Showing 24001 words to 27000 words out of 123508 words

Chapter 9 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

521

zura ta fara sallah. Cikin nutsuwa da bin ka'idojin sallah.

Tana idarwa ta yi adduointa daga bisani ta mayar da komai yadda yake ta koma cikin parlorn.

"Hadiza kinci abincin dazun?"

"Eh Hajia. Bayan naci nema na kwanta."

"Ko dan gaba ki dena kina cin abinci ki kwanta. Ki dinga bari se abincin yayi digesting first. "

"Dajastan.?"

"Afuwan. Ina son nace ki bari abincin ya ., Wannan . Sorry. ..Ah"

"Tanason tace ki dinga bari abincin da kikaci ya tsurga. Kafin ki kwanta " cewar Nassem daya shiga alokacin.

"Oh yes. Tsurga."

Umma Hadiza tayi murmushi

"Kingane ko Hadiza? "

"Nagane Hajia. Allah ya saka da alkhairi."

"Aamin ya rabbi "

"Da akwai abunda zan kama kafin na tafi?"

"A'a babu. Ki tsaya kici abincin rana ko zaki tafi da shi kici a gidah ?"

"To Hajiya."

"Okay great. "

Dr. Hameedah da kanta ta nufi kitchen din. Masu dafa abincin gidan har sun dafa sun kawo. Wata food flask ta dakko me girma ta zuba mata abincin aciki .

"Daga yau ga food flask din abincin ki Hadiza. "

"Hajia du wannan?"

"Eh..."

"Nagode. Allah ya saka da alkhairi. Abincin yayi yawa Hajia. Kinga na dazu ma na rage zan tafi dashi. Da kin rage."

"Ki dena cewa haka Hadiza. Naga yaran naki ba maza bane. Sai mace daya dake zuwa makaranta ? Ko ta iya girki?"

"Eh su uku ne Hajia. Eh ta iya babu lefi."

"To banason musu Hadiza. Kije kuci da yaran dan Allah kinji?"

"Toh Hajia. Allah ya saka muku da alkhairi. Yasa a mizani"


"Amin Hadiza "

Dr. Hameedah ta fice daga kitchen din. Yayinda Umma Hadiza ta sharce hawayen farin ciki. Ta zura hijabinta. Hadi da harhada komai ta zura a hijabi.

"To Hajia zan tafi. Sai zuwa da safen ko?"

"Allah ya kai mu Hadiza. Ki gayda yaran."

"Zasuji insha Allah. "

Ta fuce daga cikin gidan tana mai kambama dattako irin na uwar dakin nata Haj Hameedah.

Har ta karasa gidah. Zuciyar ta bata dena yaba kyawawan halaye na Hajia hameedah ba. Tabbas an nuna mata karamci da tsantsar mutunci .

Ta shige gidan bakinta dauke da sallama. Zainab ta amsa tana kan kujera turmi agabanta tana dakan kuli.

"Umma sannu da zuwa " cewar Waheedah data fito daga cikin daki

"Yauwa Waheedah. "

"Waye ne ... Iyye?" Kande ta shiga kwarara murya fitowarta kenan daga bandaki. Zanin ya dage ana hango jemammun duwaiwukanta a waje. Bayan sarai tasan ummah Hadiza ce.

"Ni ce Marka."

"Ah ni fa in ce naga anyi wuff an shige. Ashe sarki da nadi ce. An dandalo arziki an boye a kurya."

"Kayya Marka kiyi hakuri. Ba haka bane."

Ta yamitsa fuska bayan ta daga hannu ta nana shi a shamilallun cinyoyinta da ba tsoka sai kashi

"Kaji tsoron mutum. Wato Hadiza tunda aka samo miki aikatannan kike wani daga kai kina hura hanci. To bari kiji hurerar bappajo (mahaifiyar Umma Hadiza ) itace tsarar cacar baki na ba ke ba. Dande ta mutu ne da girman Allah da yau har gidan bappajon senaje mun kwashi yan kallo da ita. Mtssss! Aikin kawai." Ta karasa fada hade da kwafa ta koma cikin bandakin

Jikin ummah Hadiza a sanyaye ta shige cikin dakin su. Waheedah nata rarrashinta. Duk yadda taso ta cije sai data kasa. Wasu zafafan hawaye suka shiga reto a fuskar ta. Domin dan aikin nan data samu ya tsolewa Marka idanu har bata iya boye hassadarta .

Dakyar da temakon Waheedah Umma Hadiza ta dena kukan . Ta kasafta abincin. Kuskus ne da jar miya dataji kaji da daffaffen kwai guda 3 . Ta ware musu nasu. Sannan ta dibawa Marka da na MalamNalado da na Inna Sa'adatu.

Ko da aka kaiwa Marka sam tace ba zata karba ba sai an canza mata da kashin hakarkari an saka mata cinya mai tsoka. A Kuma kara mata miyar.

Babu ma. Sai takan abicinta Umma Hadiza ta kalato ta karawa Markan Waheedah ta mayar mata ta karba. Tana danna loma tana aibata su

Inna Sa'adatu ma da Waheedah ta kai catai ba zata karba ba. Karamun dan tah hamisu yasa kukan seyaci. Sai data talle masa keya sau 3. Da karin rankwashi biyu a tsakar kansa. Sannan ta dungurar masa abincin a gaban sa hade da doriyar lailayo ashar ta dura masa

Su kuwa su Waheedah sunaci kunnuwan su na motsawa. Ga karin na safe na Zayn da aka barwa Umman na su dana kitchen da akace ta hade.

Su Najib sai yagar nama suke suna hadawa da abincin. Farin ciki marar misaltuwa ya bayyana a fuskokin su. Ciki harda Kamal da ke kwance a gefe shima yaci ba laifi.

Umma Hadizan nata basu labarin yadda ake mutinta ta agidan na THE ADAMS FAMILY!!!


❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°
[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β Β  πŸ’ž
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:19_

Γ—Γ—Γ—

Sannu ahankali, Kwanakin mu nata ja, Ya yinda awanni da mintuna suke shudewa. Kwanakin Umma Hadiza da fara aiki bakwai cif. Sati daya kenan

Hakan kuma yayi dai dai da kammalawar karashen aji na daya na babban sakandiren su Waheedah.

Lamarin sai godiyar ubangiji. Don zance na gaskiya Allah ya kara saukakawa Umma Hadiza da ahalinta. Ci da shan su acan acan. Don na safe kawai suke saya su ci. Na rana da wanda zasu ci da daddare Umma Hadizan na tahowa dashi daga gidan aikin na ta.


=========. ===========.



Tunda ta tashi da safe bayan ta gama zuba ruwan, Dauraye kwanuka tayi ta kife hade da kunna turaren wuta na tsinke.

Daki ta koma. Umman su na kwance . Idanunta sun kada sunyi jazir. Ya yinda jikinta ya dau zafi sosai.

Waheedan ta taba jikinta tana rausayar da kai. Cikin rawar murya tace,

"Umma .. Jikin ki zafi."

"Waheedah ya akai?. Bari na tashi ."

"Umma baki da lapia. Muje kyamis"

"Lapia ta lau Waheedah." Ta fada cikin dauriya.

Nan da nan hawaye suka shiga reto a kyakkyawar fuskar waheedan.

"Umma Allah ya baki lapia. Wayyo Allah na Umma."

Umma Hadiza taja siririn tsaki. Cikin kufulewa ta dubi Waheedah

"Allah zan make ki idan kika sake mun kuka. Shikenan ni ba dan adam bace kamar kowa da ba zanyi rashin lapia ba? Haba Waheedah."

"Ummah kiyi hakuri "

"Yauwa, Kin leqa dakin su Yayan na ku?"

"Eh ya koma bacci shi "

"Toh. Ki duba kasan samirar can akwai dari biyu ki sayo kosai ga ragowar biredin jiya nan sai ku hada ku ci. "

"Umma ke fa?"

"Je ki ki sayo ke dai"

"Tah "

Bata sake cewa komai ba, Ta miqe ta dauki kudin bayan ta zura hijabin ta.

Tana tafe tana tunanin halin da ta baro mahaifiyar tasu aciki. Ta sayo kosan ta dawo gidah.

"Umma gashi "

"Toh. Dibi naki ki kai musu"

"Umma ke fa?"

"Wai Waheedah menene haka iyye? Ina magana kina yi. Zaki tashi ko sai na bar miki wajen?"

"Kiyi hakuri Umma."
Da sauri ta dibi nata jikinta na bari. Ta gutsiri biredin ta mayar musu nasu

Ta tashi ta kai dakin su Najib. Bayan ta kwankwasa yar kofar kafin ta shiga.

"Umma na kai musu "

"Madalla " cewar Umma Hadiza. Ta miqe dakyar tana gyara zaman hijabin jikinta.

Tun dazu take son tatafi gidan aikinta . Amman data yunkura zata tashi sai jiri ya debeta.

Tanata daurewa dai. Har ta tsaya a tsaye. Waheedan nata kallonta cike da tausayawa.

Har ta kai kofa jikake luuuuuu! Wani jirin ya sake dibanta. Sai dabas tayi zaman dabaro a kofar dakin. Ya yinda kanta ya bugu da kofar dakin.

"Wayyo sannu Umma." Waheedah tayi kanta da sauri cike da tausayawa

"Umma sannu "

"Uhum."

"Ina ne yake maki ciwo Umma?"

"Ba ko'ina Waheedah."

"Umma gashi kin fadi "

Umma Hadiza bata sake ce mata komai ba. Ta miqe zata tashi nanma ta sake zubewa a kΓ sa

Da sauri waheedan ta nufi wajen Yayan su Kamal.

"Yaya" tace da shi

Ya tsaya yana sauraron me zata ce? Hannun sa dauke da biredi da kosai yana ci ,

"Umma ce Yaya."

"Meya faru da ita?"

"Batada lapia. Tanata faduwa da ta miqe "

Bai sake cewa komai ba. Bai kuma tsaya ta karasa fada ba. Ya miqe dukkuwa da shi dinma jikin sa babu kwari.

A bakin kofar dakin ya hangi Umman tasu tanata kokarin tashi. Har tayi amai awajen dan kadan sai nishi take

"Ummah.. SubhanAllah! Ashe baki da lapia?"

Ta dan juyar da kanta gefe kawai. So take ta miqe ta kasa

"Waheedah gyara wajen bara na sako riga mu tafi asibiti "

"Babu inda zanje Yayan su. Lapia ta lau "

"Ummah bakida lapia. Maybe zazzabin malaria dinnan ne da aketa yi wallahi. Kiyi hakuri "

Umma Hadiza ta sake miqewa cikin dauriya wai ita gidan aikinta zata je. Tana tafiya tana kama bango.

Marka dake kofar dakinta tana kallon su ta tabe baki kawai.

Cikin haka sai ga malam Nalado ya shiga gidan yana wakar garaya.

Yaja yai turus ganin su baki daya a tsakar gidan

"Menene haka. ? "

"Umma ce batada lapia Baba."

"Zo nan mai sunan malam. Ni na aika na iro ya kira mun kai." Cewar Marka cikin muryar isa da gadara.

"Umma batada lapia Baba."

"Meye garungamun sa da ita? Iyye? Ni fa Malam nagaji da saye sayen da kukeyi." Cewar Inna Sa'adatu data fito daga cikin dakinta. Daman tun dazun tana leken su ta wundo.

"Najib zo ka rakani mu kira Nase me kyamis." Cewar Kamal. Ya fice dan tsabar kidimewa jikin sa ko riga babu sai dogon wando. Yayinda Najib ke binsa a baya yanata sauri shima.

Jikin su baki daya yayi laasar ganin yadda mahaifiyar tasu ke tsiyaya amai.

Marka ta ja kwafa tana girgiza kafafu.

"Wannan amai dai a bincike sa , Ahto "

Malam Nalado yayi mata alamar da tayi shiru. Fuskar sa da alamun rashin jin dadin kalaman mahaifiyar tasa.

Umma hadiza na jin su. Ta kasa cewa komai. Baki daya amai ne ke kwarara tamkar zata amayar da kayan cikinta saboda azaba harda kakkari.

"Sannu Umma..."
Kada kai kawai take. Ta kasaa amsa waheedan

Cikin haka sai ga Najan Isubu ta zo ta da sauri. Mayafinta ko gama yafuwa baiyi ba.

Ta shiga gidan cikin kidimewa . Da sauri tayo kan Hadizan tana sallallami

"Sannu Hadiza. Yanzu su Kamal ke gayamun ...."

"Gayyar Munafukai... " cewar Marka.

"Debo kasa a waje Waheedah ki sauri "

Nan da nan Waheedah ta fita ta ebo kasar ta kawo. Najan ta zuba awajen da Hadiza ke aman. Tanata doka mata sannu.

"Ni fa nagaji da nuniyar isar da ake a gidan nan mai sunan Malam."

"Marka kiyi hakuri."

"Sai yaushe ne Hadiza zata bar gidan nan?"

Da sauri Najan ta juya tana kallon Marka. Hakama Umma Hadiza da Malam Na lado.

Waheedah baki daya sai kanta ya kulle sahoda meyasa Umman su zata bar gidan akan me? Bayan ga Inna Sa'adatu nan da yaranta

"Shekara nawa kenan kuna rokana da rufa rufar zancen nan? Nagaji. Nace nagaji. An kai ni makura. Ai yaranta sun girma ba jinjiraye bane. Ko yanzu aka aurar da Wahidin zata haihu. Don haka maganar a boye zance haka nan ya isa."

"Marka d..."

"Ya isheki Naja"

"Shekara nawa Hadiza zata dauka tana zaman yaranta... Bayan tun tuni auren su da mai sunan Malam ya kare? Iyye? Nace sai yaushe zata tashi ta bar mana gidah?........


❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯❀‍πŸ”₯

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„πŸ˜„

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°πŸ₯°[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β  Β Β  πŸ’ž
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:20_


======


"Haba Marka.... Menene haka fisabilillahi?"Najan Isubu ta fada cikin tsantsar takaicin Markan.

"Yo ai gaskia ne. Hakurina ya kare . Sai yaushe ne Hadiza zata bar gidan nan.?"

"Marka wai meyasa kike mantawa da igiyar aure baa hannun ki take ba? Menene riba shiga tsakanin su da kike yi? Idan ya shikata na menene tana zaman yayanta za ki takura sai ta tafi?"

"Saboda bana raayin zamanta anan din."

"To ki rabu da ita mana tunda ba akan ki take ba ."

"Kinga Najaatu tun muna sheda juna ki bar shiga hancina ki kudundune. Ina tsoron ranar da zan samu Isubu na sanar masa duk tsegemun da kike yi. ... "


"Yo Marka idan kin gaya masa ma ai ba wani muguntar nake ba. Na menene don ina aminta da surukar ki zaki dasamun qusar tsana? ... Me Hadiza ta miki? Tun ranar da aka kawo Hadiza a matsayin matar Malam kika tsaneta. Saboda me? "

"Saboda Tsayyabu uban Dan Ali....(mahaifin Najan) idan kin gano su wanene to saboda su na tsaneta. Akeken banza da wofi, Afiruwa. Ke ba tsaran maida magana ta bace. Kinyi kadan " Marka ta karasa fada tana nuni da yatsanta a fuskar Najan Isubu tamkar zata tsone mata idanu.

Waheedah ta kasa magana. Ta kasa zama Kuma . Tana tsaye tamkar sanda. Gaba daya duk wata laka ta jikinta ta mutu. Sam ta kasa gane inda maganar su ta dosa .

"Umman su da Babansu auren su ya rabu tun shekarun baya? Kai gaskia bata yadda ba. Ta shiga girgiza kai ita daya. Tana yin baya da baya ...saura kadan ta doka kanta a bango Najan Isubu ta riqota da sauri

"Menene haka Waheedah.?"

"Dan Allah dagaske ne? Dagaske ne auren Umma ya rabu? Dagaske ba aure?" Ta shiga tambayar Najan Isubu. Muryar ta cikin kidima da tsantsar tashin hankali.

"Kinyi wanka kinci abinci?" Tambayar da Najan ta mata kenan.

"Eh."

"Toh zura hijabin ki. Kije gidan aikin mahaifiyar ku. Ki sanar musu batada lapia ne. Duk aikin da takeyi su gaya miki kiyi. Kafin Allah ya tashi kafadunta kinji ko?"

"Ai t...."

"Bar musu Waheedah. Jeki kawai "

"Bansan inane bangaren ba Aunty "

"Inde kin shiga gidan ki tanbayi sashen da Umman ke aiki. Kingane? Shine na fari kafin dayan sashen."

"Tohm "

Bata sake cewa komai ba. Ta shiga dakin ta dakko hijabinta. Dan turaren ruwanta da Yayan su ya bata ta dakko ta dan diga a tafun hannunta ta shafe jikinta da shi. Ta zura hijabin gabanta na tsananta bugawa

Sai waiwayon Umman su dake durkushe tana numfarfashi take. Najan Isubu ta daga mata hannu ta nai mata alamar da ta tafi kawai.

Waheedah ta fice daga gidan . A kwanar layin gidan ta ci karo da su Kamal . Suna ganinta dukkan su su biyun suka shiga tambayar abun da ke damunta ? Ganin yadda hawaye daya na bin daya ke kwarara a idanunta.

Musanman da suka bar mahaifiyar tasu a gidah cikin matsanancin hali na rashin lapia.

"Menene wai Waheedah .. Umma ce? Wani abun ya sake faruwa da ita?"

Cikin sake fashewa da wani sabon kukan. Hadi da kifa kanta a jikin bango tace,

"Marka tace lalle Umma tabar gida."

"What nonsense....!!! Akan wane dalili?" Kamal ya tambaya cikin zafin rai.

"Wai ba aure a tsakanin su da ...."

"Bangane ba aure ba. Wannan wane irin rayuwa ce?. A yanzu ta sa ya saki Umman kenan? Kuma dan tsabar renin hankali a ...."

"Wai yaya sun dade da rabuwa ..."

"Innalillahi wa inna ilaihi rajiun!!! " Kamal ya shiga maimaitawa.

"Yaya kai ma baka sani ba da ma?"

"Bansan komai akai ba Waheedah... Yanzu ina Umman?"

"Tana can tana amai... Aunty Naja na temaka mata."

"Yanzu me kyamis din zai karaso .. Ina zaki?"

"Gidan aikin Umma ..."

"Yauwa gwara kije kar su jita shiru. Ki kuma share kukan nan haka. Nasan koma menene sharri ne na tuggun Marka. Duk ma menene itace kan gaba akan ganin ya wakana. Amman ba komai, Ai Allah ba azzalumin sarki bane. Zai ma Umma sakayya nan kusa da yardar Allah "

"Insha Allah.... Je ki "

Tafiya tayi tana waiwayon su. Kamal ya samu gefe ya tsugunna. Yayinda Najib ke a tsaye ya tokare bayansa da kafar sa daya. Kansa a sama yana tunani. Daman tun sanda Yayyun nasa suka fara magana. Zuciyar sa ke kai kawo akan zancen.

Cikin haka mai kyamis din ya zo ya same su. Daman ca yayi suyi gaba kafin ya tattara komai ya cinmasu

Najib ya yi masa iso cikin gidah. Dakyar Marka tayi shiru tana yada zance. Har mai kyamis din ya shiga yana yan gwaje gwajen sa da tanbayoyin sa akan Umma Hadiza da saboda aman data jera lokaci tanayi baki daya ta rame. Manyan idanunta sun kara firfitowa waje tubarkAllah.


Γ—Γ—Γ—NEW GRA SHURAHΓ—Γ—Γ—


Waheedah na tafe iska mai sanyayawa na kadata. Sanye take cikin doguwar riga ta atamfa baka mai zanen kujera ja

Sai hijabin dake jikinta shi ma ja ne daya amshi kwalliyar jikin atamfar ja
Kai dakaga yanayin yadda kayan suka zauna a jikinta zaka rantse gugar iron ce.

Nan kuwa kayan ma ninkin guga ta musu. Ko'ina na jikinta tsaf tsaf hatta takalmin da ke dogayen sahunta na samfarin dan madina.

Sanyayyen turaren jikinta mai dadi bame hawa kai ba nata gauraye ilahirin jikin ta.

Gabanta na tsananta bugawa. Haka ta shiga tafiya a unguwar da Umman tasu ke

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login