Showing 123001 words to 123508 words out of 123508 words
a moment’s doubt. I love you. I believe in you completely. You are my dearest one. My reason for life... 🥺😍"
"I love you with every fiber of my being... Ina kaunar ka fiye da yadda kake tunani .. I love you more than life itself.. You're my answered du'ass.. Allah yabar mun kai miji na... Muradin rai na... Mamallakin zuciya da gangar jiki na... Allah yabar mu cikin lumana da kaunar junan mu . Har gaban abadan.....".
"Aamin Yaa Rabb Baby boo... Allah ya raya mana Sultan."
Da haka suka sake shiga wata shafin kaunar. Kafin daga bisani su faada bandaki su tsarkake jikin su..
Bayan sun dawo cikin daki ne aka shiga bugo kofar
"Waheedah .... Kin tashi?"
Waheedah ta bude baki, Kafin ta tattake ta ruko hannun Zayn da iya karfin ta ta tura shi cikin bandaki ta bude kofar Maa ta shiga.
"Ina Sultan ko yana wajen Naja?"
"Eh" Waheedah ta amsata tana sosa habarta.
Kai tsaye Maa tayi hanyar bandaki tana
"Bari a tara ruwan wanka ko?"
"Akwai .... Ka...."
"Na ce kibar kunyar nan Waheedah.. Kayan undies kuma ai ba wani abu bane. Ko ni sai na wanke m....
Tana bude kofar sukayi ido hudu da Zayn dake sosa keyar sa. Ta maze kawai ta shiga cikin bandakin.
"Ina wuni au kwana Maa?"
"Kalau ..."
Ta harhada abun da zata hada a bandakin ta fita daga ciki. Waheedah tuni ta sandare a tsaye kunya duk ta kamata.
"Idan anyi ishai sai ka zo ka dau matar ka Zayn...."
"Nagode Maa Allah yaja kwana.."
Maa ta girgiza kai kawai ta fice daga cikin dakin. Ya yinda Waheedah ta zube akan gado tana rufe kanta da pillow kunya dukta isheta
Zayn kuwa ko a jikin sa... Daman haka yake so... Bai je ko'ina ba. Har akayi ishai. Suka tarkata suka koma gidan su.
Baby sultan ne kawai ke ceton maman sa awajen Zayn. Duk inda Waheedah ta saka kafa Zayn na like da ita kamar super glue. Ta kance,
"Dan Allah Darling ka kyale ni .... Kabari nayi feeding baby sultan ."
"Ki sassauta mun kada ki manta ke ce FARHATAL QALB na... Kin gama zama mun dukkanin wani FARIN CIKIN ZUCIYAH... "
Tare sukeyin renon. Lamarin nasu sai masha Allah....
Bayan wata 9 da haihuwar sultan. Allah ya albarka ci Ahlam. Itama ta haife sankacececiyar jarirya mai kama da Zayn . Wadda taci sunan Ummimi suna kiran ta da Daneen..
Burin Zayn ya gama cika.. Matan sa masu kaunar sa. . Da kuma arzikin iyali masu tarin albarka .. Alhamdulillah!
Hakika dukkanin wani bangare ya samu wadatar ZUCIYA da FARIN CIKI. Allah ya albarkan ce su ta fannoni da dama. Lamarin sai godiya ga Allah domin shidin mubawayi ne gagara misali....
*ALHAMDULILLAH!!*
*_DUKA DUKA ANAN NI NANA HAFSATU ZAN DASA AYA... ABUN DA NAYI KUSKURE ACIKI RABBANA YA YAFEMUN WANDA NAYI DAIDAI ALLAH YA BAMU LADAN DUKA AMIN ..GODIA GA TARIN MASOYA LITTATTAFAN ZAFAFA BIYAR WADANDA SUKA SAYA. DAMA WADANDA SUKA SAYA TULAREN WUTAN YERWA INCENSE AND MORE. ALLAH YA KARA ARZIKI MAI ALBARKA . SAI MUN HADU A ZAFAFA NA GABA IDAN MAI DUKA YA KAI MU. AMIN💕💕_*