"Ko yanzu daga

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login