Showing 21001 words to 24000 words out of 123508 words
4... _MASARAUTA_ 350
*(Mss xoxo)*
5... _KUFAN WUTA_ 350
*(Huguma)*
_Duk biyar 1500_
*_____________________________*
*_ZAFAFA BIYAR BATCH G (Da ake kanyi yanzun)_*
1... _FARHATAL QALB_
*(mss xoxo)*
2... _GURBIN IDO_
*(Huguma)*
3... _SANADIN LABARINA_
*(Hafsat Rano)*
4... _INAYAH_
*(Mamu gee)*
5... _BABU SO_
*(Bilyn Abdull)*
_KuΙinsu a yanzu 1k duk biyar_
*YADDA ZAKU BIYA NAKU KUDIN BOOKS DIN:*
_ACCOUNT NAME:_
*HAFSAT UMAR KABIR*
_BANK NAME:_ *ZENITH BANK*
_ACCOUNT NUMBER;_
*_2270637070_*
_SAI A TURA SHEDAR BIYA ZUWA GA:_
*_07040727902_*
_IDAN KUMA KATIN MTN ZAKU TURA KO VTU SAI A TURA TA:_
*_09134848107_*
*_Muna godiya da zaΙin zafafa biyar πππππ»_*
[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
Β Β Β Β Β Β Β Β Β Β Β π
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:16_
"A tsallaken unguwar nan ta gaba. Inda ake kira da Mahe janshan."
"Oh okay nagane inda take fada Maa. Wajen gidan su Ibro me gadi. Mahe junction."
"Oh okay nagane..... "
"Eh to.. Ta nan unguwar taku suke bi su karasa makarantar saboda yafu kusa. Tsallaka titi kawai zasuyi. Idan ta unguwar mu ne kuwa sai sunyi shatale tale."
"Eh gaskia kam tanan din zai fi. Allah basu sa'a."
"Aamin Yaa rabbi Hajia."
"Secondary kenan?"
"Eh sakandire. Tana aji na daya na babbar sakandire. Sauran aji biyu ta kammala."
"Allah sarki ... Ashe ma ba wata babba bace. "
"Eh .. Daga yayan su sai ita. Dan akwai tazarar shekaru ma tsakanin su. Sai kaninta Najib. Shekara daya da wata biyar ne a tsakanin su ita da shi"
"Allah sarki. Allah raya su duka "
"Aamin Yaa Rabbi ..."
"Maa! Abincin."
"Idan na gidah kake so yana kitchen. Na Zayn kuma ya .."
"Ah banason na akhi. Maa."
Nadra na daga dinning ta kufce da dariya harda kyakyatawa. Itama Umma Hadiza ta murmusa .
"Ai haka suke . Basuda aiki se tsokanar yayan su "
"Allah sarki... "
Cikin haka sai ga sakkowar dan autan ta Moha daga sama. Sanye cikin kayan bacci yanata murmurza idanu
"Maaa ."
"Habibi.... Zo, Ka tashi?"
"Uhm..."
Da gudu ya rungumeta. Ta dora shi akan cinyarta .
"Baka gaysheta ba."
"Ina wuni ?"
"Lapia kalau dan baby. Ka tashi daga baccin?"
"Uhm..."
"Me zaka ci? Oats da pancake ?"
"Nadra je ki masa reheating tun dazu daman na yi masa "
"Okay Maa."
"Kayi brush?"
"Eh .."
"Ka kuskure da mouthwash dinka?"
"Uhm uhm"
"Muje a kuskure. Monday dai insha Allah zakay resuming school. "
Riko hannun sa tayi suka hau saman tare. Daga kuskura bakin ta hada masa da wanka. Ta sauya masa kaya zuwa English wears. Riga da wando na jeans. Rigar spider man.
Sannan suka sakko tare. Ta zura bakar abaya ta yane kanta da mayafin abayar. Dayan hannunta kuma rike da jaka.
"Nadra ki hada masa komai. Ni zan tafi asibiti "
"Okay Maa "
"Hajia fita zaki yi?" Cewar Umma Hadiza. Ta miqe daga zaunen da take
"Eh nace miki inada tiyata dazu ko? Toh zan tafi yanzu ne. Lokacin ya kusa."
"Allah ya temaka, Amin"
"Aamin Yaa rabbi. Bazan wani jima ba zan dawo insha Allah "
"To Hajia Allah ya bada saa yasa ayi aikin cikin nasara "
"Allahumma Aamin Hadiza."
"Akwai abunda zaayi?"
"Kai babu gaskia. Sai dai.. ko..ko ko dauraye ledar abincin can kawai. Kuma dan Allah ki zauna kici abincin nan kafin a gama na rana kinji ko? Da wanda Zayn ya bari duk ki hade."
"Insha Allah Hajia. "
"Yauwa, Sai na dawo "
"Sai kin dawo. Allah ya tsare hanya Amin."
"Amin Yaa rabbi. "
Nan da nan ta isa ga wajen dinning area ta dauki ledar da aka jera abincin akai ta fita da ita wajen famfon wajen. Ta kada omo tayi masa sabi uku ta dauraye ta shanya. .
Ko data kammala. Abincin ta dakko na wajen Zayn dana kitchen din ta hade su waje daya tana kallo
Kayan dadi ne fal. Don wainar kwai ma fala fala har 3 masu nauyi. Nan da nan ta daddauki komi ta raba kashi 3. Taci kashi daya ta kora da ruwa.
Gyatsa tayi ahankali. Ta dora da hamdala tana kambama kyautatawa irin ta Hajia Hameeda da yaranta.
Yar tabarmar dake gefen sink ta janyo ta shimfida ta kishingida. Dake akwai ac a kitchen din. Sanyi mai dadi ya kama ciki da wajen sa. Nan da nan wani daddadan bacci ya shiga fuzgarta. Har dai yayi nasarar dauke ta. Ta shiga bacci tana sauke numfashi ahankali .
*****
Koda ya fita, Direct mota ya shiga ya tada ta ya tafi construction site dinsu.
Nan dinma bai wani mayar da hankali sosai ba. Illa dai ya dudduba files ya kuma ciccike abubuwan da suka kamata hade da saka hannu a wasu ayyukan.
Ya kwantar da kansa ajikin kujera . Yayin ya kallon sa ya koma saman pop. Hankalin sa da nutsuwar sa suka tafi izuwa yanayin daya samu kansa dazu da Waheedah.
Ya rasa mai yasa gaba daya tunanin yanayin su na dazu ya kasa fita daga kwakwalwar sa. Zuciar sa na masa zillo. Yayinda ransa ke hasaso masa wasu tunanin na daban.
Wayar sa nata agajin dauka. Baki daya hankalin sa baya kai sam bai ji ba. Sai da akayi knocking kofar ofishin sau 3 tukun sannan ya samu kansa da dawowar tunani.
"Yes...."
Sakataren sa ne ya shiga ofishin . Cikin girmamawa yace da shi,
"Ranka ya dade. Me gidah wai yana kira baka dauka, Yace ka kira shi idan ka karasa abunda kake."
"Okay tohm."
Sakataren na fita, Zayn ya dau wayar sa da sauri yana dubawa. Tabbas mahaifin na su ya kira sa har sau uku bai dauka ba.
Cikin sauri ya kira shi ya na mai gyara zaman airpod din kunnen sa.
"Assalam Abiey... Eh! Barka da rana. Afuwan Abiey. Okay Ummimi? Alright zan je yanzu naga abubuwan da suka dace a sayo. Tohm. A huta lapia." Yana gama wayar ya zurata a aljihun gaban rigar sa.
Tashi yayi daga kan kujerar ya fice daga cikin ofishin. Kai tsaye ya wuce wajen motar sa. Ya shige ciki ya nufi hanyar gidah kai tsaye.
Kan titin da zai shigar da kai kan hanyar zuwa gidan su ta baya . Wata mota ta mutu akan titin. Wadda ta haddasa go slow sosai. Gashi irin babbar gingimarinnan ce tafkekiya mai dauke da shanu aciki. Kuma motar zatayi U-turn sai ta tsaya chak ta lalace awajen.
Hakan yasa motocin da zasu shige . Da wanda zasu miqe da masu yin kwana duk sun tsaya chak. Ba dama ka juya ka canza hanya. Traffic din ya riga da yayi jamming .
Takaicin hakan yasa Zayn sakin siririn tsaki. Ya kara ac hade da saukar da kujerar sa tayi baya. Ya dan kwantar da kansa.
Wayar sa ya janyo yana duba mails. Chan ya koma kan Whatsapp . Group dinsu na dangin THE ADAMS FAMILY ya hada tarun sakonni fal.
Shiga yayi da niyar clearing ya ga hotuna rututu sunata turawa. Harda na Ahlam data turo bakin style din the bratz.
Nan danan ya danna button din clearing ba tare dayabi kan tattaunawar sa suke ba. Ya kashe datar ya ajiye wayar a agefe.
Cikin haka sai ga dandazon yan makarantar government senior secondary school shurah an ta so su. Sunata tudadowa.
Dake titin a tsaye yake chak saboda motar data lalace, Hakan ya sanya daliban samun damar wucewa hankulan su a kwance.
Waheedah da ke tafe tare da su Hindu Allah Allah take ta koma gidah. Saboda yadda kanta ke sara mata.
Tamkar ance ya dago. Ya samu kansa da sauke kwayar idanun sa akan.....
β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
πππππππ
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°_*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
Β Β Β Β Β Β Β Β Β Β Β π
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:17_
Β
Β Akan yan makarantar dake wucewa. Wasu na tafe suna ciye ciye. Wasu suna hirarrakin su yayinda wasu ke tafiya kawai.
Ya kifa kansa akan sitiyarin motar yayin da fuskar sa ke kallon waje. Tamkar almara yana sake bude idanun yaga tamkar yarinyar nan ta dazu. Suna tafe su uku. Biyu na hira, Ya yin da ita kuma kawai tafiya take. Amman daka gansu kasan atare suke.
Hannunta daya ta saka ta na gyara zaman gilashin idanunta da suka kara mata kyau. Ya sake bude idanu. Wata zuciyar na ingiza shi. Da shi kansa ya kasa gane menene dalilin?
Ya sake matse idanu ya bude. Wannan karon kuma ba ita yagani ba. Wasu ne daban yan makarantar su ma su uku suna tafe.
Girgiza kai yayi kawai. Kenan yarinyar nan gizo ta fara masa.? Har idanun sa ke nuna masa hotanta bayan ba ita din ba ce.
Ya sauke zucia . Hade da kunna rediyon motan. Labarai akeyi na kasa da yadda ruwa ya yi gyara awasu guraren.
Wayar sa ce ta shiga kara. Mahaifin sa ne ke kiran sa. Nan da nan ya dauka ya dauka.
"Hello Abiey. Na'am, Wallahi Abiey ban karasa ba. Wani hold off ne ya tsare ni. No! Mota ce ta lalace. Amma suna gyarawa. Alright insha Allah."
Dakyar aka iya gyara babbar motar data lalace. Aka samu aka mayar da ita gefe yayin da motoci suka shiga wucewa hanyar su .
Zayn yaja dogon tsaki yana waiwayar motar. Banda rashin bin kaidar tuki na garin kano. Taya babbar gingimari zata biyo hanyar kananun motoci?
Da takaicin hakan ya karasa gidah. Tun daga nesa masu gadi suka wangale masa gate ya shige,
Kai tsaye ya wuce sashen da su Ummimi ke zama idan sun zo. Hannun sa dauke da notepad da pen.
Ya shiga zagaye parlukan sashen da dakunan ciki. Harta bandakuna da duk wasu sockets na gidan sai daya dudduba komai. Ya rubuta abubuwan da suke bukatar a canza da wadanda babu a kawo.
Yana gama rubutawa ya shiga mota ya koma office. Kai tsaye ya wuce babban ofishin mahaifin su dake cikin kamfanin. Dankareren ofishin mai dauke da manyan rubutun: Professor Adams Nasser.
Sai daya fara knocking kafin ya bude kofar ya shiga bakinsa dauke da sallama.
Mahaifin nasa na zaune akan wata kujera mai cin mutane uku. Center table na gabansa yana cike wasu takardu.
Tsugunna wa yayi har kasa ya gayshe da mahaifin na su. Kafin ya miqa masa takardar da yayi rubuce rubuce ajiki.
Mahaifin nasa ya karba yana dubawa. Hade da gyara zaman gilashin da ke jikin fuskar sa.
Take Waheedah ta sake fado masa a zuciar sa. Ya runtse idanun sa da sauri. Kamshin turaren ta na dawainiya a kofofin hancin sa.
Mahaifin nasa ya daga kai ya dube shi.
"Ya akai Zayn?"
Ya bude idanu da saurin sa yana girgiza kai hade da soso kasan keyar sa.
"Bakomai Abiey...."
"To masha Allahu. Kana ji ko?"
"Eh Abiey."
"Zan turawa su Simon list dinnan. Sai su kai komai gidan. Yanzu ka biya wajen Lajawa kace gobe idan Allah ya kai mu yazo gida "
"Tohm Abiey. Insha Allahu "
"Yauwa Allahumma bareek."
"Aamin..."
"Zaka iya tafiya."
"Tou Abiey . A huta lapia "
Ya bude kofa ya fice zuwa inda suke buga snooker shi da abokan sa, A bakin wani pool site
Ko da yaje ma kasa tabuka komai yayi. Ya koma kan kujera ya zauna kawai .
Useey abokin sa dake gefen sa da wayar sa a hannu yace dashi,
"Maza ya ne?"
"Steady oga."
"Nagan ka yau pale. Akwai damuwa ne?"
"Bakomai fa. Kawai nagaji ne."
"Toh Allah yabamu saa. "
"Aamin."
Cikin haka sai ga wasu yan mata su biyu sunje wucewa, sunci ado cikin dogayen riguna fitted. Mayafan su shara shara kamar na tatar koko.
Lameen dake buga snooker da Awais ya riqe bakin sa. Karasawa wajen su Useey dake zaune shi da Zayn
"Wow woah, wawwww"
"Meye hakan sekace ambulance. Haba kaman wasu yan kwana kwana."
"Wasu masu zafi na hango mana. ."
"Suna Ina?"
"Gasu can zasu tsarar da me napep."
Useey ya miqe yana hango su. Tsayawa sukayi su na kallon su banda Awais da Zayn.
"Kallo daya bisa ka'ida dai akace." Cewar Zayn da ke zaune yana duba wayar sa. Don shi ko tashi bai yi ba.
Ussey da Lameen suka tsallaka har inda suke a tsaye sunata tsara su. Kowanen su ya karbo number wadda tayi masa. Useey ya zaro sabuwar dari biyar ya mikawa mai napep din. Yaja suna masu daga musu hannu
Suka tsallaka sunata dariya. Awais yace dasu,
"Ba dai kyau wallahi. Zaku batawa yaran mutane lokaci. Soo not fair. "
"Sai mu zauna mata su bace mana? Ga dama agaban mu?" Lameen ya amsa shi yana daria.
"Rabu dashi. Kasan meyasa yace haka lameen?"
"A'ah."
"Saboda already an hadashi da matar aure."
"Dan an hadani da wadda zan aura sai akace bani da damar kara wasu ukun? "
"Eh dukda hakan kasan dai baka isa ka auro wata nan kusa ba. Sai ka fara aurar sury.."
"Kyale su aboki na. Tunda sunada hankali sukayi fatali da sanin hakan." Cewar Zayn . Fuskar sa a hade.
Ussey ya tuntsire da dariya har yana riqe ciki,
"Banda kai da abun ka abokina. Kai da shi ai du kanwar ja ce. Kai har gwara gwara shi ma, A iya cewa yana da damar karo uku. Kai fa you can't marry any other girl da bata cikin naku family . Dole sai yarinya yar cikin dangin ku. Jinin ku, Kuma tsatson ku daya . Na yan uwan ku The Adams family.."
"Ku inda ake nuna muku a har kullum ba shi kuke hanga ba. "
"Rabu dasu maza, Su je suci gaba da yaudarar yaran mutane. At the very end su zo su auri wadanda basu taba tsammani ba."
"Kai de banza ne Awais. Ji wani mugun fata."
Dariya suka kyalkyale baki daya. Kafin su cigaba da yin snooker din su.
"Ni yunwa ma nake ji."
"To ina zamu je.?"
"Okay I'm out. Later." Zayn yace dasu. Domin shi gaba daya baya cin abokcin eateries ko roadside ko na ordering. Harta na masu aiki bayaci sai wanda Maa ta dafa masa da hannun ta ...
β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯β€βπ₯
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
πππππππ
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°π₯°[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
Β Β Β Β Β Β Β Β Β Β Β π
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:18_
Nadra ce ta shiga kitchen din. Hango Umma Hadiza tayi a kwance tanata baccinta hankali kwance, Tausayi ta bata. Ta rufo mata kofar ahankali don kada ta tashe ta.
Tana komawa parlor ba dadewa sai ga mahaifiyar su ta dawo, Dr. Hameedah. Bakinta dauke da sallama,
"Wa'alaykm Salam., Maaa"
"Naam Nadra." Ta karasa fada a gajiye hadi da zubewa a kan kujera . Saboda madaukakiyar gajiyar data kwaso.
"Ban ruwa mara sanyi Nadra "
"Aha MΓ a."
Da sauri ta dakko ruwan a wani mini cooler kaman fridge dake gefen side tables.
"Gashi."
Karba tayi in da sauri tafara sha bayan tayi Bismillah. Sai data shanye tukun sannan ta yi hamdala.
"Ina Hadiza?"
"Tana bacci."
"Allah sarki baiwar Allah."
"Amma kitchen floor fa Maa."
"Haba Nadra ya zaki bar ta ta kwanta a kitchen ? Bayan ga maids restroom nan ."
"Maa bansani ba fa. Kawai na shiga kitchen an ba dadewa naga tana baccin. "
"Ke tun dazu kina Ina?"
"Moha ne ya dame ni sena solving masa puzzle. So Ina sama."
"Mtssss " Dr. Hameedah ta saki tsaki hade da miqewa tsaye tayi kitchen din. Sam bataji dadin kwanciyar da Umma Hadiza tayi a tsakiyar kasan kitchen ba. Bayan ga dakin maaikata nan da suke hutawa da gado da kayan kallo aciki
"Hadiza... Hadiza."
"Naam Hajia. " Umma Hadiza ta tashi da sauri. Da ke batada nauyin bacci. Har damkwalin ta ya zame.Kanannadedden gashin fulani baqi wuluk me sheki ya bayyana.
"Kin dawo.,? Sannu da dawowa Hajia. Bacci ya dauke ni. A gafarce ni. " Ta karasa fada kanta a kΓ sa.
"Haba Hadiza meye haka? Uhm?"
"Nayi lefi Hajia. Banda sharri na bacci ya kwasheni a wajen aiki na? Dan Allah k."
"Ya isa haka mana Hadiza bar bada hakuri Dan Allah. Kaman wadda kikayi wani lefi? Dawowata kenan nima. Nake tambayar Nadra kina Ina tace kina bacci a kitchen. Kinji abunda yaban haushi kenan. Taya ga dakin maaikata nan da gado aciki. Meyakwan ta nuna miki. Tayi shiru."
"Wallahi batada lefi Hajia. Don basusan ma nayi bacci ba Allah. Ni kai na na gama duk abunda zanyi. Sena janyo tabarma dake iska na busawa. Wallahi bansan sanda bacci barawo ya sace ni ba. Don ko a gidah bana wannan baccin. Naurar nan ce masha Allahu take ta busa ni. " Ta karasa tana mai nuna air conditioner din dake buso sanyi
Dr. Hameedah tayi murmushi kawai.
"Muje na nu na miki dakin."
"Da girman Allah Hajia baccin nan na gama shi haka nan. "
"Kinyi sallah?"
"A'ah. Anyi ne? Lalle na jima ina bacci."
"Uku fa ta kusa "
"Kai! Lalle na jima. SubhanAllah; bara nayi alwala. "
"Ga dakin can da bandaki aciki "
"Toh Hajia."
Bakinta dauke da sallama ta shiga cikin dakin. Kwarai matuka ya tafi da ita. Yanayin tsaruwar sa harda kayan kallo. Tamkar dakin amarya amman ace dakin masu aiki ne?
Ta jinjina kai tana sake yabawa da tsaruwar bandakin bayan tayi addua ta shiga ciki.
Ta kama ruwa hade da dauro alwala bayan ta kuskuro bakinta saboda baccin da tayi.
Tuni har an shimfida mata sallaya da hijabin sallah. Nan da nan ta ta