Showing 54001 words to 57000 words out of 123508 words

Chapter 19 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

530

Kina rowar buda baki. " Marka ta fada tana yamutsa fuska

"Tuba nake uwar kowa. Marka tsohuwa mai ran karfe .. kowa ya ja da ke juji ne...."

"Najan Isubu manyan kasa. "

"Wane ni ga ku? Tuba nake . Fatan na same ki lapia?"

Marka ta shiga busa hanci da daga kai. Jin yadda Najan Isubun ke fadada mata kai da washin da take mata. Ta dan yi yatsina. Kafin ta gaftari ragowar goron hannun ta tace,

"Lapia Lau... Ya Isubu kalau yake idan kun waya ko?"

"Alhamdulillah Marka .. Yama gaysar da ku."

Naja ta karasa fada hadi da yaye yamfadin kofar dakin da Waheedah ke ciki. Ta zura kanta tana duba komai.

Shigewa ciki tayi. Ta tsaya tana bin dakin lungu da sako. Gabas da yamma.

"Dawo ta nan ki dauke wadannan. Bar daukar kaya masu nauyi kina budurwa kinji ko?"

"Tohn aunty ..." Ta karasa fada hade da sunkuyawa ta debi kayan da ke bayan kofa.

Najan Isubu taja mayafi tayi madaurin kugu da shi. Ta shiga jan drawer a hankali har ta futar da ita daga dakin

Sannan Waheedah ta tayata suka karasa fito da sauran kayayyakin. Shigar Najib kenan gidan. Najan Isubun ta sanya shi ya curo yamfadin kofar dakin da aseberin da ke jikin window din dakin.

"Kayan sawar ku ne anan din ko...?"

"Eh ..."

"To kwashe su ki zuba acikin wadancan Ghana must go din."

"Toh.."

"Yauwa bara na leka na kira dan gwangwan din... "

"Tom aunty..."

"Marka zan wa dan gwangwan iso..."

Bata tanka ta ba. Tayi kwafa dai kawai. Ganin hakan ya sanya Najan Isubu fita ta yiwa dan gwangwan da zai sayi kayan iso.

Ya shigo da sallama. Ya gayshe dasu. Kana ya shiga kallon kayan yana taba wasu daga ciki don jin ingancin su. Bayan ya gama gani duka.

Najan tace su fita. A wajen sukayi maganar kudin kayan. Baki daya ya saye su dubu biyar da dari hudu da hamsin.

Sauran yan kayayyakin nasu Waheedah ta mayar dakin su Yaya Kamal.

Kudin kuma Najan ta riqe su a hannunta bayan ta basu ajiya sun ki. Kan zata kaiwa Umma Hadizan da kanta.

××××

Haka rayuwar ta cigaba da garawa. Kwanakin Waheedah 3 agidan Najan Isubu. Da asubah take komawa wajen su Yaya Kamal .

Kudin kayan da aka sayar. Umma Hadizan ta baiwa Najan Isubun dubu daya dakyar ta karba

Sauran kudin kuma ta barwa su waheedan a hannun su. Saboda karin kumallo da sauran abubuwan dazasu bukaci kudi na yau da kullum.

Sati daya kuwa da tashin Waheedah. Wata mata ta tare adakin. Bazawara ce dake sana'ar abinci da zobo.


××××××

Najan isubu da kanta bisa jagorancin gwaggo haule suka samu Marka da maganar karbar Waheedah . Marka tace batasan zance ba.

Ta gwammace waheedan tayita karakainan neman matsugunin kwana amman bata amince tafiyar ta ba baki daya. Bayan ba wani abun take mata ba. Hassada ce zalla take yi. Don kada waheedan ta je inda zata huta taci cima mai dadi...

Hakan ya sanya su Umma Hadiza suka dakata da zancen. Har yazamto ma Umma Hadizan ta dakatar da zuwan Waheedah gidan na su the Adams family saboda gudun kar Moha yayi kuka.

Yayinda rana ke zama yammaci. Yammaci ta zama dare. Dare ya waye. Lalle Allah buwayi ne gagara misali.

Ranar wata sanyayyar juma'a da asubah. Bayan Najib ya tafi masallaci. Waheedah Kuma na tsakure a daki wajen Zainab suna kwance.

Haka kawai waheedan tun kafin safiya ta nemi bacci a idanunta ta rasa. Yayinda gabanta keta faduwa.

Tana idar da salla tadauki kwano don siyo musu yar tsala da kunu.

Najib ya dawo daga sallah. Ganin Yayan nasu har yanzu a kwance yake. Ga lokaci nata tafiya. Duk kuwa da bashida lapia shi ya sama bai tashe shi sunje masallaci ba saboda jikin nasa ba kwari gwara yayi agidah.

Hakan ya sa har ya kwanta akan katifar sa ya mike da sauri. Ya shiga tashin dan uwan nasa.

"Yaya.... An yi asubah fa. Ban tashe ka ba saboda naga baka jin dadi ne...." Ya shiga tashin sa shiru.

Yasake tattaba kafafun sa yana kiran dan uwan na sa.

"Yaya.... Ka tashi kayi sallah...."Nan ma shiru ba amsa.

Hakan yayi dai dai da shigar Waheedah dakin. Ta cire hijabin ta ta a jiye a kyauran kofa.

"Bacci yake har yanzu?"

"Eh...." Najib ya amsata a sanyaye.

Hannu tasa ta dago nasa da sauri hannun ya koma baya luuuu ya fadi.

"Yaya Kamal.... Yaya... Yayan mu." Ta shiga tashin sa sosai tana kallon Najib.

"Daman haka yakan yi ..?"

"Be taba wannan nauyin baccin ba..."

Ta saka kunnenta a kofar fuskar sa wai ko zata ji numfashin sa. Nan ma shiru.

Da sauki jikinta na rawa ta fita . Malam nalado ne a tsaye yana gyara rigar jikin sa.

"Baba."

"Naam Waheedah..."

"Baba zo kaga Yaya be tashi ba."

Da sauri ya bi bayanta suka shiga dakin. Ya tattaba Kamal din. Ya mirginar da fuskar sa. Ya taba jijiyar wuyan sa da ta hannayen sa. Doguwar ajiyar zuciya ya sauke kansa a kasa.

"Baba menene?"

Bai ce komai ba. Ya janyo zanin gadon dake jikin katifar ya rufe Kamal din baki dayan sa.

Ya mike ya fuce zuwa kofar dakin Marka. Waheedah ta bishi. Yayinda gabanta ke tsananta bugawa da sauri da sauri.

"Ya akai me sunan malam?"

"Marka.... Allah ya yiwa..."

"Menene . Yayiwa me? Iyye?" Ta fada yayinda zaninta ke neman kuncewa.

"Kamalu ne Marka.... Allah ya masa rasuwa...."

._INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_


_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:42_

_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._

___

*Tana* jiyo sanda mahaifin su ke sanar da rasuwar Yayan na su. Jijiyoyin jikinta suka saki. Ta nemi kwari ta rasa.

Ta zube zaman dabaro. Hannuwanta dafe da bakinta. Wasu hawaye masu dumi suka shiga kwaranya daga fuskarta.

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun..... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.... Shikenan? Shikenan Yaya ka tafi ka bar mu? Yaya shikenan babu kai? Wayyo Allah na.... Ummanmu. Yayan mu ya rasu. Ya rasu Umma... Na shiga uku..."

Inna Sa'adatu ta leka fuskarta cikin dakin don ganewa idanunta

"Toh.... Allah ya jikan rai... Allahu Akbar." Ta furta tana girgiza kai.

Marka ta koma ta zauna tana daga kai.

"Allah sa karshen wahalar kenan ... Yarannan yadda ake jelar asibiti da su. Gwara ai da Allah ya karbi ran sa. Uwar ta huta itama...." Marka ta fada gatsal ba tare data auna rashin hankalin zancen na ta ba.

Sosai Najib ke kuka... Yanata girgiza Yayan nasu.

"Yaya... Ka tashi Yaya... Baka rasu ba Yaya... Dan Allah ka tashi."

Kuka yake sosai wiwiwi. Jijiyoyin goshin sa sun fito radau. Yanata birgima yana kuka.

Yayin da Waheedah ma ke kukan a kofar dakin Marka .

"Bar birgima yar nan...." Cewar Deluwa matar da ke haya.

Malam Nalado ya fice yanata sauri ya gayawa liman. Liman din ya sanar da rasuwar da lokacin da za'ayi masa sallah a kai shi madakata.

Najan Isubu na jiyowa ta isa gidan tanata salati da sallallami. Tayi kuka sosai tana girgiza kanta.

"Marka ... Yanzu kin kyauta da abunda kikayi? Gashi nan kin raba da da mahaifiyar sa. Bai rasu agabanta. Sati wajen nawa? Basa ganin juna. Sai dai taga gawar ta sa. ? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Kamalu Allah ya jikan ka da rahama. Annabi yasan da zuwan ka. Allah ya shayar da kai ruwan alkausara kamalu... Bakada wani hali na daban fyace na kirki da girmama na gaba da kai... Allah ya dubi biyayyar ka ya saukaka maka tambayar kabari kamalu .. Allah ya kyautata makonci ya jikan dukkanin wadanda suka rigamu da gidan gaskiya. Muma idan tamu tazo Allah yasa mu cika da Imani .. wannan jinya da ka sha kamalu Allah yasa kankarar zunubai ce . ...Aamin"

Sai data kai karashe. Marka ta ja Wani dogon tsaki. Ta tashi daga zaunen da take a daki ta fito har gaban Najan Isubu. Tamkar zata tsone mata idanu. Haka ta daga yatsa tana mai mata nuni. Cikin dakushewar murya da tsantsar jin haushi ta shiga ce wa,

"Kinga Naja... Kisan ire iren maganganun da zasu dinga fitowa daga bakin ki. Da girman Allah ko Ruwaida kinga dai itace kusan tsarata ko? To ko ita ki tambayeta tayi kadan a gayan magana .. Zaki ce na raba su da Hadiza waye waye .. Kina so ki nuna ni na kashe shi ne ko me? Bayan wannan cutar tasu ance tun suna 'kankana take kashe su. Bayan shi din da yayi dogon zango? ..... Yo wannan da rayuwar sa ai gwara da yake a ma .."

"Dan Allah marka kar ki karasa......"

"Yo ai kece naga kina neman doramun lefi bayan dama can nakasassu ne. Da samun su gwara r..."

"Ko wanne rayayye fa matacce ne watan watarana Marka . Lapia ko akasinta bashi ke sa Allah ya karbi rai ba. Rigar gado ce mutuwa. Wanda kowanne dan adam seya sakata ..Kinga Waheedah an sanarwa Umman ku ne?"

Waheedah dake tsiyayar da hawaye bata samu damar magana ba. Sai jujjuya kai da take kawai . Yayin da hawaye keta kwaranya a kyakkyawar fuskar ta .

Kawai tunano zaman shakuwar su take da Yayan nasu. Yayan su mai fara'a da mutunci. Sam bashida girman kai. Gashi da biyayya da kyautatawa.

Kenan duk shawarar da yake gaya mata da adduuoin da yake yi. Na tafiya ne kenan? Sallama ce yake yi ta haka? Ashe duniyar zai bari baki daya?

Ta sake fashewa da kuka sosai . Har tana shessheka... Najib ma na ta rera kukan sa mai ban tausayi ga duk wanda ya saurara.

Najan isubu ta fice daga gidan tanata sauri.

"Ina wuni aunty ..?" Cewar wani dan adaidata sahu da suke makota.

"Kwana dai ko... Ina kayi dan Allah..?"

"Gangaren durumi.."

"Yauwa muje ka saukeni dan Allah a gidan gwaggo haule ."

"Me kankara?"

"Eh.."

"Toh shigo.... Ance wai yaran nan kamalu ya rasu ko?"

"Ya wuce wai... Ya rasu da gaske. "

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Allah yasa karshen wahalar kenan... Gaskia gayen nan ya jima yana jinya." Ya karasa fada yana girgiza kai

"Aamin..."

Har kofar gidan ya sauketa. Ta janyo nera hamsin ta miqa masa.

"Ah ki basshi... Allah ya kara hakuri..."

"Aamin...."
Jikinta asanyaye ta shiga cikin gidan bakinta dauke da sallama..

"Wa'alaykm Salam...."

Suka amsa. Alokacin Umma Hadiza har ta zura hijabinta .zata tafi gidan aikin ta

"Ahh Najan Isubu... Maraba lale..." Cewar gwaggo haule dake zaune akan wata tabarma tana tsintar shinkafa.

"Naam gwaggo..."

"Ahh Najaatu...."

"Naam Hadiza.... Har zaki tafi?"

"Eh wai so na ke na kammala aikina da wuri. Inason zuwa wambai na tsinto rigunan sanyin su kamalu.."

Najaatu ta dan kwakwalo murmushi kawai ta nemi waje ta zauna .

"Wani wajen kika je ne?" Umma Hadiza ta sake tambayar ta.

"A'ah daga gidah na ke...." Tanata jujjuya yadda zata sanar da zancen mutuwar.

"Wani abun ya faru ne Naja?" Gwaggo haule ta tambayeta. Suka zuba mata idanu su duka suna jiran amsar da zata bayar

"Ai daga gidan su Waheedan nake..."

"Toh.... Rashin lapiar ce dai?"

"Kinji ko gwaggo? Daman wallahi baki daya kwanakin nan haka naketa wasu irin mafarkai.."

"Kwarai har kikace zaki sa a kirawo su kamalu ku gaysa ki ga jikin na su . To ya ake ciki najaatu..?"

Najan Isubu ta sauke nannauyar ajiyar zuciya ta kasa cewa komai. Kanta a kàsa. Yayin da idanunta suka kawo ruwa.

Umma Hadiza ta zauna a gefen gwaggo haule. Ta hada hannuwanta biyu .

"Waye ya rasu acikin yaran najaatu?"

Najan Isubu ta daga kai ta dubi Umma Hadiza da sauri. Gwaggo haule ma ta kalleta tana mamakin maganar da tayi.

"Rasuwa kuma?" Gwaggo haule ta tambaya.

"Eh gwaggo.... Tabbas cikin yaran ne wani ya rasu... Ko dukan su ne? Kadan daga iko da kudira ta ubangiji..."

"Hakane .... Innalillahi wa inna ilaihi rajiun.. Naja waye ya rasu?"

Najan Isubu ta daga kai ta kallesu. Hawaye daya na bin daya

"Kamalu ne gwaggo... Allah ya karbi ran kamalu.."

Umma Hadiza ta sauke zuciya. Ta ja salati

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun... Allah ka jikan kamalu .. Allah kayi masa rahama. Allah ka gafarta masa. Allah ka kyautata makwancin sa. Ka sadashi da annabin rahama... Allah ka bashi nasarar amsa tambayoyin kabari. Allah ka yalwata kabarin sa. Allah kasa aljannar firdwas ce makoma agare shi . Da dukkanin musulmai baki daya... Aamin" Umma Hadiza ta fada. Batayi hawaye ba. Amman idanunta sun kada sunyi cazir. Da alama kukan zuci take yi.

"Aamin Aamin Hadiza..."

"Kiyi hakuri Hadiza ..."

"Hakuri mun godewa Allah Naja'atu. kowa ai dan haka ne... Ko ba jima ko ba dade . Lokacin sa ne yayi..."

"Hakane.. Allah ya gafarta masa. "

"Aamin...."

"Na yafe maka kamalu .. Duk kuwa da babu abunda ka yi mun. A iya sani na da wanda ban sani ba .. Na yafe maka duniya da lahira Kamalu... Allah ya gafarta maka...."

Najan Isubu kawai zuba idanu tayi tana bin Umma hadiza da kallon namijin kokarin da tayi.

Gwaggo haule ta mike ta shiga daki ta dakko hijabi ta zura . Can sai ga mijinta ya shigo yanata sauri shima .

Suka gaysa da Najan Isubu . Ya shiga daki ya dakko hula ya fito..

"Malam kai ma ka ji ne?"

"Eh wallahi .. Jana'iza karfe 10. Allah ya jikan kamalu ya rahama masa. Ya dace da yardar Allah. Don yaran nan sam ba yada matsala. Baya fada da kowa. Ba shi da hayaniya ba rashin kunya. Ba bin yaran banza . Insha Allahu aljanna ce makoma agare shi.. Anata yabon sa"

"Aamin Yaa rabbi .... "

"Allah ya baki hakurin rashi Hadiza..."

"Aamin ..."

Ya fuce da sauri ya bar su. Kafin su ma su tattara komai su barshi. Su fita

"Ni Marka tace kar na soma takawa kofar gidan nan...."

"Mutuwa ce yanzu ai Hadiza. ."

"Ta zama dole ai ... Dole ki je Hadiza.."

Suka gangara suka samu adaidaita suka shiga. Ya kai su har kofar gidan. Mutane sun fara taruwa sosai.

Maza nata alwalar sallar Janaza. Suka shige cikin gidan.

Waheedah na ganin Umman su tatafi ta rungumeta tanata kuka. Umma Hadizan ta sake dakewa bata zubar da hawaye ba. Yayin da labbanta keta kwarara adduar samun ceton rahamar Allah ga kamalu.

"Shigo kuyi sallama Hadiza ... Waheedah kema.. Kai Najib zo."

Umma Hadiza ta shiga ciki. Fuskar Kamal ce kawai a bude. Yayin da dukkanin jikin sa ke a rufe da likkafa ni.

"Allah ya gafarta maka kamalu.. Allah ya yafe maka dukkanin zunuban ka.. Allah yasa aljanna ce makoma agare ka. Allah ya maka rahama. Allah ya maka rahama. Kyawawan halayen ka nagari Allah yasa su bika Kamalu.. " Tana karasa fada ta mike ta koma tsakar gidah kan tabarma ta zauna

Waheedah da Najib kuwa sai da akayi da gaske aka bambare su daga cikin gawar aka fita da ita. Aka sallaceta aka tafi da ita makabarta.

Yan taaziya sai tudadowa sukeyi anata yiwa Umma Hadiza taaziyyah. Masha Allahu ba wanda ke binsa bashi ba kuma wanda yake bi. Ya samu shedu da dama daga bakuna nagari

Yar tsalar da kunun dakyar gwaggo haule ta tasa Najib da Waheedah a gaba suka ci. Sauran akayi sadaka da su .

Nan da nan kuwa mutane keta kawo kayan abincin don samun lada.

Najan Isubu ta kira Indo ta sheda mata halin da ake ciki. Ya yin da indon ta sanarwa the Adams family.

Washegarin rasuwar kuwa Haj Hameedah da Nadra da indon suka zo gidan sukayi musu taaziyyah . Da sadakar buhun shinkafa da carton na taliya da jarkar mai da kuma dubu biyar.

Haka akai ta zaman makoki har na tsawon kwanaki. Kafin aka share makokin kowa ya koma inda ya fito.

Gwaggo haule ta tasa Waheedah agaba tatafi da ita. Najib kadai aka bari anan din.

Amman kullum abincin safe , Rana dana dare

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login