Showing 45001 words to 48000 words out of 123508 words
yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰*_RANO SCRUMPTIOUS MEAL_*
_(Where every flavour tells a story .....)_
*_By HAFSAT RANO_*
_(Mother/wife/writer)_
_08030811300_
_IG:Rano_scrumptious_meal_
_INA MA'ABOTA ABINCI? WATO *TRADITIONAL FOOD IN KANO*? GANGARIYAR ABINCI NA AL'ADUN HAUSA DA NAHIYAR KETARE? BA ANAN KADAI MUKA TSAYA BA. MUNA DA LEMUKA WATO *LOCAL DRINKS*. ZAKU IYA KAWO NA HIDIMOMIN LIYAAFA MUYI MUKU_
_MU NA YIN:_
*_FUNKASO_*
*_ALKUBUS_*
*_SINASIR_*
*_WAINA_*
*_ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI)_*
*_COW TAIL/COW LEG (DAB'URI)_*
*_CHICKEN AND FISH PEPPER SOUP_*
*_LOCAL DRINKS:_*
_HIBISCUS (ZOBO)_
_GINGER_
_AMAANI FRUITY SHAKE_
_MUN TANADAR MUKU MOUTHWATERING ABINCI KALA KALA WADANDA KE GINA JIKI DA KARA LAPIA. ABINCIN MU A TSAFTACE YAKE. KUMA MUNA YIN SU NE AKAN YADDA KOWANNE MUTUM ZAI IYA CI . AKWAI SPECIAL SOUPS NA MASU ULCER WADANDA BABU YAJI. AKWAI KUMA NA PEPPER DEM GANG GA MASU SON HOT AND SPICY...._
_KADA KU MANTA MUNA YIN NA TAKEAWAY/ORDER . MUNA KUMA YIN NA BIKI (WE CARTER TO SMALL/LARGE EVENT...._
_FUNKASO TO PAIR WITH COW TAIL:2K_ _WITHOUT COW TAIL:1K_
_ALKUBUS TO PAIR WITH ASSORTED MEAT (KAYAN CIKI) 2K. WITHOUT ASSORTED MEAT :1K_
_PLS NB: PAYMENT VALIDATES INTEREST..... DELIVERY WITHIN KANO:500 NAIRA_
________
*_FARHATAL-QALB_*
_(FARIN CIKIN ZUCIYA)_
_NA_
_NANA HAFSATU_
__PG: 36_
*Dakyar* Waheedah ke iya bude idanunta. Saboda tsananin yadda kanta ke sarawa. Kanta na mata madaukakin ciwo. Ya yinda gangar jikinta ta dauki zafi rau tamkar garwashin wuta.
A haka Kamal ya shiga dakin a daddafe don shima ba dadin yake ji ba. Ya nemi waje ya zauna akan wata kujera ta tsugunno.
"Sannu Waheedah..."
Bude idanun tayi da suke rufewa da kansu. Sunyi jawur da su. Sun kara furfutowa waje tubarkaAllah.
"Yaya Kamal.... Kai zan wa sannu. Ya jikin?"
"Da sauki ... Alhamdulillah. Ya jikin?"
"Da sauki..." Ta fada tana mai cije labbanta. Ta miqe ta zauna dakyar daga kwanciyar da ta ke.
"Yanzu Najib ze kawo miki ruwan gishiri ki sha. Saboda karfin jikin naki .. Kin sha panadol din ko?"
"Ban sha ba... Zan sha yanzu."
"Yana ina?"
"Gashi nan..." Ta nuna masa kan murfin samira. Ya dakko ya tashi ya tafi dakin su ya dawo da pure water guda 3.
"Ungo sha maganin... Wannan sai a hada miki ruwan gishirin ko . (ORS). ?"
"To Yaya ... Ka koma ka huta." Ta fada a wahalce
Ya danyi murmushi kawai. Yana dada kallonta sosai. Lalle Waheedah batata lapia sosai. Don bata kwanciya akwai kazar kazar. Bata taba cewa ta gaji akan aikace aikace.
"Mu idan muna kwance ba lapia Waheedah ba ki taba kosawa. Komai da komai yi mana kike yi ba gajiwa. Ubangiji Allah ya baki lapia ya sa kaffarane. "
"Aamin Yaya..."
"Kibar kukannan haka kinji?
"Tohm ...Yaya" Ta fada muryar ta na rawa.
Ba jimawa kuwa Najib ya shigo hannun sa dauke da leda baka. Ruwan gishirin ne sachet 3 aciki da kuma pure water rabin leda a dayan hannun sa.
"Dakko jug dincan ka hada mata. Ka ga ka fara dauraye shi tukun ka ji?"
"Tom Yaya."
Najib ya debi ruwa a kwalla ya wanke jug din ya hada mata ruwan gishirin ya miqa mata.
"Ka da ki sha ruwa sai kin gama shan sa.."
"Tohm Yaya...." Ta amsa shi.
Kasan zuciyar ta ta tuno yayan nasu da tuni yanzu yana aiki a asibiti ko wata ma'aikata data shafi harkar lapia ko kamfani. Domin chew (community health extension worker) ne shi kafin ciwo ya kankame shi baki daya..
Har ya mike yar wayar sa mai torch light ta shiga kara a aljihun sa, Ganin number Najan Isubu ce. Hakan ya sa ya dauka da sauri. Ya kuma koma ya zauna
"Wa'alaykm Salam... Ina wuni? Ah Alhamdulillah wallahi. Waheedah? Da sauki gata ta dan zauna... Eh shima yana nan. To bara na turo shi. Mungode, Allah ya saka da alkhairi. Amin. Okay tohm "
"Ka karasa hada mata...?"
"Eh. Gashi nan tana sha ma "
"Yauwa. Kaje gidan Najan Isubu ka karbo abinci. Umma ce ta bata ta kawo mana.."
"Allah sarki Umma. Muna ran ta. Uwa mai dadi. Allah ubangiji ya saka mata da mafificin alkhairi. "
"Aamin Yaa Rabbi ."
"Aamin."
"Bara na dan watsa ruwa "
"Tohm Yaya..."
Kamal ya fice zuwa bandaki. Yayin da Najib ya fice zuwa gidan Najan Isubu. Daki ya zama sai Waheedah ita kadai tana zaune. Kanta a sama.
Marka ta leka ta windown tana tabe baki. Kafin ta shiga ciki ba ko sallama ba re sannu
" A koke."
"Naam Marka ."
"Ungo debo mun ruwa acikin nan..." Ta miqa mata wani bokitin karfe kato.
Waheedah ta cika da madaukakin karshen mamakin halin ko in kula irin na Marka. Yanzu yanayin da take ciki na rashin lapia haka zata fita ta ebo ruwa bayan ga su Zainab can tana jiyo karakainan surutan su.
"Ko ba zaki ebo bane? Yo naga ma fuskar ki a murtuke kaman zararriyar zakan ya. Zaki hau kai na da bugu ne?..."
Waheedah ta girgiza kanta da a'a. Ta miqe dakyar. Jiri na neman kayar da ita. Amman a haka dai ta daure ta karbi bokitin tana dafa bango. Har ta fice daga dakin.
"Mene nan? Gayyar munafurci." Marka ta shiga bude kwanuka. Harda daga jug din ruwan gishirin da kalar sa tayi kaman lemo. Ta kwankwada zata sha banza ta dauka lemo ne. Da sauri ta fuce ta isa ga rariya ta amayar da shi tana tabe baki
Wani jiri ya kwashi Waheedah. Tayi sama dabas tayi zaman yan bori a kà sa. Nan da nan ta sa kuka. Ba wai kukan faduwar da tayi bane. A'ah kuka ne akan zallar kiyayyar da Marka ke nuna musu a cikin dukkanin jikokin ta... Sun zama saniyar ware acikin jikoki. Tsana ce ta ke musu mai yiwuwar fassarawa.
Kamal ya fito daga bandaki da sauri. Ya ajiye kwandon sosan wankan su a gefen daki. Ya nufi wajen Waheedah da ke sheme ta na kuka babu mai tanka mata. Ya dagata da sauri yana dudduba kafafunta da hannuwan ta.
"Ba inda kika ji rauni ko? Eh Waheedah."
"Babu Yaya..."
"Me zakiyi da bokitin nan.?"
"Ruwa.. Zan debowa Marka."
Ya dauki bokitin ya fice waje ya ebo ruwan ya kai dede kofar dakin Marka ya ajiye .
"Ba kai daya nake so ba .... Kai biyar nake bukata." Ta karasa fada tana yatsina.
"Yaya zan ebo."
"Keda baki da lapia. Barshi "
"Uhm se an ebo dai. " Marka ta sake fada hade da sakin guda.
"Wai ni Marka karfe nawa zamu tafi ne. Naga garin ya fara hadewa " cewar Inna Sa'adatu.
Marka ta sheke da dariya tana murna . Farin ciki ya wanzu a fuskar ta sosai tace,
"Mai jegon ma ta kira wayar mai sunan Malam. Tace ko mai dare da yardar Allah zasu zo nan. Anan zatayi wankan ina tunani "
'ahto Alhamdulillah.. Allah ya kawota."
"Aamin."
Kamal ya cigaba da zubawa Marka ruwa. Har sai da yayi kai biyar tukun sannan ya ajiye bokitin. Ya koma ya temakawa Waheedah ta koma daki. Sannan ya shige dakin su. Saboda jikin sa har ya fara ciwo.
Marka ta debi ruwa tayi bandaki tana yan wake wakenta.
Ba jimawa Najib ya shiga gidan dauke da babbar kular abinci ya kai daki wajen Waheedah.
"Gashi ..."
Waheedah ta daga kai ta kalle shi.
"Ku zuba ku ci..."
"Bari na kira yayan...."
Ya je dakin su ya kira Yayan na su. Dan har ya kwanta ma shi Kamal din yanata juye juye.
"Gani nan......" Ya fada a wahalce.
Ko da suka koma dakin suka bude kular, Waina ce da funkaso da sinasir da alalan cikin ganye. Sai miya dauke da nama fal a kulle a leda baka babba
"Samo wuri ka zuba shi ..."
"To Yaya."
Najib ya samu mazubi ya zuba komai. Suka debi nasu suka bar na waheedah. Sauran kuma zasu dumama suci.
Fitowar Marka daga bandaki kenan. Zahara'u yar autar Marka. Wadda ta haihu tace zata biyo gidah komai dare. Ce ta shigo gidan
Tana gaba yaran ta 3 wani na bin wani suka biyo ta a baya. Ita kuma da jaririn a bayanta. Yayinda mijin na ta Adamushe yana bayan su yana muzurai.
"Oyoyo oyoyo..." Yara sukayi kan zahara'u da yaranta anata murna.
Marka ta karbi jaririn tanata masa wasa.
Adamushe ya harde kafafu yaci magani. Fuskar sa ta cika tayi fam tankar zata fashe cikin kolokuwar bacin rai . Ya saita hannun sa setin kan fuskar Zahara'u tamkar zai waska mata mari yace,
"Na sake ta saki 3 ....... Babu komeee. Sannan wannan bakin jaririn da hanci hura hura da girman Allah ba 'da na bane. Ba jini na bane. Na karkare miki zance. Wadancan ukun ma ban amince na waje na bane. " Yana karasa fada ya yi hanyar zaure zai fuce ...
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE__INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
*_FARHATAL QALB_*
_(FARIN CIKIN ZUCIYA)_
_NA_
_NANA HAFSATU_
_37_
_____
*Marka* ta sha gaban sa da sauri. Zaninta har yana neman kuncewa. Saboda tsabar gigicewa da matotowar tashin hankali. Daurin dankwalin ta ya fado kasa. Duddugaggen farin gashin kanta ya bayyana. Gaba daya kan gaba da baya a gwaigwaye yake kamar konanniyar ciyawa.
"Adamushe... Bangane zancen da kake yi ba.?"
Tana magana ne hannun ta daya akan kullun zanin jikin ta yayinda dayan hannun kuma tana nuna zahara'u da shi.
Adamushe ya bushe da dariya har da kakatawa. Kafin yayi shiru ya sake murtuke fuskar sa ya na cin magani
"Marka da hausa fa nayi magana...."
"Haba 'dan nan... Fisabilillahi! Akan wane dalilin zaka saketa? Saki har 3? Ana murna ta haihu .. Ta haifo da sarfacecen namiji. Kuna zaman zaman ku. Ko dai asiri ne dan nan?"
Adamushe ya sake yamutsa fuska. Yana mai duba agogon da ke wutsiyar hannun sa. Ya dago ya dubi Marka ransa a bace,
"Tambaya kike yi? Bana ra'ayin cigaba da zama da ita ne. Sannan bana kaunar ta. Dama can fanko ce aka lullube aka aura mun ita .. Maza take kulawa awaje. Tana hulda da maza. Ke Marka, Baki dayan yaran nan ba nawa bane. Ba jinina bane."
Marka ta shiga hada hannuwa tana sallallami. Can ta dora hannayenta akanta tana surutai.
"Kai kira baban ku." Inna Sa'adatu ta tura a kira malam na lado
"Wallahi Adamushe yarinyar nan duk inda nutsattsiyar yarinya ta kai. Zahara'u ta kai. Ko a gidan nan tun tana karama ma wallahi batada abokin fada. Ko musu ba'ayi da ita. Batada kwaramniya bare hayaniya. Da girman Allah wadannan yaran naku ne. K..."
"Kinga kiyi shiru da Allah . Sumumu ka sau. Micijin kaikayi sari ka noke.... Wannan yarinyar muguwar munafuka ce. Annamimancin ta yayi yawa. Ga makirci yar iska. A sati sai ta fita sau 6. Bata iya zama agida. Kwanakin baya makota ne sukayi taron dangi suka mata dukan tsiya gatanan ki tambayeta. Bashi kuwa data ciyo yafu a kirga. Du ta debe kayan ta ta sayar a kasuwar tsaye. Zamana da ita ya kare. Na fada zan sake nanatawa..."
Malam Nalado ya shiga gidan bakinsa dauke da sallama. Hannun sa dauke da wuka da raken da yake sayarwa. Fuskar sa dauke da damuwa. Tun tafiyar Umma Hadiza ga kuma wani tashin hankalin.
"Ina wuni..?.." Adamushe ya gayshe da malam na lado. A tsaye. Kafafuwan sa a jikin bango ya tokare
"Lapia Alhamdulillah Adamu... Ya iyayen kalau?"
"Lapia..."
"An samu karuwa Kuma ... Allah ubangiji ya raya "
"Amin. Allah ya raya muku .."
Malam na lado yayi shiru bai ce komai ba. Adamushe ya hura iska bakinsa yana mai daga hannuwan sa sama,
"Na gama magana.. Yarinya dai da kuka liqamun gatanan na dawo muku da ita. Zamana da ita ya kare."
"Ka tsaya Adamu muyi magana ta hankali... Zauna muyi magana "
"A'a Malam. Babu wata magana anan gaba kuma. Na fada bari na sake nanatawa .. Na ce na saki zahara'u saki 3. Babu kome. Idan Allah ya bata miji taje tayi aure. Yara su uku gasu nan. Da jaririn ta a hannu. Duka ba nawa bane. Ba jini na bane wadannan yara. Ku tuhumi yar ku."
Yana karasa fada ya gyara takalman sa ya fice. Malam Nalado ya biye bayan sa yana kiran sa.
"Adamu . Adamushe... Adamushe..."
Sam ko dar beyi ba. Tamkar ba da shi dinne ake magana ba.
Mutane sai bin su suke da kallo, Adamushen yayi gaba. Yayin da Malam Nalado ke bin sa a baya yanata sauri yana doka masa kira.
Waheedah na zaune akan katifa tana jiyo kukan aunty zahara'u kanwar mahaifin su.
Tabbas duk da ba kauna a tsakanin su. Da kuma mutunci a tsakani. Saboda gaba daya Markan ta dora zahara'un akan aqidar tsanar su baki daya da Umman su.
Tana jiyo komai. Lamarin ya bata tausayi sosai. Haka kawai cikin yan mintina ta tashi daga matsayin matar aure zuwa bazawara. Ga yara har 3 mahaifin su yace ba yaran sa bane
Ta goge hawayen ta da kasan mayafinta dake daure akanta. Ahankali ta tattaka ta fita zuwa tsakar gidan
"Ina wuni aunty zahara'u .?"
Bata amsa ba. Sai ma harara data banka mata.
Sum sum ta miqe ta koma daki ta zauna. Ta janyo plate din abinci tana ci tana korawa da ruwan gishiri har ta cinye baki daya.
Marka ta zama kamar mahaukaciya. Ta dora hannu aka tana karade tsakar gidan. Taje karshen bango ta koma can wajen zaure. Ita kadai tanata maganganu tamkar sabuwar mahaukaciya.
Yayinda zahara'u ke ife ife tanata birgima tana yawo. Jaririn na hannun inna Sa'adatu ta zabga tagumi itama..
"Ashe abunda yaron nan zeyi kenan yace zai kawota gidah? Wannan yaro wannan yaro Allah ka kwashe masa albarka. Uwar sa fureratu har ta koma ga Allah Ina binta bashin jaka biyu. Wallahi ban yafe mata ba kuwa. Da nace na yafe amman na janye yafiyar dan malafar kan uban sa. " Marka ta ja kururuwa tana hawaye. Ta cigaba da cewa,
"Ya cuce mu..yaron nan ya gama da mu.."
"Wayyo Allah na ..... Marka .. wayyo Allah na" zahara'u ta kurma ihu tana jan kanta tamkar zata yage gashin kan ta.
Haka dai ranar baki daya gidan tamkar zaman makoki haka yayi. Tsit ba surutun kowa . Sai kukan jaririn . Ga makota da Marka ta shelantawa zahrau ta haihu sunata zuwa . Sam marka ta kasa sanar da su ai aure ya kare
Bakinta ya mutu murus. Ba maganar nan tata ta tsiya . Tayi tagumi taja kwafa. Haka tayita yi tana canza wajen zama.
Yadda taga rana haka taga dare. Batayi bacci ba. Tanata tunanin mafita. Zuciyar ta kuma na kitsa mata wasu abubuwan da dama.
××××××××
Gidah ya shiga ya sauya kaya zuwa wasu na yadi . Riga da wando. Bai saka hula ba, Sai gashin kansa daya taje kawai.
Ya feshe dukkanin jikin sa baki daya da turaruka. Kafin ya wuce sashen mahaifiyar su. Haj Hameedah.
Bakinsa dauke da sallama ya