Showing 51001 words to 54000 words out of 123508 words
Yaa Rabbi.."
"Yauwa ... Ya ya jikin su Najib da Yayan ku?"
"Allah ya kara sauki yasa kaffarane."
"Amin Amin Umma .."
"Najaatu na aiko muku da abinci ko?"
"Tana aikowa... Kusan kullum sai mun dumama munci washegari ma"
"Yauwa Alhamdulillah... Daman abunda yasa banason daya daga cikin ku yazo nan din ya karba. Ba komai bane fyace sai dai don kada tarzoma tataso. Shi yasaka nake cewa Najan ta turo Wanda zai riqa kawo muku."
"Ana kawowa. Allah ya shi albarka...."
"Amin Yaa rabbi . Ai ba abunda zan cewa da su Hajia. Sai fatan Allah ya saka su gama da duniya lapia. Ya kuma kara musu arziki mai tarin albarka. Da wadatar zuci mai dimbin alkhairi...."
"Aamin Umma...."
"To shikenan sai kin dawo... Kada ki manta ki fa biyo tanan din.. Kamar yadda Hajia ta fada "
"Insha Allah.... Umma."
Sukaa rabu. Umma Hadiza ta shiga gidan The Adams Family. Ita kuma Waheedah ta miqe ta nufi makaranta. Tana tafe tana tunanin rayuwa da wasu qalubale na cikin ta ....
A haka har ta karasa makarantar. Ta tsallaka titi ta shige. Saura minti 5 a fara tsaron yan latti. Tana shiga kuwa ta sake numfashi na samun nutsuwar zuciyar bata makara ba...
×××××
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE__*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:40_
_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA ZAFAFA NA *KUDI NE* DAN ALLAH KI/KA BIYA KI KARANTA DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA .._
____
*Kan* sa ne ke matukar sarawa. Ya sake ballo panadol pain and cold ya sha da ruwa. Kujerar da yake kai irin me jujjuya dinnan ce.
Ya kwantar da kansa . Idanun sa a rufe. Kansa na kallon sama. Ya lula duniyar tunani.
Agogon da ke dauraye a wutsiyar hannun sa ya kalla. Ya miqe ahankali ya hada komai cikin wani royal blue brief case da sauran wasu takardu masu muhimmanci. Kafin ya dau wayar sa. Ya zura a aljihu ya fice daga office din.
Wajen parking terrace ya je. Ya shiga motar ya tayar da bismilla. Ya fice daga ofishin yanata tunanin inda zashi. Gidan su ko gidan sa?
Ya samu kansa da wucewa gidan nasa. Ko a wannan karon zai samu abunda zai saka a bakin sa.
Don bayaso sam ya fara kai wa mahaifiyar su Haj Hameedah korafe korafe. Akan auren da baa dau lokaci da yin sa ba.
A hanya ya tsaya ya shiga wani grocery store ya sissiyo wasu fresh kayan miya da sauran veggies.
Ya bude mota ya zura su aciki. Tukun shima ya zauna ya tashi motar. Kai tsaye yayi gidan sa
Ledojin niqi niqi ya nufi hanyar da zata sadaka da cikin gidan baki daya.
Tun daga bakin kofar ya fara hamami. A bakin kofa yaci karo da warin takalmin sa daya cire jia. Ciki harda warin safa daya. Dayan kuma tana tana kan kafar bene.
Bai tashi tsinkewa da lamarin ba sai da idanuwan sa sauka akan wasu almajirai su biyu. Suna wanke wanke.
Dayan almajirin hannun rigar sa ma ya shiga cikin ruwan daurayar. Gashi rigar tasa tayi dukundukun.
Dayan kuma ya hautsina kwanukan abincin. Duk ya saka su cikin ruwa daya .
Wani abu yazo masa makogaro ya tokare. Gyaran murya yayi suka juya suna kallon sa. Dukkan su yara ne. Kuma kowanne rigar sa da wando daban daban. Duk a yage kuma a kazance.
"Tana ina?" Ya samu kansa da tambayar su
"Sama tayi."
"Eh sama ta haye ."
Ya gyada musu kai kawai . Saman ya shiga taka matattakalar benen da 'dai 'dai.
Bakinsa dauke da sallama ya tura kofar da zata sadaka da parlorn. Tana hakimce akan kujera. Yayinda kunnuwanta ke sakale da earpiece. Har Zayn na jiyo wakar psquare alingo da take ji. Saboda tsanin yadda ta kure volume din.
Sallama ya sake yi har sau uku. Sam bata jin sa. Sannan kuma ta baya yake hangota. Ita bata ganin sa.
Ya karasa ta baya ya zare earpiece din na duka kunnen. Da sauri ta juya don ganin waye? Ganin sa ne ya sa ta tadan fadada murmushin ta
"Ka dawo ....?"
"Uhm.... "
"Bread and tea. Ko indomie and egg?".
Kallonta yake sosai. Kallo mai cike da madaukakin mamakin halayenta. Saboda tsabar cin kayan flour da indomie har upset stomach ya samu.
Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya kawai. Ta koma kusa da shi. Ta hada hannuwan su waje daya tana matsawa.
"Ina tambayar ka kayi shiru..... Uhm? Darling sweety ... Sweety darling..."
Zayn ya kakaro murmushi kawai ahankali yace da ita,
"Na koshi... Fita ma zanyi. "
"Tohm shikenan sai ka dawo "
Ya mike ahankali ya zareta daga jikin sa. Ya sauka kasan. Almajiran har sun kammala wanke wanken suna share parlorn kasan da corridor.
Ya bisu da kallo kawai ya fice yana girgiza kansa cikin takaici. Kai tsaye ya shige mota ya tasheta ya dauki hanyar gidan su.
Dawowar Haj Hameedah ke nan daga asibiti. A tare suka shigar da motocin su. Tana gaba yana biye da ita a baya.
Suka faka motocin na su. Ya bude mota da sauri ya fita ya karbi jakar hannun ta bayan ya tsugunna har kasa ya gayshe ta.
"Ashe yanzu kika dawo kema?"
"Eh... Dr, Victoria ta zo shi yasa "
"Oh .. okay! Allah ya temaka Maa."
"Aamin..."
Suka nufi cikin sashen na su. Umma Hadiza ce ta bude musu kofar da kararrawa ta kada.
"Ah Hajia sannu da dawowa .. "
"Sannu Hadiza. Ke zanwa sannu."
"Ina wuni?" Zayn ya gayshe ta.
"Lapia kalau.... Ya aiki?"
"Alhamdulillah.."
"Allah ya temaka ya bada sa'a."
"Amin nagode." Ya amsata. Don har cikin zuciyar sa yaji dadin adduar da Umma Hadizan ta yi masa.
Zama yayi akan kujera yana kallon tv. Yayin da Haj Hameedah ta haye sama. Sai datayo wanka ta sauya kaya tukun sannan ta sakko kasan.
"Ah kana nan....?"
"Eh Maaa.."
Ya amsata yana sosa keyar sa.
Ta danyi murmushi kafin tace
"Daga wajen aiki ka ke ne...?"
"Eh..." Ya ce da ita. Don bayaso ta gano halin da yake ciki.
"Bari a kawo maka abinci to."
"Tohm...." Ya amsa ta. Kasan zuciyar sa kuwa wani dadi ne ya mamaye shi.
Ba jimawa kuwa Maa ta ajiye masa tray agaban sa mai dauke da abinci sai kamshine ne ke tashi
Nan da nan kuwa ya shiga zira abincin yana murmushi. Ya cinye tas yana hamdala .
"Yayi dadi ..?"
"Tab sosai .. yafu dadi dadi .."
"Ah lalle ya maka dadi .. To Hadiza ce tayi "
Ji yayi tamkar ya dawo da abincin yayo aman sa.
"Waccen?"
"Ita dai ... Gashi kuma kaci lapi lau har kana yabawa..."
Kasa magana yayi. Ji yake tamkar ya rusa da kuka...Haj Hameedah tayi murmushi tana girgiza kan ta.
"Ko hasidin iza hasada ba ze kushe abincin nan ba."
Shi dai baki daya Haj Hameedah ta gama daure shi da jijiyoyin wuyan sa. Ya samu kansa da kasa magana kawai. Saboda gaba daya ya rasa abun cewa.
"Ina Ahlam ?"
"Tana gidah...."
"Ba dai wata matsalar ko?"
Tamkar yace akwai. Sai Kuma ya danne kawai. Don shi mutum ne mai kaunar sirri da zurfin ciki.
"Babu ko?"
"Eh..."
"To masha Allah .."
Door bell ce ta sake kara. Umma Hadiza da ke kitchen ta je ta bude da sauri. Waheedah ce a tsaye. Ta shiga tana murmushi .
"Assalamu alaikum..." Zazzakar muryar ta mai kama da anbusa sarewa ta doki dodon kunnen sa. Har ya kasa hakuri sai daya juya ya kalleta
"Kin dawo ...?"
"Eh Ummaa ."
Ta nufi wajen Haj Hameedah ta tsugunna har kasa.
"Ina wuni Maa?"
"Lapia kalau beautiful Waheedah .. Ya karatun?"
"Alhamdulillah..."
"A nata tayi ko?"
"To Allah ya bada sa'a. "
"Aamin Aamin...."
Tamkar ba zata sake cewa komai ba. Sai Kuma ta juya bangaren Zayn .
"Ina wuni...?"
Bai amsa ba ya juyar da kansa gefe. Waheedah ta miqe ta koma kitchen wajen Umman su.
"Meye haka...?"
"A'ina?"
"Ya yarinya ta gayshe ka ka ki amsawa ka juyar da kan ka? Meye hakan?"
"Ban ji bane."
Tsaki Maa ta saki. Ta miqe daga kujerar tayi kitchen.
Moha dake bacci a sama ya sakk6ko yanata murje idanuwa.
"Ahhh Waheedah...." Ya kwalla kara ganinta yanata murna harda rawa.
"Um my boy...." Ta dauke shi tanata masa wasa shi kuma yana dariya.
"Yaushe kika zo?"
"Yanzu...."
"Yayaaaa... Let's play hide and seek..."
"Tsaya ... Yanzu ka tashi ko?"
"Uhm."
"To ka fara brush sai wanka sai abinci. Idan kaci sai muyi wasan ko.?"
"Ba zaki tafi ba ko?"
"Eh mana..."
"Pinky promise?"
"Yay .. pinky promise."
Suka hada yatsun su. Haj Hameedah sai kallon su take cike da so da shakuwa.
Zayn ya karaci zaman sa shi kadai ya mike. Yayi wa mahaifiyar sa sallama ya tafi.
Waheedah Kuma ta temakawa Moha yayi brush. Ta Tara masa ruwa akayi masa wanka. Yaci abinci . Tukun sannan suka fata wasan
Yayinda su Umma Hadiza da Haj Hameedah ke magana. Anan Haj Hameedah ta roki Umma Hadiza data sanar da ita komai.
Sai data buga ta raya tukun sannan dakyar Umma Hadizan ta sanar mata komai. Ta kuma kira Waheedah itama ta dora da wasu abubuwan
Ciki harda batun yadda suka wanye da Marka da safiyar yau. Haj Hameedah har hawaye ta zubar na tausayi.
Anan ne ta kawo kokon barar samun Waheedah . Kan Umman ta bata Waheedah ta karasa makaranta awajen ta. Har ya zuwa auren ta. Saboda tsananin kaunar da Moha ke yi Mata.
"Kinyi shiru Hadiza ..."
"Ba shiru nayi ha Haj ... Ai da na kowa ne. Kuma da kyakkyawar mu'amala da zuciya kikeson kasancewar Waheedah a tare da ke. Idan ni na amince akwai kakarta da mahaifin ta. Sai hukuncin da suka zartar..."
"Tohm shikenan ni de ina kan bakana. Ina kuma fatan hakan ya zamo mana alkhairi agare mu baki daya .."
"Allahumma Aamin..."
"Kije ki sanar da Najan Isubu kan yadda za'ayi da kayan dakin. Tunda Markan ta kafe..."
"Tohm Umma... Maa na tafi "
"Tohm Waheedah... "
Moha harda kukan sa. Dakyar dai aka yageshi daga jikin waheedan. Ya tafi shi kuma ya koma dayan parlorn da suke ce da shi study anan ya zauna ya nata kuka .
Umma Hadiza kuwa tacika da madaukakin mamakin Haj Hameedah da irin kaunar da take musu ko kadan ba kyama ko ganin kaskanci. Kasancewar su din ba wasu bane. Fyace talakawa da ke neman cin yau dana gobe ..
×××××××
_INA MASOYA KUMA MA'ABOTA KAMSHI MA SU KAUNAR KAMSASAWA A KODA YAUSHE? DOMIN KAMSHI RAHAMA NE.._
_TO KU MATSO, DOMIN WANNAN KARON MA ZAFAFA BIYAR SUN ZO MU KU DA TALLAN MASARAUTAR KAMSHI NA KAMFANIN TURAREN *YERWA INCENSE AND MORE*_
_A *YERWA INCENSE AND MORE* ZA KU SAMU TURARUKAN WUTA NA *GIDAH, NA KAYA, NA TSUGUNNO* BA A NAN KADAI SUKA TSAYA BA. AKWAI *KHUMRAHS* MASU KAMSHIN LARABAWA DANA FRUITS KAI DAMA KAMSHIN TURAWA. AKWAI KHUMRAHS TA MATAN AURE DA TA YAMMATA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN WANKA DANA SHAFAWA BAYAN AN KAMMALA WANKA.* BA ANAN TURARUKAN NA SU SUKA TSAYA BA. AKWAI *KULACCAM* MAI MATUKAR KAMSHI DA SANYAYA ZUCIYA, SANNAN SU NA DA *MADARORIN TURARUKA NA JIKI DA NA KAYA*_
_AKWAI TURAREN *AL'AJABU NA TSUGUNNO DA KHUMRAH* DIN SA_
_SANNAN SU NA DA *TURAREN GASHI NA CREAM DA KUMA SPRAY DIN SA NA FESAWA*_
_BA ANAN SUKA TSAYA BA. SU NA DA *TURAREN MOPPING, DA NA BANDAKI AKWAI NA RUWAN WANKI DA NA FESAWA A DRAWER KO AKWATI*_
_AKWAI KAYAN GYARARRAKI NA FATA. KUJERAR TSUGUNNO, KASAKE NA WUTA, COAL IGNITER TA KUNNA GARWASHI, ELECTRIC BURNERS DA ENGLISH COAL_
_AKWAI LAFFAYAS DA SAURAN TURARUKA NA KAMSHI KALA KALA_
_SU NA BADA KAYAYYAKIN SU AKAN FARASHIN SARI KO SAYA AKAN DAYA DAYA. SANNAN SUNA TURA KAYAYYAKIN SU KO'INA A FADIN NAJERIYA DA KETARE. KAYAN SU YAN CHADI NE DA SUDAN DA KUMA YERWA WATO MAIDUGURI._
_KYAU, INGANCI DA RAHUSA SAI KAYAYYAKIN KAMFAMIN YERWA INCENSE AND MORE. SAI KUN GWADA ZAKU BAMU LABARI_
_NAMBAR TARHON SU DA ZAA KIRA KO MUSU MAGANA TA WHATSAPP ITACE: 08095215215_
_INSTAGRAM HANDLE DIN SU: @yerwaincense_and_more_
_YERWA INCENSE AND MORE: A NUMBER ONE STOP SHOP FOR HEAVENLY EXOTIC SCENTS AND MORE_
❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥❤🔥
*_ZAFAFA BIYAR din samari ne a rayuwar INAYAH,kowanne a cikinsu akwai wani murdadden Al'amari da ya shata layi tsakaninsa da ita,wawakeken sirri wanda a koda yaushe take kiransa da SANADIN LABARINA_*
*_Amma babban abun mamakin a koda yaushe shine,ita dai tasan cewa BABU SO tsakaninsu MEYA KAWO SHI?_*
*_Duk da haka tana tunanin yun qundun bala ta fitar da FARHATUL K'ALB a cikin ZAFAFA BIYAR din samarinta,duk da batason su zame mata GURBIN IDO wanda har kullum ba ido bane_*
😄😄😄😄😄😄😄
*YA KUKAJI SALON MASU KARATU?*
*YADDA SALON YA BAMBANTA DAKO YAUSHE HAKA LABARAN SUKA BAMBANTA DA DUKKA LABARANMU NA BAYA*
INAYA(riba biyu)___mamughee
SANADIN LABARINA___Rano
BABU SO___Billynabdul
FARHATUL K'ALB___Miss xoxo
GURBIN IDO____Huguma
*ZAKI YARDA AYI TAFIYAR NAN BABU KE MADAM?*
*_GARZAYA KI BIYA NAKI KUDIN KAN FARASHI KAMAR HAKA_*
Biyar:::1k
Hudu:::700
Uku::::500
Biyu::::400
Daya:::300
*_zaki saka kudin ta wannan account number din_*
HAFSAT UMAR KABIR
2270637070
Zenith bank
*Saiku tura shaidar biya zuwa ga*
07040727902
*IDAN KUMA KATIN WAYA NE ZAKU TURA TA NAN TARE DA SHAIDAR BIYAR*
09134848107
*_THANKS FOR THE CONTINUED PATRONAGE_*🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰🥰[11/23, 9:01 PM] Mummyn Yara: _*FARHATAL-QALB*_
_(FARIN CIKIN ZUCIYAH)_
💞
_NA_
_NANA HAFSATU_
_(MX)_
_AREWABOOKS:MISSXOXO_
_WATTPAD: MISSXOXO00_
_ZAFAFA BIYAR PAID NOVELS_
_PG:41_
_WANNAN LITTAFI DA MA SAURAN NA *ZAFAFA* NA *KUDI* NE. DAN ALLAH KI/KA BIYA KUDI KI/KA MALLAKI NA KI. DON GUDUN SHIGA HAKKOKIN MASU RUBUTAWAR DA MA WADANDA SUKA CIRE KUDI SUKA SAYA..._
___
*Waheedah* na tafe akan hanya tana mamakin maganganun Haj Hameedah. Su kuma haka Allah ya yi su da kaunar mutane? Kyautatawa da sanin ya kamata?
Ta sauke zuciya tana mai kambama dattako irin na Hajia Hameedah. A haka har ta karasa unguwar su
Kai tsaye ta wuce gidan Najan Isubu. Bakinta dauke da sallama ta shiga. Najan na share tsakar gidan.
Da sauri Waheedah ta karbi tsintsiyar bayan tayi sallama.
"Da kin basshi Waheedah.."
"A'a aunty zan karasa."
"Toh sannu da kokari. Allah ya saka da alkhairi..."
"Aamin Amin"
Waheedah ta tattare tsakar gidan tas ta zuba dattin a shara. Sannan ta isa ga wata jarka ta tsiyayi ruwa ta wanke hannuwan ta da wani guntun sabulu data gani a gefen buta.
"Zo ga abinci Waheedah.."
"Wallahi a koshe nake aunty..."
"Abar marmari ce... Shinkafa da wake. To bari dai na zuba miki ki kai wa Yayan ku da Najib... Ya ya jikin na su kuwa? Ina tason shiga idan na kintsa komai .."
"Tom aunty... Angode. Allah ya saka da alkhairi. Da sauki. Na baro su a gidah "
"Amin Aamin..To Alhamdulillah"
"Aunty daman Umman mu ce ta aikoni wajen ki..."
"Tohn Allah sa muji alkhairi Waheedah."
"Aamin ... Dama dazu ne da safe Marka ta zo da wasu samari su biyu. Na san su ma ..."
"Kwarai na ji zancen dazu a shagon Na'Ateeku. Fandau na fada. Kinsan uwar guntsi fetsi ce "
"Eh... Tohm shine wai Markan zata bada hayar dakin. Tace na tattare kayana."
"SubhanAllah.... Wallahi da naji suna zancen a shagon. Bata fadi wani daki bane. Da girman Allah na dauka dakin dake waje ne... Kai Marka batada kirki wallahi. Yanzu ya ake ciki...?"
Waheedan ta sheda mata komai ba abunda ta bari. Ta karkare da,
" Shine bayan na sanarwa Umman tace na gaya miki . Ko da akwai abubuwan da zaa tsitstsinta a sayar.. Tace dai na gaya miki. Dik abunda kika yanke yayi."
Najan Isubu ta sauke zuciya tana matsa hannuwa. Cikin zuciyar ta kuwa tattare yake da tunanin yadda zata bullowa lamarin. Saboda gudun sharrin Marka ..
"Shikenan Waheedah... Allah ya dafa mana, Aamin."
"Amin aunty "
"Dauki abincin kije... Zan biyo sahun ki insha Allah ... Allah ya dafa mana ya kawo mana mafita. Kije gani nan. Insha Allah."
"Tohm Aunty..."
Waheedah ta dauki kwanon abincin dake kamshin man kulli da albasa. Gefe daya kuma kamshin yajin tafarnuwa ne yake tashi.
Ta fice daga gidan bayan tawa Najan Isubun sallama.
Gidah ta nufa. Ta shiga bakin ta dauke da sallama.
Yaya Kamal na daga gefen dakin su a zaune ya tsakure. Yayinda Marka ke ta kai da kawowa a cikin dakin Umman tasu. Wanda ya zamana na waheedah a yanzu.
Ta gama fito da kwanuka da wani kwali babba da kayan su ke a ciki. Da sauri waheedan ta ajiye kwanon abincin agaban Kamal.
"Gashi nan ku ci Yaya .. Kai da Najib. "
Marka ta watsa mata wani banzan kallo tana mai nuna dakin da yatsanta daya.
"Shiga ki kwaso sauran tarikicen kayayyakin ku. Kin zo kin tsaya qerere a kai na saboda rashin girmamawa ga nagaba da ke. "
"Kiyi hakuri..." Ta fada a raunace. Kafin ta ajiye yar jakar ta a gaban Kamal ta shiga dakin da sauri.
Dan wulaakancin Marka baki daya ta hautsina dakin. Wasu ababen fashewar baki daya sun fashe a tsakiyar dakin. Sauran tsakin dafawar su da wani ragowar manja baki daya Marka ta antayar da su a dakin..
Waheedah ta karasa fitar da komai ahankali. Wata drawer dinsu ce da kayan su ke ciki ta kasa janyota. Gashi hatasan kiran Yayan su. Ganin ba lapia ce dashi ba.
Tanata kiciniya sai ga Najan Isubu ta shiga tanata rangajin rangada sallama .
"Ko bakwa ji ne inata salamu alaikum.?"
"Yo sallamar ce kikayi ta iya cikin ki...