Showing 117001 words to 120000 words out of 123508 words

Chapter 40 - Farhatul Qalbi Hausa Novel Complete

Mamugee   

08 Dec 2024

541

Ko zaman lapia zai kara wanzuwa dik kuwa da ahakan ma Alhamdulillahi..

Sun amince da maganar sa. Don raba gidan ma wani kwanciyar hankalin ne. Da dai-daita tsakanin su. Domin wata kazantar da ba ka gani ba tsafta ce.

Nan da nan kuwa farfesa Adams ya ba wa Zayn wani gidah bungalow (flat/marar bene.) Kyauta. Mai kyau da shi a layin su Haj Hameedah din amman daga karshe yake shi ta baya.

Zayn ya saka aka fente masa shi. Aka sake gyara shi sosai. Ya zuba masa kaya masu matukar kyau da tsada.

Ya kuma samu Ahlam da zancen tayi murna kwarai da gaske. Domin tafu kaunar ita kadai anata gidan ta bararraje yadda take so..

Zayn bai gayawa Waheedah ba. Sai ana'i satin da zata koma. Suna zaune a parlour su ukun .

Suna kallon film din titanic. Yana shan fruits din dake gaban sa. Suna hira jefi jefi. Ya ce,

"Kun kasance duk abin da na taba so a soyayya. Kun sanya ni jin ana kaunata ta hanyoyin da ba zan iya tsammani ba. Ba zan taba neman karin ba. Ina son ku da ni tare har abada. Daga yanzu har zuwa numfashi na na karshe, zan ci gaba da kaunarku..Ina son ku sosai ..Na rasa yadda zan yi da son ku har ban san kalmomin da suka dace ba don bayyana abin da nake ji game da ku. Babu wata kalma da zata iya misalta kaunata a gare ku! Na kuma ji dadin yadda kuke mu'amala a yanzu sosai... Har cikin rai na nake jin dadin hakan. Allah kuma ya kara mana zaman lapiya Amin ya rabbi..."

"Amin...." Suka amsa baki daya.

"Ke Waheedah baki sani ba. Amman Ahlam ta sani . Na sanar da ita .."

Waheedah ta daga kai ta kalle shi ya jinjina mata kai alamar tabbatarwa.

"Nan gidan kamar yadda yake da sunan Ahlam .. Kema Allah yayi na sama maki wani matsugunin wanda yake da sunan ki kema... Amma fa wani hanzari ba gudu ba... Ba bene ba ne flat ne.. Sannan kuma ba anan unguwar ba ne... A tasu Maa ne." Ya fada yana tsokanar Waheedah daga karshe.

Wani FARIN CIKI ne ya mamaye ZUCIYAr Waheedah da gauraye . Murmushin fuskarta yaa fadada. Kai kana kallon ta kasan taji dadin zancen sa.

Ba dan Ahlam na wajen ba. Har tukwicin sumba ta so ba shi. Sai ta danne dai . Ta shiga godiya agare shi. Zayn yaji dadin hakan kwarai matuka.

Ahlam ma ta tayata farin ciki. Ana'i washegari zata koma Zayn ya kai su gidan su wajen Haj Hameedah da Haj Aisha. Tun safe har rana. Da rana kuma ya dau Waheedah ya kai ta wajen Umman su gidan gwaggo haule. Acan ta karasa wuni har dare.

Washegari kuma akai mata rakiya gidan ta dake nan layin su The Adams family amman daga karshe.

Tsayawa bayyana yadda gidan ya tsaru ma bata lokaci ne. Komai yaji zam zam.... Sai fatan Allah yasa a tsofe lapia yasa kuma an shiga a sa'a.

Ya kuma kawo musu zuriya dayyiba. Domin har yanzu shiru daga Ahlam din har Waheedah. Gashi tuni har zahara'u yar Marka ta haihu. Ba tazara da ke kwanika ta keyi ko auren ta na baya. Shekara na cika ta sake sullubo wani. Ta shiga renon su su biyu .

*GIDAN MALAM NA LADO*

_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._

_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_

_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_

_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_

_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_

_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_

_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_

_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_

_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._

_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_

_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_

_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_


_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_

❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥❤‍🔥

*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*

*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*

*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*

😄😄😄😄😄😄😄

*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*

*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*

INAYA(riba biyu)___mamughee

SANADIN LABARINA___Rano

BABU SO___Billynabdul

FARHATUL K'ALB___Miss xoxo

GURBIN IDO____Huguma

*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*

*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*

Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300

*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*

HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank

*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902

*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107

*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰
[11/23, 9:02 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
                     💞
_NA_


_NANA HAFSATU_
_(MX)_


_AREWABOOKS:MISSXOXO_

_WATTPAD: MISSXOXO00_


_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_


_PG:70_


*_FINALE/END (KARSHE)_*


_______

  **Jikin na Marka ya sake saaki. Baki daya sai dai a kwantar a tayar. Sauki daya ta samu ta hanyar maganar ta da ta dawo. Amman itama dakyar maganar ke fita. Cikin wata iriyar murya mai wahalar wa.

Najib kusan kullum yana gidan. Daya dawo daga makarantar boko zai je gidan. Da ke yana ajin karshe na babbar makaranta ta sakandire.

Umma Hadiza na kokarin temakawa da su Marka da yan kudade na daga ribar kasuwancin tah. Tana yi ne kawai saboda Allah da albarkacin yaranta da haifa daga gidan.

Haka ma Deluwa da ke kokarta wa a nata bangaren. Don itama tanada marar lapia acikin yaranta yan biyu.

Zahara'u kuma ta nuna gajiyawa. Ba sosai take zuwa gidan ba ma. Ta kance Na'Ateeku ya hanata. Ko kuma yara ba lafiya.

Malam Nalado ya tsaya tsayin daaka akan rashin lafiyar mahaifiyar sa Marka.

Duk kuwa da ba tsayayyakin aiki ne da shi ba. Da ake biyan sa, Aikin karfi ya saka a gaba ka'in da na'in.

Ya kan je kasuwa ya yi wa yan kasuwa daako su dan bashi na cin abinci. Sai ya soke kudin sa a aljihu. Ya sake gangara wa wajen maagina yayi musu leburanci. Ko na ebo musu ruwa su ko kasa da daukar bulalluka.

Ta hakan ya ke samu ya rufawa kansa asiri da kula da lafiyar Marka. A boye kuma ya kan bawa yaran inna Sa'adatu su kai mata gidan su.

Deluwa kuwa wani lokacin ma ita kan temaka masa. Idan tayi cinikin abincin sayarwar da ta ke.

Su zabba'u kuwa daman ba sa bi takan yiwa Marka wani abun arzikin. Kan su kawai suka sa ni. Su kance a baya ai dama Nalado da zahara'u ta nuna tafu kauna. Don haka su babu ruwan su da harkokin ta.

Su kanzo dai su dubata da dan lemo da ayaba. Wataran kuma su karkade jikin su su tafi. Babu ko sisi.

×××

Marka na tsakar gidah kaman kayan shanya akan tabarma .

Daga gefen wajen dakin girki kuwa Deluwa ce tanata jefa danwake.

Wani yaro dan gidan zahara'u yana wasa da wani kara ya daga shi sama ya cilla. Bai fadi a ko'ina ba sai fuskar Marka .

Ta ke ta kece da kuka. Cikin dashasshiyar muryar ta mai fita a sarke ta ce,

"Shege, Dan iska... Ka ci malafar kan uban ka Adamushe. Matsiyaci. Gayyar masifa."

Gashi ba dama ta saka hannu ta mulmula wajen. Yaron ya kece da dariya.

"Yi hakuri marka .." ya fada yana sake tuntsirewa da dariya .

"Kai mekayi Abbati? Matsa daga nan, Sannu Marka .." cewar Deluwa da sai da ta jiyo maganganun Marka ta gano wani abun abbatin ya aikata.

Dai dai lokacin da malam na lado ya shiga bayan sa kuma wani tsoho ne mai farin gemu yana dogarawa da sanda.

"Assha. SubhanAllahi Marka. Menene kike kuka. Deluwa menene?"

"Yo ka tambayi matsiyaciya.?  Ai so ta yi karan ya chake mun idanu nima na dai na gani tamkar yar wajen ta. Wannan mata, wannan mata, Allah dai ya kwashe miki albarka..."

"Assha marka bar cewa haka.... " Malam na lado ya fada. Kafin ya sake cewa,

"Ga malam me carbi na kofar dawanau ya zo duba ki."

"Ayho to .. Sannu malam .."

"Yauwa sannu Marka ... Ina wuni?"

"Alhamdulillah Malam."

"Ya karfin jikin na ki?"

"Da sauki "

"Masha Allahu... Ubangiji Allah ya baki lafiya. Yasa zakkar jiki ce. Allah yasa wannan ciwo na ki kankarar zunubai ce. Allah ya tashi kafadun ki.. Ya sa...

Bai karasa ba zahara'u ta shigo cikin gidan tana koke koke.

"Marka Allah ya isa tsakani na da ke. Wayyo Allah na. Wayyo . Wayyo ..."

Duk suka tsaya suna bin ta da kallo. Malamin ya sake mayarda zaman gilashin kara masa gani cikin idanun sa.

"Assha.... Wacece wannan din?"

"Zahara'u ce autar mu." Malam na lado ya fada yana matsa yatsun sa.

"SubhanAllahi.... Ki ke fadaawa mahaifiyar ki wadannan tsauraran kalamai haka? Assha assha."

Zahara'u ta zube a jikin bango tana mai harba kafafun ta.

"Ya shika ni .... Shi ma ya shika ni. Shika 3 kuma. Yace ba zai iya dawainiya da yara majinyinta har biyu ba. Munje asibiti an gwada su. Suna da ciwon amosanin jini ta sikila (sickle cell..) wayyo Allah na... Marka kin cuce ni.. Kin ha'ince ni. Allah ya isa tsa...

Malam na lado ya samu kansa da faskara mata zafafan maruka har biyu hagu da dama na fuskar ta.

Marka ta sandare da jin bayanin zahara'u. Ciwon amosanin jini yaran zahara'un ke da shi? Maganganun Najan Isubu suka shiga dawo mata na shekarun baya.. Alokacin da zata hada Waheedah da shi. Inda Najan ke ce mata Na'Ateeku fa shima ba lafiyar ce dashi ba. Wani tokararren abu ya tokare mata a makogaro . Sai dai idan Hadiza ce ta kai sunan ta gidan boka.

Dattijon ya dube su duka. Yana wa malam na lado kallon karin bayani. Nan dai Nalado ya sheda masa komai . Tun faruwar neman da Na'Ateeku yayiwa yar wajen sa Waheedah. Da yadda auren ya koma kan zahara'u. Da tarihin ciwon da ke kan Najib da ma marigayi yayan su Waheedah, wato Kamal.

Marka ta kece da kuka... Cikin muryar me cunkushe da damuwa tace,

"Ko kaffara ba zan ba sai dai idan Hadiza ke bibiyar mu da sihiri. Ta jefe rayuwar mu baki daya.... Ya zaai ace. Da fari bayan da nace tabar gidan nan tin da dama auren ya kare tuni. A ranar data tafi Adamushe ya zo ya sau zahara'u saki 3 agaban mu. Yace yara ba nasa bane. Gasunan zube muna zaune da su. Mai sunan Malam ya zo ya auro Deluwa itama gatanan yara biyu du ba lafiya. Waçcen dayar makauniya ce ma tamkar dai diyar Hadiza da ke saka gilashin kara gani to ita wannan yarinyaa ma baki daya bata gani. Akazo ranar daurin auren zainabu yar Sa'adatu a ranar mijin itama ya sauta... Sannan kuma auren zahara'u na biyu dan ana bakin ciki ta haifo har biyu shine Hadiza ta shiga ta fita ta sanyawa yaran irin ciwon yaranta su biyu. Ciwon da ya kashe dan ta na fari kamalu. Gashi Najib yana da shi shi ma. Sannan ace yaran zahara'u na wajen Na'Ateeku suma du su biyun suna da shi? Bayan ciwo ga shika har 3? Ni ma bata bar ni ba. Ta kassarani gashi nan ta lalatamun rayuwa sai dai a kwantar a tayar. Baki daya malam wannan matar ta batamun rayuwa ta da ta iyalina gaba ki dayan mu... "

Malam me carbi na kofar dawanau yayi murmushi kawai. Yana mai girgiza kansa,

"Ki sauri ki ce Astagfirullahi.... Wani bai isa yayi wa wani wani abun ba. Ba tare da Allah ya rubuto haka kaddarar sa zata kasance ba.... Kuma in dai Hadiza dai kike nufi wacce ke wajen haulatu yayar ta. Matar Nalado ta fari. Maganar gaskiya ba zata aikata mugun abu ba... Dukkanin abubuwan da kike fada ya shafeta haka zalika kema ya shafeki Iya. Yaranta sunada ciwon sikila. Diyar ta ya macen kuma bata gani sai da temakon gilashi. Haka zalika ke kika sanyaa Nalado ya rabu da ita..Yaran nan nata jikoki ne agare ki Marka. Ko ba komai itama uwar 'yayan dan cikin ki ce.

"Kada ma ki sake cewa wani ya tozarta miki rayuwa ta hanyar sanya miki ciwo ko gurbata rayuwar ahalin ki. Wannan ba dai dai ba ne. Baki imani da kaddara ba Iya. Babu hutu da kwanciyar hankali ga bawa a wannan rayuwa ta duniya sai yayi imani da qaddarar Allah. Wato ya sakankance cewa duk abinda Allah ya qaddara mai aukuwa ne, kuma abinda be so faruwar sa ba, to haqiqa bazai faru ba. Haka kuma lallai al'umma da zata taru gaba daya domin ta cutar da bawa da wani abu, to ba zasu iya ba sai dai da abinda Allah ya rubuta zai same shi. Hakanan da zasu hadu domin su amfanar dashi, ba zasu iya ba face da abinda Allah ya rubuta.

"Ma’anar Imani da Qaddara:
Imani da qaddara na nufin yarda tare da gaskatawa cewa, babu wani alhairi ko sharrai da zai sami dan Adam face bisa qudura da hukunci na Allah Madaukakin Sarki. Sarki ne kuma shi, da yake aikata abin duk da ya so; ba abin da zai iya kasancewa, face da sani, da kuma yardarsa. Babu kuma wani abu a faadin duniyar nan, da yake wajen qarfin ikonsa, Madaukakin sarki ta fuskar samuwa ko rashi; shi yake samarwa da sarrafa shi. Amma, tattare da haka, ya shimfidaa wa bayinsa wasu umarce-umarce da hane-hane, wadanda a cikinsu, ya ba su cikakkiyar damar tsare alfarmarsu ko tozarta ta; babu wanda zai tilasta su. Iyakar abin da yake wurin shi ne, al’amurran za su ci gaba da gudana ne gwargwadon iko da zabin ransu. Amma, yana da kyau a sani cewa, da su bayin nasa, da wannan dama da iko da suke da su, duk Allah Madaukakin Sarki ne ya halicce su. Saboda haka duk wanda ya shiriya daga cikinsu, rahama da jinqai ne, na Allah ya sauka gare shi. Haka kuma duk wanda ya bace, hikimarsa ce Madaukakin Sarki, ta tabbatar da haka. Babu kuma wanda ya isa ya tambaye shi dalili a kan haka. Amma, baya gare shi subhanahu wa ta’alah,  kowa abin tambaya ne.       

"Iya, Imanin nan kuma da iko da qudura irin na Allah Madaukakin Sarki, Daya ne daga cikin rukunnan imani, kamar yadda jawabin manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ya bayyana a lokacin da mala’ika Jibrilu ya tambaye shi a kan abin da imani ya qunsa. Sai ya karba masa da cewa: “Shi ne ka yi imani da Allah, da Mala’ikunsa, da littafansa, da Manzanninsa, da Ranar Qarshe. Ka kuma yi imani da qaddara ta alhairi da ta sharri.”[Muslim:8]

"Ina fatan wannan dan karin haske daga cikin dan ilimin da na sani zaki duba agare shi. Ki kuma tabbatar wa kan ki da bawa baya tsallake kaddarar da Allah ya ketara masa. Imani da ita kawai zaki. Ki karba da hannu dubu. Sai Allah ya dube ki da idanun rahama ya kawowa rayuwar ki sauki... Kar Allah ya karbi ranki acikin wannan yanayin da kike ciki. Kinsan kuma Allah baya yafe zaluncin da kayiwa bawan sa. Hakanan kuma adduar wanda aka zalunta batada hijabi ga Allah .. Ki roki dukkanin wadanda kika aibata wa rayuwa ko kika zalunta. Ko Allah zai dube ki da rahamar sa. Ya sassauta maki halin da kike ciki."

Hawaye suka shiga zurara daga idanun Marka..

"Allah na tuba Astagfirullahi... Ka yafe ni. Allah na karbu kaddara tah. Allah kasa hakanne mafificin alkhairi agare ni da iyali na baki daya .. Deluwa, Mai sunan Malam, Zahara'u da ma su zabba'u dan Allah dukkanin ku ku yafe mun .. "

"San samu gaba daya ahalin na ki su taru waje daya. Ki nemi gafarar su. dukkanin su manya da kankana... Kinji ko?"

"Insha Allahu malam... Amman bana jin zasu yafe mun. Na aikata abubuwa marasa dadi "

"Zasu yafe miki insha Allahu... Domin Allah ma kullum cikin yi masa laifuka muke. Kuma idan muka roke shi yana yafe mana. Ballantana mutum dan Adam. Insha Allahu dukkanin su zasu yafe miki... Allah ya yafe mana baki daya."

"Aamin Yaa rabbi."

"Aamin.."

"Sai ku tsayar da rana nan kusa ku tara iyalan baki daya. Insha Allah nima zan zo don tausasar harsuka. Allah ya ara mana rana yasa muna da rabon haduwa."

"Amin malam. Nagode Allah ya saka da alkhairi. Ya kara lafiya."

"Amin Amin tare da ke da sauran baki daya.."

Yayi musu sallama ya tafi. Bayan ya kara jawa zahara'u kunne ya tsawatar hadi da mata fada sosai akan muhimmancin girmama iyaye da tausasar harshe idan zaa yi musu magana. Ya kuma saka ta bawa Marka hakuri hade da neman yafiyar ta.

Malam na lado ya shige gaba yayi masa rakiya...

Marka nata tsiyayar hawaye. Idan ta kallo yaran Deluwa marasa lafiya da daya makauniya. Ga tulin yaran Adamushe ga biyu na wajen Na'Ateeku masu dauke da cutar amosanin jini.

Ta sake fashewa da kuka. Ganin dukkanin aibatawar da takewa yaran Hadiza . Gashinan nata ma sun samu. Gaba da baya kowanne na da irin na sa ciwon. Ga ita kanta data zama jangwam sai dai a kwantas a tayas. Gefe daya zahara'u na rera nata kukan.

Baki dayan su dai zukatan su ba dadi. Damuwa ta taru

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login